09 Ga Mayu, 2016
Daga: Amir Abdulazeez
B
|
abu kafar yaɗa labarai da mafi yawan talakawan Najeriya suka dogara da ita
domin samun bayanai kamar rediyo wataƙila saboda araha wajen mallaka da kuma
sauƙin sarrafawa. A gefe guda kuma babu kafar da ake jibgawa kowacce irin shara
a Najeriya, musamman ma Arewa, kamar ita
rediyon. Akwai tarin matasloli da suke damun sauran kafafen yaɗa labarai irin
su talabijin, jaridu da kuma yanar gizo; amma kusan babu kafar da ta kai
rediyon fuskantar matasaloli iri daban-daban.
A cikin manya da ƙananan gidajen rediyo kusan guda 150 ko sama da haka da
muke dasu a ƙasarnan, sama da 50% mallakar gwamnatocin jihohi ne da na Gwamnatin Tarayya. Misali, aƙalla kowacce
jiha tana da gidan rediyo mallakarta guda ɗaya a zangon AM, wasu jihohin da
dama suna da ƙarin tasha ɗaya ko sama da haka a zangon FM. Bayan haka, Gwamnatin
Tarayya tana da gidajen rediyo ɗai-ɗai a kan zangon FM a kowacce jiha waɗanda
ta buɗe a shekarar 2003 domin faɗaɗa shirye-shiryen da babban gidan rediyo na ƙasa
yake gabatarwa daga Abuja zuwa dukkan sassan ƙasarnan. Duk wannan lissafi bai
haɗa da gidajen rediyoyi da dama a Najeriya waɗanda suke yaɗa shirye-shiryensu
a kan yanar gizo kaɗai ba.
Mallakar kafafen yaɗa labarai a ɓangaren gwamnati ko wasu sassanta ba wani
sabon abu bane a duniya kuma ba wani abin damuwa bane. Hasalima wasu
manya-manyan kafafen yaɗa labarai da ake taƙama dasu a duniya wajen shahara da ƙwarewa
irinsu BBC, Muryar Amurka, da DW duk mallakar gwamnati ne. Abinda yake matsala
shi ne idan masu riƙe da madafun iko suna yin amfani da waɗannan kafafen yaɗa
labarai domin amfanin kansu da ‘yan korensu. Ba wai an ce kada waɗannan kafafen
yaɗa labarai su tallata manufofi da aiyukan gwamnati ba, amma ya kamata su yi
abin cikin hikima da ƙwarewa kuma su bayar da cikakkiyar dama ga masu yin adawa
da manufofin gwamnatin domin su mayar da martani.
Kafafen yaɗa labarai, musamman gidajen rediyo mallakar gwamnatocin jihohi
sun zama kafafen yi wa gwamnoni tumasanci da bambaɗanci. Mafi yawan
shirye-shiryensu sun karkata wajen yabon gwamnatin da take mulki komai kuwa irin
ta’asar da take aikatawa. Wani lokaci, waɗannan gidajen rediyo su kan gabatar
da shirye-shirye masu muhimmanci da zasu ilmantar da kuma faɗakar da al’umma,
to amma saboda wannan ɗabi’a tasu mai ban haushi, da yawa an haƙura da
shirye-shiryen nasu baki ɗaya. Haka za a ci gaba da tafiya; ana ɗiban kuɗin
al’umma wajen gudanar da irin waɗannan kafafen yaɗa labarai, a gefe ɗaya kuma shugaban
ƙasa, gwamnoni da muƙarraban jam’iyya mai mulki suna amfani da waɗannan kafafe
tamkar mallakarsu na ƙashin kansu?
Wani lokaci ina tattaunawa da wani ma’aikacin gidan rediyo mallakar
gwamnati a wata jiha a Arewa maso yammacin Najeriya; sai yake bani labarin wani
gwamna da aka taɓa yi wanda a lokacinsa ba a isa a sanar da ko da ɗaurin auren
wani ɗan jam’iyyar adawa ko mai alaƙa da shi ta wannan kafa ba. A wasu lokutan
da kansa gwamnan yake bugo wa manajan gidan rediyon waya yace a katse kowanne
irin shiri da ake yi, a saka masa wata waƙarsa ta siyasa wadda yake so. Wannan
kaɗan ne daga cikin irin yadda wasu gwamnonin suke yi wa irin waɗannan kafafen
yaɗa labarai mulkin mallaka. A wasu lokutan kuma ba laifin gwamnan bane da
kansa, muƙarrabansa ne da ‘yan jam’iyyarsa suke yin uwa da makarɓiya a gidajen
rediyon, shi kuma gwamnan sai ya kasa hanasu saboda dalilai na siyasa. Wani
lokaci kuma manajan gidan rediyon da gwamna ya naɗa ne yake mayar da gidan
rediyon fagen bambaɗanci da tumasanci ga gwamna domin ya gyara miyarsa; shi
kuma ƙila gwamnan dama haka yake so.
Kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati su ya kamata a ce sun zamo abin misali
ta hanyar fin kowa nagarta domin su ba
kuɗi suke nema ba kamar na ‘yan kasuwa kuma an kafasu ne domin su bauta wa
jama’a ba gwamna ko shugaban ƙasa ba. An ƙaddara cewa su mallakar jama’a ne
kuma wasu kafafe ne na sadarwa, faɗakarwa, wayarwa da kuma tallata manufofin
kishin ƙasa da ci gaba. To amma maimakon haka, sun zama kafafen farfaganda da ɗaukar
bangare tare da goyon bayan son zuciya. Wannan ita tasa mafi yawancin jama’a
suka ƙaurace musu domin sauraron na ‘yan kasuwa masu zaman kansu duk kuwa da
cewar ba finsu ƙwararrun ma’aikata ko iya gabatar da shirye-shirye aka yi ba.
Kafafen yaɗa labarai na talabijin, suma haka gwamnatoci suka lalata
al’amarinsu tare da sauke su daga bin ƙa’idojin aikin jarida inda ba abinda ake
yi sai tallan masu mulki da kuma hana ‘yan adawa damar faɗar albarkacin baki.
To amma, daɗinta ita talabijin ba ma kowa ne yake da ita ba kuma ba dukkan masu
itan bane ma suke da isasshiyar wutar lantarkin da zasu dinga kallonta
akai-akai ba. Su kuwa jaridu mallakar gwamnatoci, mafi yawancinsu sun durƙushe,
gwamnatocin sun kasa riƙe su. Ita kuwa yanar gizo ta kowa ce, babu wani mai
mulki da zai iya hana faɗar albarkacin baki a cikinta ko kuma yace sai abinda
yake so shi mutane zasu karanta. Matsalar kawai ita ce, yanar gizo tana da
matuƙar matsala domin ana yawan yaɗa ƙarya da labaran ƙanzon kurege ta wannan kafa kuma ana yawan amfani da ita wajen ci
wa jama’a da masu mulki mutunci da yi musu
ƙage a inda basu ji ba basu gani ba.
Kasancewar halin da kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati suka samu kansu,
mutane da yawa sai suka ƙaurace musu, suka koma na ‘yan kasuwa. Idan bamu manta
ba, har a shekarar 1999 babu gidan rediyo mallakar ‘yan kasuwa ko ɗaya da yake
aiki ka’in da na’in a Arewacin Najeriya, sannan waɗanda suke a kudanci basu fi
a ƙirge su ba. Yanzu irin waɗannan gidajen rediyo sun mamaye ko’ina amma har a
yanzu haka akwai tsirarun jihohin da basu da gidan rediyo masu zaman kansu ko ɗaya,
sai dai na gwamnati. Irin waɗannan jihohi suna fuskantar cikas sosai wajen faɗin
albarkacin bakinsu. Matsalar a nan ita ce, su ‘yan kasuwa kuɗi suke nema domin
sun zuba maƙudan kuɗaɗe wajen samun lasisi da kuma kafa injina. Bayan haka suna
kashe maƙudan kuɗaɗe wajen samar wa da kansu wutar lantarki, biyan haraji da
albashin ma’aikatansu. Wannan ce ta sa, mafi yawancinsu kuɗi sune abinda suka fi
nema ido rufe. Sakamakon haka, sai ‘yan siyasa da sauran jama’a suka yi amfani
da wannan dama wajen mayar da su gurin zubar da kowacce irin shara suka ɗebo. A wasu lokutan, matuƙar
kana da ‘yan kuɗinka a aljihu, sai kaje ka biya a barka kai ta faɗar irin sakarcin
da kake so da sunan siyasa; mutane su yi ta faɗin ƙazantar bakinsu amma wai su
kira shi da faɗin albarkacin baki. Waɗanda basu da ilimi ko ƙwarewar da ya
kamata su yi magana a sauraresu, sai su shiga gidan rediyo mai zaman kansa su
yi ta soki burutsu wai su ga masu ‘yanci, banza ta faɗi.
Lokacin da ministan yaɗa labarai da ci gaban al’adu na gwamnatin Shugaba Buhari,
Alhaji Lai Mohammed ya kama aiki kimanin watanni shida da suka wuce, ya yi alƙawarin
cewar Gwamnatin Tarayya zata yi wa kafafen yaɗa labaranta garanbawul domin su
amfani dukkan ‘yan kasa ba wai waɗanda suke mulki ko ‘yan jam’iyya mai mulki kaɗai
ba. Daga wancan lokaci zuwa yanzu, alamu sun nuna an ɗan soma samun canji kaɗan
ba da yawa ba musamman a kafafe irinsu NTA, FRCN, NAN da dai sauransu. Ya kamata
jihohi su bi sahu wajen kawo gyara ga kafafen yaɗa labarai. Yana da kyau masu
mulki su fahimci cewar aikin da suka yi ko suka ƙi yi wa talakawa shi zai yi
musu alƙalanci ba wai mallake kafafen yaɗa labarai ba. Kan mutane yanzu a waye
yake; idan sun yi abu mai kyau ko mara kyau, za a samu kafar da za a faɗa, koda
sun hana a faɗa a kafar gwamnati.
Yana da kyau, ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa, NUJ ta dinga yi wa
ma’aikatanta masu aiki a irin waɗannan kafafen yaɗa labari na gwamnati bita ta
musamman tare da fahimtar dasu cewar aikin jama’a suke yi ba na mai mulki ba
kuma ‘yan siyasa basu da ikon tilasta musu
kauce wa dokokin aikin jarida don kawai suna masu mulki. Su nuna musu
cewar, idan suka haɗa kansu, za su iya bin duka matakan da suka dace domin
tsaftace aikinsu da ƙin yarda a lalata musu shi. NUJ ta fahimtar dasu irin
zubewa da ƙimarsu da mutuncin aikinsu yake yi wajen yi wa masu mulki bambaɗanci da tumasanci a
rediyo da sunan yaɗa labarai ko aikin jarida.
Majalisun dokoki na jihohi da na tarayya, ya kamata su kalli wannan matsala tare da duba yiwuwar yin dokokin da zasu hana
gwamna ko shugaban ƙasa ikon naɗa ko tuɓe shugabannin gidajen yaɗa labarai
mallakar gwamnati domin samar musu da ‘yancin kansu.