Fassara

Wednesday, March 23, 2016

Kwankwaso, Ganduje da Siyasar Aika-Aika

18 Ga Maris, 2016


Daga: Amir Abdulazeez

B
abu wanda wannan rikicin siyasar tsakanin Kwankwaso da Ganduje za ta bai wa mamaki sai wanda ba ya bibiyar al’amuran siyasar Jihar Kano da Najeriya ko kuma a’a yana bibiya amma ba ya fahimtar yadda abubuwa suke tafiya. Don haka ba rigimar ce yanzu abin mamaki ba, fara ta da aka yi da sanyin safiya kafin tafiya ta yi nisa shine abin mamaki. Kodayake akwai waɗanda suka so ma ayi wannan rigima tuntuni ma kafin wannan lokaci, to amma masu hasasshe sun tabbatar wa da irin waɗancan mutane masu azarɓaɓi tun a lokacin da gwamna Ganduje ya cika kwanaki 100 a kan mulki cewar rigima fa za a yi ta, sai dai jiran lokaci. Ba wai abubuwan da suka faru a zuwan Kwankwaso ‘ta’aziyya’ ne ya tada rigimar ba, sune dai suka munanata.

Bari mu manta da batun wanene da gaskiya ko kuma wanene ba shi da gaskiya a cikin wannan al’amari, mu manta da waye ya yi butulci ko waye bai yi ba. Kai mu ma manta  da batun wanene zai yi nasara, wanene kuma zai sha kashi. Mu tambayi kanmu da su waɗannan shugabanni biyu masu rigima, shin wannan rikici shi ya kamaci kowannensu a dai-dai wannan lokaci kuma menene sakamakonsa?

Bari mu fara da Gwamna Ganduje. Maigirma gwamna yana da manya-manyan maƙiya guda uku a yanzu kuma duka a cikinsu babu Kwankwaso. Sahun gaba a cikin maƙiyan Ganduje sune masu kiran kansu magoya bayansa waɗanda suka fara yi masa kamfen ɗin tazarce a 2019 tun ma kafin ya cika kwanaki 100 a kan mulki. Wasu daga cikin irin waɗannan ‘magoya baya’ basu ma san da Ganduje ba sai bayan ya samu takara, wasu ma sai bayan ya ci gwamna, amma bambaɗanci da bani-na-iya tasa su suka fi kowa fada yanzu a gurinsa. Duk wani magoyin bayan gwamna na gaskiya ba wai na son zuciya ko rinto ba, kamata yayi ya mayar da hankali wajen taimaka masa da faɗar gaskiya komai ɗacinta, shawarwari da addu’a domin ya sauke nauyin da yake kansa kuma ya samu ya gama zangonsa na farko lafiya cikin nasara ba tare da an samu aika-aika ba.

Maƙiyin Ganduje na biyu shine faɗuwar farashin ɗanyen man fetur wanda ya haddasa masifar ƙarancin rashin kuɗin shigar da shi da takwarorinsa gwamnoni suke ciki. Bayan haka, yunƙurinsa na rage kaifin wannan matsala ta hanyar zafafawa a kan karɓar haraji, ya kawo wa gwamnatinsa baƙin jini da rashin fahimta a gurin mutanen Kano. Ko an ƙi ko an so, wannan za ta dakushe ƙoƙarin gwamnatinsa na ganin ta yi abin kirki. Wannan matsala ita kaɗai ta isa ta hanashi ya wanye da mutanen Kano lafiya wanda tun a yanzu da yawa daga cikinsu sun fara yi masa laƙabi da mai zango ɗaya kuma suke kallonsa a matsayin mai rauni wanda ba zai iya mulkin ba ma.

Matsalar Ganduje ta uku ita ce ƙunshin  da tsarin gwamnatinsa. Kwata-kwata yanayin ƙunshin gwamnatinsa bai nuna cewar so ake yi a cimma wani abu na a-zo-a-gani ba. Mafi yawan naɗe-naɗensa sun fi maida hankali ga biyan bashi ga waɗanda suka wahaltawa kamfen ɗinsa da kuma waɗanda zasu taimakeshi ya yaƙi Kwankwaso ko kuma ‘yan bambaɗanci. Banda haka, fama da rashin kuɗin shiga bai hana gwamnatin yin naɗe-naɗe barkatai marasa kan gado ba. Bugu da ƙari, bayan watanni 10, har yau gwamnatin bata nuna alamun tana da wata alƙiblar da tasa a gaba ba; waɗanne abubuwa ne zata fi mayar da hankali  a kansu; noma, kiwon lafiya ko me? Idan Ganduje ya tsaya faɗa da Kwankwaso ba tare da ya yi maganin waɗannan maƙiya nasa ba, to lallai a ƙarshe za a samu aika-aika.

Bari mu dawo kan Kwankwaso. A yanzu Sanatan Kano ta tsakiya, babu abin da ya kamata mu yi masa sai jaje kuma mu ji tausayinsa saboda dalilai da yawa, amma ga kaɗan daga cikinsu. Na farko dai, Kwankwaso yana girma amma lamurransa suna ƙara lalacewa. A matsayinsa na wanda yake tunkarar shekaru 60 da haihuwa a duniya, ya kamata a ce ya haƙura da mugunyar aƙidarsa ta ba-zai-bi-ba, sai dai a-bi-shi. Kullum gani yake shine mai sawa da hanawa kuma a haka zai dauwama. Tunaninsa, shi ya kafa kowa, ya kuma manta cewar shima kafa shi aka yi. Taƙamarsa shi babbane kuma jagora, amma abubuwan da yake yi wani sa’in, masu baki da kunu da ‘yan aika-aika ma baza su yi ba.

Abu na biyu da ya kamata  a yi wa Kwankwaso jaje a kansa shine tsananin matsawa kansa da yayi sai ya zama Shugaban ƙasar Najeriya. Ba wai muradin zama shugaban ƙasar ne laifi ba, yadda yake ƙaddamar da muradin nasa ne matsala. Duk wanda baya goyon bayan takararsa, to ganinsa yake kamar maƙiyinsa ne, me yiwuwa shi a ganinsa ƙila dole ne kowa ya goyi bayansa sai kace kowa bawansa ne. Ya manta dimokraɗiyya ake yi ba wai aika-aika ba.

Abin jaje na uku ga Kwankwaso shine duk da farfaganda, surutai dan nuna yafi kowa iyawa da yayi ta yi  a lokacin mulkinsa, sai gashi gwamnatinsa ta ƙare da zarge-zarge da kuma yawan bashi da ba a taɓa jin irinsa ba a tarihin Kano. Har yanzu Sanata Kwankwaso ko magoya bayansa sun kasa yi wa jama’ar Kano cikakke kuma gamsasshen bayani a kan zarge-zargen da ake yi masa na wawashe kuɗaɗen ƙanannan hukumomin Kano da rana tsaka tare da yin kamfen ɗin takararsa ta shugaban ƙasa dasu. Daga an tayar da wannan magana sai magoya bayansa su fara yi wa jama’a labarin irin aiyukan da ya shimfiɗa, sai kace yin aiki wani lasisi ne da mutum kuma zai ɗebi kuɗin jama’a. Idan da nine Kwankwaso, zan mayar da hankali ne wajen wanke kaina daga waɗannan zarge-zarge domin karsu zamarmin tangarɗa a 2019, a maimakon yunƙurin nuna wa Ganduje cewar bai isa ba, nine isasshe.  Kai ko ba don 2019 ba, zan yi hakane don gudun kada waɗannan zarge-zarge su lalata min tarin aiyukan alkhairin dana yi a mulkina kuma ta yadda ba zan bari sunana ya shiga cikin tarihin waɗanda ake zargi da yin aika-aika da kuɗin Kano ba. Sannan kuma ba zan ci gaba da kallon Kano kaɗai kamar ita ce zata bani shugaban ƙasa ba, Najeriyar zan dinga kalla gabaɗaya.

A ƙarshe, akwai shawarwari, duk da dai cewar faɗa ko rikicin siyasa irin wannan ba a cika samun wani sulhu mai ma’ana a cikinsa ba, amma dai kowa akwai hanyar da zai bi don kada ya zamo abin dariya a gurin mutane. A mayar da makamai na zahiri, a ci gaba da yin faɗan ta-ciki-na ciki a baɗini.

Ya kamata Gwamna Ganduje yayi amfani da tarin ƙwarewarsa da hangen nesansa da kuma haƙurinnan da aka sanshi da shi wajen taka-tsantsan a wannan rigima. Ko ba komai, shi ne wanda nauyin jama’ar Kano yake kansa ba wai Kwankwaso ba, ya dubi illar da rigimar za ta iya yi wa wannan nauyi da yake kansa. Sannan kuma gwamna mai ci yanzu, ya tuna cewar fa ya bamu labari a baya cewar duk nasarorin da tsohon maigidansa ya samu, tare suka samu; mai zai hana ya rungumi aika-aikar da suka yi tare?

Kwankwaso! Kwankwaso! Kwankwaso! Sau nawa na kira ka? Lokacinka ya wuce, ka gode wa Allah; kaf  a tarihin siyasar Kano babu wanda ya kai ka sa’a da samun ni’imomi. Ganduje ko Buhari duk baza su hana ka zama shugaban ƙasa ba, idan Allah Ya so, faɗa ko rashin faɗanka dasu ba zai sa ko ya hana komai ba. To wai me neman Shugaban ƙasa ma, ina shi ina wani faɗa? Ganduje kuma, ba kai zaka cireshi ba, ka barshi da mutanen Kano domin su suka ɗaukeshi aiki. Idan ka ci gaba da faɗa da shi, akwai fa tarin aika-aikar da zai iya bankaɗowa wacce mai yiwuwa ba zaka so jinta ba, kai shima baza ta yi masa kyau ba. Idan kuma kana ganin ka yarda da kanka kuma zaka iya kare kanka, to ga fili ga mai doki.

‘Yan uwana talakawa, wannan rigima ce ta ‘yan siyasa, kada mu yarda su raba mana kawuna ko kuma magoya bayansu su raina mana hankali, duk maganace ta buƙatar kai da son zuciya, ba don mu ake yi ba. Irin haka ta faru ba sau ɗaya ba sau biyu ba, ya kamata mu ɗauki darasi, idan kuma mun ƙi, to zamu ga aika-aika.


Twitter: @AmirAbdulazeez