Fassara

Tuesday, August 16, 2022

Manufata ga Jihar Jigawa (IV)

 

6 ga Augusta, 2022



Daga: Mustapha Sule Lamido

Kamar koyaushe, zan fara da gode wa dukkan jama’ar Jihar Jigawa bisa goyon baƴan da suke nuna mana. Wannan aiki da nake yi na ware lokaci domin yin bayanin manufofinmu dalla-dalla, ya nuna cewa muna da cikakken shirin tunkarar aikin dake gabanmu. Ina so na jaddada cewa muna da ƙuduri mai ƙarfi, tanadi cikakke da kuma abokan aikin da ake buƙata don aiwatar da waɗannan manufofi. Kuma mun dogara ga Allah domin jagoranci bisa hakan. Ina kira ga dukkan jama’ar Jigawa da su bamu ƙuri’unsu a watan Maris na 2023, Insha Allahu ba zasu yi nadamar hakan ba.

Wannan babi shine tattaunawata ta biyu kuma ta ƙarshe a kan ilimi. Cimma manufofinmu na ilimi yana buƙatar tallafin dukkan masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu. Saboda haka ne muke ta tuntuɓar ƙwararru da ƙungiyoyin ɗalibai, malamai, iyaye, lakcarori da ma’aikata. Waɗannan mutane zasu taimaka wajen inganta manufarmu da kuma aiwatar da ita idan mun samu nasara. Don haka, aiki tare dasu tun daga farko zai taimaka ƙwarai wajen kyautata aikin bayar da ilimi.

Idan kuka bamu dama, cikin yardar Allah zamu sake fasalin tsarin karatun Almajiranci domin gyarashi da kuma ingantashi. Farko zamu fara da ƙididdigar yawan makarantun Allo da tsangayu da kuma yawan almajirai da alaramommi a faɗin jihar. Sannan sai mu kafa kwamitin masana wanda zai ƙunshi alarammomi, ma’aikatan ilimi da kuma ƙwararru. Wannan kwamiti zai fito da wani tsari mai ɗorewa kan tsangayu. Dama akwai tsohon tsari na lokacin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan wanda jihoji irinsu Sokoto suka ɗora a kai. A ƙetare kuma, na yi bincike a kan tsarin tsangayu a ƙasar Malaysia wanda ya samar da gyara sosai; akwai kuma wasu tsarukan masu kyau a ƙasashen Afrika ta Yamma. Zan miƙa wa wancan kwamiti bayani game da irin waɗannan tsaruka domin mu cimma burinmu na samar da sabon tsarin almajiranci gyararre, tsaftatacce, nagartacce kuma ɗorarre.

Muna da ƙuduri kan ilimin gaba da sakandiri. A yanzu haka muna da manƴan makarantu guda 14, jami’oin Gwamnatin Tarayya guda biyu, ta jiha guda ɗaya da mai zaman kan ta guda ɗaya. Akwai polytechnic guda uku, kwalejin ilimi guda ɗaya, makarantar fasahar sadarwa guda ɗaya, makarantun ilimin kiwon lafiya guda huɗu da kuma kwalejin ilimin shari’a guda ɗaya. Dukkan waɗanda suke mallakar jiha zasu samu cikakkun kuɗin gudanarwa dai-dai da yanayin tattalin arziƙin da muka samu kanmu a ciki kuma zamu ƙarfafesu domin neman haɗin guiwa a ciki da wajen jihar domin samun tallafin yin bincike da nazarce-nazarce ga Malamai da ɗalibai. Gwamnatin Jihar Jigawa zata ƙulla alaƙa da su don aiwatar da bincike da nazarce-nazarcen da zasu taimaki Jihar.

Insha Allahu zamu bada tallafin karatu ga ɗaliban da suke karantar aikin likita, injiniya, aikin lauya da sauran sassa masu muhimmanci ga ci gaban al’umma. Sauran ɗalibai kuma zasu samu tallafi dai-dai da ƙwazonsu. Ɗaliban da suka fita da digiri mai lambar yabo ta ɗaya suna da babbar damar samun aiki a gwamnati ko tallafin ƙaro karatun digiri na biyu a ciki ko wajen Najeriya. Ɗaliban Digirin Digirgir wato Ph.D ƴan asalin Jihar Jigawa waɗanda bincike ko nazarinsu yake da alaƙar kawo mafita ga matsalolin jihar kai tsaye ko ba kai tsaye ba zasu samu tallafin gwamnati.

Rahotanni daban-daban na ciki da wajen ƙasarnan sun nuna adadin waɗanda suka iya cikakken karatu da rubutu a jiharmu bai wuce 25-30%, a tsakanin manya zalla kuma 38.3%. A cewarsu, hakan na nufin Jigawa ce jiha ta huɗun ƙarshe a wannan ɓangare; sauran su ne Taraba, Katsina da Borno. Komai tantamarmu ga sahihancin irin waɗannan rahotanni, ya zama wajibi mu yi aiki tuƙuru don ganin mun shiga cikin sahun jihohi goman farko nan gaba, ko kuma aƙalla mu samu damar kaiwa  adadin waɗanda suka iya karatu da rubutu 50% a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ta ɓangaren samun damar shiga makaranta, Jigawa ita ce ta 32 a cikin jihohi 36 da Abuja yayin da kuma muke na 30 a ɓangaren zuwa makarantar kansa. A jimlace, kimanin 60% na ƴan Jigawa basu da ko wane irin shaidar karatu kamar yadda waɗancan rahotanni suka nuna. Waɗannan alƙaluma ne masu ban tsoro da ya kamata mu tashi tsaye domin canzawa cikin gaggawa.

Akwai ƙoƙari da aka yi a baya domin gyara sha’anin ilimi a Jihar Jigawa. Tsakanin shekarar 2007-2015, an gina cibiyoyin Haɓɓane 56 domin ilimin Fulani mata wanda suke ƙari a kan makarantun makiyaya 172. A tsakanin wannan lokaci, an samar da cibiyoyin ilimin manya guda 1,350. An gina makarantu na musamman guda biyu, Makarantar yara masu kaifin basira ta Bamaina da kuma Makarantar Makafi ta Dutse. Bincikenmu ya nuna cewa an yi watsi da mafi yawancin makarantun Haɓɓane da kuma makarantar Makafi ta Dutse. Amma kuma abin farin ciki shi ne, an ƙara yawan cibiyoyin ilimin manya izuwa 1,917 da kuma na ilimin makiyaya zuwa 418. Sai dai kuma suna fama da rashin isassun ma’aikata wanda Insha Allahu muke da ƙudurin samarwa idan mun samu dama.

Matsin tattalin arziƙi da ake ciki yanzu ba lallai ya bari a aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga kowa ba duk da son da muke yi wa hakan. Amma dai muna da ƙudurin bai wa yara mata ilimi kyauta har zuwa sakandiri yayin kuma da marayun cikinsu zasu samu har zuwa gaba da sakandiri a faɗin Jiharmu. Zamu duba yiwuwar sauƙaƙawa ko bayar da ilimi kyauta ga ƴaƴan masu buƙata ta musamman.

Zamu ba walwalar malamai muhimmanci sosai domin inganta aikinsu. Zamu yi nazari kan albashin malamai tare da burin ƙarashi da wani kaso dai-dai da yanayin da tattalin arziƙin jihar zai bada dama. Insha Allahu zamu ƙirƙiri alawus-alawus domin ƙarfafar malamai tare da samar da hanyar martaba malaman da suka yi fice wajen riƙe aikinsu da kyau a faɗin jihar. Zamu bada horo kan horo ga malamai domin su faɗaɗa iliminsu yayin da zamu yi ƙoƙarin samar da cikakkun kayan aiki garesu cikin yardar Allah. Zamu samar da damar tattaunawa lokaci-lokaci tsakanin Malaman makaranta da ɓangaren gwamnati game da nasarori ko matsalolin da suke damunsu. Zamu yi amfani da bayanan da muka samu daga tattaunawar domin samar da gyara a gaba.

Zamu dinga shirya gangamin taron shekara kan ilimi wato Jigawa State Annual Education Summit a turance wanda zai gudana tsawon sati guda domin baje kolin ilimi. Wannan taro zai samu gayyatar baƙi daga ko’ina. Burinmu shine, a cikin shekaru 35 masu zuwa, Jigawa zata zamo cikin jihohi biyar mafi ilimi da ci gaban rayuwa a Najeriya kamar yadda manufarmu mai dogon zango ta tanada.


Gobe ta Allah ce
©Santurakin Dutse