Fassara

Thursday, July 28, 2022

Manufata ga Jihar Jigawa (II)

 

8 ga Juli, 2022

 

Daga: Mustapha Sule Lamido


Yau zan fara da roƙon al’umma da su je su karɓi katunan zaɓensu na din-din-din (PVC) a ofisoshin Hukumar Zaɓe dake ɗaukacin ƙananan hukumomi. Waɗanda kuma basu yi rajistar zaɓe ba, su daure su gaggauta yin hakan. Hukumar zaɓe ta INEC ta tsawaita lokacin yin rajistar zaɓe tun daga ranar 30 ga Yuni, 2022. Ina kira ga dukkan ƴan uwana mutanen Jigawa da mu yi amfani da wannan dama domin yin rajista ga wanda ba shi da ita. A yau kimanin katunan zaɓe na din-din-din guda miliyan 20 ne a jibge waɗanda ba a karɓa ba a faɗin Najeriya. Daga watannin Yuni zuwa Disambar 2021, akwai katunan zaɓe 33,183 da ba a karɓa ba a Jigawa kaɗai. Mu yi rajistar zaɓe, ita ce ƴancinmu wajen sauya makomar Jiharmu da ƙasar mu. 

Kafin mu ci gaba, ina so na yi ƙarin haske a kan abubuwa guda biyu; na farko, shawarwarinku zasu iya tasiri wajen kyautata waɗannan manufofi namu, hakan na nufin a koyaushe zamu iya yi musu gyaran fuska su dace da ƙarin buƙatunku da kuke turowa a kullum. Ƙofa a buɗe take don jin naku ra’ayoyin domin sakasu a inda ya dace. Dama ai a zahirin gaskiya manufofin ba wai nawa bane, na mutanen Jigawa ne gabaɗaya. Na biyu, zan ci gaba da tuntuɓar dukkan sassan jama’ar da nake so na hidimtawa saboda ba nine kaɗai na san maganin matsalolin da muke ciki ba. Wannan na nufin, ba wai burina in yi mulki  a Jigawa ba, burina shine mu haɗu daku tare don kai wa ga ci.

Don cimma burukanmu na ci gaban Jigawa, za mu buƙaci haɗin guiwa da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen ƙasarnan. Saboda haka, tuni na fara tattaunawa da Shugaban ƙasar gobe Insha Allah, Maigirma Atiku Abubakar kan buƙatar ba wa Jigawa kulawa ta musamman idan Allah Ya sahale masa. Sannan na fara ɗaukar matakai domin samun cikakkiyar fahimta kan yadda za a samu haɗin guiwa da hukumomi da ƙungiyoyi na ƙasashen duniya domin ci gaban Jigawa da mutanenta.

Daga bibiyar raayoyin jama’a, na fahimta cewar akwai masu shakku game da yiwuwar ko zamu iya aiwatar da waɗannan manufofi. Wasu masharranta ma har sun rawaito wai mun yi ikirarin gudanar da Jigawa ba tare da kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ba. Wannan ba gaskiya bane; mu ba masu siddabaru bane; abin da muke cewa shi ne muna da tsare-tsaren gajere da dogon zango waɗanda zasu kai Jigawa dukkan wani matakin ci gaba sannu a hankali. Nasarar aiwatar da waɗannan tsare-tsaren kuma zai dogara ne da irin haɗin kai da gogon bayan da jama’a suka bamu.

Yanzu haka an ayyana Jigawa a matsayin jiha ta uku mafi talauci a Najeriya inda 87.2% na mutanen ta suke cikin matsin rayuwa. Wannan wani abin takaici ne da ya kamata mu yi aiki tuƙuru tare domin canzawa. ƙiyasin ƙiddigar jama’a na 2022 ya nuna Jigawa tana da mutane 6,842,307, kenan jiharmu tana da isassun jama’ar da zasu iya canza makomarta. Idan da zamu ci nasarar ɓullo da wani yanayi da zai tallafawa mutane miliyan ɗaya kacal su dinga samun ƙarin N3,000 duk sati daga cikin kasuwancinsu, jimilla zasu samar da naira biliyan 3 a sati ko kuma naira biliyan 12 a wata. Wannan adadi ya ninka naira biliyan 5.6 da Jigawa ta karɓa daga Gwamnatin Tarayya a watan Yulin 2021 sau biyu da kusan kwata. Zamu iya cimma wannan tare.

Yanzu haka, muna da ayari na ƙwararru waɗanda suke tattara mana bayanai kan buƙatu da matsalolin ƙananan hukumomi 27. Zamu tsananta tara waɗannan bayanai idan mun ci zaɓe. Da zarar an rantsar damu wanda hakan zai bamu damar sanin muhimman bayanan sirri na gwamnati, zamu auna halin da Jigawa take ciki. Da zarar mun yi wannan, zamu saki jadawalin aiwatar da manufofin a cikin ƴan satuka. Waɗannan zasu yi tasiri kan lokacin da zamu ɗauka wajen aiwatar da manufofinmu. Kamar yadda na faɗa a baya, abin ba siddabaru ko aikin kwana guda bane.

Mataki na gaba shi ne gaggauta zaƙulo mutane masu kishi, jajircewa da ƙwarewa waɗanda zamu yi aiki dasu. Alhamdulillah, mataimakina Dr. Babandi Ibrahim Gumel ƙwararre ne, wanda tare da shi tunma daga yanzu mun fara rubuta sunayen nagartattun mutanen da zamu iya aiki da su. Damuwarmu ita ce ƙwarewarsu da kishinsu ba wai shahara ko buwayarsu ba. Zamu ɓullo da hanyar tantance ƙoƙarin jami’an gwamnati lokaci-lokaci, kuma za a maye gurbin duk wanda ba ya aiki yadda ya kamata. Babu wanda zai zama shafaffe da mai matuƙar ba Jigawa ce a gabansa ba.

Tunanin cewa haɗin kai ba zai samu ba Jigawa, wannan munana zato ne. Da zarar mun kafa amintacciyar gwamnati mai adalci ga kowa, za a samu dunƙulewar mutane domin kawo ci gaba. Haɗa kan mutane ba wai yana nufin kawar da bambance-bambancen dake tsakaninsu bane, yana nufin basu ƙwarin guiwa da tausasarsu ta yadda waɗancan bambance-bambance ba zasu hanasu yin aiki tare wajen ci gaban al’ummarsu ba. Muna da manufofi kaifiyyan kan haka waɗanda a yanzu ba zamu fito dasu fili ba sai lokacin ya yi. Zamu inganta mulki a ƙananan matakai ta hanyar tabbatar da gwamnatocin ƙananan hukumomi masu ƴanci da tsari. Zamu sake fasalin ma’aikatun gwamnati domin rage ɓarna, inganta aiki da mayar dasu hadiman al’umma ba na wasu tsirarun mutane ba.

Ina sane da fargabar wasunmu game da ƙwarewata. Ina da abubuwa guda uku da zan faɗa kan wannan. Farko dai, aikin gwamnati ko riƙe tarin muƙamai ba shi ne kaɗai ma’aunin ƙwarewa  Misali, da yawa basu taɓa shiga gwamnati ba, amma suna da baiwa iri-iri. Shugabanci ba aikin ofis bane kawai, ƙwararren ma’aikacin gwamnati zai iya zama rarraunan shugaba. Abu na biyu, a Najeriya tun 1999 mun ga yadda aka zaɓi ma’aikata da waɗanda suka re tarin muƙaman gwamnati tsawon shekaru amma basu tsinana abin kirki ba. Marigayi Abubakar Rimi ya zama gwamnan tsohuwar Jihar Kano yana ɗan ƙasa da shekaru 40 a lokacin da wasu suke ganin bai ƙware ba, amma ya zamo babban abin alfahari a tarihin Najeriya. Na uku, sarrafa kujerar gwamna ba aikin mutum guda bane. Kujera ce da ake gudanar da ita da taimakon Majalisar Zartarwa da ma’aikatan gwamnati tare da sa idanun Majalisar Dokoki da ɓangaren Shari’a. Gwamna ba wai mutum ne da yake da ikon yin abin da ya ga dama ko yanke hukunci shi kaɗai kai tsaye ba.

Da wannan, ina ganin na kammala muƙaddimar manufofina ga Jihar Jigawa. Nan gaba, zan maida hankali kai tsaye wajen bayanin gundarin abubuwan dake gabanmu waɗanda muke sa rai zasu kai jiharmu ga ci. Kan gaba a wannan batutuwa shi ne ilimi, sannan ilimi sannan kuma ƙarin ilimi. Na gode.

    

Gobe ta Allah ce

©Santurakin Dutse

No comments:

Post a Comment