10 Ga Disamba, 2016
Daga: Amir Abdulazeez
A
|
llah (SWT) cikin hikimarSa da SahalewarSa Ya ƙara zagayo damu wata shekarar
kuma mun riski watan Rabiul Awwal, wanda a cikinsa ne aka haifi fiyayyen
halitta Annabi Muhammadu (SAW). Kusan kamar yadda ya kan kasance a mafi yawan
shekaru, taƙaddama ta kan kaure a kan halaccin maulidi ko rashin halaccinsa,
dacewa ko fa’idarsa da rashinsu. A cikin masu wannan taƙaddama kowanne yana da
madogara ko hujjarsa da yake ganin ita ce karɓaɓɓiya. Abin farin cikin dai shi ne,
kowanne ɓangare yana son Annabi Muhammadu, saɓanin kawai shi ne hanyar da za a bi
wajen nuna soyayyar. To amma, duk ba ma wannan ba tukunna, tambayar da ya
kamata mu tsaya mu yi kanmu a matsayin al’umma, ita ce wane irin so muke wa Manzon
Allah kuma me aiyukanmu suke cewa game da son da muke cewa muna masa?
Wannan tambaya ta zamar mana kusan wajibi duba da yadda kullum son Annabi yake
ƙaruwa a baki a cikin al’ummarmu, amma kuma kullum bijire wa koyarwarsa take ƙara
hauhawa. Yanzunnan za ka ga an yi kare-jini-biri-jini da mutum a kan halacci ko
rashin halaccin maulidi, amma anjima kaɗan in ka ba shi amana sai ya ci, in kai
alƙawari da shi sai ya saɓa, in yai magana sai yai ƙarya. Ko kuma yanzu mutum
zai ɗauki littafin Sahihul Bukhari ƙato ya tafi karatu, ya shafe awanni ana
biya masa hadisan Manzon Allah, amma a kan hanyarsa ta dawowa zai fara cin
naman mutane.
Kowacce shekara guraren yin maulidi ƙaruwa suke yi, guraren karatuttukan
hadisan Manzon Allah ƙara yawa suke yi, masu waƙe ko bege na yabon manzo ƙaruwa
suke yi, amma kuma kullum lalataciyyar mu’amala da munanan halaye irin waɗanda Manzon
Allah ɗin ya hana sai ƙara samun gindin zama suke yi. Tambayar da ya kamata mu
yi wa kanmu, wai shin son Manzo Allah ɗin ba shi da alaƙa da koyi da shi ne?
A wannan al’ummar da muke ciki, akwai waɗanda suke ikirarin sun yarda da alƙur’ani
amma basu ma yadda da fassarar da Manzon Allah Ya yi wa alƙur’anin ba wato
hadisai, kuma suna nan a tsakaninmu suna kiran kansu masoya Manzon Allah. Mutanen
dai da ka ce sun yi ƙarya da suka rawaito hadisi, sune dai suka adana ƙur’anin
har ya zo gareka; ko kuwa a gun Manzon Allah ka samu ƙur’anin kai tsaye? Mutumin
da baka yarda da fassarar da ya yi wa alƙur’anin da aka saukar masa ba sai
fassarar da ka yi wa kanka, shi ne kake ƙauna? Wacce irin ƙauna ce wannan? A wannan
al’ummar ne, ake zagar wa Manzon Allah
iyalansa, abokansa, shaƙiƙansa, amintattaunsa da masoyansa a filin Allah. Masu yin hakan suna nan a tsakaninmu kuma wai su
ma masoyansa ne.
A wasu sassa a ƙasar Hausa, al’ada ta fi sunna daraja domin sai al’ada ta
hana aure, sunna ba ta hana ba. Duk
mu’amalar da ka ɗauka a wannan zamanin da muke ciki sai ka ga mafi yawancin yadda ake gudanar da
ita ya saɓa da tsagwaron abin da Annabi ya koyar. Tun daga kan aure, kasuwanci,
zamantakewa, mu’amala da sauransu. Ba wai ana nufin babu nagari ba ko babu masu
koyi da Annabi a aikace ba; a’a, ana nufin gamayyar halayyar al’umma.
Wani babban kuskure da masu yawa daga cikin al’ummar Musulmi, musamman na ƙasar
Hausa suke yi shine, na ɗauka da suke yi cewar son Allah da Manzonsa a baki shi
ne kawai abin da ake buƙata, to amma akwai sauran abubuwa na aiki masu tarin
yawa da matuƙar amfani, waɗanda rashin kiyayaesu zai iya kawo babbar alamar
tambaya dangane da nagarta ko ingancin son da kake wa Allah ko manzonSa.
A abubuwan da Manzon Allah ya siffanta da su na kyawawan halaye, kaɗan daga cikinmu ne suke ƙoƙarin
kamantawa. A abubuwan da yake fushi da su, kaɗan daga cikinmu ne basu tsunduma
tsamo-tsamo a cikinsu ba. Wannan shi ne halin da muke ciki.
Masana binciken halayya da ɗabi’un ɗan Adam sun yi ittifaƙin cewar ‘yan Najeriya
musamman Hausawa suna daga cikin mutane da suka fi kowa nuna son Annabi a fili
a Duniyar Musulunci, an yarda cewar Hausawan Arewacin Najeriya suna daga cikin waɗanda
suke ƙoƙarin yin maulidi da hidindimu. To amma kuma sai dai kash! Idan da za a
auna, da sai a gano cewar miyagun halaye da gurɓataciyyar mu’amala ta yi mana
katutu. Wannan ƙalubale ne ba ƙarami ba a kanmu domin kuwa duk wanda yake ikirarin
abu, to alamun wannan abun gaskiya ne, shi ne a gan shi a aikace.
Gurɓacewar mu’amalarmu da yanayin zamantakewarmu a yanzu ta kai ta kawo
muna zaune cikin rashin ‘yan uwantaka. Idan jifa ya wuce kanka, to ya faɗa kan
kowa. Ba ka gudun ka yi wa mutane abin da kai baka so a yi maka. Muna zaune kullum neman juna
muke da sharri ba alkhairi ba. Kowa so yake kowa ya aikata kuskure ya yi ta
faman yamaɗiɗi, amma idan an yi alkhairi sai ka ji gum. Kowa tsoron yin harkar
kuɗi yake yi da kowa. Wannan masifa har
ina?
Koyi da Manzon Allah a haƙiƙance ba a baki ba, shi zai yi mana maganin wannan.
A cikin jama’a, idan ana zaune, har ƙagara ake yi mutum ɗaya ya tashi a
saka faifansa, a fara zaginsa ana cin namansa. Ƙarya kuwa ta zama ita ce mafi
akasarin zancenmu. Duk maganar da aka faɗa, kowa zai karɓe ta ne cikin shakku
da zargi. Idan an faɗa maka farashin abu a kasuwa, gani kake cutarka za a yi. Babu
aminci a tsakaninmu. Cin amana a kasuwanci, zamantakewa, aiki, maƙotaka, abota,
duk ba wani baƙon abu ba ne a cikin mu’amalar mutanen wannan zamani.
Da ka taɓa mutane, sai su ce sun fi kowa son Annabi, amma kuma a halayyarsu
babu irin ta Annabin. Annabi Muhammad (SAW) shi ne mutumin da ya fi kowa iya
mu’amala a tarihin duniya, kuma shi Musulmi ne, da shi aka ce Musulmi su yi
koyi. Ina koyin yake?
Idan muna buƙatar son da muke yi wa Annabi ya zamo abin gaskatawa da
amfanarwa, to sai mun gyara zuciyoyinmu, addininmu, halayenmu da zamantakewarmu
ta hanyar yin koyi da dukkan halayensa da kuma ƙauracewa abubuwan da ya hana.
Idan ba haka ba, yawan maulidinmu ko sauraron wa’azinmu ba zai kaimu ko’ina ba.
Allah
ya bamu ikon gyarawa.
Shafin
Mallam Amir a Twitter shi ne:
@AmirAbdulazeez
No comments:
Post a Comment