Fassara

Wednesday, November 15, 2017

Ganduje, Masu Shayi da Makomar Jihar Kano

15 Ga Nuwamba, 2017



Daga: Amir Abdulazeez

L
okacin da aka rawaito cewar Gwamnatin Jihar Kano ta kashe Naira miliyan 208 wajen tallafa wa masu sana’ar shayi da burodi guda 5,200 a faɗin Jihar Kano, mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu. Wasu da yawa sun kushe ko sun yaba wa abin saboda dalilai na siyasa, wasu kuwa saboda wasu manufofi masu kyau da suke ganin hakan ya saɓawa ko ya yi dai-dai da su. Amma babban abin la’akari shi ne, mu manta da waɗanda suka samar da tsarin ko jam’iyyarsu, mu kalli tsarin a ƙashin kansa, mu ga ta ina zai samar wa da Jihar Kano ci gaba? Kar mu manta fa yanzu ba irin da bace da gwamnati take da kuɗi faca-faca da zata yi wadaƙa dasu.

Farko dai, irin wannan tsarin na tara mutane a raba musu tallafi da kuɗin gwamnati, ba baƙon abu bane a Jihar Kano. Mafi yawan masu kushewa saboda dalilai na siyasa, su ma nasu gwanayen sun yi irinsa a baya. To amma, ya kamata mu yi tunani, wane irin ci gaba Jihar Kano ta samu a tsawon wannan shekaru ta dalilin biliyoyin kuɗaɗe da aka kashe wajen yin wannan tallafi? Tun farko ma, menene tabbacin cewa waɗanda ake bai wa irin wannan tallafi sun cancanceshi?

Misali, ta yaya zamu gane cewa waɗanda Gwamna Ganduje ya tallafawa kwanakin da suka wuce masu shayin ne na gaske, ba wasu ‘yan koren siyasa aka zaɓo ba? Menene tabbacin cewar ba zamu kuma ganin fuskokin waɗancan masu shayi ba gobe idan za a bada tallafi ga masu gyaran babura? Kowanne mai shayi ake tallafawa, ko kuwa sai wanda ba shi da jari kuma yana so ya haɓɓaka sana’ar tasa da gaske? Wane tanadi gwamnati ta yi don sa ido wajen ganin an yi amfani da kayan da ta raba maimakon sayar da su? Shin gwamnati za ta dinga bin kowacce sana’a ne tana bai wa masu ita tallafi? Shin menene haƙƙin waɗanda suma masu shayi ne kuma ‘yan Kano mabuƙata kuma basu samu wannan tallafi ba?

Shin rabawa masu shayi kayayyaki ne zai gyara sana’ar ko kuwa tsayawa a kalli tushen me yasa tattalin arzikin ya kai lalacewar da har sai an tallafa musu ya kamata? Shin gwamnati ta sallama cewar bata da wasu manufofi ingantattu da zasu inganta tattalin arziki ta yadda kowa zai tallafi kansa ba tare da an bi mutane ana raba musu kuɗaɗe da kayan tallafi ba? Ina muka kwana kan burin gwamnati na ganin mutane ne zasu zamo masu tallafar gwamnati da kuɗin shiga a maimakon ita ta ɗebi kuɗaɗenta tana raba musu? Wannan rabe-raben tallafi, da wace manufar ci gaban Kano mai ɗorewa ya dace kuma ta ya zamu auna nasararsa ga wannan manufa a yanzu ko a nan gaba?

Da zarar mutum ya yi ƙoƙarin nemo amsoshin wannan tambayoyi sai ya ga gabaɗaya abin ba shi da wata muhimmiyar manufa ta ci gaba a gajere ko dogon zango. Muhimmiyar manufarsa ita ce siyasa. Tsirarun da Allah Ya taimaka suka yi amfani da nasu tallafin ta hanya mai kyau, nasu ya ɗore. Ba za ce gwamnati ta daina bada tallafi ba duba da irin yanayin al’ummarmu; to amma ba kara zube barkatai ba don siyasa. A tsaya a kalli abin bisa manufa ta ci gaba mai ɗorewa kuma a yi abin a muhallinsa ga waɗanda zai amfanar.

Jiha kamar Kano wacce aka yi wa nisa kuma take da burin ganin ta cimma takwarorinta irinsu Lagos, Ogun da Rivers, ya kamata a ce tana da wani tsarin ci gaba mai ɗorewa wanda babu siyasa a cikinsa maimakon a same ta tana kashe Naira Miliyan 208 wajen rabawa ‘yan koren siyasa da aka kira da masu shayi ba.

Kimanin watanni biyar baya, wani bincike ya kai mu ga zagaya wasu muhimman madatsun ruwa na Jihar Kano. A yayin binciken wanda ya ƙunshi wasu malamai da ɗalibai masu sha’awar nazari kan harkokin ruwa  da tusarrufinsa daga Jami’ar Bayero, ya maida hankali a cikin abubuwa da dama, wajen gano gazawar madatsun ruwanmu wajen biyan buƙatun Jihar Kano na tattalin arziki da kuma na yau da kullum duk kuwa da yawansu da kuma girmansu.

Kididdiga ta nuna  cewar duk Najeriya, babu Jihar da take da yawan madatsun ruwa kamar Kano. Jihar tana da kimanin madatsu 26 wanda girman kowanne ya kama daga ‘yan hektoci zuwa aƙalla hekta 17,800. Wasu daga cikin madatsun kamar Watari, Tiga, Challawa-Goje, Bagauda, Tomas, Karaye, Pada, da sauransu, suna daga cikin mafi girma a Najeriya. To amma duk da haka, gwamnati ba ta zuba isasshen jari ko yin wani tsari nagartacce da zai sa noman rani ya mamaye ƙananan hukumomi 38 na wajen birni da muke dasu ba. Duk da wannan ni’ima da dama, matasan Kano suna zaune cikin rashin aikin yi ta yadda a yanzu jihar ana ƙaddara ta a matsayin kan gaba wajen mafi yawan masu shaye-shaye a faɗin Najeriya.

Me ya kawo wannan? Rashin wani tartibin tsari mai ɗorewa na ci gaban jihar wanda za a dinga aiwatarwa cikin shekaru. Ci gaban Jihar Kano a yanzu ya dogara kacokam a kan gwamnan da yake mulki; abinda ya ga dama shi za a yi ko da kuwa akwai dubannan abubuwan da suka fi shi muhimmanci. ‘Yan majalisunmu da sauran masu ruwa da tsaki kuwa sun zama hoto. Idan banda haka, babu wani dalili da zai sa gwamna ya ɗebi biliyoyin nairori ya gina gadar sama ko ya sayi motoci ya dinga rabawa masu ƙarfi ko kuma ya sayi kayayyaki yana rabawa magoya bayansa da sunan masu shayi, bayan asibitocinmu suna zaune babu wadatar magani da isassun ma’aikata, makarantunmu suna zaune babu kujeru da ingantattun malamai, masana’antunmu suna nan a rufe a lalace, sannan dubban matasa suna zaune babu abin yi ba.

Mun ga lokacin da gwamnati ta dinga ware biliyoyin Naira tana fasa tituna masu kyau da sunan rabasu biyu a ƙananan hukumomin da babu asibiti ko kuma ake da asibitocin da ba zaka sayesu Naira miliyan guda ba. Magoya baya kuma suna tafi suna murna. Gudanar da ci gaban Kano kusan ya dogara kacokam a kan siyasa. Kowanne gwamna idan ya zo burinsa ya shimfiɗa sabon tsarinsa wanda yake cike da burin gina siyasarsa da ta magoya bayansa fiye da burin gina jiharsa da al’umma. Ya ishi gwamnoninmu abin kunya a ce daga 1999 zuwa yanzu, a irin albarka da tagomashin da Allah Ya yi wa Kano, amma wai ba zamu iya biyan albashi ba ba tare da mun jira kuɗi daga Gwamnatin Taryya ba.
  

Twitter: @AmirAbdulazeez   

No comments:

Post a Comment