Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Matsalolin Motar Haya A Kano………

10 Ga Satumba, 2014.

Daga: Amir Abdulazeez

D
uk da cewar harkar sufuri ta na ɗaya daga cikin harkoki mafi muhimmanci a rayuwarmu ta yau, amma ba ma ba ta cikakkiyar kulawar da ta ke buƙata. Akwai haƙƙoki da yawa a kan gwamnati, direbobi, mamallaka abubuwan sufuri da kuma jama’ar gari, waɗanda sai mun kula da su sannan harkar za ta inganta.
Duk da cewar ba ni da cikakken ilimi a kan yadda  harkar sufuri ta haya ta ke gudana a mafi yawan jihohin Najeriya, amma ina da cikakkiyar masaniyar cewar harkar ta na cikin yanayi mara kyau a Jihar Kano. Fiye da kashi uku bisa huɗu na al’ummar Jihar Kano sun dogara ne da motocin haya domin zirga-zirgarsu. Ƙalilan ne suke da abubuwan hawa nasu na kansu. Wannan ta na nuna cewar jama’a suna da haƙƙin  kawo gyara a kan yadda tsarin motocin haya suke gudanar da aiyukansu. Idan da mutane za su saka kishi a zuciyoyinsu ma, ba sai sun jira gwamnati ta sa hannu a waɗannan al’amura ba.

Idan mu ka kalli girman Kano da yawan mutanenta waɗanda a ke ƙiyasata yawansu da sama da miliyan 12, to za mu ƙiyasata cewar aƙalla yawan motocin da suke zagayawa a kan titunan Kano sun haura miliyan guda ko kuma wani abu makamancin haka. A cikin wannan adadin, za mu iya cewa 65% motocin haya ne, ko dai tasi-tasi ko kuma bas-bas. Bisa wannan lissafi, idan ka ɗauke Jihar Lagos, babu jihar da ake kai kawo kamar Kano, amma da wahala a samu jihar da tsarin sufurin hayar ta ya ke kara zube kamar Kanon.
Abu na farko dai, a Kano ba ka buƙatar izini ko shawarar kowa ko wata hukuma kafin ka mallaki motar haya ko kafin ka zama direban motar haya. Idan ma akwai wata doka ko hukuma mai kula da hakan, to ba ta aikin ta. Wannan ta sa a yau za ka iya sayen motocin haya ko guda nawa ka ke so kawai ka zuba a kan titi kuma ka sa su su dinga bin hanyar da suka ga dama. Sannan kuma, in dai ka iya mota, to kawai sai ka kama tuƙa motar haya, da wuya a samu mai ce maka uffan. Me yiwuwa idan aka yi sa’ar gaske jami’an Road Saftey su tambaye ka diraba lasin sau ɗaya ko sau biyu a shekara.

Shekarun baya, Gwamnatin Kano ta fara tilastawa bas-bas yin wani fentin kore da ruwan ɗorawa domin a iya ganesu, amma yanzu da alama an daina ƙarfafa dokar kamar da. Sannan kuma kwanakin baya, lokacin da matsalar tsaro ta ta’azzara, gwamnati ta ɓullo da tsarin yi wa babura masu ƙafa uku rajista bayan da aka soke achaɓa, amma wannan rajista ba mu samu labarin ta haɗa da bas-bas ko tasi-tasi ba.

Abu na biyu, motocin haya a Kano suna ɗauka da sauke fasinja a duk inda suka ga dama. Babu wata tsayayyiyar madakata wato Bus Stop, kawai za su iya tsayawa a kowanne lokaci, kuma mafi yawanci ba sa kunna sigina ko su nuna alamar tsayawa. Bayan haka kuma motocin haya su kan yi lodi a inda suka ga dama, ko’ina a Kano tasha ne. Kwanakin baya hukumar kula da harkar sufurin kan  titunan Jihar Kano wato KAROTA ta ɗan kawo gyara a kan wannan al’amura ta hanyar hana lodin fasinjoji a wasu gurare, to amma hakan bai magance ko da 20% na matslar ba. Sannan kuma, ita kan ta KAROTA ɗin ta yi sakaci kwana biyu, domin inda ta hana tsayawar a baya, yanzu duk kusan an dawo ana tsayawa.

Abu na uku, mafi yawan motocin haya a Kano tsofaffi ne kuma lalatattu, wasu ma sun gama mutuwa. Da yawa daga cikinsu, bai kamata a bar su su dinga ma hawa kan titi ba balle ma su ɗebi mutane. Me yiwuwa wannan ce ta sa direbobin motocin suke yin tuƙin da suka ga dama, domin basu da asara ko an buga musu. Wannan ya taimaka da gaske wajen lalata yanayin tuƙi tare da ƙin bin dokokin kan titi a cikin Birnin Kano. Bayan haka wasu daga cikin direbobin ba su da tarbiyya balle ɗa’a. Sai ka ga mutum ya na tuƙi daga shi sai singileti ko gajeren wando, ko ka ga kwandastan bas ya na zagi da yi wa fasinjoji sa’annin iyayen sa rashin kunya.

Abu na huɗu, da yawa a cikin motocin hayar Kano ba sa son biyan harajin N20 ko N50 a rana wanda gwamnatocin ƙananan hukumomi ta kan sanya musu. Sai ka ga mai bayar da rasit ya na yi wa direba magana, amma sai ya ga dama zai kula shi, kamar ya na nuna shi ya fi ƙarfin gwamnati ko kuma ita gwamnatin ba ta damu da harkar sa ba. Ga shi kuma wani lokacin farashin motar haya a Kano ba shi da wata ƙa’ida, wani lokaci kwandasta sai ya caje ka yadda ya ga dama sai dai a yi ta rigima. Wani lokacin kuma su ɗauko fasinja da niyyar za su kai shi wani waje amma sai su ƙi ƙarasawa da shi, kawai sai su juye shi a inda suka ga dama, masu adalcin cikinsu ne ma suke saka shi a wata motar ko su dawo masa da wani ɓangare na kuɗinsa.

Abu na biyar, mafi yawancin masu motar haya ba sa ɗaukar adadin fasinja dai-dai da abin da motar za ta iya ɗauka ba. Misali a cikin tasi, sai su cusa mutum huɗu a baya kamar kayan wanki, mutum biyu kuma a gaba, tare da cewa wani ma cinyarsa a kan giya ko hanbrek ɗin motar ya ke, da ƙyar direba zai dinga sarrafa motar saboda matsatsi. Idan kuma bas ce, sai a zuba mutane a maleji, wani lokacin har da but dan hauka. Maimakon haka, ai kyautuwa ya yi a ɗan yi ƙarin kuɗin mota N10 ko N20. Kwanaki da na shiga bas daga unguwarmu zuwa ‘Yankura, na kalli yadda muka gwamutsu a cikin ta, babu wani sararin da iska ta ke zagayawa ko kaɗan, sai na ce  a raina yanzu abin Allah Ya kiyaye, da cutar Ebola za ta zo Kano, ai da babu hanyar da za ta fi saurin yaɗuwa kamar a cikin motocin haya.

Bayan haka sai ka ga an gwamutsa maza da mata su matsu sosai a kujera ɗaya. Sai kawai ka ji rabin jikin matar aure a kwance a jikinka a cikin tasi ko bas, wai ai motar haya ce, larura ce. Idan muka je lahira, dukkanmu sai mu taru mu yi wa Allah bayanin wannan wacce irin larura ce haka. Irin wannan gwamutsa maza da mata da muke yi a cikin motocin haya shi yake kawo taɓarɓarewar tarbiyya da kuma masifu iri-iri. Zai iya zama ɗaya daga cikin dalilan da Allah SWT Ya sa ya ke jarrabtar mu da bala’o’i iri-iri.

Waɗannan matsaloli sai mun taru mun haɗa ƙarfi da ƙarfe sannan za mu iya yaƙar su kuma dole mu ɗauke su da gaske ba da wasa ba. Mu matsalar mu ita ce, in dai abu bai shafi neman kuɗi ko neman abinci ba, to ba mai muhimmanci ba ne.

Ƙungiyoyin direbobi da masu motocin haya su tashi tsaye wajen tsaftace sana’arsu. Gwamnati ta kafa tsauraran dokoki da matakai kuma ta tabbatar ana binsu. Gwamnatain  Kano za ta iya faɗaɗa aiyukan hukumar KAROTA don su ƙunshi magance waɗannan abubuwa sannan kuma jama’ar gari su bayar da haɗin kai tun da ba wanda ya fi su cutuwa da wannan matsala ta hanyar bin duk wasu dokoki da za a gindaya tare kuma ƙauracewa dukkan mai motar da bai cika ƙa’idoji ba.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.


No comments:

Post a Comment