10 Ga Afrilu, 2016
Daga: Amir Abdulazeez
R
|
anar 28 ga watan Maris aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da ya kafa
tarihi a Najeriya. Zaɓen da ya yi sanadiyyar kawar da jam’iyya mai mulki ya
kawo jam’iyyar adawa kan mulki a karo na farko a tarihin dimokraɗiyyar Najeriya. Haƙiƙa irin
wannan ba ta cika faruwa ba a Nahiyar Afrika tun daga lokacin da turawan mulkin
mallaka suka bai wa ƙasashen nahiyar ‘yancin kai har zuwa yau. Hasalima, kullum
al’amuran zaɓuka ƙara lalacewa suke yi saboda ƙudurin da mafi yawan shugabannin
Afrika suke da shi na dauwama a kan mulki.
Jam’iyyar APC ta ɗare kan mulki bayan tsawon shekaru 12 da jam’iyyun adawa
suka shafe suna fafutukar ganin sun kawar da PDP daga mulki ba tare da sun samu
wata ƙwaƙƙwarar nasara ba. Bayan kujerar shugaban ƙasa, ta kuma samu nasarar
kafa rinjaye a Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma Dattijai ta Sanatoci. Bugu
da ƙari, ta samu damar kafa gwmanati a jihohi 23 cikin 36 da ake dasu a ƙasar
nan. Saboda haka tun daga sama har ƙasa, sama da 65% na madafun ikon
gwamnatocin ƙasarnan a hannun jam’iyyar yake kai tsaye.
Daga kafa gwamnatin APC zuwa yanzu, aƙalla an samu shekara ɗaya; wannan na
nufin cewar jam’iyyar ta cinye kashi ɗaya bisa huɗu na wa’adin da ‘yan Najeriya
suka zaɓe ta tayi. Sakamakon haka, akwai buƙatar a kalli irin jagorancin da
gwamnatin ta APC ta gabatar a tsawon wannan lokaci domin ganin ko kwalliya ta
fara biyan kuɗin sabulu. Kafin a yi hakan, akwai buƙatar a yi waiwaye adon
tafiya don ganin irin rawar da PDP ta taka a tsawon shekaru 16.
Tsakanin Gyara da Kuma Ɓarnar
PDP
A jimlace zamu iya cewar, PDP ta gaza, nesa ba kusa ba wajen ciyar da
Najeriya gaba a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki domin kuwa mafi yawan
matsalolin da muke ciki a 1999 a lokacin da jam’iyyar ta fara mulki, sune dai
suke damunmu har a shekarar 2015 da ta bar mulki. To amma kuma, duk da tarin ɓarna
da lalata ƙasa da mafi yawancin ‘yan Najeriya suke kallon jam’iyyar PDP ta yi, akwai
wasu abubuwa na kirki da ta taɓuka. Babu shakka dole mu yarda cewar PDP ta taka
rawar gani sosai wajen lalata al’amuran zaɓe da nagartacciyar dimokraɗiyya a ƙasarnan
tare da ɗaukaka matsayin cin hanci da rashawa da yi wa doka karan tsaye a Najeriya.
To amma ta wani ɓangare, PDP ɗin, musamman
a ƙarƙashin jagorancin Obasanjo da ‘Yaradua, ta taimaka wajen farfaɗo da
tattalin arziƙin ƙasa. Misali, lokacin da Obasanjo ya karɓi mulki a hannun
sojoji, asusun ajiyar Najeriya na ƙasar waje, abin da yake cikinsa bai
wuce dala biliyan huɗu ba kacal, amma
lokacin da ya bar mulki zuwa lokacin da
‘Yaradua ya rasu, akwai sama da dala miliyan 60 a cikin wancan asusu.
Kodayake ana kallon Jonathan a matasayin wanda yafi kowa ɗaurewa cin hanci
da rashawa gindi, amma alokacinsa ne zaɓuka suka fara gyaruwa, abinda har ya
kai ga samar da ingantaccen zaɓen da ya kawar da shi daga mulki.
Duk da irin wadaƙa da kuɗin gwamnati da ake kallon PDP ta yi, akwai abubuwa
da ta tafi ta bari wanda APC zata iya ɗorawa a kai.
Halin da APC ta Samu da Najeriya
Jam’iyyar APC ta karɓi Najeriya a lokacin da ƙasar take cikin wani
mawuyacin hali. Farko dai akwai rarrabuwar kai da ƙin jinin juna bisa dalilai
na addini da ƙabilanci da ya kai matakin ta’azzarar da bai taɓa kaiwa ba tun
bayan gama yaƙin basasa na Biafra a shekarar 1970. Bayan haka, akwai faɗuwar
farashin man fetur wanwar wanda wani lokaci tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013,
farashin gangarsa guda ɗaya ta kai dalar Amurka 100 zuwa 140. A kwanakin baya,
ganga ɗaya sai da ta kai dala 30, a yanzu ana sayar da ita tsakanin dala 39
zuwa 41. Wannan na nufin cewar kuɗin shigar Najeriya ya ragu da kaso kusan biyu
bisa uku. Jam’iyyar APC ta samu Najeriya a cikin badaƙƙaloli daban-daban na
almundahana da kuɗin ƙasa, ta samu an yi wa asusun ƙasa wakaci ka tashi tun
daga kan matakin tarayya har zuwa jihohi.
Jam’iyyar APC ta gaji babbar matasala wacce ita ce ta harkar tsaro. Daga
cikin wannan matsala akwai Boko Haram, fashi da makami, satar shanu, garkuwa da
mutane, tada zaune tsaye a yankin Niger-Delta, satar ɗanyen mai, bangar siyasa,
faɗan Fulani makiyaya da manoma, rikice-rikicen addini da na ƙabilanci a sassa
daban-daban da dai sauransu.
Jam’iyyar ta gaji sauran matsaloli waɗanda suka haɗa da rashin ɗorarren
samuwar man fetur, dogaron tattalin arziƙin ƙasa a kan man fetur, durƙushewar
noma, rashin wadatacciyar wutar lantarki, rashin ingancin noma da masana’antu
da dai sauransu.
A ina APC ta Samu Nasara Cikin
Shekara Guda?
Duk da yake ba zai yiwu a ce an ga ƙwaƙƙwaran sauyi a cikin shekara guda
ba, amma an ce wai Juma’ar da zata yi kyau, daga Laraba ake gane ta. Abu na
farko muhimmi da gwamnatin APC ta fara yi shi ne wajen taimaka wa jihohi 27 da
maƙudan kuɗaɗe a matsayin rance domin su samu su biya tarin albashin da
ma’aikatansu suke binsu na wata da watanni. Wannan ta taimaka wajen ceto mafi
yawan jihohin da ƙananan hukumominsu daga faɗawa mawuyacin hali.
Gwamnatin Tarayya ta APC ta taka rawar gani ta fuskar yaƙi da Boko Haram,
duk da dai cewar har yanzu akwai matasalar a Arewa maso gabashin ƙasarnan amma
nasarar da aka samu a bayyane take. Sai dai kuma a sauran matsalolin tsaro
irinsu satar shanu, rikicin Fulani da manoma, garkuwa da mutane, har yanzu
gwamnatin tana da sauran aiki a gabanta.
Jam’iyyar APC ta duƙufa gadan-gadan wajen yaƙi da cin hanci da rashawa
musamman wajen tuhumar jami’an gwamnatin da suka gabata. Misali shine yadda
gwamnatin ta bankaɗo badaƙƙalar sayen makamai a ofishin Sambo Dasuki da kuma
yadda EFCC ta samu wani sabon ƙarfi wajen tuhuma da gurfanar da waɗanda ake
tuhuma da satar dukiyar gwamnati a gaban kotu. Sai dai kuma wani hanzari ba
gudu ba shine, gwamnatin har yanzu ba ta samu nasarar tabbatar da ko da mutum ɗaya
a matasyin mai laifi ba a gaban kotu a tsawon sheka guda. Idan aka tafi a haka,
mutum nawa zata samu damar kammala shari’unsu a cikin shekaru huɗu? Bayan haka,
ana zargin gwamnatin da ƙyale wasu shafaffu da mai ‘yan jam’iyyar APC tare da
maida hankali a kan ‘yan adawa kawai. Sannan kuma ana ganin gwamnatin a wasu
lokuta ba ta yin biyayya ga umarnin kotu a wannan yaƙi da take yi.
Duk zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ƙarƙashin Hukumar Zaɓe ta mulkin
APC, an kwatanta adalci. Ko jama’iyyar adawa ta PDP zata shaidi hakan. Wannan
nasara ce babba.
Wata nasara kuma ita ce, yadda gwanatin take ƙoƙarin tsaftace al’amaura a
dukkan matakai na gudanarwa. Banda haka, ƙimar Najeriya ta farfaɗo ƙwarai da
gaske a idon duniya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, duk da cewa wasu suna sukar
Shugaba Buhari a kan yawan tafiye-tafiye da yake yi zuwa ƙasashen ƙetare.
A Ina Matsalolin APC Suke a
Shekara Guda?
Gwamnatin jam’iyyar APC ta ɗauki sama da watanni shidan farkon mulkinta tana
jan ƙafa da sanɗa; ta shafe tsawon wannan lokaci ba tare da ministoci da sauran
jami’an gwamnati ba. Wannan ta taimaka ƙwarai wajen kawo wa gwamnatin cikas a
kan tafiyar da aiyukanta. Har kawo yanzu akwai naɗe-naɗen masu muhimmanci da
gwamnatin take ta jan ƙafa wajen yinsu.
Bayan haka, gwamnatin tarayya ta APC har yanzu bata yi wani yunƙuri ba a
hukumance na ganin ta haɗa kan ‘yan Najeriya duba da yadda kawuna suka rarrabu
a kan siyasa, addini, ƙabilanci da ɓangaranci dab da zaɓen shekarar 2015.
Wannan rarrabuwar kai har yanzu tananan tana ƙara cigaba, kuma ɗaya daga cikin
sakamakonta kuwa shine sabon yunƙurin kafa ƙasar Biafra da aka taso da shi ‘yan
satattaki kaɗan bayan kafa sabuwar gwamnatin. Bugu da ƙari, ‘yan Kudu suna yi
wa gwamnatin kallon kamar tana fifita ‘yan Arewa.
Babbar matasalar gwamnatin jam’iyyar APC ita ce yadda ta kasa shawo kan
matsalar man fetur a Najeriya wacce ake ta fama da ita. Banda haka, ta kasa tsayawa
a kan wata tartibiyar manufa dangane da sashen man fetur. Yau ta faɗi wani abu,
gobe kuma sai ta canza, jibi kuma sai ta aikata wani abin daban.
Dangane da tattalin arziƙi, gwamnatin ta kasa shawo kan tashin farashin
Dalar Amurka da sauran kuɗaɗen ƙara waje da muke tsananin buƙata domin sayo
kayayyaki daga waje. A gefe ɗaya kuma, tsadar kayayyaki sai ƙara ta’azzara take
yi.
Kasafin kuɗin 2016 wanda shine na farko da jam’iyyar APC ta yi a mulkinta
yazo da kura-kurai da aringizo da yawa-wani abu da ba a yi tsammaninsa a gurin
gwamnati mai taƙama da gaskiya da riƙon amana ba.
Me ya kamata APC ta Yi?
Har yanzu jam’iyyar APC tana da sauran shekaru uku a cikin huɗun da aka zaɓeta
ta yi; akwai buƙatar ta yi waiwayen watannin da ta shafe a kan mulki kuma ta yi wa kanta alƙalanci da
kanta. Inda ta yi kurakurai, to ta yi ƙoƙari da gaggawar gyarawa, inda ta samu
nasara sai ta yi ƙoƙarin ɗorawa a kai.
Maganganu da ƙulle-ƙullen siyasar 2019 da suka dabaibaye jam’iyyar tun
kafin a je ko’ina, kamata ya yi a ajiye su waje ɗaya, ‘yan jam’iyyar su haɗa
kai don ganin sun sauke nauyin da jama’ar Najeriya suka ɗora musu tukunna.
Yana da kyau jam’iyyar ta bar ƙofarta a buɗe wajen karɓar shawarwari komai ɗacinsu
kuma koda daga wurin maƙiyansu ne. Bayan haka kuma ya kamata su sani cewar
lokaci ba abokinsu bane a yanzu, dole sai sun zage damtse.
©Mujallar
Mikiya 2016