12 Ga Fabrairu, 2016.
Daga: Amir Abdulazeez
T
|
un bayan gama Yaƙin Duniya na Biyu a shekarar 1945 tare da bayyanar ƙasashen
Amurka da Rasha a matsayin mafi ƙarfin-faɗa-a-ji a duniya, Dalar Amurka ta fara
kuma take ci gaba da gauraye duniya. Lokacin kuwa da yaƙin cacar baki wanda aka
fi sani da Cold War tsakanin ƙasashen
Rasha da Amurkar ya zo ƙarshe a shekarar 1991 tare da bayyanar ƙasar Amurka a
matsayin ƙasa ɗaya tilo mafi ƙarfi a duniya, tuni Dalar Amurka ta game ko’ina a
faɗin duniya; ta zama takardar kuɗi ta ƙasa da ƙasa, sannan kuma ma’aunin
darajar sauran kuɗaɗen ƙasashen duniya. Kodayake takardar kuɗi ta Euro wanda ake amfani da ita a Nahiyar
Turai da Pound Serling to Ingila sun
fi ta daraja ta fuskar tsada, amma basu ko kama ƙafar ta ba wajen hada-hada da
karɓuwa ba.
Ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Yakubu Gowon ta ɗauka tun
bayan kammala yaƙin basasa shine na ƙirƙiro da takardar kuɗi ta Naira a
shekarar 1973. Kafin wannan lokacin, Najeriya tana amfani ne da takardar Pound Sterling ta Africa ta Yamma wacce
take da kwatankwacin daraja ɗaya da Pound
Sterling ta Birtaniya a wancan lokaci, kusan ma babu wani bambanci
tsakaninsu. Ita kanta Nairar da aka ƙirƙiro daga baya, kusan darajar su ɗaya da
Pound Sterling ta birtaniya, har
akwai lokutan ma da ta ɗara ta a daraja a lokutan da aka fuskanci tsadar ɗanyen
man fetur wanda Najeriya take kan ganiyar haƙowa a wancan lokaci. A tsakanin
shekarun 1978 zuwa 1982, akwai lokacin da sai mutum ya bayar da Dalar Amurka
biyu sannan za a bashi Naira ɗaya; ma’ana, Naira ta ninka Dala a daraja a
wancan lokaci.
Duk da zargin karya tattalin arziƙi da sojoji suka yi wa gwamnatin Shugaba
Shehu Shagari, amma har ya bar mulki ana canza kowacce Dalar Amurka ɗaya a kan
tsakanin Naira ɗaya zuwa ƙasa da haka. Lokacin da Janar Babangida ya yi wa Janar
Buhari juyin mulki, ana canzar kowacce Dalar Amurka ɗaya a kan Naira ɗaya zuwa
biyu. A lokacin Babangida ne, Najeriya ta rungumi tsarin gudanar da tattalin
arziƙi na Hukumar Bayar da Lamunin Kuɗi ta Duniya (IMF) tare kuma da karɓar
maƙudan kuɗaɗe a matsayin rance daga wannan hukuma. Wannan tsari da Babangida
ya kawo wanda aka fi sani da SAP, tsarin da tun da farko ya kasa samun shiga a
gurin gwamnatin Janar Buhari, shi masana da dama suke ganin ya jefa Najeriya a
cikin mawuyacin halin tattalin arziƙin da har yanzu bata farfaɗo ba. Bayan ‘yan
wasu lokuta da kankamar tsarin SAP, a shekarar 1991, Dalar Amurka ɗaya sai ta
koma Naira goma. Lokacin da Babangida ya tafi a 1993, tuni Dalar Amurka guda ɗaya
ta koma tsakanin N22 zuwa N57, ya danganta da alƙaluman gwamnati ko
na ‘yan canji. Dalar Amurka ta dinga hawa ba ƙaƙƙautawa a hannun gwamnati da
‘yan canji tun daga lokacin Shugaba Abdussalmi har zuwa lokacin Mulkin Shugaba
Jonathan inda ta zama N86, N100, N140
har sama da haka. A yau Dalar Amurka ɗaya a hukumance, ana canzar ta ne a kan N197,
a hannun ‘yan kasuwa kuwa tana kaiwa N310
zuwa N315. Babu wata lalacewa ko taɓarɓarewa
da za a iya kwatantata da wannan.
Kafin a san magani, ya kamata a fahimci cuta tukunna. Duk da cewar mafi
yawan ‘yan Najeriya suna ɗora alhakin faɗuwar darajar Naira da taɓarɓarewar
tattalin arziƙi a kan tsarin SAP na turawan yamma da Shugaba Babangida da Ministan
harkokin kuɗinsa na wancan lokacin, Cif Olu Falae, to amma ya kamata mu kalli
wasu dalilan da dama bayan wannan. Tun daga shekarar 1973 zuwa 2016, kowanne ɗan
ƙasa ya bada gudunmawarsa wajen lalacewar darajar Naira. Akwai laifin gwamnati,
shugabanni, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ma’aikata da kuma talakawa.
Tun farko dai ƙasashen Afrika ciki har da Najeriya da kuma sauran dukkan
ƙasashe masu tasowa sun tafka babban kuskure wajen tunanin cewar ƙasashen
Turawa masu ƙarfin tattalin arziƙi zasu ji tausayinsu ko kuma zasu kawo wani
tsari wanda zai taimakesu tsakani da Allah ba tare da wani kitso da kwarkwata
ba. Kullum hasashen irin waɗancan ƙasashe shine ya za a yi mu dauwama a ƙasa,
su suna sama, to ta yaya zasu bamu wani taimako nagari? Ci gaba da taɓarɓarewarmu,
ita ce ci gaba da bunƙasarsu; idan muka zama iyayen gidan kanmu, wa zasu mulka
balle har su yi masa fankama? Kullum burinsu su dinga tsakuro tallafi suna bamu
kamar almajirai ko kuma su bamu rancen maƙudan kuɗuɗe domin mayar damu bayin
ƙarfi da yaji. Ƙasashe irinsu China, India da Brazil da suka farga tun da wuri
suka yi watsi da dogaro a kan Turawa, yau sun tsaya kai da fata sun ciyar da
kansu gaba, kuma sun fita daga ƙangin bauta. A yau ƙananan ƙasashe da dama sun
haramtawa kansu amfani da kayayyakin Turawan Yamma domin bunƙasa nasu na gida Dole
ne Najeriya ta kama hanyar bin sahun waɗannan ƙasashe koda kuwa a faro zamu sha
baƙar wahala kafin mu murmure.
Tsawon shekaru da yawa, Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin shugabanni
daban-daban sun ƙyale ƙasar ta dogara da ɗanyen man fetur ba tare da ta maida
hankali a kan noma, kiwo da bunƙasa
masana’antu ba. Wannan ta jawo, babu wata muhimmiyar hanya da kuɗaɗen ƙasar
waje suke shigo mana sai ta hanyar ɗanyen man fetur, kuma gashi tataccen fetur ɗin
sai mun fita wata uwa duniya mun sayo shi tunda mun bar namu matatun a lalace,
hakan ya kawo faɗuwar darajar Naira, musamman a yanzu da farashin ɗanyen man ya
faɗi wanwar a kasuwar duniya. Bayan haka
kuma, gwamnatoci da yawa da suka shuɗe basu tashi tsaye sun ɗauki takardar Nairar
ita kanta da muhimmanci ba balle su kare ta. Ana zargin da yawa daga cikin
shugabannin Najeriya da ‘yan siyasarta da wawushe kuɗin ƙasa, kuma abin
takaici, maimakon su ajiye su a Najeriya ko kuma su zuba hannun jarin a Najeriya,
a’a sai su ɗebi kuɗin su ajiye su a ƙasashen waje. Daga 1999 zuwa 2015, Allah
ne kaɗai ya san iya dukiyar da ɓarayi daga cikin shugabannin Najeriya,
ma’aikata da ‘yan siyasa suka sata suka kai ƙasar waje, wannan ya taimaka wajen
karya tattalin arziƙin ƙasa da kuma karya darajar Naira.
Sana’ar canji, wacce kwata-kwata da ba a san da ita ba a Najeriya sai daga
baya ta taka rawa wajen lalata darajar Naira duk da cewar kuma ta taimaka wajen
sauƙaƙa samun kuɗaɗen ƙasashen waje tare kuma da samar da sana’a ga mutane da
dama. Babbar matsalar ita ce, su ‘yan canji riba ce zalla kuma tsababa kawai a
gabansu ba wai makomar darajar Naira ko kishin ƙasa ba. Wannan ce ta kawo
lalacewar sana’ar canji kuma a maimakon ta zamo mataimakiya wajen kare martabar
Naira, zai ta zamo wata hanyar da ake amfani da ita wajen kassara Nairar tare
da ɗaukaka darajar kuɗaɗen ƙasashen waje domin kawai a ci riba. Bayan haka
kuma, wasu mutane suna yin amfani da harkar canji ko kuma ‘yan canjin wajen karɓo
kuɗaɗen ƙasashen waje a hannun gwamnati kuma su ɓoyesu ko kuma su yi amfani dasu
ta hanyoyin da zasu cutar da tattalin arziƙin ƙasa. Dole sai an tsaftace tare da yin
garanbawul ga wannan sana’a idan har ana so a samu farfaɗowar darajar Naira.
Mafi yawan ‘yan kasuwarmu, kullum tunaninsu shine su fita ƙasar waje su
sayo kaya, a maimakon su maida hankali wajen samar da fasahar ƙera kayan a nan
gida Najeriya da kansu. Kusan kowa yafi son daga-buhu-sai-tukunya, kawai ya
sayo kaya ya sayar ya ci riba a karan kansa, koda ƙasar za ta mutu. Bugu da
ƙari kuma, mafi yawan ‘yan kasuwar basa biyan haraji balle gwamnati ta ɗan ƙaru
da wani abu. Wannan tasa mun wayi gari kusan komai da muke amfani da shi, shigo
dashi ake daga ƙasar waje, hatta tsinken sakace. Mu kusan babu mai shigowa ya
sayi namu kayan, amma kullum muna kan hanya wajen sayo kayan wasu; wannan ta
taimaka wajen faɗuwar darajar Naira. Mafi yawan ‘yan Najeriya babu kishin ƙasa
a gabansu, kowa burinsa kawai ya gamsar da kansa ko ya biya buƙatarsa, babu
ruwansa da makomar ƙasa. Wannan ita tasa mafi yawancin mutane, burinsu su sayi
kayayyakin ƙasashen waje, a dalilin haka
ne ma kayayyakin da aka sana’anta a Najeriya suke yin kwantai kuma waɗanda suke
yinsu suke watsarwa suna koma sayo na ƙasar waje. Kullum tunaninmu wai kayan ƙasar
waje yafi kyau, to ta yaya namun zai yi kyau, idan bama saya? Munata rage wa
kanmu ƙarfi muna ƙarawa masu ƙarfi ƙarfi; wannan ta kawo faɗuwar darajar Naira.
Idan da barci muke , to ya kamata yanzu mu farka. Takardar kuɗin ƙasa wata
aba ce mai martaba da ƙima wacce take nuna irin darajar tattalin arziƙi da kuma
darajar ƙasar ita kanta. Yanzu Naira ta hau kan wata turbar taɓarɓarewar da ba
a taɓa gani ba kuma idan muka zuba ido cewar gwamnati ce kaɗai za ta gyara ta,
to kuwa zamu sha mamaki. Idan muka yi wasa sai mun wayi gari Naira ta koma bata
da amfanin komai sai zubarwa. Duk da cewar wannan matasala ta kwararo a cikin
shekaru sama da 40 baya, amma idan muka haɗu a kan manufar kawo gyara, to Naira
zata farfaɗo ko da kuwa ba yanzu yanzu ba.
Tun da farko dai dole gwamnati ta maida hankali a kan harkar noma tare da
samar da isasshiyar wutar lantarkin da
zata bai wa masana’antu dama domin su farfaɗo su dinga aiki ka’in da
na’in. Banda haka, dole ne a tsaurara matakan ladabtarwa a kan masu satar
dukiyar ƙasa suna zuba hannun jari a ƙasashen
waje. Dole ne gwamnati ta zage damtse wajen dawo da dukkan kuɗaɗen Najeriya da
aka sace daga ƙasashen waje. Kodayake Turawan yamma da sauran wasu ƙasashe baza
su so a janye wannan ɗimbin dukiya wadda take ƙarawa tattalin arziƙinsu ƙarfi
ba, amma wannnan ya zama dole in har muna so mu cigaba. Bayan haka, idan
gwamnati tana so ‘yan Najeriya su sayi kayayyakin da aka ƙera acikin ƙasar, to
sai ta zamo abin koyi. Dukkan abin da zata saya, ita ma ta dinga sayen na cikin
gida kuma ta rage bai wa kamfanunuwan ƙasashen waje kwangila sai ya zama dole.
Bayan haka ta duba yiwuwar kafa dokar hana shigo da rukunin wasu kayayyakin da
za a iya ƙerawa a nan gida ko kuma ta sanya haraji mai tsanani a kansu.
Dolene ‘yan siyasarmu, musamman na 1999 zuwa 2015 su karɓi alhakin ɗaiɗaita
mana tattalin arziƙi da jefamu a cikin mawuyacin halin da muke ciki da suka yi.
Wajibine a kawo ƙarshen siyasar kuɗi domin guje wa ɓarnatar da dukiyar ƙasa.
Yanzu ‘yan siyasarmu saboda tsananin rashin kishin ƙasa, idan zaɓe ya matso,
duk wata Dalar Amurka da manyan kuɗaɗen ƙasashen waje dake cikin Najeriya sai
sun sayesu domin su saya ko su ƙwaci zaɓe, saboda suna so su dauwama a kan
mulki, alabashi ita kuma ƙasa taje can ta shiga halin da zata shiga babu
ruwansu. Naira ta yi musu rashin daraja da yawa, don haka Daloli suke rarrabawa
domin su ba sai an yi kayansu ba niƙi-niƙi. Dalolin da ya kamata a sayar wa da
‘yan kasuwa domin su saro kaya, ‘yan siyasa da masu mulki duk sun sayesu; wacce
take hannun gwamnatinma kuma sun yi amfani da alfarmarsu sun saye, a wasu
lokutanma sun sace su kai tsaye. Ta
yaya Naira ba zata lalace ba?
Wajibi ne ‘yan kasuwar mu su haɗu a kan yadda zasu dinga ƙera kaya da kansu a maimakon sayosu
daga ƙasashen waje. Babu shakka, wannan wani abu ne mai wahala, amma idan suka
sa kansu zasu iya, kuma a kwana a tashi, zasu saba har su zama ƙwararru. Yanzu
ga Aliko Dangote nan, ai bai zama mai kuɗin Africa baki ɗaya ta hanyar shigo da
simiti ba, ya zama ne ta hanyar sana’antashi ya fitar zuwa wasu ƙasashe ko kuma
a biyoshi har inda yake a saya. Mu kuma talakawa da mafi yawan masifa take ƙarewa
a kanmu, mu yafi kamata ma mu tashi tsaye. Kowa ya yi duba na tsanaki a kan
kansa ya ga
shin yana sayen kayan da aka ƙera a Najeriya?
Idan akwai abin da ake ƙerawa a Najeriya, to ka ƙyale na ƙasar waje. Idan kana ganin na ƙasar
wajen yafi na gida kyau, to sayensa da kake yi ne yasa yafi na gidan kyau, idan
ka koma sayen naka, shima zai yi ingancin da watarana zai fi na ƙasar wajen.
No comments:
Post a Comment