Fassara

Monday, May 9, 2016

Kafafen Tumasanci da Yaɗa Bambaɗanci

09 Ga Mayu, 2016



B
abu kafar yaɗa labarai da mafi yawan talakawan Najeriya suka dogara da ita domin samun bayanai kamar rediyo wataƙila saboda araha wajen mallaka da kuma sauƙin sarrafawa. A gefe guda kuma babu kafar da ake jibgawa kowacce irin shara a Najeriya, musamman ma Arewa, kamar ita rediyon. Akwai tarin matasloli da suke damun sauran kafafen yaɗa labarai irin su talabijin, jaridu da kuma yanar gizo; amma kusan babu kafar da ta kai rediyon fuskantar matasaloli iri daban-daban.

A cikin manya da ƙananan gidajen rediyo kusan guda 150 ko sama da haka da muke dasu a ƙasarnan, sama da 50% mallakar gwamnatocin jihohi  ne da na Gwamnatin Tarayya. Misali, aƙalla kowacce jiha tana da gidan rediyo mallakarta guda ɗaya a zangon AM, wasu jihohin da dama suna da ƙarin tasha ɗaya ko sama da haka a zangon FM. Bayan haka, Gwamnatin Tarayya tana da gidajen rediyo ɗai-ɗai a kan zangon FM a kowacce jiha waɗanda ta buɗe a shekarar 2003 domin faɗaɗa shirye-shiryen da babban gidan rediyo na ƙasa yake gabatarwa daga Abuja zuwa dukkan sassan ƙasarnan. Duk wannan lissafi bai haɗa da gidajen rediyoyi da dama a Najeriya waɗanda suke yaɗa shirye-shiryensu a kan yanar gizo kaɗai ba.

Mallakar kafafen yaɗa labarai a ɓangaren gwamnati ko wasu sassanta ba wani sabon abu bane a duniya kuma ba wani abin damuwa bane. Hasalima wasu manya-manyan kafafen yaɗa labarai da ake taƙama dasu a duniya wajen shahara da ƙwarewa irinsu BBC, Muryar Amurka, da DW duk mallakar gwamnati ne. Abinda yake matsala shi ne idan masu riƙe da madafun iko suna yin amfani da waɗannan kafafen yaɗa labarai domin amfanin kansu da ‘yan korensu. Ba wai an ce kada waɗannan kafafen yaɗa labarai su tallata manufofi da aiyukan gwamnati ba, amma ya kamata su yi abin cikin hikima da ƙwarewa kuma su bayar da cikakkiyar dama ga masu yin adawa da manufofin gwamnatin domin su mayar da martani.

Kafafen yaɗa labarai, musamman gidajen rediyo mallakar gwamnatocin jihohi sun zama kafafen yi wa gwamnoni tumasanci da bambaɗanci. Mafi yawan shirye-shiryensu sun karkata wajen yabon gwamnatin da take mulki komai kuwa irin ta’asar da take aikatawa. Wani lokaci, waɗannan gidajen rediyo su kan gabatar da shirye-shirye masu muhimmanci da zasu ilmantar da kuma faɗakar da al’umma, to amma saboda wannan ɗabi’a tasu mai ban haushi, da yawa an haƙura da shirye-shiryen nasu baki ɗaya. Haka za a ci gaba da tafiya; ana ɗiban kuɗin al’umma wajen gudanar da irin waɗannan kafafen yaɗa labarai, a gefe ɗaya kuma shugaban ƙasa, gwamnoni da muƙarraban jam’iyya mai mulki suna amfani da waɗannan kafafe tamkar mallakarsu na ƙashin kansu?

Wani lokaci ina tattaunawa da wani ma’aikacin gidan rediyo mallakar gwamnati a wata jiha a Arewa maso yammacin Najeriya; sai yake bani labarin wani gwamna da aka taɓa yi wanda a lokacinsa ba a isa a sanar da ko da ɗaurin auren wani ɗan jam’iyyar adawa ko mai alaƙa da shi ta wannan kafa ba. A wasu lokutan da kansa gwamnan yake bugo wa manajan gidan rediyon waya yace a katse kowanne irin shiri da ake yi, a saka masa wata waƙarsa ta siyasa wadda yake so. Wannan kaɗan ne daga cikin irin yadda wasu gwamnonin suke yi wa irin waɗannan kafafen yaɗa labarai mulkin mallaka. A wasu lokutan kuma ba laifin gwamnan bane da kansa, muƙarrabansa ne da ‘yan jam’iyyarsa suke yin uwa da makarɓiya a gidajen rediyon, shi kuma gwamnan sai ya kasa hanasu saboda dalilai na siyasa. Wani lokaci kuma manajan gidan rediyon da gwamna ya naɗa ne yake mayar da gidan rediyon fagen bambaɗanci da tumasanci ga gwamna domin ya gyara miyarsa; shi kuma ƙila gwamnan dama haka yake so.

Kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati su ya kamata a ce sun zamo abin misali ta hanyar fin  kowa nagarta domin su ba kuɗi suke nema ba kamar na ‘yan kasuwa kuma an kafasu ne domin su bauta wa jama’a ba gwamna ko shugaban ƙasa ba. An ƙaddara cewa su mallakar jama’a ne kuma wasu kafafe ne na sadarwa, faɗakarwa, wayarwa da kuma tallata manufofin kishin ƙasa da ci gaba. To amma maimakon haka, sun zama kafafen farfaganda da ɗaukar bangare tare da goyon bayan son zuciya. Wannan ita tasa mafi yawancin jama’a suka ƙaurace musu domin sauraron na ‘yan kasuwa masu zaman kansu duk kuwa da cewar ba finsu ƙwararrun ma’aikata ko iya gabatar da shirye-shirye aka yi ba.

Kafafen yaɗa labarai na talabijin, suma haka gwamnatoci suka lalata al’amarinsu tare da sauke su daga bin ƙa’idojin aikin jarida inda ba abinda ake yi sai tallan masu mulki da kuma hana ‘yan adawa damar faɗar albarkacin baki. To amma, daɗinta ita talabijin ba ma kowa ne yake da ita ba kuma ba dukkan masu itan bane ma suke da isasshiyar wutar lantarkin da zasu dinga kallonta akai-akai ba. Su kuwa jaridu mallakar gwamnatoci, mafi yawancinsu sun durƙushe, gwamnatocin sun kasa riƙe su. Ita kuwa yanar gizo ta kowa ce, babu wani mai mulki da zai iya hana faɗar albarkacin baki a cikinta ko kuma yace sai abinda yake so shi mutane zasu karanta. Matsalar kawai ita ce, yanar gizo tana da matuƙar matsala domin ana yawan yaɗa ƙarya da labaran ƙanzon kurege ta wannan  kafa kuma ana yawan amfani da ita wajen ci wa  jama’a da masu mulki mutunci da yi musu ƙage a inda basu ji ba basu gani ba.

Kasancewar halin da kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati suka samu kansu, mutane da yawa sai suka ƙaurace musu, suka koma na ‘yan kasuwa. Idan bamu manta ba, har a shekarar 1999 babu gidan rediyo mallakar ‘yan kasuwa ko ɗaya da yake aiki ka’in da na’in a Arewacin Najeriya, sannan waɗanda suke a kudanci basu fi a ƙirge su ba. Yanzu irin waɗannan gidajen rediyo sun mamaye ko’ina amma har a yanzu haka akwai tsirarun jihohin da basu da gidan rediyo masu zaman kansu ko ɗaya, sai dai na gwamnati. Irin waɗannan jihohi suna fuskantar cikas sosai wajen faɗin albarkacin bakinsu. Matsalar a nan ita ce, su ‘yan kasuwa kuɗi suke nema domin sun zuba maƙudan kuɗaɗe wajen samun lasisi da kuma kafa injina. Bayan haka suna kashe maƙudan kuɗaɗe wajen samar wa da kansu wutar lantarki, biyan haraji da albashin ma’aikatansu. Wannan ce ta sa, mafi yawancinsu kuɗi sune abinda suka fi nema ido rufe. Sakamakon haka, sai ‘yan siyasa da sauran jama’a suka yi amfani da wannan dama wajen mayar da su gurin zubar da kowacce  irin shara suka ɗebo. A wasu lokutan, matuƙar kana da ‘yan kuɗinka a aljihu, sai kaje ka biya a barka kai ta faɗar irin sakarcin da kake so da sunan siyasa; mutane su yi ta faɗin ƙazantar bakinsu amma wai su kira shi da faɗin albarkacin baki. Waɗanda basu da ilimi ko ƙwarewar da ya kamata su yi magana a sauraresu, sai su shiga gidan rediyo mai zaman kansa su yi ta soki burutsu wai su ga masu ‘yanci, banza ta faɗi.

Lokacin da ministan yaɗa labarai da ci gaban al’adu na gwamnatin Shugaba Buhari, Alhaji Lai Mohammed ya kama aiki kimanin watanni shida da suka wuce, ya yi alƙawarin cewar Gwamnatin Tarayya zata yi wa kafafen yaɗa labaranta garanbawul domin su amfani dukkan ‘yan kasa ba wai waɗanda suke mulki ko ‘yan jam’iyya mai mulki kaɗai ba. Daga wancan lokaci zuwa yanzu, alamu sun nuna an ɗan soma samun canji kaɗan ba da yawa ba musamman a kafafe irinsu NTA, FRCN, NAN da dai sauransu. Ya kamata jihohi su bi sahu wajen kawo gyara ga kafafen yaɗa labarai. Yana da kyau masu mulki su fahimci cewar aikin da suka yi ko suka ƙi yi wa talakawa shi zai yi musu alƙalanci ba wai mallake kafafen yaɗa labarai ba. Kan mutane yanzu a waye yake; idan sun yi abu mai kyau ko mara kyau, za a samu kafar da za a faɗa, koda sun hana a faɗa a kafar gwamnati.

Yana da kyau, ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa, NUJ ta dinga yi wa ma’aikatanta masu aiki a irin waɗannan kafafen yaɗa labari na gwamnati bita ta musamman tare da fahimtar dasu cewar aikin jama’a suke yi ba na mai mulki ba kuma ‘yan siyasa basu da ikon tilasta musu  kauce wa dokokin aikin jarida don kawai suna masu mulki. Su nuna musu cewar, idan suka haɗa kansu, za su iya bin duka matakan da suka dace domin tsaftace aikinsu da ƙin yarda a lalata musu shi. NUJ ta fahimtar dasu irin zubewa da ƙimarsu da mutuncin aikinsu yake yi wajen  yi wa masu mulki bambaɗanci da tumasanci a rediyo da sunan yaɗa labarai ko aikin jarida.

Majalisun dokoki na jihohi da na tarayya, ya kamata su kalli wannan matsala  tare da duba yiwuwar yin dokokin da zasu hana gwamna ko shugaban ƙasa ikon naɗa ko tuɓe shugabannin gidajen yaɗa labarai mallakar gwamnati domin samar musu da ‘yancin kansu.