Fassara

Tuesday, June 5, 2018

Ina Dimokraɗiyyar Take?


29 ga Mayun 2018


Daga: Amir Abdulazeez

M
afi yawancin mutanen Najeriya su kan fahimci cewa Ranar Dimokraɗiyya ta zagayo ta hanyar kafafen yaɗa labarai musamman a jaridu. Kamar kowacce shekara, wannan lokacin ma shafukan jaridun ƙasar nan sun cika taf, wasu ma ba masaka tsinke da saƙonnin taya juna murna da ‘yan siyasa suke wa junansu ko kuma ‘yan korensu da masu neman gindin zama a wurinsu suke yi. Wani abin la’alkari ma shi ne, mafi yawan masu taya murnar da wasu waɗanda ake taya wa murnar ma, ko dai basu fahimci ma manufofin dimokraɗiyyar ba, ko kuma aƙidu da aiyukansu sun yi hannun riga da manufofinta.

Lokacin da rahotanni suka fita a kwanakin baya kan ƙin bayyana da Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa gaban Majalisar Dattawa ta ƙasa ba tare da wani ƙwaƙƙwara ko karɓaɓɓen dalili ba, da yawa sun shiga ruɗani a kan ko dimokraɗiyya tana aiki a ƙasar nan. Idan har babban mai tabbatar da doka da oda na ƙasa zai yi irin haka, ko ma bisa wacce irin hujja ko uzuri ya yi hakan, dole a dinga samun shakku a cikin tsarin da muke tafiya a kai. A kowacce ƙasa, majalisa ita ce zuciyar dimokriyya komai lalcewar ta. Idan har za a wofantar da ita ko a dinga raina ta ta irin wannan sigar, dole a ji tsoron makomar dimokraɗiyyar ita kanta.

An yarda cewa, majalisar ƙasar nan ta zubar wa da kanta mutunci da daraja tuni a cikin shekarun da suka gabata, amma dai a dokar ƙasa, kusan ita ce gaɓar dimokraɗiyya mafi amfani, don haka ta cancanci  a ce tana da girma da ƙarfin da zata iya gayyatar ko da shugaban ƙasa ne a kowanne lokaci, ba ma wani na ƙasa da shi ba ko ma waɗanda ya naɗa ba. Girmama majalisa a matasyin gida ya sha bambam da girmama ɗai-ɗaikun mutanen da suke cikinta. Wai tukunna ma, bai ishi dimokraɗiyyar mu abin Allah wadai ba a ce tsawon shekarunnan, muatanen da ake da shakku a kansu ne kullum suke zama ‘yan majalisu, kuma babu alamun hakan zai kau a nan kusa?

Daya daga muhimman abubuwan da suka faru kafin bikin Ranar Dimokraɗiyyar wannan shekara, shi ne zaɓukan shugabannin jam’iyyar APC mai mulki na mazaɓu da ƙananan hukumomi a faɗin ƙasa a karo na farko tun bayan shekarar 2015. A hankalce, ya kamata wannan ya zama wani ma’auni na irin ci gaba ko ci bayan da dimokraɗiyyarmu take samu. A mafi yawan waɗannan zaɓukan, babu wani abu da ya nuna tasake zani ta fuskar inganci ko tsari. Waɗanda suka shaida yadda zaɓukan suka ƙasance a wasu ƙananan hukumomi zasu iya bada hujjar cewa babu abin da ya gudana sai son zuciya a mafi yawan gurare.

Farko dai, abin da ya faru a zaɓukan shugabancin na APC ba wani abu ne sabo ko baƙo ba, abu ne da aka saba da shi tun ba yau ba. Abin baƙin cikin kawai shi ne, yadda hakan ya ma zama jiki har ake kallonsa a matsayin shi ne ma dimokraɗiyya da ƙa’idojinta a kusan kowacce jam’iyya ta ƙasar nan kuma muke murna muna farin ciki kowacce shekara. Da wahala mutum ya iya tuna wani lokaci da wata jam’iyya a Najeriya ta gudanar da sahihin zaɓukan shugabancinta cikin lokaci da ƙa’ida, gaskiya da adalci a faɗin ƙasa ba tare da kama-karya, son zuciya da saɓa ƙa’idar ita kanta jam’iyyar da hukumar zaɓe ta ƙasa ba.

Wani lokacin idan mutum ya zauna, sai ya dinga tunanin wai shin nawa ne daga cikin mutanen da suka zama shugabannin ƙasa, gwamnoni da ‘yan majalisu daga shekarar 1999 zuwa yanzu idan da ingantaciyyar dimokraɗiyya ake aiwatarwa a Najeriya? Idan da jam’iyyu suna yin zaɓukan fidda gwani na adalci, mutane nawa ne zasu samu takara tun ma da farko? Mutane nawa ne suka ci zaɓe aka ƙwace musu a 2003 da 2007? Idan da doka da oda na aiki yadda ya kamata, nawa ne zasu kammala wa’adin mulkinsu lafiya?

Yayin da muke murna da cikar dimokraɗiyya shekaru 19 a Najeriya, har yanzu gwamnati ba ta bada gamsasshe ko cikakken martani  a aikace kan zarge-zarge daga cikin gida da ƙasashen ƙetare kan bisa yadda sojoji ke cin zarafin farar hula a yayin gudanar da aiyukansu a Arewa maso Gabas ba. Har yanzu muna fama da tuhume-tuhume kan yadda ake saɓa wa umarnin kotuna a wannan dimokradiyyar da muke ta murna a kai. Gidajen bursun dinmu sun zamo wasu gurare da ake wa kallon na cin zarafin bil adama ba are da wani ƙwaƙƙwaran mataki ba. Waɗannan sune kaɗan daga cikin abubuwan da ya kamata dimokraɗiyyar mu ta mayar da hankali a kai.

Me muke wa murna duk shekara? Muna murna ne ga ainihin ci gaban da aka samu a dimokraɗiyyance ko kuwa muna farin ciki ne da ƙarewar mulkin soja? Daga 1999 zuwa yanzu, wane ci gaba muka samu ta fuskar faɗin albarkacin baki, dimokraɗiyyar cikin gida a jam’iyyu, mulki da adalci da gaskiya, bai wa kowanne bangaren gwamnati hakkinsa, gyare-gyaren kundin dokokin zaɓe, daidaito tsakanin ‘yan ƙasa a gaban doka, da sauran rukunnan dimokraɗiyya? Wane ma’uanai muka samar wajen auna ci gaba ko ci bayan da muke samu ta fuskar dimokraɗiyya?

Yayin da muke murna da wannan dimokraɗiyyar, ya zama wajibi mu tuna cewa har yanzu yawan dukiyarka ne abin da ya fi komai tasiri wajen yin nasara a zaɓe; mutane suna cin zaɓe ba tare da wata manufa ba; shugabannin jam’iyyu a dukkan matakai suna samuwa ne ta hanyar nune ba zaɓe ba; iyayen gida su suke juya siyasa ba jama’a ba; mafi yawan ‘yan Najeriya basu da cikakken ilimin siyasa da zaɓe; babu wani hukunci da ake yi wa masu maguɗin zaɓe; zaɓukan ƙananan hukumomi sun koma wasan yara; ana amfani da ƙarfin mulki wajen murƙushe marasa mulki a zaɓe; kotuna da yawa ba sa cikakken adalci ga korafe-korafen zaɓe; hukumar zaɓe ba ta da cikakken ‘yanci, da sauran wasu tarin matsaloli.

Kamar ko yaushe, Ranar Dimokraɗiyya ta wannan shekara ba ta wuce wani lokaci na shugabanni da ‘yan siyasa cika baki kan aiyukan da suka yi  a gwamnatance wanda ma’aikatansu suka tsara musu a rubuce ba. Wasu daga cikin waɗannan aikace-aikace ma maimaita zancensu kawai ake yi kowacce shekara. Kodayake hakan ba aibu bane tunda ranar dama ta kan dace da lokacin da suke bukukuwan cikarsu wasu shekaru  a kan mulki, amma ya kamata lokacin ya fi maida hankali wajen duba ci gaban mu wajen kyautata mu’amalarmu  a ɗaiɗaiku da kuma ƙasa baki ɗaya ta fuskar dimokraɗiyya.

Yin murna da mulkin farar hula na tsawon shekaru 19 a ƙasar da aka yi shekara da shekaru a karkashin mulkin soja ba zai zama kuskure ba, amma ya kamata murna ta wuce gaban bada hutu, gabatar da ƙasidu ko ɓarnatar da kuɗaɗe wajen talla a shafin jaridu. Ya kamata ta zama wani yanayi na duba yadda wannan mulki na farar hula ya kawo ci gaba wajen bai wa mutane dama ba tare da nuna bambanci ba.

Ba wanda zai tsammaci dimokraɗiyyarmu ta zamo ba ta da wata matsala ko aibu ba a cikin shekaru 19 kacal , amma dai ya kamata a tashi tsaye. Wane yunƙuri muka yi a cikin waɗannan shekaru? Waɗanne nasarori muka samu? Ina kura-kuran suke?

Twitter: @AmirAbdulazeez

No comments:

Post a Comment