Fassara

Mutum Huɗu

Daga: Amir Abdulazeez

Akwai wasu mutum huɗu, suna da daɗin mu'amala; mutumin da yake tauna magana sosai kafin ya faɗe ta; mutumin da ba ya yin alƙawari sai ya san zai cika shi; mutumin da yake tsananta bincike da yi wa mutane uzuri kafin ya kamasu da laifi da kuma mutumin da yake yi wa mutane alkhairi ba don lallai su saka masa ba.

Mutum huɗu, duk haƙurinka sai kun ɓata dasu; mutumin da buƙatarsa ce kawai buƙata a kowanne lokaci; mutumin da bai san zuru ko kawaici ba; mutumin da sharrin da aka yi masa kawai yake tunawa banda alkhairi da kuma mutumin da kullum tunaninsa ba zai ci gaba ba, ba tare da kai ka ci baya ba.
#MutumHuɗu

Akwai mutane guda huɗu, koda sun rainaka, to sun yi a banza; mutumin da ka san ƙuruciyarsa; mutumin da ka san talaucinsa kuma kai masa hanyar arziƙi, mutumin da ka yi jinyarsa a lokacin da ba zai iya yi wa kansa komai ba da kuma mutumin da ka taɓa koya wa karatu.

Kada ka yarda ka yi sabo da mutum huɗu; mutumin da maganarsa mai kyau amma kullum aikinsa mara kyau; mutumin da ba ya gudun yi wa mutane abin da shi ba ya so a yi masa; mutumin da kuɗi ko abin duniya sune ma'aunin komai a gurinsa da kuma mutumin da kullum burinsa ya samu abubuwa cikin sauƙi ba tare da ya sha wahala ba.

Mutum huɗu, ka bisu a sannu; mutumin da ya rigaka wayewa ko ya fi ka ƙwarewa ta kowanne fanni; mutumin da ake daɗewa sosai kafin a ga ɓacin ransa; mutumin da ya san sirrinka ciki da bai da kuma mutumin da ba ya neman komai a wajenka.

Kada ka yarda alaƙarku ta yi nisa da mutum huɗu; mutumin da in ya faɗi magana ba ya cikawa, mutumin da yake yawan kawo sukar mutane gurinka; mutumin da yake raina alkhairi da kuma mutumin da yake nuna son kansa a fili, a cikin kowanne lamari.

Duk rintsi kada ka yarda ka zamo ɗaya daga cikin mutane huɗu; wanda ba ya neman mutane sai buƙatarsa ta taso; wanda ba ya alkhairi face sai ya yi gori; wanda yake yawaita yin magana a kan abin da bai sani ba da mai yawan bada labarin kansa ko irin gwanintarsa.

Mutane huɗu, ka yi hankali dasu; wanda kullum yake yabonka ba ya gaya maka kuskurenka; wanda ba ya tashi yin abun kirki sai a gaban jama’a; mutumin da yake take laifinsa ya hango na wasu da wanda yake sassauya halayensa a gurin mutane daban-daban.

Akwai wasu mutane huɗu da basu da yawa a cikin kowacce al’umma; wanda yake haƙura da buƙatarsa a kan ta wasu; wanda ba ya iya samun abin duniya ya ci shi kadai; wanda yake bari sai dai a ji labarin gwanintarsa a gurin wasu da kuma wanda zai lallasheka ko da ya fi ka gaskiya saboda a zauna lafiya.

Mutane huɗu sun huta da hayaniyar da zata hanasu zaman lafiya; wanda ba shi da abin faɗa mai amfani kuma ya yi shiru, wanda ya samu ɗaukaka amma ba ya nunawa; wanda aka yi wa sharri kuma ya saka da alkhairi da wanda aka kaishi bango kuma ya yi haƙuri.

Mutum huɗu, ƙwarewarsu ta isa; wanda zai juya maka ra’ayi ba tare da ka sani ba; mutumin da zai mu’amalanci maƙiyinsa har ya koma masoyi; wanda ba ya bari laifin wani ya shafi wani ko kaɗan da kuma mutumin da yake yi wa kansa da kansa hisabi kuma ya gyara kuskurensa ba tare da wasu sun kula ba.

Ko za ka ci amanar kowa, to banda ta mutum huɗu; wanda yake baka bashi ba tare da shaidu ba; wanda ya barka ka ke shiga ko’ina a cikin gidansa; wanda ba ya ɓoye sirrinsa a gabanka saboda amincewa da wanda ya ɗoraka a kan hanyar neman abincinsa.

Mutum huɗu, ba zasu yi farin jini ba komai dagewarsu; mai surutu amma ba ya sauraro; mai son ya burge amma shi ba a burge shi; mara haƙuri amma mai son shi a yi haƙuri da shi da kuma mai ƙwuiya rowa kuma ga shegen kwaɗayi.

Anya kuwa akwai abin da zaka iya yi wa mutanannen huɗu in banda addu'a? Mutumin da ya shagalta da laifi har ya daina ganinsa a matsayin laifi; mutumin da ba ya jin tausayi ko ganin girman kowa; mutumin da tarin 'ya'yansa da jikokinsa basu hanashi aikata ɓarna ba da kuma mutumin da yake cin haƙƙin jama'a kuma yake murna don an barshi da Allah.
#MutumHuɗu

No comments:

Post a Comment