Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Matsalolin Motar Haya A Kano………

10 Ga Satumba, 2014.

Daga: Amir Abdulazeez

D
uk da cewar harkar sufuri ta na ɗaya daga cikin harkoki mafi muhimmanci a rayuwarmu ta yau, amma ba ma ba ta cikakkiyar kulawar da ta ke buƙata. Akwai haƙƙoki da yawa a kan gwamnati, direbobi, mamallaka abubuwan sufuri da kuma jama’ar gari, waɗanda sai mun kula da su sannan harkar za ta inganta.
Duk da cewar ba ni da cikakken ilimi a kan yadda  harkar sufuri ta haya ta ke gudana a mafi yawan jihohin Najeriya, amma ina da cikakkiyar masaniyar cewar harkar ta na cikin yanayi mara kyau a Jihar Kano. Fiye da kashi uku bisa huɗu na al’ummar Jihar Kano sun dogara ne da motocin haya domin zirga-zirgarsu. Ƙalilan ne suke da abubuwan hawa nasu na kansu. Wannan ta na nuna cewar jama’a suna da haƙƙin  kawo gyara a kan yadda tsarin motocin haya suke gudanar da aiyukansu. Idan da mutane za su saka kishi a zuciyoyinsu ma, ba sai sun jira gwamnati ta sa hannu a waɗannan al’amura ba.

Idan mu ka kalli girman Kano da yawan mutanenta waɗanda a ke ƙiyasata yawansu da sama da miliyan 12, to za mu ƙiyasata cewar aƙalla yawan motocin da suke zagayawa a kan titunan Kano sun haura miliyan guda ko kuma wani abu makamancin haka. A cikin wannan adadin, za mu iya cewa 65% motocin haya ne, ko dai tasi-tasi ko kuma bas-bas. Bisa wannan lissafi, idan ka ɗauke Jihar Lagos, babu jihar da ake kai kawo kamar Kano, amma da wahala a samu jihar da tsarin sufurin hayar ta ya ke kara zube kamar Kanon.
Abu na farko dai, a Kano ba ka buƙatar izini ko shawarar kowa ko wata hukuma kafin ka mallaki motar haya ko kafin ka zama direban motar haya. Idan ma akwai wata doka ko hukuma mai kula da hakan, to ba ta aikin ta. Wannan ta sa a yau za ka iya sayen motocin haya ko guda nawa ka ke so kawai ka zuba a kan titi kuma ka sa su su dinga bin hanyar da suka ga dama. Sannan kuma, in dai ka iya mota, to kawai sai ka kama tuƙa motar haya, da wuya a samu mai ce maka uffan. Me yiwuwa idan aka yi sa’ar gaske jami’an Road Saftey su tambaye ka diraba lasin sau ɗaya ko sau biyu a shekara.

Shekarun baya, Gwamnatin Kano ta fara tilastawa bas-bas yin wani fentin kore da ruwan ɗorawa domin a iya ganesu, amma yanzu da alama an daina ƙarfafa dokar kamar da. Sannan kuma kwanakin baya, lokacin da matsalar tsaro ta ta’azzara, gwamnati ta ɓullo da tsarin yi wa babura masu ƙafa uku rajista bayan da aka soke achaɓa, amma wannan rajista ba mu samu labarin ta haɗa da bas-bas ko tasi-tasi ba.

Abu na biyu, motocin haya a Kano suna ɗauka da sauke fasinja a duk inda suka ga dama. Babu wata tsayayyiyar madakata wato Bus Stop, kawai za su iya tsayawa a kowanne lokaci, kuma mafi yawanci ba sa kunna sigina ko su nuna alamar tsayawa. Bayan haka kuma motocin haya su kan yi lodi a inda suka ga dama, ko’ina a Kano tasha ne. Kwanakin baya hukumar kula da harkar sufurin kan  titunan Jihar Kano wato KAROTA ta ɗan kawo gyara a kan wannan al’amura ta hanyar hana lodin fasinjoji a wasu gurare, to amma hakan bai magance ko da 20% na matslar ba. Sannan kuma, ita kan ta KAROTA ɗin ta yi sakaci kwana biyu, domin inda ta hana tsayawar a baya, yanzu duk kusan an dawo ana tsayawa.

Abu na uku, mafi yawan motocin haya a Kano tsofaffi ne kuma lalatattu, wasu ma sun gama mutuwa. Da yawa daga cikinsu, bai kamata a bar su su dinga ma hawa kan titi ba balle ma su ɗebi mutane. Me yiwuwa wannan ce ta sa direbobin motocin suke yin tuƙin da suka ga dama, domin basu da asara ko an buga musu. Wannan ya taimaka da gaske wajen lalata yanayin tuƙi tare da ƙin bin dokokin kan titi a cikin Birnin Kano. Bayan haka wasu daga cikin direbobin ba su da tarbiyya balle ɗa’a. Sai ka ga mutum ya na tuƙi daga shi sai singileti ko gajeren wando, ko ka ga kwandastan bas ya na zagi da yi wa fasinjoji sa’annin iyayen sa rashin kunya.

Abu na huɗu, da yawa a cikin motocin hayar Kano ba sa son biyan harajin N20 ko N50 a rana wanda gwamnatocin ƙananan hukumomi ta kan sanya musu. Sai ka ga mai bayar da rasit ya na yi wa direba magana, amma sai ya ga dama zai kula shi, kamar ya na nuna shi ya fi ƙarfin gwamnati ko kuma ita gwamnatin ba ta damu da harkar sa ba. Ga shi kuma wani lokacin farashin motar haya a Kano ba shi da wata ƙa’ida, wani lokaci kwandasta sai ya caje ka yadda ya ga dama sai dai a yi ta rigima. Wani lokacin kuma su ɗauko fasinja da niyyar za su kai shi wani waje amma sai su ƙi ƙarasawa da shi, kawai sai su juye shi a inda suka ga dama, masu adalcin cikinsu ne ma suke saka shi a wata motar ko su dawo masa da wani ɓangare na kuɗinsa.

Abu na biyar, mafi yawancin masu motar haya ba sa ɗaukar adadin fasinja dai-dai da abin da motar za ta iya ɗauka ba. Misali a cikin tasi, sai su cusa mutum huɗu a baya kamar kayan wanki, mutum biyu kuma a gaba, tare da cewa wani ma cinyarsa a kan giya ko hanbrek ɗin motar ya ke, da ƙyar direba zai dinga sarrafa motar saboda matsatsi. Idan kuma bas ce, sai a zuba mutane a maleji, wani lokacin har da but dan hauka. Maimakon haka, ai kyautuwa ya yi a ɗan yi ƙarin kuɗin mota N10 ko N20. Kwanaki da na shiga bas daga unguwarmu zuwa ‘Yankura, na kalli yadda muka gwamutsu a cikin ta, babu wani sararin da iska ta ke zagayawa ko kaɗan, sai na ce  a raina yanzu abin Allah Ya kiyaye, da cutar Ebola za ta zo Kano, ai da babu hanyar da za ta fi saurin yaɗuwa kamar a cikin motocin haya.

Bayan haka sai ka ga an gwamutsa maza da mata su matsu sosai a kujera ɗaya. Sai kawai ka ji rabin jikin matar aure a kwance a jikinka a cikin tasi ko bas, wai ai motar haya ce, larura ce. Idan muka je lahira, dukkanmu sai mu taru mu yi wa Allah bayanin wannan wacce irin larura ce haka. Irin wannan gwamutsa maza da mata da muke yi a cikin motocin haya shi yake kawo taɓarɓarewar tarbiyya da kuma masifu iri-iri. Zai iya zama ɗaya daga cikin dalilan da Allah SWT Ya sa ya ke jarrabtar mu da bala’o’i iri-iri.

Waɗannan matsaloli sai mun taru mun haɗa ƙarfi da ƙarfe sannan za mu iya yaƙar su kuma dole mu ɗauke su da gaske ba da wasa ba. Mu matsalar mu ita ce, in dai abu bai shafi neman kuɗi ko neman abinci ba, to ba mai muhimmanci ba ne.

Ƙungiyoyin direbobi da masu motocin haya su tashi tsaye wajen tsaftace sana’arsu. Gwamnati ta kafa tsauraran dokoki da matakai kuma ta tabbatar ana binsu. Gwamnatain  Kano za ta iya faɗaɗa aiyukan hukumar KAROTA don su ƙunshi magance waɗannan abubuwa sannan kuma jama’ar gari su bayar da haɗin kai tun da ba wanda ya fi su cutuwa da wannan matsala ta hanyar bin duk wasu dokoki da za a gindaya tare kuma ƙauracewa dukkan mai motar da bai cika ƙa’idoji ba.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.


Manyan Nasarori da Matsalolin Gwamnatin Kwankwaso

10 Ga Satumba, 2014.


Daga: Amir Abdulazeez

M
utane da yawa a Kano, Arewacin Najeriya da ma sauran sassan Najeriya suna matuƙar bibiyar al’amuran siyasa da gwamnati a Kano tare da nuna sha’awar samun bayanai akan irin  mulkin da Kwankwaso ya ke yi a Jihar Kano. Mai yiwuwa hakan bay a rasa nasaba da irin shahara da Jihar Kano ta yi a faɗin ƙasarnan ko kuma shaharar da shi Kwankwason ya yi a siyasar wannan lokaci da muke ciki. Waɗanda suka riski wani ɓangare na amfanin gwamnatin su kan ɗauka cewar babu wani abu da gwamnatin ta shimfiɗa sai nasara yayin da kuma wasu waɗanda suka riski wani ɓangare na takalmin ƙarfen gwamnatin, sai su kan ɗauka cewar babu abin da ta shimfiɗa sai matsala.
Yanzu haka saura kimanin watanni takwas gwamnatin Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ta kammala wa’adin ta na shekaru huɗu wanda shi ne dawowar ta a karo na biyu a Jihar Kano. Babu shakka watanni takwas ba za su hana a yi wa abin da aka shafe watanni 40 ana gudanar da shi alƙalanci ba.

Gwamnatin Kwankwaso ta zo gangara kuma da wahala a ɗan wa’adin da ya rage mata ta yi wani abu sabo wanda ba ta bayyana shi a baya ba. Idan aka yi sa’a ma ta ƙarasa ɗumbin aiyukan da ta ke kan yi yanzu kafin wa’adinta ya ƙare, to sai a gode wa Allah. Idan kuma hakan ba ta samu ba, to babu shakka za a gode mata saboda kafa harsashin manyan aiyuka masu matuƙar amfani da ta yi, waɗanda gwamnati mai zuwa ya kamata ta ƙarasa kuma ta ɗora a kan mafi yawa daga cikinsu.
Duk wanda ya karanta kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2014, zai lura cewar akwai aiyuka da yawa da kasafin ya ƙunsa waɗanda an riga an fara su tun shekarun 2012 da 2013. Don haka bisa ga dukkan alamu kasafin kuɗin gwamnatin na shekarar 2015 zai mayar da hankali kacokam wajen ƙarasa dukkan aiyukan gwamnatin na shekarun 2011, 2012, 2013 da 2014.
Dawowar Kwankwaso mulkin Kano a karo na biyu ya bar tarihi ta kowanne ɓangare. Akwai abubuwa masu kyau da ya yi waɗanda ba za a taɓa mantawa da su ba, haka kuma akwai matsaloli waɗanda ba za a taɓa mantawa da su ba.


NASARORI

5. ƘAWATA BIRNIN KANO: Gwamnatain Kwankwaso ta ƙawata Birnin Kano fiye da kowacce gwamnati a tarihi. A yanzu da wahalar gaske a samu wani titi mai kwalta, komai ƙanƙantarsa, a cikin birni da kewaye wanda babu fitilu masu haske ba, sannan kuma ba a fashin kunna waɗannan fitilu a kowacce rana. Sannan kuma yanzu haka gwamnati ta na kan gyarawa da zamanantar da dukkan ƙofofin tsohon Birnin Kano na asalin tarihi, kuma gyaran ba na wasa ba, wasu mu rushesu a ke yi ana sake gina su.
Gwamnatin Kano ta na kwashe shara a cikin Kano ba ƙaƙƙautawa, don haka birnin a cikin tsafta yake a mafi yawan lokuta. Wannan ƙari ne a kan tsaftace birnin da ake gudanarwa a kowacce Asabar ɗin ƙarshen wata. Sannan kuma duk wani gini mallakar gwamnati, an gyara katangarsa kuma an fente shi tare da sanya fitilu masu haske a jikin bangwayensa. Banda wannan kuma, an sassaka intalo-intalo a gefunan tituna da sauran gurare, kuma an gyara wasu daga cikin shatale-talen Kano tare da ƙawata su. Bayan duka waɗannan, akwai guraren shuke-shuke na musamman da aka ware, wasu don shaƙatawa, wasu kuma don shuke-shuken kawai. Sannan kuma an samar da gadojin tsallaka titi da ƙafa a gurare da yawa, wanda hakan ya samar da tsari a kan yadda mutane masu tafiya a ƙasa suke amfani da tituna.
Wani abin sha’awa kuma, da zarar wani abu ya lalace ko ya samu matsala a cikin birnin, nan da na za ka ga an zo an gyara shi an mayar da shi yadda ya ke, ko kuma an ƙara masa kyau da nagarta.

4. ƘARASA AIYUKAN TSOHUWAR GWAMNATI: gwamnatin Kwankwaso ta bai wa mutane mamaki wajen ƙaraswa ko ɗorawa a kan aiyukan gwamnatocin baya. Misali, gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta tafi ta bar aiyukan titunan da ta fara ba ta gama ba, amma kwankwaso ya ƙarasa su, kamar titin da ya taso daga Tal’udu zuwa Mandawari zuwa Kasuwar Kwari kuma ya haɗe da Titin Ibrahim Taiwo, sannan akwai titin da ya tashi daga Kurna Makaranta ya haɗe da Kabuga, da sauran waɗansu titunan. Sannan kuma gwamnatin Shekarau ta tafi ta bar tsaruka, kamar tsarin yin gidaje da yawa a gefunan garin Kano domin sauƙaƙa cinkoso da kuma tsarin faɗaɗa tituna, waɗanda duk Kwankwaso ya aiwatar da su.
Dogon ginin Magwan da Marigayi Abububakar Rimi ya gina kuma aka yi watsi da shi shekara da shekaru, yanzu haka Kwankwaso ya sa ana gyara shi domin mayar da shi makaranta.
Shirin gwamnatin Shekarau na wadata Kano da ruwa ta hanyar gina matatun ruwa manya na Tamburawa da Watari bai samu cikakkiyar nasara ba sai a zuwan Kwankwaso. Domin Kwankwaso shi ne yanzu ya ke shimfiɗa manya-manyan bututun da ya ke ɗauko wannan ruwan daga matatun zuwa ga jama’a domin amfani. Yanzu haka kimanin 50% na baki ɗayan Jihar Kano sun fara amfana da wannan ruwa.

3. MANYAN TITUNA DA MANYAN AIYUKA: kafin dawowar Kwankwaso, babu titin sama ko ɗaya a cikin garin Kano, amma mai yiwuwa kafin ya tafi, Kano za ta zama ta na da huɗu lafiyayyu, guda uku kuma daga ciki, gwamnatinsa ce ta yi su. Kwankwaso ya faɗaɗa dukkan hanyoyin shigowa Kano in banda titin Katsina, a ciki akwai Titin Gwarzo, Titin Hadejia, Titin Zaria da Titin Panshekara. Duk waɗannan ƙari ne a kan tituna da dama a ciki da wajen Kano da gwamnatin ta ke ɓarjewa ta na gyarawa da waɗanda ta ke faɗaɗawa da kuma ƙirƙirowa. Akwai titunan ƙarƙashin ƙasa da gwamnatin ta ke yi gadan-gadan yanzu haka a Gadon-Kaya Da Kabuga.
Wasu manyan aiyukan na tarihi da gwamnatin ta ke kan yi sun haɗa da gina tashar wutar lantarki mai zaman kan ta daga madatsun ruwa na Challawa da Tiga mai ƙarfin megawatt 35, da kuma rufe shahararren Kogin Jakara domin yin titi a kansa. Bayan haka akwai yuurin samar da tashoshin manyan motoci guda biyu.
Gwamnatin Kwankwaso ta samar da birane guda uku sukutum a Jihar Kano. Biranen sune Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo.
Gwamnatin Kano a ƙarƙashin Kwankwaso ta yi bakin ƙoƙari wajen bai wa kowanne fanni kulawa dai-dai gwargwado. Sassan lafiya, noma wasanni, ruwa, kimiyya da fasaha duk an taɓa su, sai dai a ce wani ɓangaren ya fi wani samun kulawa a gwamnatin.

2. SAMAR DA AIYUKAN YI DA ƊA’A A CIKIN AL’AMURA: kafin dawowar gwamnatin Kwankwaso,  a Kano ba a tsoron gwamnati; idan ta sa doka, ƙa’ida ko tsari ba a cika bi ba, ko kuma sai an ga dama a ke bi. Yanzu a Kano, wannan ta kau domin da wahala gwamnati ta faɗi abu a tsallake shi.
Bayan haka, kafin dawowar Kwankwaso, akwai ma’aikata da yawa da suke wasa da aikin gwamnati, amma daga zuwansa ya gyara musu zama sannan kuma ya fitar da ɗaruruwan ma’aikata na boge, na ƙarya waɗanda ake karɓe kuɗaɗen gwamnati da sunansu daga cikin tsari. Ko shakka babu, Kwankwaso ya yi maganin ɓarayi masu sace kuɗin gwamnati tun daga kan ƙananan hukumomi har zuwa jiha.
Gwamnatin Kwankwaso ta samar wa da dubban mutane aiyukan yi a gwamnati da kuma sana’o’i. Ta rarrabawa mutane da yawa tallafi domin yin jari da kuma rancen kuɗi da kayan aiki don bunƙasa sana’a.
A ƙarƙashin Hukumar Hisba, gwamnatin ta aurar da zaurawa da ‘yan mata sama da 1000 a Kano, wanda shi kansa wannan wani nau’i ne na samar da ɗa’a da tarbiyya. Gwamnatin ta hana barace-barace a kan titi tare da samar da tsari na musamman domin tallafawa da koyawa waɗannan mabarata  sana’ao’i domin dogaro da kansu kuma ta hana sakin dabbobi barkatai a kan titi.
Kwankwaso ya kafa hukumar KAROTA wacce ta taka rawar gani wajen kawo tsari da doka akan titunan Kano bda kuma harkar sufurin kan titi baki ɗaya.

1. INGANTA ILIMI: me yiwuwa wannan shi zai zamo bakandamiyar Gwamnatin Kwankwaso. Gwamnatin Kano a shekaru uku da suka gabata ta taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta ilimin addini, firamare, sakandire, jami’a da sana’o’i.
Kwankwaso ya gina ajujuwa manya masu bene a kusan ɗaya bisa ukun na makarantun firamaren Kano baki ɗaya. Wannan ƙari ne  a kan ciyar da yara kyauta da basu kayan makaranta. Gwamnatin ta samar da ƙarin makarantun sakandire kuma ta ɗauki nauyin ɗaruruwan ‘ya’yan talakawa domin yin digiri na ɗay da na biyu a ƙasashen duniya daban-daban.
Idan mutane ɗarin da gwamnatin Kwankwaso ta ɗauki nauyi domin koyo tuƙin jirgi a ƙasar Jordan suka kammala, me yiwuwa Jihar Kano za ta iya zama jiha guda ɗaya mafi yawan matuƙa jirgin sama a faɗin Nahiyar Africa. Haka kuma ‘yan mata 100 da suke karatun likita a ƙasashen ƙetare za su taimaka wajen zamowar Jihar Kano kan gaba a yawan mata likitoci a Najeriya idan sun kamala karatunsu.
Gwamnatin Kano ta gina tare da gyara wasu makarantun islamiyyu da yawa, sannan ta samar da sabuwar jami’a sukutum mai suna North West University. Wannan ƙari ne akan dukkan makarantun gaba da sakandire na Jihar Kano da gwamnatin ta gyara kuma ta ɗaga darajarsu izuwa masu yin karatun NCE ko digiri. Kai  a taƙaice dai gwamnatin ta mayar da ilimi kyauta tun daga firamare har jami’a ga ‘yan asalin Jihar.
Bayan waɗannan, da wahala a samu wata sana’a ta gargajiya ko ta zamani wacce Kwankwaso bai yi wa babbar makaranta ba sukutum. Akwai makarantun koyon sana’o’i, noma, kasuwanci, tuƙi, kiwo, tsaro, wasanni da dai sauransu a warwatse a ƙananan hukuomi daban-daban na Kano.


MATSALOLI

5. KWANKWASIYYA: ɗaya daga cikin manyan matsalolin gwamnatin Kwankwaso shi ne ɗarikar sa ta Kwankwasiyya. Ya yi amfani da ƙarfin gwamnati ko dai kai-tsaye ko kuma kai-zaune wajen tilasta wannan aƙida ta sa a kan jama’ar Kano. Babu yadda za a yi Kwankwaso ya shigo da kai cikin gwamnatinsa sai ka sa jar hula, idan kuma ka na cikin ta sai ka saka ta don kada a yi waje da kai. Abin kamar almara.
Kwankwaso ya yi amfani da kuɗin gwamnati da dukiyar al’umma ya yi aiyuka amma duk ya bi ya rubuce su da sunan ɗarikarsa wacce kuma ita ba hukuma ce ta gwamnati ba. Idan ɗan kwangila ya yi wa gwamnati aiki bai rubuta sunan Kwankwaso a jiki ba, to ba lallai ne gaba idan ya nemi kwangila a ba shi ba, don haka tsirarun aiyuka ne kawai za ka ga babu sunan Kwankwasiyya a jiki.
Kafin zuwa Kwankwaso ya zargi gwamnatin baya da sanya siyasa a cikin harkokin gwamnati inda ya yi kira ga kantomomin ƙananan hukumomi na wancan lokaci, a matsayinsu na ma’aikata da su daina yarda ana yin amfani da su a siyasa. Sai ga shi babu kantomomin da suka kai na Kwankwaso shiga da taka rawa a cikin siyasa. Bayan haka sama da kimanin 90% na mata, matasa da sauransu da ya bai wa jari ko tallafi a ƙarƙashin shirinsa na CRC dukkansu ko dai ’yan Kwankwasiyya ne ko kuma ‘yan uwan ‘yan Kwankwasiyya ko waɗanda suka kama ƙafa da su. Akwai matan da suka dinga samun jarin sau da yawa a maimakon sau ɗaya domin su ‘yan ɗariƙar ta sa ne.
Sannan kuma an zargi gwamnati da yin amfani da kuɗaɗen jama’a ta na sayen jajayen huluna buhunna-buhunna ana rabawa a ƙananan hukumomi, wai dole sai an yi aƙidar Kwankwasiyya.

4. TAKURAWA DA TAUYEWA: zai yi wahala a samu gwamnatin da ta takurawa mutane, ma’aikata da ma muƙarrabanta kamar  gwamnatin Kwankwaso ba. Gwamnatin ba ta fiye duba masalahar jama’a ba a mafi yawancin abin da ta ke yi. A wasu lokutan, aiyukan da gwamnatin ta sa kan ta, shi za ta yi ko da kuwa ba shi ne mafi dacewa ga jama’ar wannan guri ba. Sannan kuma kullum tunanin gwamnatin shi ne  sai an yi komai ta ƙarfi sannan zai samu nasara kuma a hakan ma sai an yi shi cikin gadara. Sannan gwamnatin ba ta fiye girmama dokar da ba ita ta kafa ba.
Tsaruka na Ihsani da gwamnati ta ke yi domin kyautatwa ma’aikatan ta , Kwankwaso ko dai ya raunata su ko kuma ya yi musu ƙanshin mutuwa. Sai an ga dama a ke bayar da ɗan kuɗin gero da na rago da ma’aikatan suka saba samu a baya. Tsaruka na kyautatwa jama’a da gwamnatin baya ta ke yi kamar su ciyarwa lokacin azumi duk sun yi rauni a gwamnatin sa.
Gwamnatin Kano a ƙarƙashin Kwankwaso ta hana har da ma muƙarrabanta su yi aikinsu. Sai ka ga abin da bai kai ya kawo ba wanda bai wuce a bai wa wani jami’in gwamnati dama ya aiwatar da shi ba, amma gwamna sai yace zai aiwatar da kansa, da alam bai yarda da kowa ba sai kansa. Sannan kuma majalisar dokokin Jihar Kano ba ta taɓa zama hoto ko ‘yar amshin shatar gwamna ba kamar a wannan lokaci. Duk dokar da gwamna yak e so a ƙirƙira ko a yi wa gyaran fuska, to an gama kawai ba tare da wani ɓata lokaci ba. Hatta shugabancin majalisar ma, gwamna ne ya ke da ta cewa a kan sa.
Bayan haka, gwamnatin ta kawo tawaya a tsarin aiyukan ta da kanta domin aiyuka da yawa ta kan yi su ne kawai a inda za a gani, kamar bakin titi amma ba a inda suka dace ba. Misali, manyan ajujuwa benaye na firamare, da wahala gwamnatin ta gina muku shi idan makarantar ku ba a bakin titi ta ke ba, komai buƙatar ku da shi, kuma ko da makarantar a bakin titi ta ke, ba lallai ne a duba inda ya dace ba a cikin makarantar, a’a sai inda zai kallo titi a ga tambarin Kwankwasiyyar nan ƙarara.

3. ƘANANAN HUKUMOMI : A ƙarƙashin gwamnatin Kwankwaso ne Jihar Kano ta samu kantomomi waɗanda sune mafi daɗewa a kan mulki a tarihi ba tare da an shirya zaɓe ba. Sannan kuma gwamnatin ita ta shirya kuma ta aiwatar da zaɓen ƙananan hukumomi mafi muni da rashin inganci a tarihin Jihar Kano. Bayan haka gwamnatin ta yi amfani da ƙarfin ta wajen ɗaurewa waɗanda bas u cancanta ba gindi domin samun mulkin ƙananan hukumomi. An zargi wasu daga cikin Ciyamomin da rashin ilimi, ƙwarewa da kuma iya aiki.
Duk waɗannan abubuwa ƙari ne a kan maƙurewa da gwamnatin ta ke yi wa ƙananan hukumomi ta hanyar hanasu kuɗaɗensu da kuma haƙƙoƙinsu. Gwamnatin ta hanasu cikakken ‘yanci tare da damar da za su yi wa mutane aiki, sai dai zaɓi irin aikin da za ayi musu a lokacin da ka ga dama ko da kuwa ba shi suke muradi ba. Shugabannin ƙananan hukumomi na wannan lokacin kusan ba su da maraba da hotuna.
Bayan haka gwamnatin ta ƙi yi wa jama’a cikakken bayanin adadin kuɗaɗen da suka shigo aljihun ƙananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya tun daga watan Mayun 2011 zuwa yanzu tare da faɗar abubuwan da ta yi da su, kuma nawa ne ya rage, kuma me ya sa ta ke hanasu kuɗaɗensu, sannan wacce doka ce ta ba ta damar yin hakan?

2. ƘWACE FILAYE DA RUGUJE GIDAJE : gwamnatin Kwankwaso ta yi rushe-rushen gidaje da ƙwace filaye nau’i biyu. Nau’in farko shi ne waɗanda ta ruguje ko ta karɓe da ba sa kan ƙa’ida ko kuma suna kan ƙa’ida amma ta na buƙatar yin wani abu mai muhimmianci da su kuma  ta bayar da isasshiyar sanarwa tare da biyan kuɗin diyya a inda hakan ta dace. Kashi na biyu shi ne wanda ta karɓe ko ta ruguje ko dai, suna kan ƙa’ida ko ba sa kan ƙa’ida, ba tare kuma da cikakkiyar sanarwa ba kuma ba tare da biyan diyya ba, sannan kuma bayan ta karɓe sai ta ɓige da yin wani abu wanda ba shi ne masalahar jama’a ba.
Mutane da yawa sun zargi gwamnatin da zalunci da kuma cutarwa ga jama’a yayin da ta ƙwace wasu filaye da dama kuma ta ruguje gidajen da aka fara ginawa ba tare da ta biya kowa diyya ba, kuma ta sake yanka waɗannan filaye ta rarrabawa ‘yan siyasa. Wannan ya na daga ciin abubuwan da suka zubarwa da gwamnatin daraja musamman a idon masu ƙaramin ƙarfi.
Bayan haka duk rushe-rushen da gwmanatin ta ke yi a tsawon shekaru uku, amma ta kasa kawo ƙarshen kasa kaya a bakin tituna da kuma ƙaro rumfunan shaguna zuwa bakin titi tare da gina kes-kes, duk dai a kan titin.

1. AIKIN TITIN KILOMITA BIYAR-BIYAR: aikin titin kilomita biyar-biyar da gwamnatin Kwankwaso ta ke yi a ƙananan hukumomi 44 zai iya zamowa aiki guda ɗaya da gwamnatin ta fi narka kuɗaɗe fiye da kowanne aiki a cikinsa kuma sannan ya zamo aiki mafi rashin nasara da gwamnatin ta yi a tsawon shekaru ukun da suka gabata. Da farko dai da wahala a samu titi guda ɗaya a cikin 44 ɗin da ake yin sa a ƙasa da naira miliyan 1000 (Biliyan 1).
A cikin kusan shekaru biyu da aka yi ana aiyukan titunan, da wahala a samu guda goma waɗanda aka kammala a cikin guda 44, wasu ƙananan hukumomin ma an daina aikin. Bayan haka wasu aiyukan titin an yi sune akan manyan titunan Gwamnatin Tarayya wanda hakan zai iya jawowa gwamnatin ta tarayya ta ɓarje su yayin da ta buƙaci yin amfani da titin ta, wannan kuwa ba ƙaramar ɓarnar dukiya bace. Irin waɗanda wannan matsala za ta iya shafa sun haɗa da Bichi, Tsanyawa, Rimin-Gado da sauransu.
Duk wannan ma kaɗan ne idan aka yi la’akari da rashin ingancin aiyukan domin wasu ma sun fara lalacewa tun kafin a fara amfani da su. A taƙaice dai gwamnatin ta yi asarar sama da naira biliyan 50 akan wannan aiki, ba tare da an samu sakamakon da ya kamata ba.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.



Yadda Shekarau da Kwankwaso Suka Lalata Siyasar Jihar Kano

28 ga Mayu, 2014

Daga: Amir Abdulazeez

T
un a zamanin NEPU da PRP, duniya ta ke yi wa Jihar Kano kallon madubin siyasar Arewacin Najeriya. Wannan ya biyo bayan aiki tuƙuru da gwarazan ‘yan kishin ƙasa irinsu Mallam Aminu Kano suka yi wajen nema wa Jihar Kano irin wannan matsayi. Domin kuwa irin nagartaccen samfurin siyasar da su Marigayi Aminu Kano, Muhammad Abubakar Rimi, Dan Masanin Kano da sauran irinsu suka gudanar a wancan lokaci, ya taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga darajar siyasar Kanon musamman a Arewacin Najeriya.

A wancan lokaci, Jihar Kano ta yi fice wajen zaɓen mutum ko jam’iyyar da ta ke so a kowanne irin mataki ba tare da tsoro, kwaɗayi ko maguɗi ba.
A shekarar 1979, Jihar Kano ta zaɓi jam’iyyar PRP duk kuwa da cewa NPN ita a ke yayi a Najeriya kuma ita ce jam’iyyar da ta fi kowacce ƙarfi. A shekarar 1983, an juya wa Muhammad Abubakar Rimi baya duk da cewa shi ne ya ke da mulki kuma a ka zaɓi Sabo Bakin-Zuwo duk da cewar bai fi  Rimin farin jini a karan kansa ko kuma sanin siyasa ba. A waɗannan  lokuta, duk ƙarfin mulkin ka, ba ka isa ka tilastawa mutane su yi irin siyasar da ka ke so ba, ko kuma ka murɗe mu su zaɓe ba. Ire-iren waɗannan abubuwa su suka sanya a ke sha’awar siyasar Kano a ko’ina a Arewa kuma ya sanya ta shahara a fadin Najeriya.


A shekarar 2003, siyasar Jihar Kano ta cigaba da kafa tarihi inda ta samu ƙarin matsayi daga madubin Arewacin Najeriya zuwa madubin siyasar Najeriya baki ɗaya. Wannan ya biyo bayan zaɓen Mallam Ibrahim Shekarau da kuma faɗuwar Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. A lokacin, an yi ikirarin cewar Shekarau ya ci zaɓe alhalin ba shi da ajiyayyar N100,000 inda ya kayar da Gwamna Kwankwaso mai ƙarfin mulki, kuɗi da alfarma. Duk Najeriya ba inda aka taɓa ganin haka a wannan lokacin sannan kuma bayan yin la’akari da lalcewar al’amuran zaɓe a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Obasanjo  a wannan shekara,  an yi ittifaƙin cewar, babu inda aka gudanar da sahihin zaɓe a duk Najeriya kamar a Jihar Kano. A wannan shekara, ba wai Gwamna Kwankwaso kadai ba, a’a, ‘yan majalisu da dama ma su ƙarfin kuɗi da mulki sun yi asarar kujerunsu. Duk da cewa akwai gagarumin tasirin Janaral Buhari a siyasar Kano a wannan lokaci, amma wannan shekara ta 2003 ita ta tabbatar wa da duniya cewar siyasar Jihar Kano ta na nan daram yadda aka santa duk da lalacewar da siyasar Najeriya ta yi. Wato kuɗin ka ko mulkinka ko maguɗin ka a Kano bai isa ya ba ka mulki ba ba tare da sahalewar talakawa ba.

Tun daga wannan lokaci, duk inda ka je sai ka ji ana cewa ai ba ka isa ka yi maguɗi ko ƙarfa-ƙarfa a Jihar Kano ba, saboda yanayin siyasar jihar ya fi ƙarfin a yi mata irin cin kashin da a ke yi a sauran jihohi.
Duk waɗannan abubuwa da na ke zayyanowa a yanzu sun zama tarihi, domin kuwa yanzu siyasar Kano ta lalace kuma ta dawo gama-gari irin ta ko’ina a Najeriya. Kai a taƙaice ma idan aka ci gaba a haka, to jihohi irin su Oyo, Edo, Imo, Nassarawa da Zamfara za su iya shan gaban Kano ta fuskar inganticciyar siyasa ta ra’ayi da ‘yanci.

Wannan lalacewar da siyasar Kano ta yi ba komai ba ne face laifin tsohon Gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau da kuma Gwamna mai ci yanzu, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ko da yak e mu kanmu mabiya mun bayar da tamu gudunmawar. Mutane da dama su na da ra’ayin cewar, a tarihin Kano, ba a taɓa samun mutanen da suka ci moriyar siyasar jihar irin waɗannan mutane guda biyu ba, amma yau ga shi su ne suka fi kowa lalata ta da yi mata mummunar illa.
Kwankwaso da shekrau su ne suka share wa maguɗin zaɓe wajen zama a Kano kuma su ne suka assasa al’adar sanya jam’iyya da shugabanninta a cikin aljihu.

Ba wai ina nufin waɗannan mutane babu wata gudunmawa da suka kawo ga ci gaban Kano ba. A’a, kowannensu ya yi mulki kuma ya bar tarihi mai kyau dai-dai iyawarsa ta hanyar yin abubuwa nagartattu da suka shafi rayuwar jama’a. To amma sun yi amfani da mulkinsu wajen gina rundunar siyasarsu da tara magoya baya. Sannan kuma sun yi amfani da damar su wajen yin abin da zai ciyar da siyasar su da ta jam’iyyar su gaba kawai, amma sun lalata tsari da ginshiƙin siyasar Kano kuma da alama hakan bai dame su ba. Aiyyukansu sun nuna cewar bas u damu ba dan tarihin siyasar Kano ya lalace in dai ta su siyasar za ta ci gaba da haɓɓaka. A taƙaice dai, sun lalata tsarin da su suka fi kowa cin moriyarsa a Kano.


Lokacin da Kwankwaso ya zama gwamna a shekarar 1999, babu wani abu na nagarta da alfarma a zahiri wanda Dakta Abdullahi Umar Ganduje bai fi shi ba. Amma saboda tsaftar siyasar Kano a wancan lokaci, ba a murɗe masa zaɓen fidda gwani na PDP  an baiwa Gandujen ba. Amma lokacin da jagorancin PDP ya dawo hannun Kwankwaso, a shekarar 2007, shi kaɗai ya yi fatali da nagartattun ‘yan takara kusan guda bakwai waɗanda suka shiga zaɓe tare da shi, ya ɗauki takara ya bai wa Ahmad Garba Bichi.

Idan muka waiwayi Shekarau, a shekarar 2003, tsaftar siyasar Kano na wancan lokaci ta sa aka yarda cewar Ibrahim Little ya karya doka ta hanyar tsayawa takara ba tare da ya ajiye muƙaminsa na shugaban jam’iyya ba, kuma ba a kalli kuɗinsa, yawan jama’arsa ko ɗaurin gindin sa ba, aka karɓe takara aka ba shi duk da cewar ba shi da kuɗi ko wani ubangida a siyasance kuma ana ganin ma ba zai iya takarar ba. Amma a shekarar 2011, lokacin da jagorancin jam’iyyar ANPP ya ke hannun Shekarau, sai ya jingine matsayinsa na jagora, ya tsaya kai da fata sai an zaɓi abokinsa Mallam Salihu Sagir Takai, kuma ya dage a kan haka inda ya yi amfani da dukkan damar da ta ke hannunsa wajen cimma burinsa duk kuwa da cewar mafi yawan ‘yan jam’iyyarsa ta ANPP ba su yarda da zaɓin nasa ba.

Sakamakon waɗannan abubuwa da Kwankwaso da Shekarau suka yi a baya, yau an wayi gari saboda lalacewar siyasa a Kano, kowa tsoron tsayawa takarar gwamna a ƙashin kansa ya ke yi domin in dai ba gwamna ko jagoran jam’iyya mai ci ne ya tsayar da shi ba to wai ɓata lokacinsa ya ke yi. Kuma komai nagartarka, ba za a taɓa samar da yanayin da zaka iya wata takarar kirki da ɗan lelen gwamna ba.

Idan muka dawo ɓangaren zaɓe, Jihar Kano ba ta san mummunan maguɗin zaɓe da danniya ba sai  a kan Shekarau da Kwankwaso. Duk da cewa a lokacin SDP da NRC, mutane da yawa na da ra’ayin cewar an yi murɗiya a zaɓen gwamna tsakanin Injiniya Magaji Abdullahi da Gwamna Kabiru Gaya; to amma wannan ma wasan yara ne a kan abin da muke gani a yanzu.
Na farko dai, mafi yawan zaɓen cike gurbi da aka yi a ƙarƙashin mulkinsu ba su da inganci. Tun daga zaɓen cike gurbin ɗan majalisar Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa a shekarar 2006, har zuwa zaɓen cike gurbi na ‘yan majalisun Kano ma su wakiltar Gaya da Garko da aka yi a shekarar 2013; akwai rashin inganci a cikinsu.

A shekarar 2007 ne, gwamnatin Mallam Shekarau ta shirya zaɓen ƙananan hukumomi mafi muni a tarihin siyasar Kano inda ƙiri-ƙiri a ka dinga musanya sunayen waɗanda aka sanar sun ci zaɓe a filin zaɓe da sunan abokan takararsu a can wani wajen daban ko a wani lokacin daban, wannan zaɓe ya yi muni ƙwarai da gaske kuma mu a wannan lokacin mun ɗauke shi a matsayin tsautsayi da ƙaddara wacce muke fatan ba za ta ƙara faruwa a Kano ba. Sai ga shi ƙasa da sati biyu da suka gabata, gwamnatin Kwankwaso ta shirya wani zaɓen mummuna irinsa wai da sunan ta rama abin da Shekarau ya yi mata. A wannan almara mai kama da zaɓe, an ayyana cewar jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun kansiloli 484 da ciyamomi 44 a Kano. To yanzu, menene abin birgewa a nan a ce babu adawa ko ɗaya kuma bayan kowa ya san hakan ba zai yiwu ba a Kano?

Da alama dai an saka talakawan Kano a tsakiya ana wasan ƙwallon ƙafa da su. Wannan ya sa su su shiga rana su hau layi don zaɓar ra’ayinsu, sai kuma a faɗi sakamakon da aka ga dama, sannan wancan ma ya aikata irin hakan wai sannan ya ce ai ramawa ya yi. Talakawan Kano su ne abin ya ke ƙarewa a kansu kuma abin takaici wai shugabanninsu su ke mu su haka.

A lokutan mulkin Shekarau da Kwankwaso, babu wanda ya ke da ikon ya zama shugaban jam’iyyar da suke ciki sai wanda suke so kuma shugabannin jam’iyya ba su da wani ‘yancin kansu sai dai ra’ayin gwamnati domin ta mayar da su jami’anta. Idan mutum ya na takara da gwamna ko ɗan lelen gwamna, shugabanni ba za su zama alƙalai ma su adalci ba, ƙarara za su nuna maka kai ba ma ɗan jam’iyyar ba ne ko kuma ka ma yi laifi da ka tsaya takara da gwamna. Mu a da sai dai mu ji labarin irin wannan abin takaicin a wasu jihohin amma ba dai a Kano ba.

A dalilin haka, yau mun wayi gari, gwamnoni su suke nada shugabannin  jam’iyya kuma ba su da wani amfani. Da ka nemi shawararsu ma, gara ka tunkari gwamnan mai mulki kai tsaye domin aikinsa kawai su ke yi ba na jam’iyya ba. Ya kamata waɗannan jagorori su koyi darasin da tarihin siyasarsu ya koya mu su. Su tuna cewar sun samu dama kuma sun rasa ta.

A gaskiya duk da cewa Injiniya Kwankwaso da Mallam Shekarau sun bai wa Kano gudunmawa a gwamnatance amma kuma sun kawo tarnaƙi ga tsarin da ta hanyar sa ne kawai za a iya samun wasu irinsu su ɓullo su ma su bayar da tasu irin gudunmawar. Yadda tsarin siyasa ya fito da su aka sansu, jama’ar Kano suka karɓe su kuma har suka samu dama, to su ma su ƙyale adalci ya tabbata a tsarin domin kowa ya samu dama ba tare da tsangwama ba. Har yanzu akwai dama a hannunsu domin su ne suke haska fitilar siyasar Kano har gobe. Idan suka bari wannan dama ta suɓuce daga hannunsu cikin wannan yanayi ba tare da sun gyara ba, to tarihi ba zai taɓa yafe mu su ba domin kuwa ba za a dinga tunawa da su irin tunawar da ake yi wa Mallam Aminu Kano ba. Mallam Aminu Kano ya samu babbar damar sa ne wajen yin jagoranci, Shekarau da Kwankwaso sun samu damar yin mulki a gwamnatance da kuma jagoranci a siyasance baki ɗaya.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.


Tsakanin Fitar da Zakka da Rashin Fitar da Ita

17 Ga Nuwamba, 2013.

Daga: Amir Abdulazeez

S
au tari sai ka ga mun samu kan mu a wani mawuyacin hali wanda babu abin da ya jefa mu a cikinsa face aiyyukanmu. Abin takaicin shine, muna yin wasu abubuwan da mun san sakamakonsu sarai amma kuma idan sakamakon ya same mu sai mu koma gefe muna takaici da mamaki kamar dama can bamu san cewa wannan abin da ya same mu shine sakamakon aiyyukanmu ba. Kamar mutum ne ya bulbule gidansa da fetur kuma ya ƙyasta ashana da hannunsa, sai bayan gidan ya ƙone kuma sai ya koma gefe yana mamaki kamar dama bai san hakan za ta faru ba. Wannan shi ne kwatankwacin wanda ya ƙi bayar da zakka kuma ya dinga mamakin me yasa jama’a suke masa hassada ko baƙin ciki akan dukiyarsa. Haka zalika, wanda ya ƙi bayar da zakka, kada ya yi mamaki don talauci ya yi yawa a gari  wanda har tsananin talaucin ya kai ga wasu sun shiga sana’ar sata kuma a wayi gari ɓarayi sun hauro gidansa sun masa sata.

A matsayin zakka na ɗaya daga cikin manyan turakun Musulunci guda biyar, ya kamata a ce wani hamshaƙin malami ne zai yi rubutu a kan ta amma idan aka duba yadda aka yi watsi da ita da kuma yadda a ke wulaƙanta ta duk da irin tasirinta a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, to sai mu ga cewa haƙƙi ne akan kowa ma ya yi tsokaci dai-dai gwargwado a kan ta har da ma ɗalibai iri na.
Idan muka kalli turakun Musulunci guda biyar, za mu ga cewa zakka ta sha bamban da ragowar turakun guda huɗu waɗanda suka haɗa da Kalmar Shahada, Tsaida SAllah, Azumi da Aikin Hajji. Ba don komai ba sai don cewa, ita zakka bayan kasancewarta ibada, akwai kuma wani gagarumin tasirin da take  da shi a fannin tattalin arziki, zamantakewa, tsaro, kai har ma da siyasa. Wataƙila wasu su yi mamakin menene alaƙar zakka da siyasa?

Idan muka kalli siyasar duniya, za mu ga cewa ɗaya daga cikin abin da yake ƙarawa ƙasashe ƙarfin faɗa a ji a duniya shi ne kyauta da taimako. Za mu ga cewa ƙasashen Kiristoci da Maguzanci masu ƙarfin tattalin arziƙi irinsu Amurka da China sun daɗa faɗaɗa ƙarfinsu ta hanyar ɗibar dukiyar da Allah Ya basu suna taimakawa ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi. Duk da cewa ba za mu kira abin da suke yi a matsayin zakka ba kuma ba suna yi ne don Allah ba, amma mu duba irin yadda wannan alheri nasu yake ƙara musu ƙarfi a siyasance. Inda a ce wadatattun ƙasashen Musulmi  masu arziƙi suna fitar da zakka  su kaita ƙasashen Musulmi da ake buƙatarta, ya za’a ga ƙarfin faɗa a jinsu a siyasance?

Ko da a ce babu malami a kusa wanda zai jawo mana ayoyi ko hadisai akan muhimmancin zakka, ya kamata mu yi tunani mai zurfi don gano hikimar da ta sa Allah SWT Ya wajabta ta. Domin sanin kowa ne cewar Allah ba Ya yin abu face sai da hikima a cikinsa, sai dai rashin ilimi, bincike, zurfin tunani ko kuma gazawa irin ta Ɗan Adam ta sa ya kasa gano hikimar. Misali, dukkan duniya an taru akan cewa dukiya ni’ima ce babba, wasu ma suna ganin ita ce mafi girman ni’ima domin tana iya kawo maka sauran ni’imomin. Ita kuma ba kowa Allah Ya ke ba wa  ita ba sai ‘yan tsiraru. Za ku yarda da ni idan nace masu kuɗin duniya ba su kai kashi uku cikin ɗari ba. Kuma me yiwuwa ku yarda da cewa yawan waɗanda suka mallaki naira miliyan ɗaya tasu ta kansu a Najeriya, ba su wuce kashi ɗaya cikin ɗari ba.
Kasancewar Allah Ya san cewa ba kowa ya ba wa dukiya ba, sai ya ɓullo da zakka domin dukiyar duniya ta dinga zagayawa a tsakanin kowa tunda ba zai yi ma’ana a ce an halicci kowa mai kuɗi ba domin rayuwar ma ba za ta yiwu a haka ba.

Ita dai zakka ba cewa aka yi kowa sai ya fitar da ita ba, a’a sai wanda dukiyarsa ta kai nisabi, idan kuma dukiyar ta kai nisabi to sai ƙarshen shekara kuma kashi ɗaya bisa 40 kacal za’a fitar. Da kai da dukiyarka fa duk mallakar Allah ne, ajiya kawai Ya baka, idan kuma ya ga dama gobe sai ya karɓe ajiyar ya baiwa wani. Haba jama’a!! Ina laifi a cikin abin da aka baka ajiya ba don ka fi kowa dabara ba kuma aka ce a sau ɗaya a kowacce shekara ka fitar da kashi ɗaya bisa 40. Kuma Wanda Ya baka ajiyarnan, ba shi za ka bai wa ba, a’a ɗan uwanka Ɗan Adam mai ƙaramin ƙarfi za ka ba wa.
Amma abin takaici yanzu, a al’ummarmu ta Hausawa ba’a mayar da zakka a bakin komai ba. Wasu ko fitar da ita ma ba sa yi, waɗanda kuma suke daurewa su fitar da ita sai ka ga  suna fitar da ita a wulaƙance, sai su tara mutane suna raba musu N100 ko N500 wai sun fitar da zakka.

Marigayi Sheikh Ja’afar Adam ya taɓa cewa zai yi wahala ka ga maikuɗi ya zo wajen malami neman fatawa akan zakka, sai dai ya zo neman fatawa akan neman aure, kasuwanci, siyasa ko wani abin daban. Yace sai ‘yan ƙalilan ne suke zuwa neman bayani akan yadda za su fitar da zakka.
Wani abin da ya kamata mu kiyaye shi ne, akwai manoma, da makiyaya waɗanda su ma suke watsi da al’amarin zakka musamman a ƙauyukanmu. To lallai ya kamata mu shiga taitayinmu. Wataƙila wannan ce ta sa noman namu na wannan zamanin ma ba ya yin wata albarkar kirki saboda ba ma fitar masa da zakka.

Zakkar nan idan mun fitar, amfanin kanmu yake dawowa, idan kuma mun ƙi fitarwa, masifar a kanmu take ƙarewa. Ita dai zakka idan ka fitar da ita, bayan cewa ka bi umarnin Allah, zai baka lada kuma zai ruɓanya maka dukiyarka, Ya yi mata albarka kuma ya ajiye maka sakamakonka a lahira, akwai amfaninta a nan duniya waɗanda ba za su ƙirgu ba. Ga kaɗan daga cikinsu.

1.      Kakkaɓe talauci: Bankin Duniya wato World Bank da ke ƙasar Switzerland yace sama da kashi 60 bisa 100 na ‘yan Najeriya suna rayuwa a ƙasa da Dalar Amurka ɗaya, kwatankwacin N160 a kullum saboda talauci kuma mafi yawancinsu a Arewacin Najeriya suke (inda Musulunci shi ne addini mafi ƙarfi a yankin). Duk wanda ya mallaki naira miliyan 40 kuma ya fitar da miliyan 1 zakka ya bai wa mutum biyu masu hankali misali. InshaAllahu baɗi su ma sai sun fitar da zakka. Idan aka cigaba a haka, to za’a wayi gari, gari guda sun zama mawadata ko masu rufin asiri, sai dai wata shekarar a ɗebi zakkar wannan garin a kai wani garin da suke da buƙata. Da muna haka a Arewacin Najeriya, da talauci zai dame mu?

2.      Maganin Hassada: Dukiya tana daga cikin abin da ake yi wa mutum hassada a kan ta. Idan kana ɗiban dukiyarka, kana bayar da zakka, za ka samu ƙarancin masu yi maka hassada da ƙiyayya domin dama wani rashin ba ka ba shi ba ne ya sa yake maka hassada.

3.      Maganin Masifa: na taɓa jin Mallam Aminu Ibrahim Daurawa yana cewa, lokacin da suka kai wa waɗanda gobarar ta rutsa da su a Kasuwar Kantin Kwari ziyara a shekarun baya, yace bayan sun jajanta musu kuma sun ba su shawarar su dinga fitar da zakka domin wannan ibtila’in ya yi kama da jarrabawa dalilin rashin fitar da zakka. Dama kuma ita zakka idan ka ƙi fitar da ita, to za ta fitar da kanta ta hanyar da ba ka so kuma ga shi babu lada, gara ma ka fitar da kanka ka samu lada. A wannan gobara ni kaina na san mutum ɗaya da naira miliyan 20 ɗinsa ta ƙone ƙurmus a cikin shago banda ɗumbin kayayyaki.

4.      Tsaro: Ɗaya daga abin da yake kawo rashin tsaro shi ne talauci. Ita kuwa zakka tana rage talauci. Don haka ɓarayi da ‘yan fashi waɗanda suke taka muhimmiyar rawa wajen haddasa rashin tsaro za su yi sauƙi.

A ƙarshe, idan da ace yadda mu ke tururuwar yin salloli biyar a masallatai, yadda muke tururuwar yin azumi lokacin Ramadan, yadda muke takarar zuwa aikin hajji, a ce haka muke takarar bada zakka, da munga canji a cikin al’amuranmu. Kuma ko da ma zakka ba ta da wani amfani a nan duniya, shin ba za mu bi umarnin Allah, mu fitar da ita ba?
Da fatan za mu nemi malamai su yi mana cikakken bayani akan yadda za mu fitar da zakka, lokacin da za mu fitar da ita da kuma waɗanda za mu baiwa ita.

© Malam Amir Abdulazeez 2013.

Gwamnonin Najeriya da Mataimakansu: Wasa Tare, Ci Ban-Ban

20 ga Janairu, 2014

Daga: Amir Abdulazeez

L
okaci ya yi da ya kamata mu tambayi gwamnonin Najeriya a kan dalilin da ya sa ba sa so mataimakansu su gaje su. Ko kuma su mataimakan gwamnonin, mu tambaye su laifukan da su ka yi wa iyayen gidan nasu da har tsananinsu ya kai su ke ƙyamar su gaji kujerunsu.
Tun da aka kafa jamhuriya ta huɗu, bayan da mulkin dimokraɗiyya ya dawo a shekarar 1999 har zuwa yanzu, mataimakin gwamna ɗaya ne tak ya taɓa gadar kujerar gwamnansa kai tsaye tare da goyon bayan mai gidan nasa, wannan kuwa shi ne tsohon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon gwamnan Jihar, Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi wanda ya karɓi mulki a hannun Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura.

Akwai tsirarun mataimakan gwamnonin da su ka gaji gwamnonin nasu amma a cikin yanayi na rikicin siyasa ko baram-baram ko kuma a dalilin wani tsautsayi da ya ratsa. Misali, Goodluck Jonathan ya gaji Diepreye Alamasiegha a matsayin gwamna bayan da Majalisar Dokokin  Jihar Bayelsa ta tsige gwamnan kan zargin cin hanci da rashawa, Mukhtar Ramalan Yero na Kaduna ya zama gwamna bayan da Sir Patrick Yakowa ya rasa ransa a hatsarin jirgin sama, Adebayo Alo Akala na Jihar Oyo ya zama gwamna na ɗan wani lokaci bayan da  Majalisar Dokokin jihar ta tsige Gwamna Rashidi Ladoja kafin daga baya kotu ta dawo da shi kan kujerarsa, Michael Botmang na Jihar Plateau wanda ya rasu kwanannan, ya zama gwamna na ɗan wani taƙaitaccen lokaci bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta tsige Gwamna Joshua Dariye kafin daga bisani kotu ta dawo da shi kan kujerarsa, Uwargida Virgin Etiaba ita ma ta zama gwamna bayan Majalisar Dokokin Jihar Anambra ta tsige Mr. Peter Obi kafin kotu ta rushe wannan tsigewa,  Aliyu Wammako ya zama gwamnan Sokoto sakamakon baram-baram ɗin da su ka yi da maigidansa Bafarawa inda ta kai shi ga komawa PDP shi kuma Bafarawan ya na sabuwar jam’iyyar da ya kafa ta DPP, Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe ya zama gwamna bayan da Gwamna Mamman Ali ya yi mutuwar ba-zato-ba-tsammani. Babu wasu alamu da su ka nuna cewa waɗannan mutane za su samu sahalewar iyayen gidansu wajen zama gwamnoni kafin waɗancan dalilai. Yanzu haka a Jihar Taraba, ba a son ran Gwamna Suntai da mutanensa, Mataimakin Gwamna Garba Umar ya ke riƙe da ragamar Jihar ba, duk kuwa da cewa shi Suntai ɗin ya na can rai a hannun Allah.

Bayan wannan, mun ga irin yadda wasu gwamnoni su ka dinga zaman doya da manja da mataimakansu, a wasu lokutan, kawai saboda mataimakan sun nuna sha’awar su gaje su. Akwai Jihar da aka ce gwamnan ya hana mataimakinsa ko da takarar sanatan da ya nema ba ganin cewa ba za a ba shi takarar gwamna ba, bisa dailin cewa wai bai kamata a ce shi ya na sanata kuma mataimakinsa ma ya na sanata ba. Ƙiriiri ya ɗauko wani can ya ba shi takarar. Wani lokacin ma gwamnonin su kan tilasta wa mataimakan nasu barin kujerunsu a kan wannan dalili ko kuma a kan wani dalili daban kamar yadda mu ka gani kwanannan a Jihar Imo tsakanin Rochas Okorocha da mataimakinsa. Irin haka ta faru a Jihar Jigawa a lokacin Saminu Turaki wanda a shekara takwas, ya yi mulki da mataimaka kusan uku da kuma a Jihar Bauchi tsakanin Mallam Isa Yuguda da Garba Gadi. A wasu jihohin irin su Kano, mun ga yadda Mallam Shekarau ya ƙare zangunan mulkinsa cikin yanayain rashin jituwa da mataimakansa guda biyu.

Wani lokacin yanayin ya kan nuna tamkar laifin na mataimakan gwamnonin ne, to amma mun ga yadda wasu mataimakan su ka dinga biyayya sau da ƙafa har tsawon shekaru takwas ga ma su gidan nasu, wani lokacin wannan biyayya ba irin baƙin jinin da ba ta janyo mu su, amma sai biyayyar ta tashi a banza. Maimakon gwamnonin su bai wa mataimakan nasu damar su gaje su, sai ka ga sun ɗauko kwamishina, sakataren gwamnati ko shugaban jam’iyya su saka a gaba. A wasu lokutan ma sai su ɗauko wani can daban su kawo. Misali a nan, Marigayi Yakowa ya na nan zaune, amma Ahmed Makarfi na Kaduna ya ɗauki tsohon kwamishina Namadi Sambo ya ba shi takarar gwamna kuma aka sa Yakowan ya bi shi a matsayin mataimaki, Abdullahi Gwarzo na Kano na nan kuma ya na nema amma Shekarau ya ɗauko kwamishina Salihu Takai ya ba shi takara, Gwamna Abdulfatah Ahmed na Jihar Kwara tsohon kwamishinan Bukola Saraki ne, Gwamna Shettima na Jihar Borno tsohon kwamishinan Ali Modu Sheriff ne, Gabriel Suswam na Jihar Benue tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya ne kuma ya samu goyon bayan Gwamna George Akume, Gwamna Babangida Aliyu na Jihar Niger tsohon Babban Sakatare ne a Ma’aikatar Birnin Tarayya Abuja, Gwamna Liyel Imoke na Jihar Cross-Rivers tsohon sanata ne kuma ya samu goyon bayan Gwamna Donald Duke. Misalan su na nan birjik, amma ba za ka ji tsohon mataimakin gwamna ba. Da alama dai kwamishinoni sun ma fi ƙima a idon gwamnonin fiye da mataimakan nasu.

Sashe na 187 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana mataimakin gwamna a matsayin wanda kujerar gwamna ba ta samuwa da kuma tafiyuwa sai da shi. Hakan na nuna cewar a tsarin aiki, babu wani makusancin gwamnan kuma abin amincewarsa kamar mataimakinsa. Haka zalika, bayan gwamnan, babu wanda ya san sirrin gwamnatin kamar mataimakinsa. To, amma, me ya sa gwamnoni ba sa son ba su dama? Wani ma ya na karɓar kujerar mataimakin ne tun farko bisa tunanin cewa idan zangonsu ya ƙare, mai gidansa zai ba shi dama, amma ina. A tunaninmu irin na talakawa, mun ɗauka wanda ku ka yi aiki tare kafaɗa da kafaɗa na tsawon shekaru huɗu ko takwas, ai ba wanda zai ɗora a inda ka tsaya kamar sa.

To wai, ko shin mataimakan ne ba su da farin jinin cin zaɓe, shi ya sa gwamnonin su ke ƙin tsayar da su? Ko kuwa dama wani dalili ne irin na siyasa ya tilasta wa gwamnonin ɗaukar mataimakan nasu tun farko amma ba su ne zaɓin su ba? shin gwamnoni su na tunanin mataimakan nasu za su ci amanar su bayan sun gaje su?  Shin biyayya da mu ke gani a fili mataimakan na yi wa gwamnoninsu, a fili ta ke kawai, amma a ɓoye abin ba haka ya ke ba. Shin gwamnonin, mugunta da baƙin ciki su ke yi wa mataimakan nasu don kar su taka irin matasyinsu ko kuwa su na tsoron ba za su iya juya su ba ne bayan sun gaje su?

Ni dai, ba zan iya bayar da waɗannan amsoshi ba, wataƙila sai su gwamnonin da mataimakan nasu, amma na taɓa ji daga majiya mai tushe, lokacin da wani mataimakin gwamna ya ke miƙa mulki a ofishinsa ga wani sabon mataimakin gwamnan a wata jiha, sai ya ke ce ma sa: ‘ɗan uwana, babu aiki mai wahalar riƙewa a siyasance irin na mataimakin gwamna. Domin kuwa, idan gwamna ya yi bajinta sai jama’a su yabe shi shi kaɗai, amma idan ya yi kuskure, sai a zageku tare’.

Hasashen da manazarta siyasar ƙasar nan su ke yi shi ne, a wannan karo ma gwamnoni da dama ba za su bai wa mataimakansu damar su gaje su ba a zaɓen 2015. A wsu jihohin ma hakan ta fito fili ko kuma gwamnonin sun bayyana wa mataimakan nasu a baki ko a aikace cewar ba za su gaje su ba. Wannan abu dai ya na da ɗaure kai musamman idan aka yi la’akari da abin da ya ke faruwa a siyasun wasu ƙasashe. Mislali, tun a farkon mulkin Marigayi Nelson Mandela, ya fara assasawa a aikace cewa mataimakinsa Thabo Mbeki shi zai gaje shi, kuma shi ya gaje shi ɗin. A ƙasar Amurka, duk da cewa su ma mataimakan ba su fiya gadar masu gidan nasu ba, amma George Bush (babban) ya gaji shugaba Ronald Reagan bayan da ya yi masa mataimaki na tsawon shekaru takwas kuma tare da goyon bayan mai gidan nasa. Shugba Bill Clinton ya goya wa mataimakinsa Al-Gore baya inda har ya samu takara a jam’iyyarsu, duk da cewa bai lashe zaɓen ba a shekarar 2000. To amma mu a nan Najeriya, ba haka abin ya ke ba. Wasu gwamnonin ma da gangan su ke ɗaukar rarraunan mataimaki, a wasu lokutan ma tsoho ko rago wanda ba ma zai yi sha’awar ya gaje su ba.

Yanzu dai mun zuba ido a shekarar 2015 mu ga ko za ta canza zani duk da cewa babu alamun hakan. Idan har ba ta canza zani ba, to duk mai sha’awar zama gwamna a rayuwarsa, a yanzu ko a gaba, ya yi tunani mai zurfi kafin ya karɓi kujerar mataimakin gwamna idan an yi masa tayi tun da dai ƙarfin gwamnonin Najeriya a siyasance, idan ya na yawa, har ya yi yawa, su kuma ba su yarda mataimakinsu ya gaje su ba.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.