30 Ga Satumba, 2015
Daga: Amir Abdulazeez
F
|
aruwar haɗarurruka masu kawo asarar rayuka da jin raunuka a
aikin Hajji ba wani baƙon abu ba ne,
amma tun bayan da adadin yawan mutanen
duniya ya haura biliyan 3 tsakanin shekarun 1960 zuwa 1970, sai ya kasance
faruwar irin waɗannan haɗarurruka ta ƙara yawaita kuma a duk lokacin da suka
faru a kan yi asarar rayuka masu yawa tare da jikkatar alhazai da dama. Yawan
mutanen duniya na ƙaruwa, yawan Musulmi na ƙaruwa sannan kuma yawan mahajatta
na ƙaruwa. Yanzu haka yawan Musulman duniya ya haura a biliyan 1.6 kuma a
dukkan shekara kusan Musulmai miliyan 2 zuwa 3 ne suke zuwa Saudiyya domin
sauke faralli.
Daga shekarar 1975 zuwa
shekarar 2015 da muke ciki, alƙaluman hukumomin Saudi Arabia sun nuna cewar sama
da mutane 4,841 ne suka rasa ransu a dalilin haɗarurruka daban-daban, yayin da
wasu dubannai suka samu raunuka. Duk waɗannan alƙaluma basu shafi alhazai waɗanda
suke mutuwa ɗai ɗai ko nan da can a dalilin wata rashin lafiya ba. Mafi yawan waɗannan
haɗarurruka dai basa wuce turmutsutsu a yayin jifan sheɗan. A cikin muhimman haɗarurrukan
da suka wakana a aiyukan aikin Hajji a tsawon shekaru 40, 8 ne daga ciki kawai basu
da alaƙa da turmutsustsu domin sun faru
ne a dalilin gobara, ruguzau, zanga-zanga da dai sauransu.
Haɗarurrukan Aikin Hajji a Shekaru 40
Duk da cewar abu ne mai wahala
a iya tantance tarihin tun lokacin da irin waɗannan muhimman haɗarruka masu
tasiri suka fara faruwa a aikin Hajji, to amma abu ne sananne cewar a duk
lokacin da a kan yi wani abu wanda yake tara dubunnai ko miliyoyin jama’a, to
dole ne baza a fitar da tsammanni yiwuwar faruwar haɗari, tsautsayi ko
jarrabawa daga Ubangiji ba. A mafi yawan lokuta, rundunar dubunnan mahajjata
masu tattaki daga wani waje zuwa wani wajen ta kan kawo turmutsutsu wanda ya kan
kawo asarar rayuka da jikkata mutane da dama.
A
ranar 2 ga watan Julin 1990,
turmutsutsu a hanyar wucewar alhazai ta Ma’aisim
wacce take fita daga Makkah zuwa Mina da kuma
filin Arafah
ya yi sanadiyyar mutuwar alhazai 1,426, da yawa daga cikinsu ‘yan ƙasashen Malaysia,
Indonesia da Pakistan. Wannan shi ne haɗari
mafi muni a cikin shekaru 40. Turmutsutsu ya yi sanadiyyar rasa alhazai da yawa
da kuma jikkkata wasu da dama a shekarun 1994, 1998, 2001, 2003, 2004, 2006 da
kuma 2015.
A ranar 15 ga Afrilun,1997, gobara a tantunan
mahajjata, ta yi sanadiyyar mutuwar alhazai 343 da raunata 1,500. Yanzu sababbin
tantuna na zamani da ake yi wa alhazai amfani dasu, an sana’antasu ta yadda wuta
ba ta iya ƙona su. Haka kuma a shekarun 1975 da 2011, gobara ta kawo asarar
rayuka da jikkata wasu da dama
a aikin hajji.
A ranar 11 ga Julin, 1991, haɗarin
jirgin saman Nigerian Airways mai
lamba 2120 wanda ya taso daga Jeddah zuwa Sokoto, ya yi sanadiyyar mutuwar
dukkan alhazai 247 ‘yan Najeriya da kuma ma’aikatan jirgin 14. Jirgin ya faɗi
ne jim kaɗan bayan tashi daga Filin Jirgin Saman Sarki Abdulaziz. Haka ma haɗarurrukan
jiragen sama sun afku a hanyar zuwa ko dawowa daga aikin hajji a tsakanin ƙasashen
duniya daban-daban a shekarun 1973, 1974, 1978, 1979 da 1980 inda kusan dukkan
alhazan da abun ya shafa suka rasa rayukansu.
Rugujewar otal ɗin Al-Gaza
a kusa da Harami
a 2006 ya yi
sanadiyyar mutuwar mutane 76 da raunata 64. Sannan faɗowar ƙugiya a cikin Harami
a ranar 11 ga Satumbar 2015 ya kashe mutane 118 tare da raunata 394.
An rasa alhazai da yawa
sakamakon ɓarkewar cututtuka da annoba a shekarun da suka gabata. Kafin fara
aiyukan Hajjin 2006, alhazai 243 ne suka rasu daga ƙasashe daban-daban
sakamakon cututtuka masu alaƙa da zuciya, gajiya, tsufa da kuma rashin lafiyar
da aka zo da ita tun daga gida. A shekarun baya cututtuka irinsu zazzaɓi,
kwalara, polio, mura da ƙyanda sun yi sanadiyyar rasuwar wasu tsirarun alhazai.
Jifan Sheɗan (rami-aljamarat)
Jifan sheɗan wanda a ke gudanar
da shi a birnin
Mina, yana daga cikin rukunan
aiyukan Hajji mafi haɗari a shekarun baya
saboda yawan jama’a, musamman a lokacin da mutanen suke
tsallaka gadar jamarat wacce take
sada su zuwa ga inda za su yi jifan. Mafi yawan cinkoso, turmutsutsu da asarar
rayuka ya kan auku ne a wajen jifan sheɗan.
Alhazai a Jamarat a shekarar 2006 |
Bayan turmutsutsun shekarar
2004, Gwamnatin Saudiyya ta yi aikace-aikace masu yawa a wajen gadar jamarat. An ƙara yawan hanyoyi da wajen
tsallakawar mutane da kuma hanyoyin fita na ko-ta-kwana.
Bayan haka kuma an musanya manyan durakun nan guda uku masu wakiltar Sheɗan ɗin
da wani shafaffen bango babba na kankare domin gujewa turereniyar da alahazai
suke yi a ƙoƙarin samun guri saitin waɗannan duraku a shekarun baya.
Bayan wani turmutsutsun a shekarar
2006, Gwamnatin Saudiya ta ƙara yin wasu rushe-rushe, sauye-sauye, faɗaɗe- faɗaɗe
da gyare-gyare a jamarat domin sauƙaƙa
wa alhazai yayin jifan sheɗan. Sannan kuma an ɓullo da tsaruka domin hana
cinkoso da kuma shiga haɗari. To amma duk da wannan matakai, an sake samun
turmutsutsu a wannan waje a shekarar 2015 da muke ciki.
Haɗarurrukan Aikin Hajjin Bana na Shekarar 2015
A baya bayannan, in banda
shekarar 1990, babu wata shekara da aka samu rashin rayukan alhazai kamar a
wannan shekara da muke ciki. Tun da farko dai, kamar kowacce shekara, an samu
mutuwar alhazai ɗaiɗaiku daga ƙasashe daban-daban sakamakon dalilai na rsahin
lafiya da kuma ajali. Bayan haka kuma faɗowar ƙugiya a cikin Masallacin Harami
a ranar 11 ga Satumbar 2015 ya kashe mutane 118 tare da raunata 394. Tuni dai
Gwamnatin Saudiyya ta tabbatar da biyan diyyar Riyal miliyan guda guda ga
iyalan mamata da kuma waɗanda suka samu nakasata din-din-din a haɗarin wannan ƙugiya.
Sannan kuma waɗanda suka samu raunuka aa basu Riyal 500,000. Bayan haka an yi
alƙawarin kujerun aikin Hajjin baɗi biyu ga iyalan kowanne mamaci tare da
sanyasu a cikin baƙin Sarkin Makka na musamman.
Faɗowar ƙugiya a cikin Masallacin Harami a ranar 11 ga Satumbar 2015 |
Ranar 24 ga Satumbar 2015, hukumomin Saudi Arabia sun
bayyana mutuwar sama
da alhazai 769 da raunatar sama da 860 a wajen jifan sheɗan. A baya bayannan masu sanya idanu daga ƙasashe
daban-daban sun fitar da sanarwar cewar adadin waɗanda suka rasu daga wannan
turmutsutsu kuma aka ga gawarwakinsu ya kai 1,090 yayin da kuma har yanzu ake
neman alhazai da dama waɗanda ba a gani ba. Wannan haɗari ya faru ne yayin da
rukunin wasu alhazai masu dawowa izuwa masaukinsu bayan sun yi jifa, suka biyo
hanyar tafiya a maimakon su bi ta hanyar da aka ware domin masu komowa inda
suka haɗu kuma suka yamutsa da alhazai masu tafiya izuwa jamrat.
Asarar Rayukan Alhazan Najeriya a Hajjin 2015
Duk da dai cewar har yanzu ba a
gama tattara yawan alhazan Najeriya da suka rasu ko suka ji ciwo a wannan aikin
Hajji na bana ba, amma a ranar Juma’ar da ta gabata shugaban hukumar alhazai ta
ƙasa, Alhaji Abdullahi Mukhtar ya bayyana adadin alhazan Najeriya da suka mutu
a wajen turmutsutsun jamrat kaɗai a
matsayin guda 74 yayin da sama da 71 suka samu raunuka yayin da yawan alhazan
da ba a gani ba ya kai 244. Alhazan da suka rasu sun fito daga jihohin Bauchi,
Borno, Cross-Rivers, Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi da Nassarawa. Waɗanda suka ɓace
kuma sun fito daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Ekiti, Abuja, Gombe, Kaduna,
Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Nassarawa, Ondo, Niger, Plateau, Rivers, Sokoto,
Taraba, Yobe da Zamfara. Wannan ya biyo bayan alhazai 6 da suka rasu yayin da 4
suka ɓata a faɗowar ƙugiyar cikin Masallacin Harami yayin kuma da wasu ƙarin 20
suka mutu tun da farko bisa dalilai na rashin lafiya ko kuma ajali.
Yanzu haka dai Shugaban ƙasa
Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa da ta
gaggauta bin ba’asin duk wani alhajin Najeriya da ya rasu, ya ji rauni ko kuma
ya ɓata domin sanar da ‘yan uwansa halin da yake ciki.
Yawan Alhazan Duniya a duk shekara
Tun daga lokacin da jiragen
sama suka zama ruwan dare a duniya, kullum yawan maniyyata aikin Hajji yake ƙaruwa
daga ƙasashe daban-daban. Wannan ya biyo bayan samuwar sauƙin sufuri saɓanin a
shekaru masu yawa a baya da ake zuwa a a motoci, jiragen ruwa, a kan dabbobi,
wasu ma har a ƙasa.
A cikin shekaru goma da suka
gabata, ƙasar Saudiyya tace ta karɓi baƙuncin yawan alhazai miliyan 25 sannan
kuma kamfanin dillacin labarai na Reuters
ya rawaito cewar a cikin waɗannan shekaru goma, shekarar 2012 ita ta fi kowacce
shekara yawan alhazai da adadin mahajatta miliyan 3.16 yayin da shekarar 2013
ta fi kowacce ƙarancin mahajatta da alhazai miliyan 1.98. A mafi yawan shekaru,
alhazan ƙasar Indonesia su kan fin na ko’ina yawa inda suke kasancewa kimanin
20% na yawan alhazan da ba ‘yan ƙasar Saudiyya ba a kowanne aikin Hajji.
Aikin Hajji a 1960 |
Tasirin Rashin Jituwar ƙasashen Saudi Arabia da Iran ga Aikin Hajji
Babu shakka, dukkan mai nazari
a kan al’amuran yau da kullum, zai ga cewar akwai rashin jituwa a tsakanin ƙasar
Saudi Arabia da kuma ƙasar Iran. Wannan rashin jituwa kuwa tana nema ta ci
gaba da kawo matsaloli a a
cikin aiyukan Hajji. Yayin da ƙasar Saudiyya take zargin alhazan Iran da ɓullo
da matsaloli da gangan domin kawo cikas ga aikin Hajji, ita kuwa Iran ta na
zargin Saudia Arabia da gazawa wajen samar da cikakken tsaro a aikin Hajji.
A ranar 31 ga Julin 1987,
mutane 400 ne suka mutu yayin da dubannai suka jikkata a lokacin da jami’an
tsaron Saudiyya suka yi arangama da wasu mahajjatan Iran masu zanga-zanga. Ko
shakka babu wannan abu ne mara daɗi wanda za a iya gujewa afkuwarsa. Ya kamata ƙasashen
biyu su yi ƙoƙari su samu daidaito a tsakaninsu
ta yadda saɓani da rashin jituwarsu a siyasance ba zai dinga shafar aikin Hajji
ba.
Ko a wannan iftila’in da ya
faru na Hajjin bana, an samu taƙaddama tsakanin Saudia da Iran a kan silar
afkuwar matsalar da kuma adadin alhazan da suka mutu. Ita dai Iran ta zargi
Saudia da ƙin bayyana ainihin adadin yawan waɗanda suka rasu inda take ganin
yawansu ya haura a 4,000, kodayake ba ta bayar da wata hujja gamsasshiya ba a
kan wannan adadi. Ita dai Iran, ita ce ƙasar da ta fi kowacce ƙasa rasa rayukan
alhazai a Hajjin wannan shekara inda sama da mahajjatanta 400 ne suka rasu.
Ta Yaya Za a Kori Gaba?
Ko shakka babu, mahukuntan ƙasar Saudiyya suna
iya bakin ƙoƙarin su domin hana afkuwar haɗurra a yayin aikin Hajji, to amma
duk da wannan ƙoƙari har yanzu idan tsautsayi ya gifta a kan samu
asarar ɗumbin rayuka da jikkatar jama’a. Ya kamata su ƙara ƙoƙari a kan ƙoƙari, kada su gajiya. Babu wani abu
da za a iya
yi wanda ya wuce rigakafi. Ya kamata Mahukuntan Saudiyya kuma su gudanar da cikakken bincike dangane da zargin wariyar launin fata da nuna fifiko ga fararen fata da ake zargin jami'anta suna yi wa alhazai.
Idan muka kalli mafi yawan haɗarurraka
kuma sai muga cewar masu alaƙa da cinkoso ne. Mataki na farko da ya kamata a a ɗauka
shi na a duba yiwuwar taƙaita yawan mahajjatan da suke fitowa daga kowacce ƙasa
a duk shekara. A duba, a tantance a gani, duk wanda ya taɓa zuwa aikin Hajji
sau biyu ko sau uku, to a dakatar da shi daga zuwa aikin sai bayan wasu shekaru
domin sauƙaƙa cinkoso. Maimakon mahajatta miliyan 2 zuwa 3 da ƙasar Saudiyya ta
ke karɓa kowacce shekara, a
rage su zuwa miliyan 1 ko 1.5. wannan zai kawo sauƙin cinkoso ƙwarai da gaske.
Sannan kuma su mahajattan su kansu,
su ƙara zage damtse wajen gujewa matakai da zasu kawo cikas. Kowacce ƙasa ta
dinga yin bita tare da ilmantar da alhazai ba wai kawai yadda za su yi ibadar
Hajji ba kaɗai, har da yadda za su gujewa haɗurra da kuma matakan da zasu ɗauka
na gaggawa idan haɗarin ya auku.
Bayan haka, ƙasashen Musulmi su
ɗauka cewar samun nasarar aikin Hajji ya rataya a wuyayensu ne baki ɗaya ba wai
a wuyan ƙasar Saudiyya kawai ba. Ita ma Saudi Arabiar, a fahimtar da ita hakan.
A taru a samar da wani kwamiti mai wakilcin dukkan ƙasashe domin gudu tare a
tsira tare. Kada a ce za a taƙaita ikon Saudiyya da hukumominta, wajen tsarin
aikin Hajji, amma ya zama sauran ƙasashe su zamo masu ruwa da tsaki wajen
tsare-tsaren cikin fahimta da manufa mai kyau.
Allah Ubangiji Ya karɓi shahadar
waɗanda suka rasu, marasa lafiya kuma, Allah Ya basu lafiya.
©Wannan rubutu mallakar Mujallar
Mikiya ne, 2015. A nemi izini kafin sarrafa shi.
A KULA: An
ciro mafi yawan bayanan dake cikin wannan sharhi daga shafin Wikipedia, daga
kamfanin dillacin labaran ƙasar Faransa na AFP, wallafe-wallafen hukumomin kula
da aikin Hajji na ƙasar Saudi Arabia, kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen
Najeriya da kuma ta wasu hanyoyi masu yawa wanda yawansu ba zai bayar da dama a
bayyanasu ba.
Shafin
Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez
No comments:
Post a Comment