Fassara

Sunday, December 11, 2016

Wane Irin So Muke Wa Manzon Allah (SAW)?

10 Ga Disamba, 2016

Daga: Amir Abdulazeez

A
llah (SWT) cikin hikimarSa da SahalewarSa Ya ƙara zagayo damu wata shekarar kuma mun riski watan Rabiul Awwal, wanda a cikinsa ne aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW). Kusan kamar yadda ya kan kasance a mafi yawan shekaru, taƙaddama ta kan kaure a kan halaccin maulidi ko rashin halaccinsa, dacewa ko fa’idarsa da rashinsu. A cikin masu wannan taƙaddama kowanne yana da madogara ko hujjarsa da yake ganin ita ce karɓaɓɓiya. Abin farin cikin dai shi ne, kowanne ɓangare yana son Annabi Muhammadu, saɓanin kawai shi ne hanyar da za a bi wajen nuna soyayyar. To amma, duk ba ma wannan ba tukunna, tambayar da ya kamata mu tsaya mu yi kanmu a matsayin al’umma, ita ce wane irin so muke wa Manzon Allah kuma me aiyukanmu suke cewa game da son da muke cewa muna masa?

Wannan tambaya ta zamar mana kusan wajibi duba da yadda kullum son Annabi yake ƙaruwa a baki a cikin al’ummarmu, amma kuma kullum bijire wa koyarwarsa take ƙara hauhawa. Yanzunnan za ka ga an yi kare-jini-biri-jini da mutum a kan halacci ko rashin halaccin maulidi, amma anjima kaɗan in ka ba shi amana sai ya ci, in kai alƙawari da shi sai ya saɓa, in yai magana sai yai ƙarya. Ko kuma yanzu mutum zai ɗauki littafin Sahihul Bukhari ƙato ya tafi karatu, ya shafe awanni ana biya masa hadisan Manzon Allah, amma a kan hanyarsa ta dawowa zai fara cin naman mutane.

Kowacce shekara guraren yin maulidi ƙaruwa suke yi, guraren karatuttukan hadisan Manzon Allah ƙara yawa suke yi, masu waƙe ko bege na yabon manzo ƙaruwa suke yi, amma kuma kullum lalataciyyar mu’amala da munanan halaye irin waɗanda Manzon Allah ɗin ya hana sai ƙara samun gindin zama suke yi. Tambayar da ya kamata mu yi wa kanmu, wai shin son Manzo Allah ɗin ba shi da alaƙa da koyi da shi ne?

A wannan al’ummar da muke ciki, akwai waɗanda suke ikirarin sun yarda da alƙur’ani amma basu ma yadda da fassarar da Manzon Allah Ya yi wa alƙur’anin ba wato hadisai, kuma suna nan a tsakaninmu suna kiran kansu masoya Manzon Allah. Mutanen dai da ka ce sun yi ƙarya da suka rawaito hadisi, sune dai suka adana ƙur’anin har ya zo gareka; ko kuwa a gun Manzon Allah ka samu ƙur’anin kai tsaye? Mutumin da baka yarda da fassarar da ya yi wa alƙur’anin da aka saukar masa ba sai fassarar da ka yi wa kanka, shi ne kake ƙauna? Wacce irin ƙauna ce wannan? A wannan al’ummar ne, ake zagar wa Manzon Allah iyalansa, abokansa, shaƙiƙansa, amintattaunsa da masoyansa a filin Allah. Masu yin hakan suna nan a tsakaninmu kuma wai su ma masoyansa ne.

A wasu sassa a ƙasar Hausa, al’ada ta fi sunna daraja domin sai al’ada ta hana aure, sunna ba ta hana ba. Duk mu’amalar da ka ɗauka a wannan zamanin da muke ciki sai ka ga mafi yawancin yadda ake gudanar da ita ya saɓa da tsagwaron abin da Annabi ya koyar. Tun daga kan aure, kasuwanci, zamantakewa, mu’amala da sauransu. Ba wai ana nufin babu nagari ba ko babu masu koyi da Annabi a aikace ba; a’a, ana nufin gamayyar halayyar al’umma.

Wani babban kuskure da masu yawa daga cikin al’ummar Musulmi, musamman na ƙasar Hausa suke yi shine, na ɗauka da suke yi cewar son Allah da Manzonsa a baki shi ne kawai abin da ake buƙata, to amma akwai sauran abubuwa na aiki masu tarin yawa da matuƙar amfani, waɗanda rashin kiyayaesu zai iya kawo babbar alamar tambaya dangane da nagarta ko ingancin son da kake wa Allah ko manzonSa.

A abubuwan da Manzon Allah ya siffanta da su na kyawawan  halaye, kaɗan daga cikinmu ne suke ƙoƙarin kamantawa. A abubuwan da yake fushi da su, kaɗan daga cikinmu ne basu tsunduma tsamo-tsamo a cikinsu ba. Wannan shi ne halin da muke ciki.

Masana binciken halayya da ɗabi’un ɗan Adam sun yi ittifaƙin cewar ‘yan Najeriya musamman Hausawa suna daga cikin mutane da suka fi kowa nuna son Annabi a fili a Duniyar Musulunci, an yarda cewar Hausawan Arewacin Najeriya suna daga cikin waɗanda suke ƙoƙarin yin maulidi da hidindimu. To amma kuma sai dai kash! Idan da za a auna, da sai a gano cewar miyagun halaye da gurɓataciyyar mu’amala ta yi mana katutu. Wannan ƙalubale ne ba ƙarami ba a kanmu domin kuwa duk wanda yake ikirarin abu, to alamun wannan abun gaskiya ne, shi ne a gan shi a aikace.

Gurɓacewar mu’amalarmu da yanayin zamantakewarmu a yanzu ta kai ta kawo muna zaune cikin rashin ‘yan uwantaka. Idan jifa ya wuce kanka, to ya faɗa kan kowa. Ba ka gudun ka yi wa mutane abin da kai baka so a yi maka. Muna zaune kullum neman juna muke da sharri ba alkhairi ba. Kowa so yake kowa ya aikata kuskure ya yi ta faman yamaɗiɗi, amma idan an yi alkhairi sai ka ji gum. Kowa tsoron yin harkar kuɗi yake yi da  kowa. Wannan masifa har ina? Koyi da Manzon Allah a haƙiƙance ba a baki ba, shi zai yi mana maganin wannan.

A cikin jama’a, idan ana zaune, har ƙagara ake yi mutum ɗaya ya tashi a saka faifansa, a fara zaginsa ana cin namansa. Ƙarya kuwa ta zama ita ce mafi akasarin zancenmu. Duk maganar da aka faɗa, kowa zai karɓe ta ne cikin shakku da zargi. Idan an faɗa maka farashin abu a kasuwa, gani kake cutarka za a yi. Babu aminci a tsakaninmu. Cin amana a kasuwanci, zamantakewa, aiki, maƙotaka, abota, duk ba wani baƙon abu ba ne a cikin mu’amalar mutanen wannan zamani.

Da ka taɓa mutane, sai su ce sun fi kowa son Annabi, amma kuma a halayyarsu babu irin ta Annabin. Annabi Muhammad (SAW) shi ne mutumin da ya fi kowa iya mu’amala a tarihin duniya, kuma shi Musulmi ne, da shi aka ce Musulmi su yi koyi. Ina koyin yake?

Idan muna buƙatar son da muke yi wa Annabi ya zamo abin gaskatawa da amfanarwa, to sai mun gyara zuciyoyinmu, addininmu, halayenmu da zamantakewarmu ta hanyar yin koyi da dukkan halayensa da kuma ƙauracewa abubuwan da ya hana. Idan ba haka ba, yawan maulidinmu ko sauraron wa’azinmu ba zai kaimu ko’ina ba. Allah ya bamu ikon gyarawa.

Shafin Mallam Amir a Twitter shi ne: @AmirAbdulazeez