23 ga Yuli, 2022
Wannan makon, zan fara da miƙa godiya ga dukkan ƴan Jigawa bisa goyon bayan da suke nuna mana, musamman ma waɗanda suke bibiyar manufofinmu ga Jihar. Haƙiƙa kun nuna mana karamci, kuma zan yi amfani da ƙwarin guiwar da na samu daga wannan goyon baya domin ganin ban baku kunya ba idan kuka bani dama. Cikin satuka huɗu da suka gabata, mun karɓi saƙonnin goyon baya, faɗakarwa da hamayya sama da guda 25,000; har yanzu muna nazarin wasu daga ciki domin ɗaukar matakan da suka dace. Muna roƙon ƙarin shawarwarinku, kuma muna son kowa ya tabbatar ya karɓi katin zaɓensa ko yin rajista ga wanda bai yi ba.
Kamar yadda na ambata a baya, tattaunawarmu ta yau, za ta maida hankali kan ilimi wanda shi ne abin da zamu fi bawa muhimmanci idan an zaɓe mu. A cikin jihohin Najeriya 10 mafi ƙarfi a fannin ilimi, guda 7 sune kuma mafi ƙarfin tattalin arziƙi. Wannan yana nufin ilimi shi ne tabbatacciyar hanyar samun ci gaba. A dunƙule, ƙudurinmu ga ilimi yana da kyau, muhimmanci da kuma faɗi. Mun yi tsare-tsare ingantattu a kan kyautata ilimin addini, boko, ilimin manya da ilimi na musamman a matakai daban-daban.
Kasancewar wannan ne karo na farko da zamu fara gabatar da abubuwan da muke da burin yi a aikace da kuma ƙudurorin da muke fatan aiwatarwa kai tsaye, akwai buƙatar na sake jaddada muhimmancin haɗin kan jama’ar Jigawa. Don haka ba zamu ci gaba da tsohuwar al’adar aiwatar da aiyukan gwamnati bisa tsarin masarautu kawai ba, maimakon hakan zamu yi aiyukan a kan gundarin buƙatu da muradan dukkan ƴan Jigawa ba tare da nuna bambanci ba. Idan an zaɓemu; zamu yi amfani da ci gaban ilimi a matsayin ginshiƙin samun haɗin kai.
Idan an zaɓe mu, muna da burin taɓa ko’ina a ɓangaren ilimi bakin gwargwado, amma zamu yi hakan daki-daki a hankali. Akwai aiyukan da zamu iya gamawa, akwai waɗanda kuma zamu assasa fandisho domin wasu su ci gaba. A taƙaice, zamu yi aiki domin inganta manhajar ilimin Islamiyya da kuma sake fasalin ilimin almajirai. Sauran abubuwan sune gyaran makarantu da ma’aikatun ilimi da ɗaukaka darajarsu; ilimi kyauta ga ƴaƴa mata, inganta ilimin yaƙi da jahilci da ilimin makiyaya; tallafin karatu na musamman ga masu karatu a fannonin neman ƙwarewa da kuma na ɗalibai masu hazaƙar lambar yabo ta ɗaya, sai kuma kyautata walwalar malamai da ma’aikatan ilimi.
Saboda muhimmancinsa, dukkanin naɗe-naɗen muƙamai a ɓangaren ilimi zasu gamu da tantancewa mai tsauri. Mutanen da suka fahimci manufofifnmu kuma suke da fasahar ƙirƙiro da wasu dabarun inganta manufofin a karan kansu ne kaɗai zamu naɗa. Ba zan yi gaggawa ko la’akari da siyasa wajen naɗa kwamishinan ilimi ba; maimakon haka, zan ɓata lokaci don bada dama ga waɗanda suke da sha’awa kuma suka cancanta su nema, mu kuma mu aunasu sosai kafin a basu dama.
Zamu ƙarfafi ɓangarorin sa idanu da ingantuwar aiki na ma’aikatun ilimi a matakin jiha da ƙaramar hukuma domin samun ingantacciyar koyarwa. Lokaci lokaci, zan dinga karɓar bayanai da kaina kuma kai tsaye a kan tasirin sauye-sauyen da zamu dinga kawowa. Zan dinga kai ziyarar ba-zata makarantu akai-akai don ganin ko ana bin tsarin kyautata koyo, koyarwa da sauran al’amuran ilimin baki ɗaya. Za a ware sashe na musamman wanda zai samu wakilci daga ofishin gwamna domin karɓar ƙorafe-ƙorafe daga jama’a a kan harkar ci gaban ilimi. Ba zamu yi wasa da ilimi ba.
Idan komai yana tafiya dai-dai, ilimi shi zai ɗauki kaso mafi tsoka a cikin kasafin kuɗin gwamnatinmu na kowacce shekara kuma zamu shawarci ƙananan hukumomi da su yi hakan. Kasancewar kuɗaɗaen gina harkar ilimi basa taɓa yawa, kuma gwamnati ba zata iya ɗaukar dukkan nauyin ba, zamu kafa Gidauniyar Tallafawa Ilimi ta Jigawa wato Jigawa Education Trust Fund (JETFund) a turance. Wannan gidauniya ko asusu zai dinga neman tallafi daga manyan masu taimako, ƴan kasuwa, ƴan kwangila, ƙungiyoyi da ma ɗaiɗaikun jama’a domin tallafa wa ilimi. Saboda a samu gaskiya da riƙon amana, za a tafiyar da wannan gidauniya bisa haɗin guiwar gwamnati da kwamitin amintattu mai wakilcin dattawan Jihar Jigawa.
Bari mu fara da ilimi a matakin farko, yanzu haka muna da makarantun firamare guda 2,490 a garuruwan dagatai 1,154 a faɗin Jiharmu. Zamu haɗa guiwa da malamai da masu ruwa da tsaki wajen auna yanayin da makarantun suke ciki kafin mu shiga aikin gyara da ɗaga darajar waɗanda suka lalace a cikinsu. Zamu yi hakan mataki-mataki inda zamu fara da mafi lalacewa daga nan kuma zamu kafa fandishon ci gaba da gyaran sauran ba tare da ɓata lokaci ba. Burinmu shi ne a cikin shekaru 4, mafi yawan makarantun Jigawa su kasance a cikin yanayi mai kyau. A kowacce mazaɓar Majalisar Tarayya, zamu gina katafariyar makarantar firamare ta gani ta faɗa wacce za ta zamo cibiyar alfaharin ilimi. A hankali kowacce ƙaramar hukuma zata samu irin wannan firamare Insha Allahu.
Yayin da muke gyara tare da gina wasu makarantun, buƙatar malamai zata ƙaru. Muna sane cewa ƙarancin malamai yana daga cikin manyan matsalolin makarantunmu. Don yin maganin wannan, zamu bawa ma’aikatan gwamnatin da basu da wani cikakken abin yi a ofisoshinsu horo domin mayar dasu makarantu. Zamu tabbatar da cewa ƴan bautar ƙasa ta NYSC da aka tura makarantu sun tsaya a kan aikinsu. Haka kuma zamu ɓullo da tsarin malaman wucin-gadi na sa-kai wanda zai ƙunshi ɗaukar matasan da suka kammala karatu kuma suka cancanta aikin koyarwa. Yayin aiwatar da duka waɗannan, zamu fito da wani tsari mai ɗorewa wanda zai kawar da matsalar ƙarancin malamai a makarantu. Daga ciki akwai ɗaga darajar aikin koyarwa ta yadda waɗanda basa ciki zasu yi sha’awar shiga, waɗanda suke ciki kuma baza su yi garajen fita ba.
Makarantunmu na sakandiri suna buƙatar kulawa. Yanzu haka muna da ƙananan sakandiri guda 571 da manya guda 269. Idan muka yi la’akari da cewa sama da ɗaliban Jigawa miliyan guda ne suke buƙatar ilimin sakandiri, to zamu ga cewa sun yi kaɗan. Ƴan Jigawa sama da miliyan 3 duk ƴan ƙasa da shekarun haihuwa 15 ne kuma 50% na wannan adadi sun kai shekarun shiga sakandiri. Insha Allahu zamu zaɓi wasu ƙananan sakandiri domin ɗaga darajarsu zuwa babba yayin da zamu gina wasu a hankali. A kowacce shiyyar Majalisar Dattawa, in Allah Ya yarda zamu gina katafariyar sakandiri sha-kundum wacce za a dinga koyar da ɗaliban kimiyya, kwamashiyal, art da fasaha a tsarin kwana da kuma jeka-ka-dawo.
Ilimin islamiyya ya samu kulawa a Jigawa tun bayan dawowar dimokradiyya a shekarar 1999, amma akwai buƙatar ƙarin aiki. Yanzu haka mafi yawancin Islamiyyu suna aiki ne ba tare da cikakken sa idanun gwamnati ba, ƙalilan daga cikinsu ne ma gwamnati ta san da zamansu. Muna da burin basu kulawa kamar na boko. Ta hanyar taimakon Malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki, zamu inganta manhajar koyarwa ta Islamiyyu a matsayin wani fandisho na shigar dasu ƙarƙashin kulawar gwamnati bakiɗaya. Da izinin Allah, zamu samar da ƙuduri wanda zai kyautata tare da inganta koyo da koyarwa a isalamiyyunmu a faɗin Jihar.
A jawabina na gaba,
zan haska ƙudurinmu na ilimin ƴaƴa mata,
yunƙurin farfaɗowa da inganta ilimin yaƙi da jahilci da na makiyaya, samar da
tallafin karatu ga ɗalibai masu hazaƙa da kuma shirin
kyautatawa malamai tare da kula da walwalarsu.
Gobe ta Allah ce
©Santurakin Dutse