Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Ta Yaya Za a Gyara Ilimi A Najeriya?

16 Ga Yuni, 2015.


Daga: Amir Abdulazeez

A
n jima ana tattaunawa tare da yin yunƙuri a kan batun farfaɗo tare da inganta ilimi a Najeriya, amma kusan babu wani abu bayyananne a ƙasa wanda ya ke nuna cewar an samu nasara ko kuma ana kan hanyar samun nasarar. Wataƙila wani ya tambaya, me ya sa za a farfaɗo da ilimi; shin a wane hali ya ke? Duk abin da ake zancen farfaɗo da shi, to ana  nufin a wani lokaci can a baya, ya na da ƙarfinsa da kuma kuzarinsa, amma a yanzu ya yi rauni. Haƙiƙa shekaru  kamar 30 zuwa sama baya, ilimin boko a Najeriya ya na da inganci ƙwarai da gaske; duk fannin da aka ce mutum ya karanta, to ba a wata tantama akan ƙwarewarsa a wannan fannin ko da kuwa shi ya fi kowa rashin mai da hankali a ajinsu. Wanda yak e da cikakkiyar shaidar gama makarantar sakandiri, ya fi mai karatun digiri a yanzu ilimi. Babu wanda ya ke tsoron tura ‘ya’yansa makarantar gwamnati domin ya na da tabbacin cewar zai samu ingantaccen ilimi. Amma a yanzu in dai ilimi mai inganci a ke so, sai dai makarantar kuɗi.

Idan muka duba tarihin shugabanni da manya-manyan masu faɗa-a-ji na ƙasarnan, sai mu ga cewar makarantar gwamnati ya yi kuma dukkan wani ilimi da wata ƙwarewa da ya ke taƙama da ita, to wancan ilimi shi ne tushensa. Abin da ya ke faruwa a wannan zamanin shi ne, ilimin ya na ƙara yawaita, amma ingancinsa ya na ƙara lalacewa. A wancan lokacin, ilimin ya na da ƙarancin yawa sakamakon rashin yawan jama’a da kuma rashin rungumarsa da al’umma ba su yi ba sosai, don haka ilimin boko sai wane da wane, to amma kuma ya na da matukar inganci.

Mafi yawancin makarantun kudi ba su haura shekarau 30 zuwa 35 da kafuwa ba, ma’ana an kafasu daga shekarar 1975 zuwa sama. Ko a wancan lokaci, ba wai an yi su ba ne saboda rashin ingancin ilimi a makrantun gwamnati, a’a ; an yi su ne saboda neman kuɗi da kuma ƙarancin makarantun su kansu. Yanzu kuwa, kusan babu inda  ake samun ilimi mai inganci sai a makarantun kuɗi masu zaman kansu. Makarantar gwamnati ta zama larura, babu wanda yak e son ta sai dole, ba don komai sai don cewar ba a bayar da wani ilimin kirki a cikinsu. A kan samu yara sun gama firamare amma ba za su iya rubuta ko da sunansu ba, haka za su tafi sakandire su gama, ba su san komai ba.

Muhimmancin ilimi ga rayuwar Ɗan Adam abu ne kusan da ba zai iya misaltuwa ko kwatantuwa ba. A dukkan abin da mutum zai yi dole sai ilimi ya shigo ciki; tun daga kan zaman rayuwar shi kansa, addini, sana’a har izuwa mu’amala da zamantakewa. Wannan ta sa dole ne a tsaya a gyara shi kuma a inganta shi domin samun kyakkyawar makoma.

Matsalar da aka sha fama da ita a baya shine gudun ilimi da ake yi musamman a Arewacin Najeriya, to amma yanzu wannan matsalar ta kau domin mafi  yawan mutane a yanzu sun koma makaranta kuma ba sa wasa wajen saka ‘ya’yansu a makaranta. Dawowar mulkin siyasa a shekarar 1999 ta bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wannan. Mutane kusan kowa ba ya son a bar shi a baya kuma ya na so a dama da shi ko dai a cikin siyasa ko gwamnati ko a wani abu mai alaƙa da ita. Wannan ita ta sa yawan masu neman ilimi ya dinga ƙaruwa tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu a Najeriya. To amma ingancin ilimin kuma fa; baya ya ke ci ko gaba?

Idan muka ɗauki tsarin ilimi  a Najeriya tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, sai mu ga cewa akwai matsaloli masu tarin yawa da suka dabaibaye shi. Matsalolin sun haɗa da rashin ingantattun malamai, rashin kyautatwa ma’aikatan ilimin, rashin kishin ilimin, rashin kyawun guraren ɗaukar ilimin, rashin kayan aiki  tare kuma da rashin aiki da shi kansa ilimin. Kodayake gwamnatoci a matakin tarayya, jihohi da ƙananan  hukumomi sun taka rawar gani a shekraun baya musamman daga 1999 zuwa 2003 wajen ganin ta samar da kyakkyawan yanayin karatu ta hanyar gine-ginen da gyare-gyaren ajujuwa, to amma har yanzu hakan bai wadatar ba domin yawan mutanen da suke buƙatar karatun ya ninninka ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi wajen samar da shi da kuma inganta shi.

Duk ma ba waɗannan matsalolin da suke zayyane a sama ne babbar mishkila ba, babbar matsalar ita ce kullum ingancin ilimin baya ya ke yi kuma gwamnati ta kasa samo bakin zaren yadda za ta gyara al’amarin. Abin kuma ƙara dagulewa ya ke duba da cewa kullum mutanen Najeriya ƙara yawa suke yi, kuma masu buƙatar ilimin ƙara ninninkawa suke yi. Wani batun kuma shi ne abubuwa sun yi wa gwamnati yawa sosai kuma kullum kuɗaɗen shigar ta ko dai ƙara baya suke yi ko kuma darajar su ƙara faɗuwa ta ke yi saboda matsalar hauhawar farashi.

Duba da wannan, akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki hanya mai sauƙi kuma nagartacciya wajen ganin ta ceto ilimi a ƙasaranan. Masu iya magana na cewa: ‘in duka ya yi yawa, na ka ake karewa’. Ko da ba zai yiwu a bi dukkan matakan inganta ilimi a Najeriya ba, to ya kamata a bi wasu daga cikin hanyoyin. Hanyoyin kuwa sun haɗa da inganta harkar malanta da koyarwa, bai wa ilimin martaba da daraja shi, sannan da tabbatar da cewa ana aiki da ilimin.

Babban mataki da gwamnati za ta ɗauka, shi ne ta bai wa kula da malamai fifiko akan komai. Wajibi ne gwamnati ta tabbatar cewa sai malamin da ya ke da cikakken ilimi da ƙwarewa ne kaɗai zai koyar a dukkan matakai. Bayan haka ta tabbatar ta na ɗaukar nauyin malaman lokaci bayan lokaci domin ƙaro karatu da yin kwasa-kwasai waɗanda za su ƙara musu ƙwarewa da sanin makamar aiki. Ban da wannnan, ya zama lallai ta ɗauki isassun malaman ta yadda aiki ba zai dinga yi wa malami yawa ba. Wato ya kasance malami bai fi ya shiga aji sau biyu ko uku a rana ba domin samun sararin yin bincike-bincike da sauran abubuwa masu alaƙa da kula da ɗalibai da kuma inganta iliminsa, sannan kuma ya kasance malami ya na koyar da ɗalibai kamar 30 zuwa 40 a lokaci ɗaya ta yadda zai iya kula da su gabaɗaya kuma ya nazarci yanayin ganewarsu da fahimtarsu amma ba ya saka ɗalibai sama da 100 a gabansa ba. Bayan haka, a samar da kyakkyawan albashi da alawus-alawus ga malaman makaranta, idan da hali ma ya kasance su suka fi kowa kyawaun albashi a cikin ma’aikatan ƙasa. Wannan zai  sa a dinga alfahari da sana’ar koyarwa  a maimakon a ƙyamace ta. Bayan duka wannan kuma sai a samar da wani tsari na sanya ido a kan malamai tare da yin tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama ya na wasa da aikinsa. Idan a ka yi wa malamai haka, to ko ba a gyara ajujuwa ba, ilimi zai farfaɗo domin sai da malami za a samu makaranta amma makaranta ba za ta samu ba in ba malami. Saboda haka gara a gyara malami a ƙyale makaranta a maimakon a ƙyale malami a gyara makaranta. Mutanen da a baya wasu ma a ƙarƙashin bishiya suka dinga karatu, amma saboda akwai ingantattun malamai, sai suka sami ilimi mai inganci.

Wani abu da gwamnati ya kamata kuma ta kiyaye shi ne muhimmancin ilimi daga tushe. Ya kamata gwamnatoci su fi mayar da hankula kan ilimin firamare fiye da na sakandire da na jami’a. Alamu sun nuna kamar cewa gwamnati, musamman ta tarayya ta fi damuwa da jami’o’i, ta fi yin aikace-aikace tare da kula da malaman jami’a fiye da sauran. Kuskuren a nan shine, ana ɗora gini ne  akan fandisho mara kyau da inganci. Ilimin firamare shi ne fandisho. Maimakon kafa jami’o’i barkatai waɗanda su kan lashe maƙudan kuɗaɗe wajen kula da su, kamata ya yi a koma a inganta ilimin firamare, domin mafi yawa tun a can suke baro ilimin.

Wata muhimmiyar matsala da ilimi ya ke fuskanta a Najeriya, ita ce ɗaukar sa da aka yi a matsayin hanyar neman abinci kaɗai. Misali kusan kowa ya na yin ilimin boko ne saboda ya gama ya karɓi takardar shaida domin ya samu aiki. Wannan ita ta kawo koma baya da cikas akan ainihin ginshiƙi da manufar yin ilimin shi kansa. Asali dai ilimi ana yin sa ne domin a koyi yadda za a sarrafa rayuwar Ɗan Adam, to amma yayin da aka ƙasƙantar da shi ya koma hanyar neman sana’a kaɗai, to dole a bi dukkan hanyoyi marasa kyau da nagarta domin ganin an same shi tunda buƙatar kawai ita ce a kawo shaidar karatu domin a ɗauki mutum aiki. Wannan ta sa manufar ilimi ta asali ta samu mummunar tawaya.

Wani ƙarin naƙasu kuma shi ne, shi kansa ɗaukar aikin, ba a yin sa dai-dai da irin ilimin da mutum ya karanta. Alfarma ta yi yawa a cikinsa, misali mutum zai karanta ilimin tarihi, amma sai ya ɓige da aikin banki, ko ya karanci ilimin fasahar injiniyanci amma sai ya ƙarke da aiki a matasyin sakatare mai sarrafa takardu.  Idan da akwai wani tasri da zai dinga tabbatar da cewa kowa abin da ya karanta, shi zai aikata, to wataƙila kowa zai mayar da hankali sosai a makaranta wajen ganin ya ƙware akan fannin ilimin da ya ke karanta gudun ka da ya ji kunya a wajen sharar fagen ɗaukar aiki ko a wajen gudanar da aikin kansa.

Abu na ƙarshe da ya kamata mu kula da shi shi ne, mu guji ɗaukaka takardar shaidar samun ilimi fiye ma da ilimin shi kansa. Wannan kuskure ne ba ƙarami ba. A zamanin yanzu sai ka ga mutum ya na da ilimin, amma saboda ba shi da shaidar ilimin sai a ƙasƙantar da shi akan wanda ya ke da takardar shaidar ilimin amma ba shi da ilimin a kansa. Wannan ita ta sa ake ta rububin samun takardar shaidar ilimi a maimakon ilimin. Zai yi kyau a dinga gwada ilimin mutum a aikace fiye da akan takarda domin wannan za ta sa kowa ya shiga taitayinsa a makaranta wajen ganin ya tsaya ya samu ingantaccen ilimi.
Ya zama wajibi a kan mu, da mu da gwamnati, mu taru mu ceto ilimi daga durƙushewa a Najeriya.


© Malam Amir Abdulazeez 2015.

No comments:

Post a Comment