3 Ga Satumba, 2015
Daga: Amir Abdulazeez
T
|
arihin ƙananan hukumomi a ƙasarnan
ya samo asali ne tun kusan daga lokacin da Turawan Ingila suka haɗa gundumar Arewaci
da Kudancin Najeriya domin samar da ƙasa ɗaya. Tun a wancan lokaci Turawa suka
samar da shiyyoyin mulkin mallaka a ƙarkashin tsarin mulki wanda ba na kai
tsaye ba na Native Authorities wanda
ya bai wa sarakuna damar yin mulki mai taƙaitaccen iko ga yankunansu kafin daga
baya a tsame sarakunan su kansu daga mulkin kacokam. Gwamnatoci daban-daban sun
sha yi wa tsare-tsaren ƙananan hukumomi gyare-gyare da kwaskawarima tare da ƙarawa
da rage adadin yawansu har sau tara daga 1914 zuwa 1999. Tasrin ƙananan
hukumomi kamar yadda muka sansu a yanzu ya samu ne daga sauye-sauyen da aka
gudanar a shekarun 1976, 1979, 1984, 1988, 1989 da 1999.
Duk da cewar gwawnatocin jihohi
daban-daban sun yi yunƙure-yunƙure daga shekarar 2000 zuwa 2007 na ganin sun ƙara
yawan ƙananan hukumomi a jihohinsu, har yanzu dai adadin yawan ƙananan hukumomi
guda 774 ne kamar yadda ya ke a Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na shekarar 1999. To
amma kuma akwai jihohin da bayan ƙananan hukumomin su, sun ƙirƙiri ƙananan gundumomin mulki da samar da ci gaba masu kama
da ƙananan hukumomin. Misali, Jihar Lagos ta na da ƙananan hukumomi 22 amma ta
na da irin waɗannan gundumomi waɗanda ita take samar musu da kuɗaɗen gudanarwa
har guda 37. Akwai irin waɗannan gundumimi a jihohin Yarabawa sosai.
Fahimtar kusan kowa ita ce an ƙirƙiri
ƙananan hukumomi domin matso da gwamnati kusa da talaka. Bayan haka, akwai ƙayadaddun
aiyuka da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na 1999 ya tanadar musu. Muhimman aiyukan
sune bayar da shawarwari da za su inganta tattalin arziƙin gwamnatin jiha;
samar da maƙabartu da gidajen kula da marasa galihu; bayar da lasisin kekuna,
kwale-kwale da kurar turawa ta ɗaukar kaya; kafawa tare da gudanar da mayanku,
kasuwanni, tashoshin mota da gidajen wanka; gina ƙananan tituna, layuka, saka fitlun kan titi da fitar
da magudanar ruwa; bai wa tittuna da layuka sunaye da yi wa gidaje lamba;
kwashe shara da kwatoci; yin rajistar haihuwa da ta mutuwa. Bayan haka an sanya
ƙananan hukumomi su zamo masu taimaka wa
gwamnatocin jihohi wajen bayar da ilimin firamare, ilimin manya da ilimin koyon
sana’o’i; bunƙasa noma da kuma yin dukkan wasu aiyuka da Majilusun Dokokin
Jihohi suka kallafa musu.
Sai dai kuma duk da waɗannan ɗinbin
aiyuka da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora wa ƙananan hukumomi, kuma bai basu damar
cin cikakken gashin kansu ba. A ƙarƙashin sashe na II, ƙananan sassan 7(1), (2) da (3), Kundin Tsarin Mulkin ya nuna cewar gwamnatocin jihohi su
zasu samar da dokokin da zasu tabbatar da wanzuwa, tsari, aiyuka da kuma kashe
kuɗaɗen waɗannan ƙananan hukumomi. Wannnan ya nuna cewa rayuwarsu kusan kacokam
ta na hannun jihohi. Wannan kusan ita ce a yanzu babbar matsalar da take damun ƙananan hukumomi.
Kafin dawowar dimokraɗiyya a
1999 har zuwa farkon dawowar ta, a kan ji ɗuriyar ƙananan hukumomi suna ɗan taɓuka
aiyukan raya ƙasa duk da cewa akwai manyan matsaloli da suke fama da su tun a
wancan lokaci. Amma yanzu kusan gwamnatocin jihohi sun kalmashe su, ba ma a jin
ɗuriyarsu, a wasu jihohin ma kamar babu su.
Babbar matsala ta farko da take
damun ƙananan hukumomi a yanzu ita ce ta tsarin zaɓar shugabanninsu. Tun bayan
shekarar 1999 inda aka gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin Najeriya bai ɗaya,
har yanzu ba a samu ingantattun zaɓuka a mafi yawan ƙananan hukumomi ba. Duk
jam’iyyar da take mulki a wata jihar, ta kan tabbatar da cewa ta lalata tsarin zaɓen
ta yadda za ta cinye 100% na zaɓukan ciyamomi da kansiloli. Gwamnoni su kan yi
amfani da hukumomin zaɓen jihohi wajen shirya gurɓatattun zaɓuka a ƙananan
hukumomi wanda dama tun farko dalilai na siyasa ba sa bari a samar da
ingantattun ‘yan takara tun da farko. Wasu jihohin ba ma sa yin zaɓen
kwata-kwata sai sun ga dama, sai dai gwamnoni su naɗa kantomomi. A Jihar
Anambra an taɓa kwashe shekaru 13
daga 2002 har zuwa
2014 ba
a yi zaɓukan
ƙananan hukumomi ba. Wata ƙarin matsalar kuma ta wannan fuskar ita ce, Majalisun
Dokoin Jihohi da dokar ƙasa ta bai wa alhakin kula da ƙananan hukumomin tare da
basu kariya sun zuba ido sun kasa kataɓus yayin da gwamnoni suke ta cin karensu
ba babbaka a kan ƙananan hukumomi.
Babbar matsala
ta biyu da take damun ƙananan hukumomi ita ce rashin basu kuɗaɗensu da gwamnoni
suke yi. Kusan yanzu ya zama ruwan dare a kowacce jiha, idan kuɗin ƙananan
hukumomi sun zo daga Gwamnatin Tarayya, sai jihohi su danne su hanasu ko kuma
su tsakurar musu abin da suka ga dama da sunan asusun haɗin gwuiwa. A tsarin
kason arziƙin ƙasa, ƙananan hukumomi su suke da kaso 21%, jihohi na da 30%, ita
kuwa Gwamnatin Tarayya take da 49%. Misali,
bayanan da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta wallafa a shafukan jaridun ƙasarnan
cikin satattakin da suka gabata sun nuna cewar an rarraba kuɗaɗe masu yawan
Naira Biliyan N923,881,185,187.63 a tsakanin gwamnatocin ƙasa a watan Yunin
2015 waɗanda aka fitar da bayanansu a ƙarshen watan Julin 2015. A wannan
kasafi, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 419.3, Gwamnatocin Jihohi 36 sun samu Naira Biliyan 254.3, Gwamnatocin ƙananan
hukumomi 774 sun samu Naira Biliyan 179.6. To amma kason ƙananan hukumomi ya na shiga ne ta asusunsu na
haɗin gwuiwa da jihohi, wanda kuma a mafi yawan lokuta jihohin ba sa basu. A wasu lokutan wasu jihohin masu ɗan
adalci su kan hanasu kuɗaɗen amma sai su yi musu aiyuka da kuɗin, yayin da wasu
kuwa su kan hanasu kuɗin da aikin bakiɗaya, sai su ɗebi kuɗin su yi aikin jiha
da su, duk da cewar su ma jihohin suna da nasu kason daga Gwamnatin Tarayya.
Wannan ya haifar wa da ƙananan
hukumomi rauni ba kaɗan ba da kuma shiga wani yanayi na rashin tabbas da rashin
makoma. Saboda rashin kuɗi, ƙananan hukumomi ba sa iya gudanar da mafi yawan aiyukan
da aka ɗora musu su aiwatar.
Babbar matasala ta uku da take
damun ƙananan hukumomi itace almundahana da cuta. Bahaushe kan ce wai idan ɓera da
sata, to daddawa ita ma da wari. Shugabanni da ma’aikatan ƙananan hukumomin Najeriya sun
yi ƙaurin suna wajen tafka almundahana da kuɗaɗen
al’umma. A lokutan da jihohin suka sakar
musu kuɗaɗensu, sai a nemi aiyukan da suka yi da kuɗin a rasa, maimakon haka
sai dai a ga ciyamomi da kansiloli da manyan ma’aikatan ƙananan hukumomi suna
wadaƙa da kuɗaɗe, suna gina manyan gidaje tare da yin buƙatun da ko yaro ƙarami
ya san sun fi ƙarfin albashi da alawus-alawus ɗinsu. Wata matsalar ta
su ƙananan hukumomin kuwa ita ce ta sakaci da wasa da aiki. Sai ka ziyarci ma’aikatun ƙananan
hukumomi sau shurin masaƙi a ranakun aiki amma ba za ka tarar da mafi yawan
ma’aikata ba. Shi kansa ciyaman da kansiloli ba sa zuwa sai sun ga dama. A mafi
yawan lokuta ba sa zuwa sai ƙarshen wata lokacin da aka turo kuɗi.
Yanzu dai ƙananan hukumomi a Najeriya
sun zamo ƙadangaren bakin tulu, a kashesu a kar tulu, a bar su, su ɓata ruwa.
Idan aka ce za a soke su, to tabbas za a raba talaka da gwamnati mafi kusa da
shi kuma mahukunta za su ƙara yin nesa da talaka. Komai lalacewarsu dai, akwai amfanin
da suke yi wa talaka na ƙasa. Bayan haka ‘yan ƙananan aiyuka masu amfanar
unguwanni da garuruwa da ƙananan hukumomin su kan yi duk za a yi asararsu domin
ba zai yiwu gwamnatocin jihohi da ta tarayya su samu damar shiga kowanne lungu
da saƙo ba.
Idan kuma aka ce za a bar ƙananan
hukumomi su ci gaba da wanzuwa, to fa waɗancan matsaloli ba za a rabu da su ba,
wataƙila ma sai dai in ba ayi wasa ba su ci gaba da ƙaruwa. Tarin kuɗaɗen da
ake turowa ƙananan hukumomi domin amfanin talaka za su cigaba da zurarewa a
banza da hofi. A shekarar 2003, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Cif Olusegun Obasanjo
ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari a kan makomar ƙananan hukumomi, amma sai
‘yan Najeriya su ka ƙi bai wa yunƙurin goyon baya domin a zaton su Obasanjo
kawai so ya ke ya ruguje ƙananan hukumomin domin Gwamnatin tarayya ta dinga riƙe
kasonsu.
Abu na farko da ya kamata a yi
domin magance waɗannan matasloli, shi ne Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kafa
wani kwamiti makamancin irin na Obasanjo, wanda zai ƙunshi wakilan ta da na
Fadar Shugaban ƙasa, wakilan ƙungiyar gwamnonin Najeriya NGF, wakilan ƙungiyar Kakakan
majalisun dokokin jihohi ta ƙasa, wakilan ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi
ta ALGON, wakilan majalisun dattawa da ta tarayya ta ƙasa, wakilan ƙungiyar ma’aikatan
ƙananan hukumomi ta NULGE, wakilan ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC da kuma wakilan ƙungiyoyin kare manufofin ci
gaba domin lalubo bakin zaren wannan matsaloli. Bayan nan majalisun dattawa da
na tarayya sai su yi wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa gyara domin ya dace da ƙudurce-ƙudurcen
da aka cimma a wancan kwamiti na farfaɗo da ƙananan hukumomi.
Kafin nan kuma kamata ya yi
gwamnonin jihohi
su yi wa kansu
faɗa, su dubi Allah, su dubi talaka, su dinga bai wa ƙananan
hukumomi haƙƙoƙinsu kuma su ƙyalesu su yi aikinsu,
su kuma a nasu
ɓangaren, ciyamomi, kansiloli da ma’aikatan ƙananan hukumomi su yi wa Allah su
gyara halayensu.
Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez