Fassara

Friday, February 12, 2016

Ta Yaya Zamu Farfaɗo da Darajar Naira?

12 Ga Fabrairu, 2016.




T
un bayan gama Yaƙin Duniya na Biyu a shekarar 1945 tare da bayyanar ƙasashen Amurka da Rasha a matsayin mafi ƙarfin-faɗa-a-ji a duniya, Dalar Amurka ta fara kuma take ci gaba da gauraye duniya. Lokacin kuwa da yaƙin cacar baki wanda aka fi sani da Cold War tsakanin ƙasashen Rasha da Amurkar ya zo ƙarshe a shekarar 1991 tare da bayyanar ƙasar Amurka a matsayin ƙasa ɗaya tilo mafi ƙarfi a duniya, tuni Dalar Amurka ta game ko’ina a faɗin duniya; ta zama takardar kuɗi ta ƙasa da ƙasa, sannan kuma ma’aunin darajar sauran kuɗaɗen ƙasashen duniya. Kodayake takardar kuɗi ta Euro wanda ake amfani da ita a Nahiyar Turai da Pound Serling to Ingila sun fi ta daraja ta fuskar tsada, amma basu ko kama ƙafar ta ba wajen hada-hada da karɓuwa ba.

Ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Yakubu Gowon ta ɗauka tun bayan kammala yaƙin basasa shine na ƙirƙiro da takardar kuɗi ta Naira a shekarar 1973. Kafin wannan lokacin, Najeriya tana amfani ne da takardar Pound Sterling ta Africa ta Yamma wacce take da kwatankwacin daraja ɗaya da Pound Sterling ta Birtaniya a wancan lokaci, kusan ma babu wani bambanci tsakaninsu. Ita kanta Nairar da aka ƙirƙiro daga baya, kusan darajar su ɗaya da Pound Sterling ta birtaniya, har akwai lokutan ma da ta ɗara ta a daraja a lokutan da aka fuskanci tsadar ɗanyen man fetur wanda Najeriya take kan ganiyar haƙowa a wancan lokaci. A tsakanin shekarun 1978 zuwa 1982, akwai lokacin da sai mutum ya bayar da Dalar Amurka biyu sannan za a bashi Naira ɗaya; ma’ana, Naira ta ninka Dala a daraja a wancan lokaci.

Duk da zargin karya tattalin arziƙi da sojoji suka yi wa gwamnatin Shugaba Shehu Shagari, amma har ya bar mulki ana canza kowacce Dalar Amurka ɗaya a kan tsakanin Naira ɗaya zuwa ƙasa da haka. Lokacin da Janar Babangida ya yi wa Janar Buhari juyin mulki, ana canzar kowacce Dalar Amurka ɗaya a kan Naira ɗaya zuwa biyu. A lokacin Babangida ne, Najeriya ta rungumi tsarin gudanar da tattalin arziƙi na Hukumar Bayar da Lamunin Kuɗi ta Duniya (IMF) tare kuma da karɓar maƙudan kuɗaɗe a matsayin rance daga wannan hukuma. Wannan tsari da Babangida ya kawo wanda aka fi sani da SAP, tsarin da tun da farko ya kasa samun shiga a gurin gwamnatin Janar Buhari, shi masana da dama suke ganin ya jefa Najeriya a cikin mawuyacin halin tattalin arziƙin da har yanzu bata farfaɗo ba. Bayan ‘yan wasu lokuta da kankamar tsarin SAP, a shekarar 1991, Dalar Amurka ɗaya sai ta koma Naira goma. Lokacin da Babangida ya tafi a 1993, tuni Dalar Amurka guda ɗaya ta koma tsakanin N22 zuwa N57, ya danganta da alƙaluman gwamnati ko na ‘yan canji. Dalar Amurka ta dinga hawa ba ƙaƙƙautawa a hannun gwamnati da ‘yan canji tun daga lokacin Shugaba Abdussalmi har zuwa lokacin Mulkin Shugaba Jonathan inda ta zama N86, N100, N140 har sama da haka. A yau Dalar Amurka ɗaya a hukumance, ana canzar ta ne a kan N197,  a hannun ‘yan kasuwa kuwa tana kaiwa N310 zuwa N315. Babu wata lalacewa ko taɓarɓarewa da za a iya kwatantata da wannan.

Kafin a san magani, ya kamata a fahimci cuta tukunna. Duk da cewar mafi yawan ‘yan Najeriya suna ɗora alhakin faɗuwar darajar Naira da taɓarɓarewar tattalin arziƙi a kan tsarin SAP na turawan yamma da Shugaba Babangida da Ministan harkokin kuɗinsa na wancan lokacin, Cif Olu Falae, to amma ya kamata mu kalli wasu dalilan da dama bayan wannan. Tun daga shekarar 1973 zuwa 2016, kowanne ɗan ƙasa ya bada gudunmawarsa wajen lalacewar darajar Naira. Akwai laifin gwamnati, shugabanni, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ma’aikata da kuma talakawa.

Tun farko dai ƙasashen Afrika ciki har da Najeriya da kuma sauran dukkan ƙasashe masu tasowa sun tafka babban kuskure wajen tunanin cewar ƙasashen Turawa masu ƙarfin tattalin arziƙi zasu ji tausayinsu ko kuma zasu kawo wani tsari wanda zai taimakesu tsakani da Allah ba tare da wani kitso da kwarkwata ba. Kullum hasashen irin waɗancan ƙasashe shine ya za a yi mu dauwama a ƙasa, su suna sama, to ta yaya zasu bamu wani taimako nagari? Ci gaba da taɓarɓarewarmu, ita ce ci gaba da bunƙasarsu; idan muka zama iyayen gidan kanmu, wa zasu mulka balle har su yi masa fankama? Kullum burinsu su dinga tsakuro tallafi suna bamu kamar almajirai ko kuma su bamu rancen maƙudan kuɗuɗe domin mayar damu bayin ƙarfi da yaji. Ƙasashe irinsu China, India da Brazil da suka farga tun da wuri suka yi watsi da dogaro a kan Turawa, yau sun tsaya kai da fata sun ciyar da kansu gaba, kuma sun fita daga ƙangin bauta. A yau ƙananan ƙasashe da dama sun haramtawa kansu amfani da kayayyakin Turawan Yamma domin bunƙasa nasu na gida Dole ne Najeriya ta kama hanyar bin sahun waɗannan ƙasashe koda kuwa a faro zamu sha baƙar wahala kafin mu murmure.

Tsawon shekaru da yawa, Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin shugabanni daban-daban sun ƙyale ƙasar ta dogara da ɗanyen man fetur ba tare da ta maida hankali  a kan noma, kiwo da bunƙasa masana’antu ba. Wannan ta jawo, babu wata muhimmiyar hanya da kuɗaɗen ƙasar waje suke shigo mana sai ta hanyar ɗanyen man fetur, kuma gashi tataccen fetur ɗin sai mun fita wata uwa duniya mun sayo shi tunda mun bar namu matatun a lalace, hakan ya kawo faɗuwar darajar Naira, musamman a yanzu da farashin ɗanyen man ya faɗi wanwar  a kasuwar duniya. Bayan haka kuma, gwamnatoci da yawa da suka shuɗe basu tashi tsaye sun ɗauki takardar Nairar ita kanta da muhimmanci ba balle su kare ta. Ana zargin da yawa daga cikin shugabannin Najeriya da ‘yan siyasarta da wawushe kuɗin ƙasa, kuma abin takaici, maimakon su ajiye su a Najeriya ko kuma su zuba hannun jarin a Najeriya, a’a sai su ɗebi kuɗin su ajiye su a ƙasashen waje. Daga 1999 zuwa 2015, Allah ne kaɗai ya san iya dukiyar da ɓarayi daga cikin shugabannin Najeriya, ma’aikata da ‘yan siyasa suka sata suka kai ƙasar waje, wannan ya taimaka wajen karya tattalin arziƙin ƙasa da kuma karya darajar Naira.

Sana’ar canji, wacce kwata-kwata da ba a san da ita ba a Najeriya sai daga baya ta taka rawa wajen lalata darajar Naira duk da cewar kuma ta taimaka wajen sauƙaƙa samun kuɗaɗen ƙasashen waje tare kuma da samar da sana’a ga mutane da dama. Babbar matsalar ita ce, su ‘yan canji riba ce zalla kuma tsababa kawai a gabansu ba wai makomar darajar Naira ko kishin ƙasa ba. Wannan ce ta kawo lalacewar sana’ar canji kuma a maimakon ta zamo mataimakiya wajen kare martabar Naira, zai ta zamo wata hanyar da ake amfani da ita wajen kassara Nairar tare da ɗaukaka darajar kuɗaɗen ƙasashen waje domin kawai a ci riba. Bayan haka kuma, wasu mutane suna yin amfani da harkar canji ko kuma ‘yan canjin wajen karɓo kuɗaɗen ƙasashen waje a hannun gwamnati kuma su ɓoyesu ko kuma su yi amfani dasu ta hanyoyin da zasu cutar da tattalin arziƙin ƙasa. Dole sai an tsaftace tare da yin garanbawul ga wannan sana’a idan har ana so a samu farfaɗowar darajar Naira.

Mafi yawan ‘yan kasuwarmu, kullum tunaninsu shine su fita ƙasar waje su sayo kaya, a maimakon su maida hankali wajen samar da fasahar ƙera kayan a nan gida Najeriya da kansu. Kusan kowa yafi son daga-buhu-sai-tukunya, kawai ya sayo kaya ya sayar ya ci riba a karan kansa, koda ƙasar za ta mutu. Bugu da ƙari kuma, mafi yawan ‘yan kasuwar basa biyan haraji balle gwamnati ta ɗan ƙaru da wani abu. Wannan tasa mun wayi gari kusan komai da muke amfani da shi, shigo dashi ake daga ƙasar waje, hatta tsinken sakace. Mu kusan babu mai shigowa ya sayi namu kayan, amma kullum muna kan hanya wajen sayo kayan wasu; wannan ta taimaka wajen faɗuwar darajar Naira. Mafi yawan ‘yan Najeriya babu kishin ƙasa a gabansu, kowa burinsa kawai ya gamsar da kansa ko ya biya buƙatarsa, babu ruwansa da makomar ƙasa. Wannan ita tasa mafi yawancin mutane, burinsu su sayi kayayyakin ƙasashen waje,  a dalilin haka ne ma kayayyakin da aka sana’anta a Najeriya suke yin kwantai kuma waɗanda suke yinsu suke watsarwa suna koma sayo na ƙasar waje. Kullum tunaninmu wai kayan ƙasar waje yafi kyau, to ta yaya namun zai yi kyau, idan bama saya? Munata rage wa kanmu ƙarfi muna ƙarawa masu ƙarfi ƙarfi; wannan ta kawo faɗuwar darajar Naira.

Idan da barci muke , to ya kamata yanzu mu farka. Takardar kuɗin ƙasa wata aba ce mai martaba da ƙima wacce take nuna irin darajar tattalin arziƙi da kuma darajar ƙasar ita kanta. Yanzu Naira ta hau kan wata turbar taɓarɓarewar da ba a taɓa gani ba kuma idan muka zuba ido cewar gwamnati ce kaɗai za ta gyara ta, to kuwa zamu sha mamaki. Idan muka yi wasa sai mun wayi gari Naira ta koma bata da amfanin komai sai zubarwa. Duk da cewar wannan matasala ta kwararo a cikin shekaru sama da 40 baya, amma idan muka haɗu a kan manufar kawo gyara, to Naira zata farfaɗo ko da kuwa ba yanzu yanzu ba.

Tun da farko dai dole gwamnati ta maida hankali a kan harkar noma tare da samar da isasshiyar wutar lantarkin da  zata bai wa masana’antu dama domin su farfaɗo su dinga aiki ka’in da na’in. Banda haka, dole ne a tsaurara matakan ladabtarwa a kan masu satar dukiyar ƙasa suna zuba hannun jari  a ƙasashen waje. Dole ne gwamnati ta zage damtse wajen dawo da dukkan kuɗaɗen Najeriya da aka sace daga ƙasashen waje. Kodayake Turawan yamma da sauran wasu ƙasashe baza su so a janye wannan ɗimbin dukiya wadda take ƙarawa tattalin arziƙinsu ƙarfi ba, amma wannnan ya zama dole in har muna so mu cigaba. Bayan haka, idan gwamnati tana so ‘yan Najeriya su sayi kayayyakin da aka ƙera acikin ƙasar, to sai ta zamo abin koyi. Dukkan abin da zata saya, ita ma ta dinga sayen na cikin gida kuma ta rage bai wa kamfanunuwan ƙasashen waje kwangila sai ya zama dole. Bayan haka ta duba yiwuwar kafa dokar hana shigo da rukunin wasu kayayyakin da za a iya ƙerawa a nan gida ko kuma ta sanya haraji mai tsanani  a kansu.

Dolene ‘yan siyasarmu, musamman na 1999 zuwa 2015 su karɓi alhakin ɗaiɗaita mana tattalin arziƙi da jefamu a cikin mawuyacin halin da muke ciki da suka yi. Wajibine a kawo ƙarshen siyasar kuɗi domin guje wa ɓarnatar da dukiyar ƙasa. Yanzu ‘yan siyasarmu saboda tsananin rashin kishin ƙasa, idan zaɓe ya matso, duk wata Dalar Amurka da manyan kuɗaɗen ƙasashen waje dake cikin Najeriya sai sun sayesu domin su saya ko su ƙwaci zaɓe, saboda suna so su dauwama a kan mulki, alabashi ita kuma ƙasa taje can ta shiga halin da zata shiga babu ruwansu. Naira ta yi musu rashin daraja da yawa, don haka Daloli suke rarrabawa domin su ba sai an yi kayansu ba niƙi-niƙi. Dalolin da ya kamata a sayar wa da ‘yan kasuwa domin su saro kaya, ‘yan siyasa da masu mulki duk sun sayesu; wacce take hannun gwamnatinma kuma sun yi amfani da alfarmarsu sun saye, a wasu lokutanma sun sace su kai tsaye. Ta yaya Naira ba zata lalace ba?

Wajibi ne ‘yan kasuwar mu su haɗu a kan yadda zasu dinga ƙera kaya da kansu a maimakon sayosu daga ƙasashen waje. Babu shakka, wannan wani abu ne mai wahala, amma idan suka sa kansu zasu iya, kuma a kwana a tashi, zasu saba har su zama ƙwararru. Yanzu ga Aliko Dangote nan, ai bai zama mai kuɗin Africa baki ɗaya ta hanyar shigo da simiti ba, ya zama ne ta hanyar sana’antashi ya fitar zuwa wasu ƙasashe ko kuma a biyoshi har inda yake a saya. Mu kuma talakawa da mafi yawan masifa take ƙarewa a kanmu, mu yafi kamata ma mu tashi tsaye. Kowa ya yi duba na tsanaki a kan kansa ya ga shin yana sayen kayan da aka ƙera a Najeriya?  Idan akwai abin da ake ƙerawa a Najeriya, to ka ƙyale na ƙasar waje. Idan kana ganin na ƙasar wajen yafi na gida kyau, to sayensa da kake yi ne yasa yafi na gidan kyau, idan ka koma sayen naka, shima zai yi ingancin da watarana zai fi na ƙasar wajen.