Fassara

Friday, October 23, 2015

Musulunci a Ibada; Kafirci a Mu’amala

23 Ga Oktoba, 2015

Daga: Amir Abdulazeez

W
ani babban kuskure da masu yawa daga cikin al’ummar Musulmi, musamman na ƙasar Hausa suke yi shine, na ɗauka da suke yi cewar Kalmar Shahda, Tsayar da Sallah, Azumtar Watan Ramadan, Bayar da Zakka ga mai dukiyar da ta kai nisabi da kuma zuwa Aikin Hajji ga mai iko, sune kaɗai Musulunci. Tabbas, waɗannan sune shika-shikan Musulunci, to amma akwai sauran abubuwa masu tarin yawa da matuƙar amfani, waɗanda rashin kiyayaesu zai iya kawo babbar alamar tambaya dangane da nagarta ko ingancin Musuluncin mutum komai yawan ibadarsa.

Akasarin Musulmai Hausawa, musamman na Najeriya, cikin sani ko rashin sani, sun raini wata fahimta da tunani a cikin ƙwaƙwalwarsu na cewar kyautata alaƙarsu da Allah (SWT) shine kaɗai abin buƙata a addinance, amma ba lallai sai sun kyautata alaƙa da bayinSa ba. Mafi yawan lokuta, mu kan manta cewa bayan haƙƙin Allah (SWT), akwai kuma haƙƙin bayinSa  a kanmu. Bayan haka kuma, abu ne mai sauƙi ka yi wa Allah (SWT) laifi ka tuba, tuba na gaskiya, kayi nadama kuma Ya yafe maka amma kuma ba zai yafe maka haƙƙin bawanSa ba har sai ka mayar masa da haƙƙinsa ko kuma ka nemi afuwarsa kuma ya yafe maka wannan laifi da ka yi masa.

Wani lokaci, na taɓa riskar mutane suna zaune ana hira, sai na shiga cikinsu na zauna. Ana zaune sai hirar wani mutum ta faɗo, nan sai kowa ya yi ta yabonsa yana shi masa albarka. Dukkan yabonsa da ake yi bai wuce a kan halayensa irinsu gaskiya, riƙon amana, kyakkyawar mu’amala da dai sauransu. Wato ba wai yabon bane laifi ko abin mamakin ba, a’a yadda aka dinga shauƙi da bege tare da nanatawa tamkar an yi maganar wani hali irin na Annabi ko Sahabi da kuma yadda suke ganin kamar samun irin wannan mutumin a duniya sai an tona. Ni na san mutumin da ake magana a kai, ba wai wasu halaye bane na daban gareshi, irin dai halayen da Addinin Musulunci ya tarbiyanci kowa  a kai ne.

Nan sai na shiga tunani mai zurfi kan yadda lalacewar al’amura suka mayar damu muke kallon mutanen kirki kamar wasu Mala’iku ba kamar ‘yan Adam irin mu ba. Wato lalacewar al’ummarmu a wannan zamani har ta kai ga cewar aikata abubuwa masu kyau irinsu gaskiya, cika alƙawari, riƙon amana da sauransu sun zama wani abin mamaki da al’ajabi? Wato yanzu idan kana da kyakkywan hali har ka zama wani daban, abin kwatance kuma abin mamaki. Ni da a zatona abubuwa irinsu sauƙin kai, girmama mutane da ganin mutuncinsu, faɗar gaskiya, tausayi; duk abubuwa ne da ya kamata a ce kowa ya dinga yi ba wai ‘yan tsirarun mutane ba. Kamata ya yi a ce ‘yan tsiraru ne a cikin mutane basa yi har a dinga mamakinsu ana kwatance da su saboda ƙarancinsu.

Masana binciken halayya da ɗabi’un ɗan Adam sun yi ittifaƙin cewar ‘yan Najeriya suna daga cikin mutane  da suka fi riƙo da addini. Sannan kuma a Duniyar Musulunci, an yarda cewar Hausawan Arewacin Najeriya suna daga cikin waɗanda suke ƙoƙarin yin ibada mai yawa. To amma kuma sai dai kash! Idan da za a auna, da sai a gano cewar babu waɗanda suke da miyagun halaye da gurɓataciyyar mu’amala kamar mu. Wannan ƙalubale ne ba ƙarami ba a kanmu domin kuwa duk wanda yake ibada domin neman yardar Allah (SWT), to alamun cewar ana karɓar ibadarsa shine a ga ba ya yawan aikata saɓo kuma ya na kyautata mu’amalarsa da bayin Allah. Karɓaɓɓiya kuma ingantaciyyar ibada bata cika haɗuwa guri guda da gurɓataccen hali ba. Idan kana ibada kuma bata hanaka mummunar mu’amala tsakaninka da jama’a ba, to ka binciki ibadar taka. Kodayake idan aka bibiya, mafi yawa daga cikin al’umma ba ma don Allah (SWT) suke yin ibadar ba. Wasu dai suna Sallah da Azumi ne kawai don sun samu kansu a cikin Musulunci kuma don kada su ƙi yi a kafurta su. Shi kuwa Aikin Hajji ma an mayar da shi wani abin kece raini da gasar arziƙi. Tir!! Ita kuwa Zakka da yake abu ce da ta shafi fitar dukiya-abar da Ɗan Adam yake tsananin so da ƙauna-babu ma wanda suka damu da ita sosai. An mayar da ita saniyar ware a cikin shika-shikan Musuluncin. Maimakon in ma gasa da kece rainin arziƙin ake so a yi, ai a Zakka ya kamata a yi ba wai a Aikin Hajji ba. Wani Malami ya na bayar da labari cewar ya ɗauki shekaru ana zuwa wajensa neman fatawoyi amma sai ya yi wata da watanni babu wanda yazo wajensa neman fatawa a kan yadda ake bayar da Zakka; amma neman fatawoyi a kan yadda za a ƙara aure kuwa ,babu magana.

Gurɓacewar mu’amalarmu da yanayin zamantakewarmu a yanzu ta kai ta kawo muna zaune sai kace dabbobi. Idan jifa ya wuce kanka, to ya faɗa kan kowa. Ba ka gudun ka yi wa mutane abinda kai baka so a yi maka. Abinda in kai aka yi wa, zai maka ciwo, ka ji zafi, sai kuma ka dinga yi wa wasu. Muna zaune kullum neman juna muke da sharri ba alkhairi ba. Kowa so yake kowa ya aikata kuskure ya yi ta faman yamaɗiɗi, amma idan an yi alkhairi sai ka ji gum. Kowa tsoron yin harkar kuɗi yake yi da  kowa. Wannan masifa har ina? A haka muke so mu ci gaba da zama muna ƙuntatawa juna zaman rayuwa?

A cikin jama’a, idan ana zaune, har ƙagara ake yi mutum ɗaya ya tashi a saka faifansa, a fara zaginsa ana cin namansa. Ƙarya kuwa ta zama ita ce mafi akasarin zancenmu. Duk maganar da aka faɗa, kowa zai karɓe ta ne cikin shakku da zargi. Idan an faɗa maka farashin abu a kasuwa, gani kake cutar ka za a yi. Wani lokacin ma har ka saya ka taho gida, za kai ta jin a ranka cewar cutar ka aka yi. Babu aminci a tsakaninmu. Cin amana a kasuwanci, zamantakewa, aiki, maƙotaka, abota, duk ba wani baƙon abu ba ne a cikin mu’amalar Hausawa Musulmi.

Tambayar da ya kamata mu yi wa kanmu ita ce, to ina Musuluncin yake a tattare da mu? Zaman mu Musulmai, wane gata hakan ya zamo wa zamantakewarmu? Mun ma fahimci Musuluncin kuwa? Da haka muke so mu tallata Musuluncin ko kuwa da haka muke so al’ummar Musulumin ta ci gaba? Shin ma Allah (SWT) yana karɓar ibadar da muke yi bisa irin waɗannan munanan halaye namu? Shin waɗannan masifun zamani da suke damunmu, basu da alaƙa da gurɓataciyyar mu’amalarmu?

Turawan Yamma waɗanda ba Musulmi ba kuma ake yi wa kallon fanɗararru sun riƙi koyarwar Addinin Musulunci hannu bibiyu a cikin mu’amalarsu da zamantakewarsu, kuma ga shi nan ƙasashensu sai ci gaba suke yi, mu kuwa gamu nan kullum sai ci baya muke yi, duk kuwa da iƙirarin addinin da muke yi a baki. Turawa sun riƙe adalci, gaskiya, amana, alƙawari, manufa, kyautatawa, ƙa’ida da sauransu. A mu’amalarsu babu cuta babu cutarwa. Mai yiwuwa sakamakon wannan kyawawan ɗabi’u nasu, Allah (SWT) Yake basu a nan duniya.

Kullum Masallatan Juma’a da guraren ibadarmu sai ƙara cika suke maƙil, amma kullum masu gaskiya da riƙon amana sai ƙara ƙaranci suke yi. Kullum yawan alhazai da maniyyata daga Arewacin Najeriya sai ƙara ƙaruwa suke, amma kuma kullum rashin adalci da rashin alƙawari sai ƙaruwa suke a cikin mu. Musuluncinnan fa, Allah (SWT) Ya kallafa mana shi don ya zamar mana gata, alkhairi da salama a tsakanimu. Bautarmu ba zata amfani Ubangiji da komai ba. Idan bamu yi amfani da Musuluncin mun taimaka tare da sauƙaƙa wa junan mu a rauywa ba, bai kamata a ce mun munana ba. Sai ka ga mutum, duk inda mai ƙoƙarin ibada yake ya kai, amma idan ka yi harka da shi, sai ya cutar da kai. Kaico! Da ka taɓa mutane, sai su ce sun fi kowa son Annabi, amma kuma a halayyarsu babu irin ta Annabin. Annabi Muhammad (SAW) shi ne mutumin da yafi kowa iya mu’amala a tarihin duniya, kuma shi Musulmi ne, da shi aka ce Musulmi su yi koyi. Ina koyin yake?

Ya kamata kowa ya yi wa kansa faɗa kuma ya tambayi kansa shin shi Musulmi ne a ibada kaɗai ko kuwa har da zamantakewa? Ta yaya zai yi ya kyautata Musuluncinsa a ibada da kuma a mu’amala baki ɗaya? Ya zai yi ya zama nagartaccen Musulmi wanda sauran Musulmai zasu kuɓuta daga sharrinsa, ba wai Musulmiya ba?

Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez  

No comments:

Post a Comment