15 Ga Nuwamba, 2017
Daga: Amir Abdulazeez
L
|
okacin da aka rawaito cewar Gwamnatin Jihar Kano ta kashe Naira miliyan 208
wajen tallafa wa masu sana’ar shayi da burodi guda 5,200 a faɗin Jihar Kano,
mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu. Wasu da yawa sun kushe ko sun yaba wa
abin saboda dalilai na siyasa, wasu kuwa saboda wasu manufofi masu kyau da suke
ganin hakan ya saɓawa ko ya yi dai-dai da su. Amma babban abin la’akari shi ne,
mu manta da waɗanda suka samar da tsarin ko jam’iyyarsu, mu kalli tsarin a ƙashin
kansa, mu ga ta ina zai samar wa da Jihar Kano ci gaba? Kar mu manta fa yanzu
ba irin da bace da gwamnati take da kuɗi faca-faca da zata yi wadaƙa dasu.
Farko dai, irin wannan tsarin na tara mutane a raba musu tallafi da kuɗin
gwamnati, ba baƙon abu bane a Jihar Kano. Mafi yawan masu kushewa saboda
dalilai na siyasa, su ma nasu gwanayen sun yi irinsa a baya. To amma, ya kamata
mu yi tunani, wane irin ci gaba Jihar Kano ta samu a tsawon wannan shekaru ta
dalilin biliyoyin kuɗaɗe da aka kashe wajen yin wannan tallafi? Tun farko ma,
menene tabbacin cewa waɗanda ake bai wa irin wannan tallafi sun cancanceshi?
Misali, ta yaya zamu gane cewa waɗanda Gwamna Ganduje ya tallafawa kwanakin
da suka wuce masu shayin ne na gaske, ba wasu ‘yan koren siyasa aka zaɓo ba? Menene
tabbacin cewar ba zamu kuma ganin fuskokin waɗancan masu shayi ba gobe idan za
a bada tallafi ga masu gyaran babura? Kowanne mai shayi ake tallafawa, ko kuwa
sai wanda ba shi da jari kuma yana so ya haɓɓaka sana’ar tasa da gaske? Wane tanadi
gwamnati ta yi don sa ido wajen ganin an yi amfani da kayan da ta raba maimakon
sayar da su? Shin gwamnati za ta dinga bin kowacce sana’a ne tana bai wa masu
ita tallafi? Shin menene haƙƙin waɗanda suma masu shayi ne kuma ‘yan Kano mabuƙata
kuma basu samu wannan tallafi ba?
Shin rabawa masu shayi kayayyaki ne zai gyara sana’ar ko kuwa tsayawa a
kalli tushen me yasa tattalin arzikin ya kai lalacewar da har sai an tallafa
musu ya kamata? Shin gwamnati ta sallama cewar bata da wasu manufofi ingantattu
da zasu inganta tattalin arziki ta yadda kowa zai tallafi kansa ba tare da an
bi mutane ana raba musu kuɗaɗe da kayan tallafi ba? Ina muka kwana kan burin
gwamnati na ganin mutane ne zasu zamo masu tallafar gwamnati da kuɗin shiga a
maimakon ita ta ɗebi kuɗaɗenta tana raba musu? Wannan rabe-raben tallafi, da
wace manufar ci gaban Kano mai ɗorewa ya dace kuma ta ya zamu auna nasararsa ga
wannan manufa a yanzu ko a nan gaba?
Da zarar mutum ya yi ƙoƙarin nemo amsoshin wannan tambayoyi sai ya ga gabaɗaya
abin ba shi da wata muhimmiyar manufa ta ci gaba a gajere ko dogon zango. Muhimmiyar
manufarsa ita ce siyasa. Tsirarun da Allah Ya taimaka suka yi amfani da nasu
tallafin ta hanya mai kyau, nasu ya ɗore. Ba za ce gwamnati ta daina bada
tallafi ba duba da irin yanayin al’ummarmu; to amma ba kara zube barkatai ba
don siyasa. A tsaya a kalli abin bisa manufa ta ci gaba mai ɗorewa
kuma a yi abin a muhallinsa ga waɗanda zai amfanar.
Jiha kamar Kano wacce aka yi wa nisa kuma take da burin ganin ta cimma
takwarorinta irinsu Lagos, Ogun da Rivers, ya kamata a ce tana da wani tsarin
ci gaba mai ɗorewa wanda babu siyasa a cikinsa maimakon a same ta tana kashe
Naira Miliyan 208 wajen rabawa ‘yan koren siyasa da aka kira da masu shayi ba.
Kimanin watanni biyar baya, wani bincike ya kai mu ga zagaya wasu muhimman
madatsun ruwa na Jihar Kano. A yayin binciken wanda ya ƙunshi wasu malamai da ɗalibai
masu sha’awar nazari kan harkokin ruwa
da tusarrufinsa daga Jami’ar Bayero, ya maida hankali a cikin abubuwa da
dama, wajen gano gazawar madatsun ruwanmu wajen biyan buƙatun Jihar Kano na tattalin
arziki da kuma na yau da kullum duk kuwa da yawansu da kuma girmansu.
Kididdiga ta nuna cewar duk
Najeriya, babu Jihar da take da yawan madatsun ruwa kamar Kano. Jihar tana da
kimanin madatsu 26 wanda girman kowanne ya kama daga ‘yan hektoci zuwa aƙalla
hekta 17,800. Wasu daga cikin madatsun kamar Watari, Tiga, Challawa-Goje,
Bagauda, Tomas, Karaye, Pada, da sauransu, suna daga cikin mafi girma a
Najeriya. To amma duk da haka, gwamnati ba ta zuba isasshen jari ko yin wani
tsari nagartacce da zai sa noman rani ya mamaye ƙananan hukumomi 38 na wajen
birni da muke dasu ba. Duk da wannan ni’ima da dama, matasan Kano suna zaune
cikin rashin aikin yi ta yadda a yanzu jihar ana ƙaddara ta a matsayin kan gaba
wajen mafi yawan masu shaye-shaye a faɗin Najeriya.
Me ya kawo wannan? Rashin wani tartibin tsari mai ɗorewa na ci gaban jihar
wanda za a dinga aiwatarwa cikin shekaru. Ci gaban Jihar Kano a yanzu ya dogara
kacokam a kan gwamnan da yake mulki; abinda ya ga dama shi za a yi ko da kuwa
akwai dubannan abubuwan da suka fi shi muhimmanci. ‘Yan majalisunmu da sauran
masu ruwa da tsaki kuwa sun zama hoto. Idan banda haka, babu wani dalili da zai
sa gwamna ya ɗebi biliyoyin nairori ya gina gadar sama ko ya sayi motoci ya
dinga rabawa masu ƙarfi ko kuma ya sayi kayayyaki yana rabawa magoya bayansa da
sunan masu shayi, bayan asibitocinmu suna zaune babu wadatar magani da isassun ma’aikata,
makarantunmu suna zaune babu kujeru da ingantattun malamai, masana’antunmu suna
nan a rufe a lalace, sannan dubban matasa suna zaune babu abin yi ba.
Mun ga lokacin da gwamnati ta dinga ware biliyoyin Naira tana fasa tituna
masu kyau da sunan rabasu biyu a ƙananan hukumomin da babu asibiti ko kuma ake
da asibitocin da ba zaka sayesu Naira miliyan guda ba. Magoya baya kuma suna
tafi suna murna. Gudanar da ci gaban Kano kusan ya dogara kacokam a kan siyasa.
Kowanne gwamna idan ya zo burinsa ya shimfiɗa sabon tsarinsa wanda yake cike da
burin gina siyasarsa da ta magoya bayansa fiye da burin gina jiharsa da al’umma.
Ya ishi gwamnoninmu abin kunya a ce daga 1999 zuwa yanzu, a irin albarka da
tagomashin da Allah Ya yi wa Kano, amma wai ba zamu iya biyan albashi ba ba tare
da mun jira kuɗi daga Gwamnatin Taryya ba.
Twitter:
@AmirAbdulazeez