Fassara

Tuesday, July 4, 2017

Ɗanmasanin Kano: Ba Rabo da Gwani ba!

04 Ga Yuli, 2017



Daga: Amir Abdulazeez

A
na gobe ƙaramar Sallah, na kai wa wani yayana da yazo Kano daga Abuja ziyara, sai muke tattaunawa kan dalilin da yasa sauran yankunan Najeriya suka fi Arewa ci gaba irin na zamani duk kuwa da cewa akwai mashahuran mutane da suka samu damammaki daban-daban a yankin fiye ma da na kowanne yanki a tarihin Najeriya. Bayan mun koka kan yadda almajiranci, jahilci, talauci, gurɓatacciyar siyasa da sauransu suke neman kassara yankin na Arewa, sai kuma muka duƙufa wajen gano bakin zaren.

Muhimmin abin da muka cimma  a ƙarshe shi ne mafi yawancin mutanen Arewa basu da sha’awar kafa tarihi ko barin wani abu da za a dinga tunawa dasu bayan sun mutu. Maimakon haka, yawa-yawansu sun fi sha’awar a tunasu da irin tarin dukiyar da suka mallaka ko kuma irin manya-manyan muƙamai ko sarautu da suka riƙe da kuma irin daular da suka shiga. Ba kasafai za kaga mutane suna da burin a dinga tunasu saboda gaskiyarsu, iliminsu, hikimarsu, riƙon amanarsu, irin sadaukarwar da suka yi kan al’ummarsu ko kuma yawan mutanen da suka taimaka a rayuwa ba. Wannan ce ta sa kusan kowa a cikin masu dama a hannunsu ya kalmashe hannnsa ya zuba wa matsalolin Arewa ido ha tare da nuna damuwa ba, duk kuwa da cewa yankunan Yarabawa da Inyamurai suna ta ƙara ci gaba a dalilin tsari da hoɓɓasa da wasu daga cikin manyansu suke yi musu.

Abin da al’ummar Arewa da kuma Najeriya gabaɗaya ta rasa shi ne yawaitar irinsu Ɗanmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a jiya bayan ya sha fama da rashin lafiya. Daga rasuwarsa jiya zuwa yau, mutane daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu a kansa amma babu wanda na ji yace za a yi asararsa ko kuma za a dinga tunawa da shi saboda yawan dukiyarsa ko irin ƙarfin mulki da daular da ya shimfiɗa ba. Za a dinga tunashi ne da irin iliminsa, hikimarsa da kuma yadda ya yi amfani dasu wajen bai wa Najeriya gagarumar gudunmawa shekaru da dama bayan ya bar gwamnati. Duk da irin muƙaman da ya riƙe, amma ba wannan mafi yawan mutane suke kallo ba.

Darasin da zamu koya daga rayuwar Maitama Sule shi ne, duk abin da kake tunanin kuɗi ko mulki zasu baka, to ilimi da ilmantarwa zasu iya baka shi ciklin ruwan sanyi da mafificiyar daraja. Yau duk inda aka ce Ɗanmasani a faɗin duniya ba ma a Najeriya ba, ko ba a ƙara Kano ba, to kowa ya san Maitama Sule ake nufi. Dakta Yusuf Maitama Sule yana daga cikin mutanen da suka fi shahara a duniyarmu ta wannan lokaci.

Daga mutuwarsa a jiya zuwa yau, miliyoyin mutane ne, musamman matasa da basu ma san wani abu da yawa game da shi ba suke ta yabonsa. To amma tambayar a nan ita ce, muna so mu kwatanta zama kamarsa? Ko kuma mu ce, hakan zai ma yiwu kuwa a wannan zamani da kuɗi ya fi gaskiya, siyasa ta fi mutunci kuma burin tara abin duniya ya fi burin barin kyakkyawan baya?

Ɗanmasani mutum ɗaya ne tamkar da dubu. Yayin da ake masa kallon mai iya magana da hikima, akwai kuma abubuwa da yawa da mutane basu sani ba game da shi. Mutum ne mai matuƙar son zaman lafiya. Ya kan kashe maƙudan kuɗaɗe don ganin ya yi sulhu a tsakanin mutane. Idan ya ji ana rigima a kan kuɗi, ya kan fitar da kuɗinsa koda iya su kenan gareshi don ya kashe rigimar kamar yadda makusantansa suka tabbatar. Yana ɗiban maƙudan kuɗaɗe yasa  a kai wa maƙiyansa ko masu alaƙa dasu domin samar da zaman lafiya.

Ɗanmasani mutum ne mai matuƙar kishin al’ada. Akwai wani lokaci a shekarar 1998 ana buga gasar ƙwallon ƙafar cin kofin duniya a ƙasar Faransa, sai Ɗanmasani ya hangi wani mutum shi kaɗai a cikin tawagar magoya bayan Najeriya a cikin talabijin sanye da kayan saƙa na Fulani. Bayan an gama gasar, sai da yasa aka nemo masa shi ya ba shi kyautar Naira dubu ɗari biyar irin ta wancan lokaci.

Ɗanmasani shi ne Ministan man fetur na farko  a Najeriya kuma shi ne mafi daɗewa a kan wannan muƙami amma lokacin da aka yi juyin mulkin 1966 sai da ya ranci kuɗin mota  kafin ya dawo Kano shi da iyalansa daga Lagos. Da ya dawo Kano kuma ba shi da gida sai gidan gado ya koma. Bayan ya gama minista, bai yi girman kai ba, ya amsa roƙon Gwamnatin Kano na ya zo ya yi mata kwamishina tunda shi bauta wa jama’a ne a gabansa. A wannan zamanin, wa zai maka haka?

Watarana Sheikh Dahiru Usaman Bauchi ya yi mafarki ya ga  Ɗanmasani Kano a cikin waɗanda Manzon Allah (SAW) ya zaɓa a matsayin dakarunsa, sai ya taka ƙafa da ƙafa ya je ya sameshi. Ya bayyana masa mafarkin kuma ya tambayeshi, shi kuwa me yake yi haka na bauta ko shi ma ya yi koyi? Sai Ɗanmasani yace shi dai bai san wani abu na musamman da yake yi ba, amma yana da wata al’ada guda ɗaya. Al’adar kuwa ita ce bakinsa ba ya taɓa rabuwa da yi wa Annabi salati ko da kuwa kuna cikin hira da shi ne yana saurarenka kafin ya mayar maka da martani.

Yau mun wayi gari babu Ɗanmasanin Kano. Da wahala mu iya mayar da kamarsa a Kano, Arewa da Najeriya. Wataƙila idan mun yi da gasken-gaske mu samu waɗanda zasu ɗan kama ƙafarsa kaɗan. A ƙasarnan muna na mutane iri biyu; ‘yan kishin ƙasa da kuma ‘yan kishin yankinsu. Maitama Sule kuwa ɗan kishin ƙasa ne kuma ɗan kishin Arewa kuma ya haɗa duka biyun ne cikin ƙwarewa da gogewa. Lokacin da Shagari ya kayar da shi a zaɓen fidda gwanin takarar Shugaban ƙasa na NPN, har ‘yan Kudu sun yi jimami. An rawaito abokin hamayya Cif Awolowo na UPN yana cewar shi da Ɗanmasani NPN ta tsayar takara a maimakon Shagari, to da ko kotu ba zai je ba bayan an kayar da shi domin ya san Najeriya zata faɗa hannun nagartacce wanda dama shi ne burinsa.

Ɗanmasani yana daga cikin tsirarun manyan ƙasarnan da suka haƙura da siyasa suka zama dattawa tun da wuri. Tun bayan jamhuriya ta biyu bai ci gaba da matsawa kansa sai an dama da shi ko kuma dole sai ya samu wani mulki ba, sai dai a roƙeshi yazo ya taimaki gwamnati. To kuma sai ga shi waɗanda suka yi ta hanƙoran sai sun ci zamaninsu sun ci na wasu, basu kama ƙafarsa wajen ɗaukaka ba. Maitama Sule na kowa ne, ba ya shiga shirgin da babu ruwansa, kuma bai yarda an ji kansu da shugabanni ba duk da cewa kuma yana yi musu gyara idan sun yi kuskure da basu shawarwari.

Lokacin da watarana ya farka daga barci ya ga duhu, sai ya umarci matarsa ta kunna fitila. Sai ta ce ai fitilar   a kunne take, to a nan sai ya gane cewar Allah ya jarrabe shi da larurar makanta. Maimakon ya ruɗe ko ya kiɗime, sai ya tashi ya yi alwala yai sallar nafila ta musamman ya gode wa Allah. Ya ce, Allah na gode maka, wannan idon babu abin da bai gani ba na duniya kuma ko a yanzu da ka karɓe shi, babu wani abu da zai rageshi. Bai yi niyyar neman wani magani ba in banda masoyansa irinsu tsohon Shugaban ƙasa Janar Babangida da suka matasa masa lamba sai an je Turai, to amma Allah Ya riga ya yi ikonSa.

Tun daga ƙarshen shekarar 2016 zuwa yanzu ake ta yaɗa jita-jitar mutuwarsa, ashe lokacinsa ne ya matso. Allah Ya ji ƙan Ɗanmasanin Kano!

Twitter: @AmirAbdulazeez