Fassara

Tuesday, September 1, 2015

Abubuwa 10 da Muka Fahimta daga Gwamnatin Ganduje a Cikin Kwanaki 100

1 Ga Satumba, 2015


Daga: Amir Abdulazeez

A
n zaɓi Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Gwamnan Jihar Kano da gagarumin rinjayen yawan ƙuri’un da ba a taɓa ganinsu ba a tarihin Jihar Kano. Bayan haka kuma shi ne Mataimakin Gwamna na farko da ya taɓa zama zaɓaɓɓen gwamna  a tarihin siyasar Kano. Kusan kowanne ɗan takara ya kan samu mulkin Kano ne ta sanadiyyar abu ɗaya zuwa biyu amma Dakta Ganduje ya ɗare kan mulki bisa dalilai masu yawa. Farko dai ya samu mulki a bisa cancantarsa ta karan kansa da gogewarsa ta fuskar aikin gwamnati da kuma siyasa tare da fifikon da ya ke da shi ta fuskar ƙwarewa a kan sauran ‘yan takara. Na biyu an zaɓe shi gwamna a dalilin ƙarfi da farin jinin jam’iyyarsa haɗe kuma da yayin ta da ake yi sannan kuma da rashin farin jinin ragowar jam’iyyun da suka kara da ta sa jam’iyyar. Abu na uku, an zaɓe shi saboda ƙarfin guguwar Shugaba Buhari wacce ta yi awon gaba da duk wani abu da ya tsaya a kan hanyar ta. Abu na huɗu, an zaɓe shi saboda ƙarfin gwamnati da ya ke hannunsu tare da kuma da farin jinin maigidansa tsohon gwamna Kwankwaso. Waɗannan sune manyan dalilan da suka kawo Ganduje kan mulki.

Alhamdulillah, kwanci tashi yanzu gwamnatin Ganduje ta kwana 100 a kan mulki kuma ko shakka babu mutanen Kano suna da tulin bure-bure da ƙudurce-ƙudurce a kan wannan gwamnati saboda irin gagarumar gudunmawar da suka ba ta. Kodayake kwanaki 100 sun yi kaɗan a iya yiwa gwamnati mai wa’adin shekaru huɗu wani cikakken alƙalanci, amma sun isa a gane inda gwamnatin da kuma Waɗanda suke jagorancin ta suka dosa tare da hasashen me za ta yi ko me za ta iya iya yi, menene ba za ta iya yi ba, musamman idan aka yi la’akari da wasu abubuwan da suka faru kai tsaye daga gwamnatin ko kuma daga wasu abubuwa da suka shafe ta ko da ba kai tsaye ba. A cikin kwanaki 100 na Ganduje, mun fahimci abubuwa da yawa, to amma ga guda 10 daga cikinsu;

Ganduje ya fara nuna ƙwarewa a aikin Gwamnati kuma zai tafi da Matasa;
Muhimmin aikin da Ganduje ya fara yi shine na rage yawan ma’aikatun Jihar Kano daga ashirin da wani abu zauwa 14 kacal inda ya harhaɗe wasu ma’aikatu da wasu domin ingantuwar aiki da kuma guje wa taci-barkatai a aikin gwamnati.
Idan kuma aka yi la’akari da naɗe-naɗen muƙaman da Gwamna Ganduje ya gudanar a cikin kwanakinsa 100, to za mu iya cewa matasa ne za su juya akalar gwamnatin Jihar Kano a shekaru huɗu masu zuwa. Duk kuwa inda aka ce an sa matasa a gaba, to za a ga aiki ba kasala da jan ƙafa in dai matasan masu kishi ne ba lalatattu ba. Sai dai kawai matsalar ita ce, ba a san ko gwamnan zai sakar wa matasan da ya naɗa mara su yi fitsari ba ko kuma kawai ya yi musu naɗin jeka-na-yi-ka ne a matsayin tukwuicin goyon bayansu lokacin yaƙin neman zaɓe. Wani lokaci kuma su matasan su kan yi ƙorafin ba a basu dama, amma kuma daga an basu sai su ƙasa bai wa maraɗa kunya. Ko ma dai menene, zuba matasa a a cikin gwamnati abu ne mai kyau da ya ke nuna an ɗauko hanyar ci gaba, sai dai kuma muna fata kada matasan da aka naɗa su juye su koma matatsa.

Har Yanzu Sabon Liman bai Wartsake daga Zama Na’ibi ba;
Duk da cewar Ganduje ya yi kwanaki 100 a matsayin cikakken liman a maimakon na’ibi da ya shafe shekaru takwas ya na yi, alamu sun nuna kamar har yanzu bai wartsake daga na’ibintaka ba.
Wasu masharhanta siyasa da harkokin mulki suna ganin har yanzu bai yi kama da gwamna mai cikakken iko ba, tamkar tsohon gwamna Kwankwaso ya na tasiri sosai a kan yadda ake gudanar da gwamnati kuma kamar shi tsohon gwamnan ya yi masa dabaibayi. Rahotannin cikin gida sun nuna cewar akwai shawarwari masu kyau da ƙudurce-ƙudurce da makusantansa  da kuma ‘yan kwamitin karɓar mulkinsa suka bashi kuma ya nuna ya karɓa, amma a cikin kwanaki 100 babu wasu alamun cewa zai yi aiki da su saboda tsoron zai baƙanta wa Kwankwaso ko kuma za su iya canza alƙiblar gwamnatinsa daga ta Kwankwasiyya. Kodayake dai shi kansa gwamna ya faɗa tun da farko cewar yadda ɗillin ta kan yi ɗillin, haka kaza ta kan yi ƙwan nan, sai dai fa ba duka ƙwai ne ya kan yi kaza ba, wani ƙwan ya kan yi gunya.

Har Yanzu Majalisar Dokokin Kano ‘Yar Amshin Shata ce;
Majalisar Dokoin Jihar Kano, kamar dukkan sauran Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya, ta kasance a mafi yawan lokuta ‘yar amshin shatar ɓangaren zartarwa. Tun daga yanayi mai kama da ɗauki-ɗora da aka bi wajen fitar da shugabancin Majalisar Dokokin ta Kano, ta bayyana a fili cewar ba lallai su iya taka wa gwamnati birki ba yayin da ta kauce hanya. Jama’ar Kano sun ɗauka za ta ɗan yi wasu tambayoyi dangane da wasu abubuwa da suka faru  a kwanakin baya kamar misalin dakatar da ma’aikatan shara sama da guda 2000 da gwamnati ta yi daga aiki da kuma hargitsi da ya taso a hukumar KAROTA, amma sai aka ji shiru. Kai a taƙaice ma da wahala a iya nuna wani abu da majalisar ta yi na karan kan ta ba wai wanda gwamna ya tura mata ba a cikin kwanaki 100 ɗin da suka gabata. Ko wannan ya na da alaƙa da cewar dukkan ‘yan majalisu 40 ɗin ‘yan jam’iyyar APC ne mai mulki ba tare da ɗan adawa ko ɗaya ba ko kuma alamu ne na ‘kyakkyawar’ alaƙa da ɓangaren zartarwa, ba mu sani ba. Kwanannan dai Gwamnatin Kano ta ware wa kowacce mazaɓar ɗan majalisa Naira Miliyan 50 domin yin aiyukan mazaɓu. Da alama dai ‘yan amshin Shata sun fara jin daɗin waƙar Shatan.

An Kashe Ofishin Fes Ledi a Kano;
Gwamna Ganduje dai za a iya cewa ya ɗora a kan inda Sanata Kwankwaso ya tsaya a yunƙurin tsame matan gwamnoni daga sha’anin mulki a bayyane. A fili dai babu wanda zai ce ya ji ɗuriyar matar Kwankwaso ko Ganduje a sha’anin mulkin Kano daga 2011 zuwa 2015. Wannan ya sha ban-ban daga abin da ya ke faruwa a lokacin tsohon Gwamna Shekarau. To amma sai dai wani abin tambaya a nan shi ne, menene laifi don matar mai mulki ta shigo cikin sha’anin mukin mijin ta da kyawawan tsare-tsare domin taimaka masa a gina ƙasa da al’umma? Wasu na ganin babu laifi idan hakan ba zai  kawo wawure dukiyar al’umma da sunan ofishin ‘First Lady’ ba. Wasu kuwa suna ganin tunda akwai Ma’aikatanun Ci gaban Mata a matakin tarayya da kuma dukkkan jihohi waɗanda suke da ma’aikatan gwamnati birjik da kwamishinoni, to babu buƙatar sai matan masu mulki sun shigo gwamnati.
Ko ma dai menene, ba za a taɓa iya raba matar mai mulki da tsoma baki a cikin mulkin sa ba, ko dai a fili ko kuma a ɓoye. Wani lokacin ma gara ta tsoma a filin, don a ɓoyen  ba a san abin da za ta angiza mijin ya yi ba.

Ganduje Sai Ya Fi Shekarau Haɗa Siyasa da Addini;
Da wahala  a samu wani gwamna a Kano da ya yi amfani da addini wajen saye zukatan jama’a ba kamar tsohon gwamna Mallam Shekarau.  A tsawon mulkinsa na shekaru takwas, kodayaushe maganar Shekarau ita ce siyasarsa addininsa kuma addininsa siyasarsa. Za mu iya cewa Shekarau ya ci ribar wannan tsari ko kuma aƙida ta sa duk da ya ke kuma a ƙarshe tsarin ko aƙidar ta sa ta saka shi a cikin tsaka-mai-wuya a siyasance.
Idan muka yi la’akari da yadda Khadimul-Islam Shiekh Ganduje da magoya bayansa suke addinantar da gwamnatinsa da siyasarsa a cikin kwanaki 100 da suka gabata, to za mu iya cewa zai dame Shekarau ya shanye nan da wani lokaci kaɗan, wataƙila ma kafin wasu kwanaki 100 ɗin masu zuwa.

Kwankwaso Ya Bar Baya da ƙura ;
Kwankwaso ya ɗebi ma’aikata da yawa, ya ciyar da ‘yan makarantar firamare abinci kyauta, ya tura ɗalibai ƙasahen duniya domin ƙaro ilimi kyauta, amma kuma ya tafi ya bar basussuka da kwantan aiyuka na kusan Naira Biliyan 400 kamar yadda Kwamitin Karɓar Mulki na Ganduje ya bayyana. Wato dai ba mu san me ya kamata mu yi ba idan mun tuna da Kwankwaso, dariya, kuka ko kuma duka biyun? Kodayake gwamna Ganduje ya fito kafafen yaɗa labarai yace waɗannan  basussuka ba laifi ba ne tunda tsabar aiki ne ya sa aka same su, to amma  a cikin kwanaki 100 da suka wuce har yanzu ba a ga wani tsari da ya bayyana ba a fili ƙarara wanda ya ke nuna yadda za a biya waɗannan basussuka kuma zuwa wane lokaci?
Bayan haka, idan aka raba aiyukan Kwankwaso gida uku, kusan sama da kashi ɗaya bai ƙarasa su ba, duk da cewa wasu ma ya dinga ƙaddamar da su a hakan ba a gama ba, sannan kuma a cikin kwanaki 100 da suka wuce babu wani daga cikin kwantan aiyukan da aka ƙarasa balle a ƙaddamar. Wasu aiyukan ma tun da Kwankwason ya tafi  ba a sake ganin ƙeyar ma’aikata ko ‘yan kwangilar a gun aikin ba. Duk wannan ma mai sauƙi ne a kan aiyukan da ake ikirarin cewar ƙarasasu za a yi, bayan a gaskiyance ma kusan ko farasu ma ba a yi ba. Idan da mai tantama, to ya ziyarci  titunan kilomita biyar biyar  da ake yi musamman a ƙananan hukumomin ƙauyuka.

Ƙananan Hukumomi basu Farfado ba Har Yanzu;
A halin yanzu, za mu iya cewa  ƙananan hukumomin Jihar Kano a mace suke murus domin akwai ƙananan hukumomin da aka rawaito cewar shugabanninsu suna yin wata guda basu  ziyarce su ba balle kuma sauran  ma’aikata.  Shekaru huɗu gwamnatin Kwankwaso ta yi ta na hana ƙananan  hukumomi cikakkun kuɗaɗensu, shi kuwa mulki ba ya yiwuwa sai da kuɗi.
Majiyoyi masu tushe sun nuna cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka bai wa Ganduje gagarumin goyon baya a tsakanin shugabannin ƙananan  hukumomi shine ko dai alƙawarin da ake cewa ya yi musu na zai dinga  basu kuɗaɗensu ko kuma kyakkywan zaton da suke masa  na cewar ba zai riƙe musu haƙƙoƙin ƙananan hukumominsu ba.
A cikin kwanaki 100 da mulkin Ganduje, har yanzu kusan ƙananan  hukumomi suna nan yadda suke, ba-cas-ba-as. Kodayake an ce har yanzu ciyamomi suna ta duban hanya dangane da batun kuɗaɗen nasu, amma sun manta cewar Ganduje shi ne kwamishinan ƙananan hukumomi a shekaru huɗun da Kwankwaso ya yi ya na hanasu kuɗaɗensu.

Tsafta Ita ce Bakandamiyar Ganduje;
Bayan rantsar da Gwamna Ganduje, sai da aka shafe kwanaki 7 cur ana kwashe shara a Kano. Bayan nan kuma gwamnatin ta ɓullo da tsarin tsafatace ma’aikatun gwamnati a duk juma’ar ƙarshen wata tare da ware ƙarin Ranar Lahadin ƙarshen wata don yin wata ƙarin tsaftar amma ba tare da an hana zirga-zirga ba. Wannan na nuna cewar  gwamnatin a tsaye ta ke  kyam a kan tsafta wanda kuma zai taimaka wajen inganta kiwon lafiya. Kowacce gwamnati ta na da bakandamiya, me yiwuwa idan aka ci gaba a haka, tsaftar muhalli zai zamo abin da za a dinga tuna gwamnatin Ganduje da shi bayan ta tafi.
Wani hanzari ba gudu ba shi ne, duk da wannan ƙoƙari na gwamnati, har yanzu ba a raba tituna da unguwannin Birnin Kano da shara. Shin mutane ne suke amfani da damar cewa gwamnati na kwashe sharar shi ya sa suke zubar da ita ko’ina ko kuwa irin abin nan ne  da ake cewa idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai?

Ganduje da Kwankwaso za su ɓata amma ba Yanzu ba;
Masana mulki sun tabbatar da cewa ba a yin sarki biyu a gari ɗaya. Sannan kuma ma’abota sharhi kan harkar siyasa suna ganin cewa mai mulki ba zai taɓa samun nasara sosai ba sai ya zamo mutumin kansa wanda kuma hakan na nufin ya ɓata da iyayen gidansa.
A 1999, Kwankwaso ya ɓata da iyayen gidansa irinsu Rimi, Musa Gwadabe, Gwadabe Satatima da Hamisu Musa. A 2003, Shekarau ya ɓata da su Janar Magashi, AVM Mukhtar, Naja’atu da su Danzago. Don haka abu ne mai wahala Ganduje ba su ɓata da Kwankwaso ba in dai ba sun matuƙar kai zuciya nesa ba wanda da wahala masu kai komo a tsakani su bari a kai zuciya nesan.
A tsawon kwanaki 100 da suka gabata, wasu  ‘yan siyasa suna ta kai gwauro suna kai mari a kan lallai sai sun haɗa Ganduje da Kwankwaso faɗa. Kwankwaso ya binne abubuwa da yawa wanda dole sai an tono su za a samu zaman lafiya, idan kuma Ganduje ya shirya barin su a binne, to ya shirya wa rungumar abin da zai biyo ba tsakaninsa da mutanen Kano. Idan kuma zai tono su, to ɓatawa da Kwankwaso ta zama dole. Ganduje mutum ne dattijo mai juriya da haƙuri kuma ya daɗe ya na haƙuri da Kwankwaso, kodayke shi ma Kwankwason ya yi haƙuri da shi, amma fa yanzu ba lallai shi sabon gwamna ya iya ci gaba da yin haƙurin da ya yi a baya ba. Saboda haka masu kai gwauro suna kai mari, me kuke ci na baka ya na zuba?

Ganduje Ya Samu Damar Kafa Tarihi;
Idan da Kano za ta samu gwamna wanda zai tsakuro halayen Kwankwaso kaɗan, ya tsakuro na Shekarau kaɗan ya haɗa waje ɗaya, to da an yi lafiyayen gwamna. Misali a samu gwamna gogagge, mai ilimi, nutsuwa, tausayi da jin shawara kamar Shekarau kuma ya zamo jajirtacce, ma’aikaci, mara tsoro, mai cika magana kamar Kwankwaso.
Ganduje ya samu kansa a cikin wani yanayi mai cike da damar kafa tarihi. Kwankwaso da Shekarau sun mulki Kano shekaru takwas-takwas, duk an ga kamun ludayinsu. Ya na da damar ya kalli alkhairansu ya yi koyi sannan kuma ya kalli kura-kuransu ya kauce musu. A kwanakinsa 100 da ya yi a kan mulki, alamu sun nuna kamar abin da ya ya ke ƙoƙarin yi kenan, kodayake yanzu ya yi wuri a iya yin alƙalanci.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, bincike ya tabbatar da cewa mutum ba ya iya zama mai kishiyoyin hali biyu lokaci ɗaya, sai dai ya zama mai zafi ko mai sanyi, mai laushi ko mai tauri. Da Ganduje ya zama kamar Shekarau, da ya zama kamar Kwankwaso wanne ya fi?

Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez   

No comments:

Post a Comment