Fassara

Tuesday, April 5, 2016

Ko Tinubu Zai Tsaya Takarar Shugaban ƙasa?

04 Ga Afrilu, 2016


Daga: Amir Abdulazeez

A
gurin mafi yawan manazarta harkokin siyasar Najeriya, ba wai abin da Tinubu yake buƙata shine abin tambaya ba; wataƙila tambayar ita ce, ko Tinubu zai samu abin da yake buƙata? Kasancewar gwamnatin Shugaba Buhari ta kammala kusan dukkan wasu muhimman naɗe-naɗen muƙamai ba tare da an ji sunansa a ko ɗaya daga ciki ba, alama ce da take nuna cewar akwai wani abu daban kuma babba da Asiwajun yake hari.

Yunƙurin Bola Tinubu a kusan tsawon shekaru goma da suka gabata na ganin ya zama Mataimakin Shugaban ƙasar Najeriya, wani abu ne da kusan duk wani mai sanya idanu kan harkokin siyasa yake sane da shi. Wannan yunƙuri nasa, duk da ya jawo masa abubuwa daban-daban na cigaba da kuma cikas, amma ya yi sandiyyar zamansa wani ƙusa kuma jigo a matakin ƙasa. Labari ya yi ta kewayawa cewar, ƙoƙarin da Tinubu ya yi na zama ɗan takarar mataimaki ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar a ƙarƙashin tsohuwar jam’iyyar Action Congress (AC)  a zaɓen Shugaban ƙasa na shekarar 2007 shi ya kawo rashin jituwa tsakaninsu wanda har ta kai ga Atikun ya bar jam’iyyar AC ɗin ya koma PDP a shekarar 2008-matakin da har yanzu yake bibiyarsa har kawo yau kuma wasu suke ganin ya taka wata ‘yar rawa wajen rashin nasarar Atikun wajen samun tutar takarar APC a shekarar 2015. An rawaito cewar shi Atiku yana ganin ba a yi adalci ba idan aka bai wa Bayerabe ko ɗan kudu maso yamma takarar mataimakin shugaban ƙasa a dai-dai lokacin da Shugaba Obasanjo wanda yake Bayerabe ne shima yake kammala shekaru 8 a kan mulki. Don haka Atiku sai ya bada mamaki wajen ɗaukar Sanata Ben Obi wanda ba a sani ba sosai daga kudu maso gabashin Najeriya a maimakon Tinubu wanda shi ya yi uwa yai makarɓiya wajen ganin shi Turakin Adamawa ɗin ya samu tikitin AC cikin sauƙi, bayan PDP ta yi masa wulaƙanci.

Rahotanni sun nuna cewar rashin amincewar Buhari na ya ajiye Fasto Tunde Bakare ya ɗauki Tinubu, ita ta kawo rugujewar ƙoƙarin haɗewa ko dunƙulewa tsakanin tsofaffin jam’iyyun CPC, ANPP da ACN a shekarar 2011 domin tunkarar Jonathan da PDP. Daga baya Buhari ya yi masa biyan bashi a 2015 inda ya yi wa Tinubu tayin bashi abinda bai samu damar bashi ba a 2011. To amma Jagaban Borgun yana sane da matsala da tarnaƙin da tsayar da Musulmai zalla za ta iya kawo wa damar da jam’iyyar APC take da shi na cin zaɓen shugaban ƙasa. Tinubu ya bai wa mutane mamaki wajen danne kwaɗayinsa tare da miƙa sunan tsohon kwamishinansa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa. Mutane da yawa suna kallon Osinbajo a matsayin wanda kawai yake riƙe da waccan kujera a madadin jagoran APC ɗin na ƙasa.

Me yasa Tinubu ya dinga fafutukar zama mataimakin shugaban kasa, ba ji ba gani? A tarihin dimokraɗiyyar Najeriya, da wahala a samu wani wanda ya ƙaunaci zama mataimakin shugaban ƙasa kamar sa. Amsar ba wata mai wahala bace; magana ce ta dabarar siyasa, me yiwuwa yana son zama shugaban ƙasa kuma yana so ya bi ta hanya mafi sauƙi, wacce ita ce ya fara zama mataimakin shugabn ƙasa. Tinubu ya samu damar da zai tsayar da kansa ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar ACN a shekarar 2011, amma bai yi hakan ba, me yiwuwa saboda ya san ɓata lokaci ne kawai kuma ƙila ba kamar sauran ‘yan siyasa ba, shi ba burinsa kawai  ace ya taɓa takarar shugaban ƙasa ba. Bayan haka kuma bai yi wani yunƙuri na zama mataimakin Nuhu Ribaɗu ba, wanda jam’iyyar ACN ɗin ta bai wa takarar shugaban ƙasa a wancan lokaci. Kodayake hakan bai ba wa mutane mamaki ba.
Dukkan jama’a, ciki har da Tinubu shi kansa sun san cewar zai yi matuƙar wahala ga wani mutum ɗan kudu maso yamma ya zama shugaban ƙasa kai tsaye a nan kusa, duba da cewar Obasanjo ya riga ya yi mulki na tsawon shekaru 8 a cikin 16 ɗin da aka yi da dawowar dimokraɗiyya a madadin wannan yankin. Da alama dai Asiwaju ya sadaukar da burinsa na zama mataimakain shugaban ƙasa a shekarar 2015 domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC, sai dai kuma ba za a fitar da ran cewar kuma a ƙarshe zai tsaya takarar shugaban ƙasar kai tsaye ba a shekarar 2019. Idan Buhari ya yanke shawarar ba zai nemi zango na biyu ba, to tamkar ya share wa Tinubu hanyar zama ɗan takarar jam’iyyar APC ne a 2019.

Idan Tinubu ya samu nasarar zama shugaban ƙasa, hakan zai zamo wani sakamako ko lada na tsawon lokaci da aka ɗauka ana tsare-tsare, haƙuri, surƙullen siyasa, zuba jari da kuma sadaukarwa. Tushen kafuwar sansanin siyasa da ƙarfin faɗa-a-jin tsohon gwamnan Jihar Lagos ɗin wanda yake ƙara faɗaɗa a kullum, ya samo asali ne daga kasancewarsa gwamna ɗaya tilo wanda ba na PDP ba a yankin Kudu maso yamma da kuma ɗaya cikin biyu a yankin Kudancin Najeriya baki ɗaya bayan zaɓukan shekarar 2003 da kuma jajircewarsa da fafutuka wajen ganin an fatattaki PDP daga yankinsa na Yarabawa tare da tabbatar da siyasar adawa a ƙasa baki ɗaya.

Wasu na kallon rashin karɓar wani muƙami a gwamnatin Buhari kawo yanzu daga ɓangaren Tinubu, kamar wani abu ne da zai iya haifar masa da matasala; wasu kuwa suna ganin hakan ma ƙarfi zai ƙara masa. Masu kallon hakan a matsala suna ganin cewar waɗansu mutane da suke cikin gwamnatin Buhari zasu yi amfani da muƙamansu wajen yin aikace-aikacen da zasu birge Buharin ta yadda zai yi tunaninsu a matsayin waɗanda zasu gaje shi domin ɗorawa a kan manufofin gwamnatinsa, hakan kuwa zai kawar da Tinubu daga lissafi. A ɗaya ɓangaren, wasu na ganin cewar rashin karɓar wani muƙami zai sa Tinubu ya mayar da hankali kan siyasarsa kuma zai raba kansa da duk wata badaƙƙala mai alaƙa da aikin gwamnati. Sannan kuma jam’iyyar APC  zata cigaba da jin cewar har yanzu yana binta bashin da baza ta iya biyansa ba. Bayan haka matasayinsa na kafi-sarki zai ci gaba da ɗorewa.

Ko shakka babu, ƙudurin Tinubu na zama shugaban ƙasa, akwai yiwuwar ya gamu da ƙalubale daban-daban. Akwai muhimman mutane da mai yiwuwa su nemi yin takara da shi tun ma daga yankinsa na kudu maso yamma. Muhimman Yarabawa irinsu Babatunde Fashola, Kayode Fayemi ko ma Yemi Osinbajo, duk zasu iya nuna sha’awarsu ga kujerar shugaban ƙasa. Muhimman ‘yan jam’iyyar APC daga yankin kudu maso gabas na Inyamurai kamarsu Chris Ngige, Ogbonnaya Onu da Rochas Okorocha suma zasu iya cewar to idan har mulki zai dawo kudu ne, to kamata yayi a ce kudu maso gabas zai dawo ba kudu maso yamma ba. Duk da irin shahararren gangancin siyasa da ragon azancin da kudu maso gabas suka yi a zaben shekarar 2015, zasu iya kallon Tinubu a matsayin wanda ya hana a basu kujerar mataimakin Shugaban ƙasa kuma zasu tashi tsaye a kansa wajen ganin bai ƙara hanasu wata damar ta samun kujerar mataimakin shugaban ƙasar ba, da ma ƙila ta shugaban ƙasar baki ɗungurugum a shekarar 2019. Wata mishkila da Tinubu zai iya fuskanta ita ce yankin Arewa wanda zai iya cewa idan har Buhari ba zai yi zango na biyu ba, to dole a ƙyale wani daga yankin aƙalla ya ƙarashe mulkin na tsawon shekaru huɗu. Mutane irinsu Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Rabi’u Kwankwaso, Nasir El-Rufa’i da kuma wasu gwamnonin APC ɗin da suka gama zangonsu na biyu duk zasu yi yunƙurin gwada damarsu idan hakan ta faru.

Kasancewar mafi yawan jam’iyyar APC a aljihun Tinubu take, zai zamo riba a gareshi sosai, to amma kuma zai iya zamo masa matsala. Ya tara maƙiya da yawa a ƙoƙarinsa na baza ƙarfin ikonsa zuwa ko’ina a cikin jam’iyyar. Babu wani mutum da ya cicciɓa kuma ya sassaka yawan mutane a cikin shugabancin jam’iyya da gwamnati kamarsa, kuma bisa ga dukkan alamu, zai iya samun goyon bayan Buhari. Sai dai kuma, kankanewarsa da babbakewarsa a kowanne bangare da kuma ƙoƙarin zama mai ruwa da tsaki a kan duk wani abu zai iya kawo masa tarnaƙi. Yanzu haka rahotanni sun fara kewayawa cewar, wasu jiga-jigan APC sun fara tunanin barin jam’iyyar saboda irin ƙarfin da Tinubu yake da shi. Kwanakin baya, an kawo masa cikas a yunƙurinsa na ƙaƙaba wa Majalisun Tarayya shugabanci; idan bai bi a hankali ba, ɓangarori da yawa a cikin APC zasu dunƙule waje ɗaya domin su yi masa taron dangi a 2019.

©Mujallar Mikiya, 2016.

Twitter: @AmirAbdulazeez

No comments:

Post a Comment