Fassara

Wednesday, October 12, 2016

Siyasar Bambaɗanci da Makomar Matasanmu

06 Ga Oktoba, 2016

 Daga: Amir Abdulazeez

C
ewar babu abinda ɗan siyasar wannan zamani ba zai iya yi ba saboda buƙatarsa, kullum ƙara bayyana yake yi a fili ƙarara. Ba wai sata, ƙarya, munafirci, rashin kunya ko maguɗi ba, a’a da yawa daga cikin ‘yan siyasarmu na wannan lokaci, a shirye suke su lalata rayuwar ‘ya’yan da ba nasu ba wajen ganin sun samu biyan buƙata ko kuma an ci gaba da kare musu muradinsu ko ta wane hali kuma komai lalacewar hanyar da za a bi wajen kare musu muradan nasu.

Duk mai lura da yadda al’amuran yau da kullum suke gudana, zai fahimci cewa an samar da wani sabon salo na wofantar da matasa da mayar dasu mabarata ko maroƙan ƙarfi-da-yaji. Irin waɗannan matasa suna shiga gidajen rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai, amma dandazonsu ya fi yawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo; shafukan da suka haɗa da Facebook, Twitter da dai sauransu. Irin waɗannan matasa basu da aiki sai tumasanci da bambaɗanci ga ‘yan siyasa da masu mulki. Irin wannan salo na tumasanci, kusan bamu taɓa ganin irinsa a ƙasar Huasa ba; ko maroƙanmu irin na da waɗanda basu da sana’a sai roƙo basu yi irin abinda ake sa waɗannan matasa suke yi a yanzu ba.

Rahotanni masu tushe sun bayyana cewar ‘yan siyasa a jihohin Arewacin Najeriya har ma da kudancin, yanzu sun ɗauki ɗabi’ar saya wa matasa wayoyi ko komfutoci da basu kuɗi lokaci bayan lokaci domin sanya kati domin su dinga shiga yanar gizo suna yi musu bambaɗanci da tumasanci wai da sunan tallatasu ko yabonsu. A cikin irin matasan da aka ɗora a kan wannan wulaƙantacciyar hanya, babu ‘ya’ya ko jikokin su ‘yan siyasar ko masu mulkin. Abin takaici ne matuƙa a ce wai a wannan ƙarni na 21 da kowa yake ƙoƙarin bai wa matasa ilimi da damammakin da zasu zama masu juya duniyar gobe, wasu mutane ko jagorori waɗanda ya kamata su shige musu gaba don tabbatar da hakan, sun koma ɗorasu a kan tafarkin roƙo, kwaɗayi, cin mutunci da wofantar da kai wai da sunan siyasa. Wani abin haushin kuma shine, su ‘yan siyasar masu yin wannan, ba haka magabatansu suka yi musu ba; hasalima, ba dan magabatan nasu sun ɗorasu a kan hanya mai kyau ba, da basu zama abinda suka zama ba a yanzu.

Akwai matasan da  a yanzu dare da rana, basu da aiki sai shiga kafafen sada zumunta suna zubar wa da kansu da gidajensu mutunci wai da sunan tallata masu mulki. Wanda kuma ba ya yin haka kuma ya zaɓi ya kare mutuncinsa, to kallonsa ake yi a matsayin maƙiyi ko ɗan adawa. Kullum kwanan duniya, in dai kana raye a Najeriya, zaka yi ta ganin abubuwa na rashin hangen nesa da sanin ya kamata iri-iri. Wani abin tun kana gane dalilin yinsa har sai kanka ya ɗaure ka koma baka fahimtarsa kwata-kwata. Mun koma, bama son dai-dai kuma bama son gaskiya; wanda ya yi gaskiya ko ya dage sai an yi dai-dai sai a mayar da shi mujiya a cikin tsuntsaye. Haka zamu ci gaba? Muna buƙatar gyara kuwa?

Farko dai dole ne waɗannan ‘yan siyasa su dubi Allah su tuna haƙƙin da yake rataye a wuyansu. A matasyinsu na shugabanni, ci gaban matasannan da dukkan al’umma gabaɗaya ya rataya a wuyoyinsu. Duk lalcewa, in bazasu iya taimakonsu wajen ci gaban rayuwarsu da dogaro da kansu ba, bai kamata su ɗorasu a hanya ta mutuwar zuciya ba. Ya kamata su tsaya tsayin daka su yi aiki tuƙuru wajen kyautatawa al’umma; idan suka yi haka, ba sai sun ɗebi kuɗin jama’a sun biya matasa su yi musu bambaɗanci ba, mutane zasu yaba musu dai-dai gwargwado. Su tuna fa cewar in da a irin wannan tafarki magbatansu suka ɗorasu, to fa da basu zama abinda suka zama ba kenan. Kuma, me zai hana su sanya ‘ya’yansu da jikokinsu su dinga yi musu irin wannan aiki a maimakon ‘ya’yan wasu?

Ya kamata ‘yan siyasa su daina amfani da damar talauci da kuma tsabar kwaɗayi da yake addabar wasu daga cikin jama’ar wannan zamani wajen  mayar da mutane maroƙa wulaƙantattu. Idan kuma ba da amincewa ko saninsu ake waɗannan abubuwa ba, to su taka wa abin burki. Su daina gudun masu faɗa musu gaskiya da basu shawara domin kawo gyara kuma su daina buɗe ƙofa ga ‘yan tumasnci da bambaɗanci.

Matasanmu kuma dole ne fa sai mun yi wa kanmu faɗa mun fahimci manufarmu a rayuwa. Talauci da neman abin duniya ba fa hauka bane; kowa yana son kuɗi amma ba ta kowacce hanya ya kamata a nemesu ba kuma samun kuɗi cikin sauƙi ba shine burgewa ba. Duk mutumin da zai dinga baka ‘yan kuɗaɗe ƙalilan domin ka dinga yabonsa a kafafen sada zumunta, to ba mai ƙaunarka bane. Idan da abin kirki ne ko na ci gaba, to ba kai zai nema ba, ɗansa ko jikansa ko ƙaninsa zai kirawo ba kai ba; ai muna gani sarai ba sai an bamu labari ba. Matasa su fahimci cewar basu da wata martaba a idon ‘yan siyasa ko amfanin da ya wuce irin wannan aiki da ake sakasu kuma da zarar ka gama aikinka, shikenan amfaninka ya wuce.

Tilas ne matasa su fahimci cewar, mai ƙaunar ka ko mai son ɗorewar mutuncinka da ƙimarka ba zai dinga biyanka kuɗaɗe ƙalilan kana zagin wani ko cin mutuncinsa ko kuma shiga wata hanya ta mutuwar zuciya ba. Mu tuna fa mafi yawan waɗannan ‘yan siyasar fa ba finmu suka yi ba, dama ce kawai suka samu, kuma idan da rabo kai ma zaka iya zama kamarsu ko ma ka fisu. Maimakon ka zauna kana yi musu bambaɗanci, mai zai hana ka yi ƙoƙarin zama kamarsu?

Matasanmu su gane cewar babu lokaci mafi amfani a garesu kamar lokacin ƙuruciya ko tashensu; lokaci ne da zasu yi amfani da shi wajen gina kansu da shirya wa ƙalubalen rayuwa, ba wai lokacin da zasu ɓata wajen karewa ko yabon wasu can da ba ci gabansu bane a gabansu. Wannan hanya ba mai ɓullewa bace; idan kunne ya ji, jiki ya tsira!

Twitter: @AmirAbdulazeez