Fassara

Sunday, April 17, 2016

Shekara ɗaya a Gwamnatin APC: Ko Kwalliya ta Fara Biyan Kuɗin Sabulu?

10 Ga Afrilu, 2016


Daga: Amir Abdulazeez

R
anar 28 ga watan Maris aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da ya kafa tarihi a Najeriya. Zaɓen da ya yi sanadiyyar kawar da jam’iyya mai mulki ya kawo jam’iyyar adawa kan mulki a karo na farko a  tarihin dimokraɗiyyar Najeriya. Haƙiƙa irin wannan ba ta cika faruwa ba a Nahiyar Afrika tun daga lokacin da turawan mulkin mallaka suka bai wa ƙasashen nahiyar ‘yancin kai har zuwa yau. Hasalima, kullum al’amuran zaɓuka ƙara lalacewa suke yi saboda ƙudurin da mafi yawan shugabannin Afrika suke da shi na dauwama a kan mulki.

Jam’iyyar APC ta ɗare kan mulki bayan tsawon shekaru 12 da jam’iyyun adawa suka shafe suna fafutukar ganin sun kawar da PDP daga mulki ba tare da sun samu wata ƙwaƙƙwarar nasara ba. Bayan kujerar shugaban ƙasa, ta kuma samu nasarar kafa rinjaye a Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma Dattijai ta Sanatoci. Bugu da ƙari, ta samu damar kafa gwmanati a jihohi 23 cikin 36 da ake dasu a ƙasar nan. Saboda haka tun daga sama har ƙasa, sama da 65% na madafun ikon gwamnatocin ƙasarnan a hannun jam’iyyar yake kai tsaye.

Daga kafa gwamnatin APC zuwa yanzu, aƙalla an samu shekara ɗaya; wannan na nufin cewar jam’iyyar ta cinye kashi ɗaya bisa huɗu na wa’adin da ‘yan Najeriya suka zaɓe ta tayi. Sakamakon haka, akwai buƙatar a kalli irin jagorancin da gwamnatin ta APC ta gabatar a tsawon wannan lokaci domin ganin ko kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu. Kafin a yi hakan, akwai buƙatar a yi waiwaye adon tafiya don ganin irin rawar da PDP ta taka a tsawon shekaru 16.

Tsakanin Gyara da Kuma Ɓarnar PDP
A jimlace zamu iya cewar, PDP ta gaza, nesa ba kusa ba wajen ciyar da Najeriya gaba a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki domin kuwa mafi yawan matsalolin da muke ciki a 1999 a lokacin da jam’iyyar ta fara mulki, sune dai suke damunmu har a shekarar 2015 da ta bar mulki. To amma kuma, duk da tarin ɓarna da lalata ƙasa da mafi yawancin ‘yan Najeriya suke kallon jam’iyyar PDP ta yi, akwai wasu abubuwa na kirki da ta taɓuka. Babu shakka dole mu yarda cewar PDP ta taka rawar gani sosai wajen lalata al’amuran zaɓe da nagartacciyar dimokraɗiyya a ƙasarnan tare da ɗaukaka matsayin cin hanci da rashawa da yi wa doka karan tsaye a Najeriya. To amma ta wani ɓangare, PDP ɗin, musamman  a ƙarƙashin jagorancin Obasanjo da ‘Yaradua, ta taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa. Misali, lokacin da Obasanjo ya karɓi mulki a hannun sojoji, asusun ajiyar Najeriya na ƙasar waje, abin da yake cikinsa bai wuce  dala biliyan huɗu ba kacal, amma lokacin da ya bar mulki zuwa lokacin  da ‘Yaradua ya rasu, akwai sama da dala miliyan 60 a cikin wancan asusu.
Kodayake ana kallon Jonathan a matasayin wanda yafi kowa ɗaurewa cin hanci da rashawa gindi, amma alokacinsa ne zaɓuka suka fara gyaruwa, abinda har ya kai ga samar da ingantaccen zaɓen da ya kawar da shi daga mulki.
Duk da irin wadaƙa da kuɗin gwamnati da ake kallon PDP ta yi, akwai abubuwa da ta tafi ta bari wanda APC zata iya ɗorawa a kai.

Halin da APC ta Samu da Najeriya
Jam’iyyar APC ta karɓi Najeriya a lokacin da ƙasar take cikin wani mawuyacin hali. Farko dai akwai rarrabuwar kai da ƙin jinin juna bisa dalilai na addini da ƙabilanci da ya kai matakin ta’azzarar da bai taɓa kaiwa ba tun bayan gama yaƙin basasa na Biafra a shekarar 1970. Bayan haka, akwai faɗuwar farashin man fetur wanwar wanda wani lokaci tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013, farashin gangarsa guda ɗaya ta kai dalar Amurka 100 zuwa 140. A kwanakin baya, ganga ɗaya sai da ta kai dala 30, a yanzu ana sayar da ita tsakanin dala 39 zuwa 41. Wannan na nufin cewar kuɗin shigar Najeriya ya ragu da kaso kusan biyu bisa uku. Jam’iyyar APC ta samu Najeriya a cikin badaƙƙaloli daban-daban na almundahana da kuɗin ƙasa, ta samu an yi wa asusun ƙasa wakaci ka tashi tun daga kan matakin tarayya har zuwa jihohi.
Jam’iyyar APC ta gaji babbar matasala wacce ita ce ta harkar tsaro. Daga cikin wannan matsala akwai Boko Haram, fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane, tada zaune tsaye a yankin Niger-Delta, satar ɗanyen mai, bangar siyasa, faɗan Fulani makiyaya da manoma, rikice-rikicen addini da na ƙabilanci a sassa daban-daban da dai sauransu.
Jam’iyyar ta gaji sauran matsaloli waɗanda suka haɗa da rashin ɗorarren samuwar man fetur, dogaron tattalin arziƙin ƙasa a kan man fetur, durƙushewar noma, rashin wadatacciyar wutar lantarki, rashin ingancin noma da masana’antu da dai sauransu.

A ina APC ta Samu Nasara Cikin Shekara Guda?
Duk da yake ba zai yiwu a ce an ga ƙwaƙƙwaran sauyi a cikin shekara guda ba, amma an ce wai Juma’ar da zata yi kyau, daga Laraba ake gane ta. Abu na farko muhimmi da gwamnatin APC ta fara yi shi ne wajen taimaka wa jihohi 27 da maƙudan kuɗaɗe a matsayin rance domin su samu su biya tarin albashin da ma’aikatansu suke binsu na wata da watanni. Wannan ta taimaka wajen ceto mafi yawan jihohin da ƙananan hukumominsu daga faɗawa mawuyacin hali.
Gwamnatin Tarayya ta APC ta taka rawar gani ta fuskar yaƙi da Boko Haram, duk da dai cewar har yanzu akwai matasalar a Arewa maso gabashin ƙasarnan amma nasarar da aka samu a bayyane take. Sai dai kuma a sauran matsalolin tsaro irinsu satar shanu, rikicin Fulani da manoma, garkuwa da mutane, har yanzu gwamnatin tana da sauran aiki a gabanta.
Jam’iyyar APC ta duƙufa gadan-gadan wajen yaƙi da cin hanci da rashawa musamman wajen tuhumar jami’an gwamnatin da suka gabata. Misali shine yadda gwamnatin ta bankaɗo badaƙƙalar sayen makamai a ofishin Sambo Dasuki da kuma yadda EFCC ta samu wani sabon ƙarfi wajen tuhuma da gurfanar da waɗanda ake tuhuma da satar dukiyar gwamnati a gaban kotu. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba shine, gwamnatin har yanzu ba ta samu nasarar tabbatar da ko da mutum ɗaya a matasyin mai laifi ba a gaban kotu a tsawon sheka guda. Idan aka tafi a haka, mutum nawa zata samu damar kammala shari’unsu a cikin shekaru huɗu? Bayan haka, ana zargin gwamnatin da ƙyale wasu shafaffu da mai ‘yan jam’iyyar APC tare da maida hankali a kan ‘yan adawa kawai. Sannan kuma ana ganin gwamnatin a wasu lokuta ba ta yin biyayya ga umarnin kotu a wannan yaƙi da take yi.
Duk zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ƙarƙashin Hukumar Zaɓe ta mulkin APC, an kwatanta adalci. Ko jama’iyyar adawa ta PDP zata shaidi hakan. Wannan nasara ce babba.
Wata nasara kuma ita ce, yadda gwanatin take ƙoƙarin tsaftace al’amaura a dukkan matakai na gudanarwa. Banda haka, ƙimar Najeriya ta farfaɗo ƙwarai da gaske a idon duniya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, duk da cewa wasu suna sukar Shugaba Buhari a kan yawan tafiye-tafiye da yake yi zuwa ƙasashen ƙetare.

A Ina Matsalolin APC Suke a Shekara Guda?
Gwamnatin jam’iyyar APC ta ɗauki sama da watanni shidan farkon mulkinta tana jan ƙafa da sanɗa; ta shafe tsawon wannan lokaci ba tare da ministoci da sauran jami’an gwamnati ba. Wannan ta taimaka ƙwarai wajen kawo wa gwamnatin cikas a kan tafiyar da aiyukanta. Har kawo yanzu akwai naɗe-naɗen masu muhimmanci da gwamnatin take ta jan ƙafa wajen yinsu.
Bayan haka, gwamnatin tarayya ta APC har yanzu bata yi wani yunƙuri ba a hukumance na ganin ta haɗa kan ‘yan Najeriya duba da yadda kawuna suka rarrabu a kan siyasa, addini, ƙabilanci da ɓangaranci dab da zaɓen shekarar 2015. Wannan rarrabuwar kai har yanzu tananan tana ƙara cigaba, kuma ɗaya daga cikin sakamakonta kuwa shine sabon yunƙurin kafa ƙasar Biafra da aka taso da shi ‘yan satattaki kaɗan bayan kafa sabuwar gwamnatin. Bugu da ƙari, ‘yan Kudu suna yi wa gwamnatin kallon kamar tana fifita ‘yan Arewa.
Babbar matasalar gwamnatin jam’iyyar APC ita ce yadda ta kasa shawo kan matsalar man fetur a Najeriya wacce ake ta fama da ita. Banda haka, ta kasa tsayawa a kan wata tartibiyar manufa dangane da sashen man fetur. Yau ta faɗi wani abu, gobe kuma sai ta canza, jibi kuma sai ta aikata wani abin daban.
Dangane da tattalin arziƙi, gwamnatin ta kasa shawo kan tashin farashin Dalar Amurka da sauran kuɗaɗen ƙara waje da muke tsananin buƙata domin sayo kayayyaki daga waje. A gefe ɗaya kuma, tsadar kayayyaki sai ƙara ta’azzara take yi.    
Kasafin kuɗin 2016 wanda shine na farko da jam’iyyar APC ta yi a mulkinta yazo da kura-kurai da aringizo da yawa-wani abu da ba a yi tsammaninsa a gurin gwamnati mai taƙama da gaskiya da riƙon amana ba.


Me ya kamata APC ta Yi?
Har yanzu jam’iyyar APC tana da sauran shekaru uku a cikin huɗun da aka zaɓeta ta yi; akwai buƙatar ta yi waiwayen watannin da ta shafe  a kan mulki kuma ta yi wa kanta alƙalanci da kanta. Inda ta yi kurakurai, to ta yi ƙoƙari da gaggawar gyarawa, inda ta samu nasara sai ta yi ƙoƙarin ɗorawa a kai.
Maganganu da ƙulle-ƙullen siyasar 2019 da suka dabaibaye jam’iyyar tun kafin a je ko’ina, kamata ya yi a ajiye su waje ɗaya, ‘yan jam’iyyar su haɗa kai don ganin sun sauke nauyin da jama’ar Najeriya suka ɗora musu tukunna.
Yana da kyau jam’iyyar ta bar ƙofarta a buɗe wajen karɓar shawarwari komai ɗacinsu kuma koda daga wurin maƙiyansu ne. Bayan haka kuma ya kamata su sani cewar lokaci ba abokinsu bane a yanzu, dole sai sun zage damtse.


©Mujallar Mikiya 2016

No comments:

Post a Comment