Fassara

Tuesday, September 1, 2015

Mecece Makomar ƙananan Hukumomin Najeriya?

3 Ga Satumba, 2015


Daga: Amir Abdulazeez

T
arihin ƙananan hukumomi a ƙasarnan ya samo asali ne tun kusan daga lokacin da Turawan Ingila suka haɗa gundumar Arewaci da Kudancin Najeriya domin samar da ƙasa ɗaya. Tun a wancan lokaci Turawa suka samar da shiyyoyin mulkin mallaka a ƙarkashin tsarin mulki wanda ba na kai tsaye ba na Native Authorities wanda ya bai wa sarakuna damar yin mulki mai taƙaitaccen iko ga yankunansu kafin daga baya a tsame sarakunan su kansu daga mulkin kacokam. Gwamnatoci daban-daban sun sha yi wa tsare-tsaren ƙananan hukumomi gyare-gyare da kwaskawarima tare da ƙarawa da rage adadin yawansu har sau tara daga 1914 zuwa 1999. Tasrin ƙananan hukumomi kamar yadda muka sansu a yanzu ya samu ne daga sauye-sauyen da aka gudanar a shekarun 1976, 1979, 1984, 1988, 1989 da 1999.

Duk da cewar gwawnatocin jihohi daban-daban sun yi yunƙure-yunƙure daga shekarar 2000 zuwa 2007 na ganin sun ƙara yawan ƙananan hukumomi a jihohinsu, har yanzu dai adadin yawan ƙananan hukumomi guda 774 ne kamar yadda ya ke a Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na shekarar 1999. To amma kuma akwai jihohin da bayan ƙananan hukumomin su, sun ƙirƙiri ƙananan  gundumomin mulki da samar da ci gaba masu kama da ƙananan hukumomin. Misali, Jihar Lagos ta na da ƙananan hukumomi 22 amma ta na da irin waɗannan gundumomi waɗanda ita take samar musu da kuɗaɗen gudanarwa har guda 37. Akwai irin waɗannan gundumimi a jihohin Yarabawa sosai.

Fahimtar kusan kowa ita ce an ƙirƙiri ƙananan hukumomi domin matso da gwamnati kusa da talaka. Bayan haka, akwai ƙayadaddun aiyuka da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa na 1999 ya tanadar musu. Muhimman aiyukan sune bayar da shawarwari da za su inganta tattalin arziƙin gwamnatin jiha; samar da maƙabartu da gidajen kula da marasa galihu; bayar da lasisin kekuna, kwale-kwale da kurar turawa ta ɗaukar kaya; kafawa tare da gudanar da mayanku, kasuwanni, tashoshin mota da gidajen wanka; gina ƙananan  tituna, layuka, saka fitlun kan titi da fitar da magudanar ruwa; bai wa tittuna da layuka sunaye da yi wa gidaje lamba; kwashe shara da kwatoci; yin rajistar haihuwa da ta mutuwa. Bayan haka an sanya ƙananan hukumomi  su zamo masu taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen bayar da ilimin firamare, ilimin manya da ilimin koyon sana’o’i; bunƙasa noma da kuma yin dukkan wasu aiyuka da Majilusun Dokokin Jihohi suka kallafa musu.

Sai dai kuma duk da waɗannan ɗinbin aiyuka da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora wa ƙananan hukumomi, kuma bai basu damar cin cikakken gashin kansu ba. A ƙarƙashin sashe na II, ƙananan  sassan 7(1), (2) da (3), Kundin Tsarin  Mulkin ya nuna cewar gwamnatocin jihohi su zasu samar da dokokin da zasu tabbatar da wanzuwa, tsari, aiyuka da kuma kashe kuɗaɗen waɗannan ƙananan hukumomi. Wannnan ya nuna cewa rayuwarsu kusan kacokam ta na hannun jihohi. Wannan kusan ita ce a yanzu babbar matsalar da take damun ƙananan hukumomi.

Kafin dawowar dimokraɗiyya a 1999 har zuwa farkon dawowar ta, a kan ji ɗuriyar ƙananan hukumomi suna ɗan taɓuka aiyukan raya ƙasa duk da cewa akwai manyan matsaloli da suke fama da su tun a wancan lokaci. Amma yanzu kusan gwamnatocin jihohi sun kalmashe su, ba ma a jin ɗuriyarsu, a wasu jihohin ma kamar babu su.

Babbar matsala ta farko da take damun ƙananan hukumomi a yanzu ita ce ta tsarin zaɓar shugabanninsu. Tun bayan shekarar 1999 inda aka gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin Najeriya bai ɗaya, har yanzu ba a samu ingantattun zaɓuka a mafi yawan ƙananan hukumomi ba. Duk jam’iyyar da take mulki a wata jihar, ta kan tabbatar da cewa ta lalata tsarin zaɓen ta yadda za ta cinye 100% na zaɓukan ciyamomi da kansiloli. Gwamnoni su kan yi amfani da hukumomin zaɓen jihohi wajen shirya gurɓatattun zaɓuka a ƙananan hukumomi wanda dama tun farko dalilai na siyasa ba sa bari a samar da ingantattun ‘yan takara tun da farko. Wasu jihohin ba ma sa yin zaɓen kwata-kwata sai sun ga dama, sai dai gwamnoni su naɗa kantomomi. A Jihar Anambra an taɓa kwashe shekaru 13 daga 2002 har zuwa 2014 ba a yi zaɓukan ƙananan hukumomi ba. Wata ƙarin matsalar kuma ta wannan fuskar ita ce, Majalisun Dokoin Jihohi da dokar ƙasa ta bai wa alhakin kula da ƙananan hukumomin tare da basu kariya sun zuba ido sun kasa kataɓus yayin da gwamnoni suke ta cin karensu ba babbaka a kan ƙananan hukumomi.

Babbar matsala ta biyu da take damun ƙananan hukumomi ita ce rashin basu kuɗaɗensu da gwamnoni suke yi. Kusan yanzu ya zama ruwan dare a kowacce jiha, idan kuɗin ƙananan hukumomi sun zo daga Gwamnatin Tarayya, sai jihohi su danne su hanasu ko kuma su tsakurar musu abin da suka ga dama da sunan asusun haɗin gwuiwa. A tsarin kason arziƙin ƙasa, ƙananan hukumomi su suke da kaso 21%, jihohi na da 30%, ita kuwa Gwamnatin Tarayya take da 49%.  Misali, bayanan da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta wallafa a shafukan jaridun ƙasarnan cikin satattakin da suka gabata sun nuna cewar an rarraba kuɗaɗe masu yawan Naira Biliyan N923,881,185,187.63 a tsakanin gwamnatocin ƙasa a watan Yunin 2015 waɗanda aka fitar da bayanansu a ƙarshen watan Julin 2015. A wannan kasafi, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 419.3, Gwamnatocin Jihohi 36  sun samu Naira Biliyan 254.3, Gwamnatocin ƙananan hukumomi 774 sun samu Naira Biliyan 179.6. To amma kason  ƙananan hukumomi ya na shiga ne ta asusunsu na haɗin gwuiwa da jihohi, wanda kuma a mafi yawan lokuta jihohin  ba sa basu. A wasu lokutan wasu jihohin masu ɗan adalci su kan hanasu kuɗaɗen amma sai su yi musu aiyuka da kuɗin, yayin da wasu kuwa su kan hanasu kuɗin da aikin bakiɗaya, sai su ɗebi kuɗin su yi aikin jiha da su, duk da cewar su ma jihohin suna da nasu kason daga Gwamnatin Tarayya.

Wannan ya haifar wa da ƙananan hukumomi rauni ba kaɗan ba da kuma shiga wani yanayi na rashin tabbas da rashin makoma. Saboda rashin kuɗi, ƙananan hukumomi ba sa iya gudanar da mafi yawan aiyukan da aka ɗora musu su aiwatar.

Babbar matasala ta uku da take damun ƙananan hukumomi itace almundahana da cuta. Bahaushe kan ce wai idan ɓera da sata, to daddawa ita ma da wari. Shugabanni da ma’aikatan ƙananan hukumomin Najeriya sun yi ƙaurin suna wajen tafka almundahana da kuɗaɗen al’umma.  A lokutan da jihohin suka sakar musu kuɗaɗensu, sai a nemi aiyukan da suka yi da kuɗin a rasa, maimakon haka sai dai a ga ciyamomi da kansiloli da manyan ma’aikatan ƙananan hukumomi suna wadaƙa da kuɗaɗe, suna gina manyan gidaje tare da yin buƙatun da ko yaro ƙarami ya san sun fi ƙarfin albashi da alawus-alawus ɗinsu. Wata matsalar ta su ƙananan hukumomin kuwa ita ce ta sakaci da wasa da aiki. Sai ka ziyarci ma’aikatun ƙananan hukumomi sau shurin masaƙi a ranakun aiki amma ba za ka tarar da mafi yawan ma’aikata ba. Shi kansa ciyaman da kansiloli ba sa zuwa sai sun ga dama. A mafi yawan lokuta ba sa zuwa sai ƙarshen wata lokacin da aka turo kuɗi.

Yanzu dai ƙananan hukumomi a Najeriya sun zamo ƙadangaren bakin tulu, a kashesu a kar tulu, a bar su, su ɓata ruwa. Idan aka ce za a soke su, to tabbas za a raba talaka da gwamnati mafi kusa da shi kuma mahukunta za su ƙara yin nesa da talaka. Komai lalacewarsu dai, akwai amfanin da suke yi wa talaka na ƙasa. Bayan haka ‘yan ƙananan aiyuka masu amfanar unguwanni da garuruwa da ƙananan hukumomin su kan yi duk za a yi asararsu domin ba zai yiwu gwamnatocin jihohi da ta tarayya su samu damar shiga kowanne lungu da saƙo ba.

Idan kuma aka ce za a bar ƙananan hukumomi su ci gaba da wanzuwa, to fa waɗancan matsaloli ba za a rabu da su ba, wataƙila ma sai dai in ba ayi wasa ba su ci gaba da ƙaruwa. Tarin kuɗaɗen da ake turowa ƙananan hukumomi domin amfanin talaka za su cigaba da zurarewa a banza da hofi. A shekarar 2003, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Cif Olusegun Obasanjo ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari a kan makomar ƙananan hukumomi, amma sai ‘yan Najeriya su ka ƙi bai wa yunƙurin goyon baya domin a zaton su Obasanjo kawai so ya ke ya ruguje ƙananan hukumomin domin Gwamnatin tarayya ta dinga riƙe kasonsu.

Abu na farko da ya kamata a yi domin magance waɗannan matasloli, shi ne Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kafa wani kwamiti makamancin irin na Obasanjo, wanda zai ƙunshi wakilan ta da na Fadar Shugaban ƙasa, wakilan ƙungiyar gwamnonin Najeriya NGF, wakilan ƙungiyar Kakakan majalisun dokokin jihohi ta ƙasa, wakilan ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ALGON, wakilan majalisun dattawa da ta tarayya ta ƙasa, wakilan ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta NULGE, wakilan ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC  da kuma wakilan ƙungiyoyin kare manufofin ci gaba domin lalubo bakin zaren wannan matsaloli. Bayan nan majalisun dattawa da na tarayya sai su yi wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa gyara domin ya dace da ƙudurce-ƙudurcen da aka cimma a wancan kwamiti na farfaɗo da ƙananan hukumomi.

Kafin nan kuma kamata ya yi gwamnonin jihohi su yi wa kansu faɗa, su dubi Allah, su dubi talaka, su dinga bai wa ƙananan hukumomi  haƙƙoƙinsu kuma su ƙyalesu su yi aikinsu, su kuma a nasu ɓangaren, ciyamomi, kansiloli da ma’aikatan ƙananan hukumomi su yi wa Allah su gyara halayensu.

Shafin Mallam Amir a Twitter shine: @AmirAbdulazeez  

No comments:

Post a Comment