Fassara

Wednesday, January 6, 2016

Shekaru 50 Bayan Sardauna: Ko Mazan Yau Zasu Yi Kamar na Jiya?

4 Ga Janairu, 2016



S
hekaru hamsin bayan juyin mulki na farko a Najeriya wanda ya yi sanadiyyar kashe Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto da Sir Abubakar Tafawa-Balewa, har yanzu waɗannan mutane sune abin misali a Arewa, Najeriya da ma wasu sassan Afrika baki ɗaya. Shekaru hamsin da kwanta damarsu, har yanzu kusan an kasa cike giɓin da suka tafi suka bari, musamman ma ta ɓangaren Sardauna. Dama-dama ma Tafawa-Balewa, an samu wasu gwarazan shugabannin a matakin ƙasa, irinsu Marigayi Murtala Ramat Muhammad da suka kwatanta yin jagoranci bisa jajircewa da adalci kamar irin nasa, amma har yanzu Arewacin Najeriya ta kasa samun wani shugaba kamar Sardauna.

Shin nagartar Sardauna ce ta yi yawan da ba za a iya mai da kamarsa ba ko kuwa lalacewar shugabannin da suka biyo bayansa ne ta kai aka kasa samun magajinsa, ko kuma dalilai biyun ne a haɗe? Ko kuwa a’a, zamani da tsarin da muke ciki a yanzu ne suka canza kwata-kwata daga irin na lokacin su Sardaunan ta yadda zai yi wahala a samu wani ya iya yin irin tasirin da Sardauna ya yi ga mutanen Arewacin Najeriya? Idan muka duba, zamu ga cewar ba wai a Arewacin Najeriya ba, har a sauran sassan ƙasar ma, da yawa suna kukan cewar an kasa maye gurbin shugabannin da suka wuce. Shin an mayar da gurbin Cif Obafemi Awolowo a yankin Kudu maso Yamma da kuma Nnamdi Azikwe a yankin Kudu maso Gabas?

Akwai lokutan da a kan samu wasu shugabanni su kafa tarihin da kusan babu wanda ake ganin zai iya zuwa ya sha gabansu a tarihin al’ummarsu, misalin irin waɗannan mutane sun haɗa da Nelson Mandela na Africa ta Kudu, Kamal Ataturk na Turkey, Mao Zedong na China, Mahatma Gandhi na India, Kwame Nkurumah na Ghana, Julius Nyerere na Tanzania, Thomas Sankara na Burkina Faso, Jamal Abdulnasir Na Masar, Patrice Lumumba na Congo da dai sauransu. A baya-bayannan akwai Lee Kuan Yew na Singapore, Hugo Chaves na Venezuela, Mikael Gorbachaev na Russia da makamantansu. Duk da cewar wasu shugabannin su kan kafa tarihi na din-din-din sakamakon kasancewar sune sahun farko tun a lokacin da ƙasashensu suke tasowa, kuma tsarin da suka bi wajen kafa wannan tarihi yanzu babu shi; misali, yawancinsu sun yi gwagwarmayar kafa ƙasashensu, yaƙin neman ‘yancin kai daga zalunci ko mulkin mallaka, jagorantar wani juyin juya hali ko kuma yaƙin ƙwato ƙasar daga wani mawuyacin hali wanda yanzu kusan duk babu irin waɗannan abubuwa. To amma,  a kan samu wasu nagartattu mutane su biyo bayansu kuma su kamanta irin nasu ƙoƙarin, wani lokacin ma har su kere su. Misali, a ƙasar Ghana, bayan Kwame Nkurumah, an samu Jerry Rawlings wanda ake wa kallon ya bar tarihi mai kyau.  A ƙasar amurka, shekaru masu yawa bayan kashe shugaba abin alfahari Abraham Lincoln wanda ya shiga tarihi, an samu John F. Kennedy wanda shi ma ana ganin an kashe shi ne a tsaka da lokacin da yake kafa tarihi ta hanyar canza Amurka.

A nan Arewacin Najeriya, su waye ake ganin sun kwatanta kamar Sardauna, Tafawa Balewa da Malam Aminu Kano? Akwai dalilai da yawa da suka taru suka bai wa Sardauna wannan kyakkyawan mazauni da yake da shi a tarihin Arewa da Najeriya baki ɗaya. Na farko dai yana daga cikin sanannun masu ilimin zamani na sahun farko a Arewa kuma yana daga cikin waɗanda suka yi gwagwarmayar samo ‘yancin kan ƙasa da kafa siyasu na wancan lokaci. Bayan haka, ya zamo Pirimiyan yankin Arewacin Najeriya gabaɗaya, yankin da yafi kowanne yanki girma da yawan ƙabilu. A wancan lokaci, idan aka haɗa yankunan Yamma, Gabas da kuma Yamma maso Tsakiya da suke a Kudancin Najeriya, duk basu kai girman ƙasa, yawan jama’a da yawan ƙabilun Arewa ba. Bayan haka, Sardauna ya samu nasara ƙwarai da gaske wajen haɗa kan kusan dukkan jama’ar Arewa wajen zama tsintsiya-maɗaurinki-ɗaya, duk kuwa da bambance-bambancen ƙabilu da addini. Banda haka, Sardauna ya gina mutane da yawa daga ko’ina a Arewa, ya ɗaga su a duniya kuma ya jawosu jikinsa sannan kuma alherinsa ya watsu kusan ko’ina ba tare da ya dunƙule shi a waje ɗaya irin yadda shugabannin yanzu suke yi ba. Banda haka, Sardauna wanda dama basarake ne, yana da ƙarfin faɗa-a-ji da tasiri mai yawa a gwamnatin tsakiya ta wancan lokaci wacce take ƙarƙashin Sir Abubakar Tafawa-Balewa, kasancewar jam’iyyarsu ta Mutan Arewa wato NPC, ita ce take da rinjaye a wancan lokaci.

Wani abu da ya ƙara jaddada matsayin Sardauna a cikin tarihi shi ne mutuwarsa a yayin da yake tsaka da bauta wa jama’arsa. Wannan ita tasa shi ya zamo gwarzo na din-din-din. Idan muka bibiyi tarihin duniya, zamu ga mafi yawancin ‘yan gwagwarmaya da jajirtatattun  shugabannin da suka tsaya a kan gaskiya duk kashe su ake. A wancan lokacin, sojoji masu juyin mulkin shekarar 1966 sun kashe Sardauna da Tafawa-Balewa amma ba tare da sun kashe wasu daga cikin takwarorin siyasarsu na kudu ba, musamman ma yankin Inyamurai; duk kuwa da cewa suma suna cikin hamshaƙan masu riƙe da madafun iko a siyasance na wannan jamhuriya ta farko. Wannan, ita tasa har gobe ake yi wa wannan juyin mulki kallon wanda aka yi shi da manufa ta ƙabilanci da ɓangaranci, kodayake waɗanda suka shirya juyin mulkin sun sha musanta hakan tare da nacewa a kan cewa sun yi ne don kishin ƙasa. Abubuwan da suka biyo bayan juyin mulki na farko da kuma na biyu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaba Aguiyi Ironsi watanni shida a tsakani su suka haddasa yaƙin basasar 1967 da ya yi sanadiyyar asarar ɗumbin rayuka da dukiya tare da taɓarɓarewa da lalacewar alaƙa da dangantaka a tsakanin ‘yan Najeriya. Tun daga wannan lokaci zuwa yanzu, har yanzu Najeriya ta kasa hawa kan turbar haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa. Ko shakka babu, da ba a yi juyin mulkin farko ba, da yanzu ba haka Najeriya take ba.

Mai yiwuwa masu juyin mulkin Janairun 1966 sun ɗauka cewar kisan da suka yi wa Sardauna da Tafawa Balewa tamkar sun tozarta su Sardaunan ne, amma basu san cewar sun share musu fagen shiga tarihi bane. Domin lokutan da suka biyo bayan kashe sun, duk lokuta ne kusan na rikici da lalcewar al’amura waɗanda garama a ce basu riskesu ba. Cif Awolowo ya rayu kusan shekaru 20 bayan kashe Sardauna kuma sau biyu yana takarar shugaban ƙasa tare da Shagari amma ba ya samun nasara. Dakta Nnamdi Azikwe ya rayu shekaru 30 bayan kashe su Sardauna kuma shima ya jarraba zama shugaban ƙasa amma abin ya ci tura kuma tun yana da rai ma sai da Ojukwu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alex Ekweme suka dusashe farin jininsa da tasirinsa a tsakanin al'ummarsa ta Igbo a lokuta daban-daban. Su Sardauna, Allah bai rayasu sun kai wani zamani da za a dinga labarin wani basu ba. Wannan ce tasa har gobe ake labarinsu.

Daga Arewacin Najeriya, bayan Sardauna da Tafawa-Balewa, an samu wasu nagartattun mutane waɗanda suka shahara duk da cewar basu kai kamar su Sardaunan ba. Akwai Malam Aminu Kano, Hassan Usman Katsina, Murtala Ramat Muhammad da Janar Muhammadu Buhari. Labarin salon siyasa, hikima, ƙaunar talakawa da iya mu’amala irin ta Malam Aminu Kano, babu inda bai game ba a faɗin Najeriya. Yunƙurin kawo gyara da gaggawa, tsayuwar daka da jajircewa, rashin amincewa da wargi ko rashin gaskiya irin na Murtala Muhammad, babu wanda bai ji labarinsu ba. Masana tarihi su kan kwatanta watanni shidan da ya yi yana mulki a mastayin masu matuƙar amfani da tasiri ga Najeriya. Mutuwarsa ta girgiza kowa ba ma a Nejeriya kawai ba, har a faɗin Afrika baki ɗaya. Yaƙi da zamba, cin hanci, rashawa da cin amanar ƙasa; ƙoƙarin kawo tsarin ɗa’a da martaba gwamnati da kuma farfaɗo da tattalin arziƙi irin na Janar Buhari a 1984 sun sa kowa shiga taitayinsa. Shigarsa siyasa a 2002 da kuma rawar da ya taka a cikin ta, ta sanya shi zamowa ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da ya fi kowa yawan magoya baya talakawa zalla a tarihin Africa. An yi ittifaƙin cewar banda  Nelson Mandela, da wahala a samu mutum ɗaya tilo da ya kai Buhari farin jini a tarihin siyasar Africa.

A wannan zamanin da muke ciki, mafi yawan shugabanni a Arewacin Najeriya a dukkan matakai, basu damu da kafa wani tarihi ba. Abin da suka fi damuwa dasu sune tsananin kwaɗayin mulki, fafutukar samun muƙami ko ta halin ƙaƙa, tara ɗumbin dukiya ta hanyar sata da zamba, murƙushe ‘yan adawa, bautar da talakawa, kewaye kansu da ‘yan bani-na-iya da bambaɗanci, haɗa ƙarya da gaskiya ba kunya ba tsoron Allah, da kuma ƙaƙaba ‘ya’yansu da ‘yan korensu a kan muƙamai na siyasa. Wannan shine halin da muka samu kanmu.  A wannan halin, ta yaya za a taɓa samun magadan Sardauna, Tafawa-Balewa, Aminu Kano, Murtala Muhammad da Janar Buhari? A wannan halin, ta yaya Najeriya da Arewa zasu gyaru? A wannan halin, ta yaya talakawa zasu shaƙi iskar ‘yanci da fahimtar makomarsu da ta ƙasarsu? A wannan halin, ta yaya shugabanni zasu samu irin girmamawa da karramawar da su Sardauna suka samu? A wannan halin, wane mai kyakkyawan hali ne zai yi kwaɗayin shiga a dama da shi a harkar gwamnati?

Allah sarki, bayan tafiyar Sardauna, Arewa ta zama koma baya; Najeriya ta zama abin tausayi; mulki ya koma wasan yara; talakawa da mabiya sun koma kwaɗayayyu masu tarewa a gindin masu muƙamai a maimakon masu kishin ƙasa da neman ci gaba. Wasu daga cikin irin shugabannin yanzu, nagartarsu ba ta kai a basu koda masinja ba a lokacin su Sardauna, yau sune gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisu, ciyamomi, kansiloli, kai har ma da shugabannin ƙasa. Waɗanda burinsu su saka riga su kece raini, babu talakawa kwata-kwata a gabansu, yau sune masu faɗa-a-ji a ƙasarmu Najeriya. Yau an wayi gari, an fi buƙatar a yi amfani da sunan Sardauna fiye da a yi koyi da shi. Yau an wayi gari, shugabanni basa tuna Sardauna sai sabgar siyasa ta tashi.  

Kungiyar haɗa kan Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) tayi yunƙuri daban-daban wajen farfaɗo da daraja da martabar Arewa tare da haɗa kan mutanenta tun lokacin da aka kafa ta, amma abin ya ci tura. Ai ƙungiya ba gwamnati ba ce. Mafi yawan gwamnonin Arewa masu riƙe da madafun iko, siyasa ce kawai a gabansu, ba wai haɗin kan Arewa ba. Ba damuwar mafi yawancinsu bane a samu zaman lafiya, a bunƙasa ilimi kuma a haɓɓaka tattalin arziƙin Arewa ba. Wasu daga cikinsu ma da su aka yi amfani aka rusa Arewar da sunan siyasa.

Allah Ya ji ƙan Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto tare da sauran mazan jiya; ba rabo da gwani ba, mayar da kamarsa.

Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez  

©Mujallar Mikiya, 2016. A nemi izini kafin a sarrafa.  

No comments:

Post a Comment