29 ga Mayun 2018
Daga: Amir Abdulazeez
M
|
afi yawancin mutanen Najeriya su kan
fahimci cewa Ranar Dimokraɗiyya ta zagayo ta hanyar kafafen yaɗa labarai
musamman a jaridu. Kamar kowacce shekara, wannan lokacin ma shafukan jaridun ƙasar
nan sun cika taf, wasu ma ba masaka tsinke da saƙonnin taya juna murna da ‘yan
siyasa suke wa junansu ko kuma ‘yan korensu da masu neman gindin zama a wurinsu
suke yi. Wani abin la’alkari ma shi ne, mafi yawan masu taya murnar da wasu waɗanda
ake taya wa murnar ma, ko dai basu fahimci ma manufofin dimokraɗiyyar ba, ko
kuma aƙidu da aiyukansu sun yi hannun riga da manufofinta.
Lokacin da rahotanni suka fita a
kwanakin baya kan ƙin bayyana da Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa gaban Majalisar
Dattawa ta ƙasa ba tare da wani ƙwaƙƙwara ko karɓaɓɓen dalili ba, da yawa sun
shiga ruɗani a kan ko dimokraɗiyya tana aiki a ƙasar nan. Idan har babban mai
tabbatar da doka da oda na ƙasa zai yi irin haka, ko ma bisa wacce irin hujja
ko uzuri ya yi hakan, dole a dinga samun shakku a cikin tsarin da muke tafiya a
kai. A kowacce ƙasa, majalisa ita ce zuciyar dimokraɗiyya komai
lalcewar ta. Idan har za a wofantar da ita ko a dinga raina ta ta irin wannan
sigar, dole a ji tsoron makomar dimokraɗiyyar ita kanta.
An yarda cewa, majalisar ƙasar nan ta
zubar wa da kanta mutunci da daraja tuni a cikin shekarun da suka gabata, amma
dai a dokar ƙasa, kusan ita ce gaɓar dimokraɗiyya mafi amfani, don haka ta
cancanci a ce tana da girma da ƙarfin da
zata iya gayyatar ko da shugaban ƙasa ne a kowanne lokaci, ba ma wani na ƙasa
da shi ba ko ma waɗanda ya naɗa ba. Girmama majalisa a matasyin gida ya sha
bambam da girmama ɗai-ɗaikun mutanen da suke cikinta. Wai tukunna ma, bai ishi
dimokraɗiyyar mu abin Allah wadai ba a ce tsawon shekarunnan, muatanen da ake
da shakku a kansu ne kullum suke zama ‘yan majalisu, kuma babu alamun hakan zai
kau a nan kusa?
Daya daga muhimman abubuwan da suka
faru kafin bikin Ranar Dimokraɗiyyar wannan shekara, shi ne zaɓukan shugabannin
jam’iyyar APC mai mulki na mazaɓu da ƙananan hukumomi a faɗin ƙasa a karo na
farko tun bayan shekarar 2015. A hankalce, ya kamata wannan ya zama wani
ma’auni na irin ci gaba ko ci bayan da dimokraɗiyyarmu take samu. A mafi yawan
waɗannan zaɓukan, babu wani abu da ya nuna tasake zani ta fuskar inganci ko tsari.
Waɗanda suka shaida yadda zaɓukan suka ƙasance a wasu ƙananan hukumomi zasu iya
bada hujjar cewa babu abin da ya gudana sai son zuciya a mafi yawan gurare.
Farko dai, abin da ya faru a zaɓukan
shugabancin na APC ba wani abu ne sabo ko baƙo ba, abu ne da aka saba da shi tun
ba yau ba. Abin baƙin cikin kawai shi ne, yadda hakan ya ma zama jiki har ake
kallonsa a matsayin shi ne ma dimokraɗiyya da ƙa’idojinta a kusan kowacce jam’iyya
ta ƙasar nan kuma muke murna muna farin ciki kowacce shekara. Da wahala mutum
ya iya tuna wani lokaci da wata jam’iyya a Najeriya ta gudanar da sahihin zaɓukan
shugabancinta cikin lokaci da ƙa’ida, gaskiya da adalci a faɗin ƙasa ba tare da
kama-karya, son zuciya da saɓa ƙa’idar ita kanta jam’iyyar da hukumar zaɓe ta ƙasa
ba.
Wani lokacin idan mutum ya zauna, sai
ya dinga tunanin wai shin nawa ne daga cikin mutanen da suka zama shugabannin ƙasa,
gwamnoni da ‘yan majalisu daga shekarar 1999 zuwa yanzu idan da ingantaciyyar dimokraɗiyya
ake aiwatarwa a Najeriya? Idan da jam’iyyu suna yin zaɓukan fidda gwani na
adalci, mutane nawa ne zasu samu takara tun ma da farko? Mutane nawa ne suka ci
zaɓe aka ƙwace musu a 2003 da 2007? Idan da doka da oda na aiki yadda ya
kamata, nawa ne zasu kammala wa’adin mulkinsu lafiya?
Yayin da muke murna da cikar dimokraɗiyya
shekaru 19 a Najeriya, har yanzu gwamnati ba ta bada gamsasshe ko cikakken
martani a aikace kan zarge-zarge daga
cikin gida da ƙasashen ƙetare kan bisa yadda sojoji ke cin zarafin farar hula a
yayin gudanar da aiyukansu a Arewa maso Gabas ba. Har yanzu muna fama da
tuhume-tuhume kan yadda ake saɓa wa umarnin kotuna a wannan dimokradiyyar da
muke ta murna a kai. Gidajen bursun dinmu sun zamo wasu gurare da ake wa kallon
na cin zarafin bil adama ba are da wani ƙwaƙƙwaran mataki ba. Waɗannan sune kaɗan
daga cikin abubuwan da ya kamata dimokraɗiyyar mu ta mayar da hankali a kai.
Me muke wa murna duk shekara? Muna
murna ne ga ainihin ci gaban da aka samu a dimokraɗiyyance ko kuwa
muna farin ciki ne da ƙarewar mulkin soja? Daga 1999 zuwa yanzu, wane ci gaba
muka samu ta fuskar faɗin albarkacin baki, dimokraɗiyyar cikin gida a jam’iyyu,
mulki da adalci da gaskiya, bai wa kowanne bangaren gwamnati hakkinsa,
gyare-gyaren kundin dokokin zaɓe, daidaito tsakanin ‘yan ƙasa a gaban doka, da
sauran rukunnan dimokraɗiyya? Wane ma’uanai muka samar wajen auna ci gaba ko ci
bayan da muke samu ta fuskar dimokraɗiyya?
Yayin da muke murna da wannan dimokraɗiyyar, ya zama wajibi mu tuna cewa
har yanzu yawan dukiyarka ne abin da ya fi komai tasiri wajen yin nasara a zaɓe;
mutane suna cin zaɓe ba tare da wata manufa ba; shugabannin jam’iyyu a dukkan
matakai suna samuwa ne ta hanyar nune ba zaɓe ba; iyayen gida su suke juya
siyasa ba jama’a ba; mafi yawan ‘yan Najeriya basu da cikakken ilimin siyasa da
zaɓe; babu wani hukunci da ake yi wa masu maguɗin zaɓe; zaɓukan ƙananan
hukumomi sun koma wasan yara; ana amfani da ƙarfin mulki wajen murƙushe marasa
mulki a zaɓe; kotuna da yawa ba sa cikakken adalci ga korafe-korafen zaɓe;
hukumar zaɓe ba ta da cikakken ‘yanci, da sauran wasu tarin matsaloli.
Kamar ko yaushe, Ranar Dimokraɗiyya ta
wannan shekara ba ta wuce wani lokaci na shugabanni da ‘yan siyasa cika baki
kan aiyukan da suka yi a gwamnatance
wanda ma’aikatansu suka tsara musu a rubuce ba. Wasu daga cikin waɗannan
aikace-aikace ma maimaita zancensu kawai ake yi kowacce shekara. Kodayake hakan
ba aibu bane tunda ranar dama ta kan dace da lokacin da suke bukukuwan cikarsu
wasu shekaru a kan mulki, amma ya kamata
lokacin ya fi maida hankali wajen duba ci gaban mu wajen kyautata
mu’amalarmu a ɗaiɗaiku da kuma ƙasa baki
ɗaya ta fuskar dimokraɗiyya.
Yin murna da mulkin farar hula na
tsawon shekaru 19 a ƙasar da aka yi shekara da shekaru a karkashin mulkin soja
ba zai zama kuskure ba, amma ya kamata murna ta wuce gaban bada hutu, gabatar
da ƙasidu ko ɓarnatar da kuɗaɗe wajen talla a shafin jaridu. Ya kamata ta zama
wani yanayi na duba yadda wannan mulki na farar hula ya kawo ci gaba wajen bai
wa mutane dama ba tare da nuna bambanci ba.
Ba wanda zai tsammaci dimokraɗiyyarmu
ta zamo ba ta da wata matsala ko aibu ba a cikin shekaru 19 kacal , amma dai ya
kamata a tashi tsaye. Wane yunƙuri muka yi a cikin waɗannan shekaru? Waɗanne
nasarori muka samu? Ina kura-kuran suke?
Twitter: @AmirAbdulazeez