Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Manyan Nasarori da Matsalolin Gwamnatin Kwankwaso

10 Ga Satumba, 2014.


Daga: Amir Abdulazeez

M
utane da yawa a Kano, Arewacin Najeriya da ma sauran sassan Najeriya suna matuƙar bibiyar al’amuran siyasa da gwamnati a Kano tare da nuna sha’awar samun bayanai akan irin  mulkin da Kwankwaso ya ke yi a Jihar Kano. Mai yiwuwa hakan bay a rasa nasaba da irin shahara da Jihar Kano ta yi a faɗin ƙasarnan ko kuma shaharar da shi Kwankwason ya yi a siyasar wannan lokaci da muke ciki. Waɗanda suka riski wani ɓangare na amfanin gwamnatin su kan ɗauka cewar babu wani abu da gwamnatin ta shimfiɗa sai nasara yayin da kuma wasu waɗanda suka riski wani ɓangare na takalmin ƙarfen gwamnatin, sai su kan ɗauka cewar babu abin da ta shimfiɗa sai matsala.
Yanzu haka saura kimanin watanni takwas gwamnatin Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ta kammala wa’adin ta na shekaru huɗu wanda shi ne dawowar ta a karo na biyu a Jihar Kano. Babu shakka watanni takwas ba za su hana a yi wa abin da aka shafe watanni 40 ana gudanar da shi alƙalanci ba.

Gwamnatin Kwankwaso ta zo gangara kuma da wahala a ɗan wa’adin da ya rage mata ta yi wani abu sabo wanda ba ta bayyana shi a baya ba. Idan aka yi sa’a ma ta ƙarasa ɗumbin aiyukan da ta ke kan yi yanzu kafin wa’adinta ya ƙare, to sai a gode wa Allah. Idan kuma hakan ba ta samu ba, to babu shakka za a gode mata saboda kafa harsashin manyan aiyuka masu matuƙar amfani da ta yi, waɗanda gwamnati mai zuwa ya kamata ta ƙarasa kuma ta ɗora a kan mafi yawa daga cikinsu.
Duk wanda ya karanta kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2014, zai lura cewar akwai aiyuka da yawa da kasafin ya ƙunsa waɗanda an riga an fara su tun shekarun 2012 da 2013. Don haka bisa ga dukkan alamu kasafin kuɗin gwamnatin na shekarar 2015 zai mayar da hankali kacokam wajen ƙarasa dukkan aiyukan gwamnatin na shekarun 2011, 2012, 2013 da 2014.
Dawowar Kwankwaso mulkin Kano a karo na biyu ya bar tarihi ta kowanne ɓangare. Akwai abubuwa masu kyau da ya yi waɗanda ba za a taɓa mantawa da su ba, haka kuma akwai matsaloli waɗanda ba za a taɓa mantawa da su ba.


NASARORI

5. ƘAWATA BIRNIN KANO: Gwamnatain Kwankwaso ta ƙawata Birnin Kano fiye da kowacce gwamnati a tarihi. A yanzu da wahalar gaske a samu wani titi mai kwalta, komai ƙanƙantarsa, a cikin birni da kewaye wanda babu fitilu masu haske ba, sannan kuma ba a fashin kunna waɗannan fitilu a kowacce rana. Sannan kuma yanzu haka gwamnati ta na kan gyarawa da zamanantar da dukkan ƙofofin tsohon Birnin Kano na asalin tarihi, kuma gyaran ba na wasa ba, wasu mu rushesu a ke yi ana sake gina su.
Gwamnatin Kano ta na kwashe shara a cikin Kano ba ƙaƙƙautawa, don haka birnin a cikin tsafta yake a mafi yawan lokuta. Wannan ƙari ne a kan tsaftace birnin da ake gudanarwa a kowacce Asabar ɗin ƙarshen wata. Sannan kuma duk wani gini mallakar gwamnati, an gyara katangarsa kuma an fente shi tare da sanya fitilu masu haske a jikin bangwayensa. Banda wannan kuma, an sassaka intalo-intalo a gefunan tituna da sauran gurare, kuma an gyara wasu daga cikin shatale-talen Kano tare da ƙawata su. Bayan duka waɗannan, akwai guraren shuke-shuke na musamman da aka ware, wasu don shaƙatawa, wasu kuma don shuke-shuken kawai. Sannan kuma an samar da gadojin tsallaka titi da ƙafa a gurare da yawa, wanda hakan ya samar da tsari a kan yadda mutane masu tafiya a ƙasa suke amfani da tituna.
Wani abin sha’awa kuma, da zarar wani abu ya lalace ko ya samu matsala a cikin birnin, nan da na za ka ga an zo an gyara shi an mayar da shi yadda ya ke, ko kuma an ƙara masa kyau da nagarta.

4. ƘARASA AIYUKAN TSOHUWAR GWAMNATI: gwamnatin Kwankwaso ta bai wa mutane mamaki wajen ƙaraswa ko ɗorawa a kan aiyukan gwamnatocin baya. Misali, gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta tafi ta bar aiyukan titunan da ta fara ba ta gama ba, amma kwankwaso ya ƙarasa su, kamar titin da ya taso daga Tal’udu zuwa Mandawari zuwa Kasuwar Kwari kuma ya haɗe da Titin Ibrahim Taiwo, sannan akwai titin da ya tashi daga Kurna Makaranta ya haɗe da Kabuga, da sauran waɗansu titunan. Sannan kuma gwamnatin Shekarau ta tafi ta bar tsaruka, kamar tsarin yin gidaje da yawa a gefunan garin Kano domin sauƙaƙa cinkoso da kuma tsarin faɗaɗa tituna, waɗanda duk Kwankwaso ya aiwatar da su.
Dogon ginin Magwan da Marigayi Abububakar Rimi ya gina kuma aka yi watsi da shi shekara da shekaru, yanzu haka Kwankwaso ya sa ana gyara shi domin mayar da shi makaranta.
Shirin gwamnatin Shekarau na wadata Kano da ruwa ta hanyar gina matatun ruwa manya na Tamburawa da Watari bai samu cikakkiyar nasara ba sai a zuwan Kwankwaso. Domin Kwankwaso shi ne yanzu ya ke shimfiɗa manya-manyan bututun da ya ke ɗauko wannan ruwan daga matatun zuwa ga jama’a domin amfani. Yanzu haka kimanin 50% na baki ɗayan Jihar Kano sun fara amfana da wannan ruwa.

3. MANYAN TITUNA DA MANYAN AIYUKA: kafin dawowar Kwankwaso, babu titin sama ko ɗaya a cikin garin Kano, amma mai yiwuwa kafin ya tafi, Kano za ta zama ta na da huɗu lafiyayyu, guda uku kuma daga ciki, gwamnatinsa ce ta yi su. Kwankwaso ya faɗaɗa dukkan hanyoyin shigowa Kano in banda titin Katsina, a ciki akwai Titin Gwarzo, Titin Hadejia, Titin Zaria da Titin Panshekara. Duk waɗannan ƙari ne a kan tituna da dama a ciki da wajen Kano da gwamnatin ta ke ɓarjewa ta na gyarawa da waɗanda ta ke faɗaɗawa da kuma ƙirƙirowa. Akwai titunan ƙarƙashin ƙasa da gwamnatin ta ke yi gadan-gadan yanzu haka a Gadon-Kaya Da Kabuga.
Wasu manyan aiyukan na tarihi da gwamnatin ta ke kan yi sun haɗa da gina tashar wutar lantarki mai zaman kan ta daga madatsun ruwa na Challawa da Tiga mai ƙarfin megawatt 35, da kuma rufe shahararren Kogin Jakara domin yin titi a kansa. Bayan haka akwai yuurin samar da tashoshin manyan motoci guda biyu.
Gwamnatin Kwankwaso ta samar da birane guda uku sukutum a Jihar Kano. Biranen sune Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo.
Gwamnatin Kano a ƙarƙashin Kwankwaso ta yi bakin ƙoƙari wajen bai wa kowanne fanni kulawa dai-dai gwargwado. Sassan lafiya, noma wasanni, ruwa, kimiyya da fasaha duk an taɓa su, sai dai a ce wani ɓangaren ya fi wani samun kulawa a gwamnatin.

2. SAMAR DA AIYUKAN YI DA ƊA’A A CIKIN AL’AMURA: kafin dawowar gwamnatin Kwankwaso,  a Kano ba a tsoron gwamnati; idan ta sa doka, ƙa’ida ko tsari ba a cika bi ba, ko kuma sai an ga dama a ke bi. Yanzu a Kano, wannan ta kau domin da wahala gwamnati ta faɗi abu a tsallake shi.
Bayan haka, kafin dawowar Kwankwaso, akwai ma’aikata da yawa da suke wasa da aikin gwamnati, amma daga zuwansa ya gyara musu zama sannan kuma ya fitar da ɗaruruwan ma’aikata na boge, na ƙarya waɗanda ake karɓe kuɗaɗen gwamnati da sunansu daga cikin tsari. Ko shakka babu, Kwankwaso ya yi maganin ɓarayi masu sace kuɗin gwamnati tun daga kan ƙananan hukumomi har zuwa jiha.
Gwamnatin Kwankwaso ta samar wa da dubban mutane aiyukan yi a gwamnati da kuma sana’o’i. Ta rarrabawa mutane da yawa tallafi domin yin jari da kuma rancen kuɗi da kayan aiki don bunƙasa sana’a.
A ƙarƙashin Hukumar Hisba, gwamnatin ta aurar da zaurawa da ‘yan mata sama da 1000 a Kano, wanda shi kansa wannan wani nau’i ne na samar da ɗa’a da tarbiyya. Gwamnatin ta hana barace-barace a kan titi tare da samar da tsari na musamman domin tallafawa da koyawa waɗannan mabarata  sana’ao’i domin dogaro da kansu kuma ta hana sakin dabbobi barkatai a kan titi.
Kwankwaso ya kafa hukumar KAROTA wacce ta taka rawar gani wajen kawo tsari da doka akan titunan Kano bda kuma harkar sufurin kan titi baki ɗaya.

1. INGANTA ILIMI: me yiwuwa wannan shi zai zamo bakandamiyar Gwamnatin Kwankwaso. Gwamnatin Kano a shekaru uku da suka gabata ta taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta ilimin addini, firamare, sakandire, jami’a da sana’o’i.
Kwankwaso ya gina ajujuwa manya masu bene a kusan ɗaya bisa ukun na makarantun firamaren Kano baki ɗaya. Wannan ƙari ne  a kan ciyar da yara kyauta da basu kayan makaranta. Gwamnatin ta samar da ƙarin makarantun sakandire kuma ta ɗauki nauyin ɗaruruwan ‘ya’yan talakawa domin yin digiri na ɗay da na biyu a ƙasashen duniya daban-daban.
Idan mutane ɗarin da gwamnatin Kwankwaso ta ɗauki nauyi domin koyo tuƙin jirgi a ƙasar Jordan suka kammala, me yiwuwa Jihar Kano za ta iya zama jiha guda ɗaya mafi yawan matuƙa jirgin sama a faɗin Nahiyar Africa. Haka kuma ‘yan mata 100 da suke karatun likita a ƙasashen ƙetare za su taimaka wajen zamowar Jihar Kano kan gaba a yawan mata likitoci a Najeriya idan sun kamala karatunsu.
Gwamnatin Kano ta gina tare da gyara wasu makarantun islamiyyu da yawa, sannan ta samar da sabuwar jami’a sukutum mai suna North West University. Wannan ƙari ne akan dukkan makarantun gaba da sakandire na Jihar Kano da gwamnatin ta gyara kuma ta ɗaga darajarsu izuwa masu yin karatun NCE ko digiri. Kai  a taƙaice dai gwamnatin ta mayar da ilimi kyauta tun daga firamare har jami’a ga ‘yan asalin Jihar.
Bayan waɗannan, da wahala a samu wata sana’a ta gargajiya ko ta zamani wacce Kwankwaso bai yi wa babbar makaranta ba sukutum. Akwai makarantun koyon sana’o’i, noma, kasuwanci, tuƙi, kiwo, tsaro, wasanni da dai sauransu a warwatse a ƙananan hukuomi daban-daban na Kano.


MATSALOLI

5. KWANKWASIYYA: ɗaya daga cikin manyan matsalolin gwamnatin Kwankwaso shi ne ɗarikar sa ta Kwankwasiyya. Ya yi amfani da ƙarfin gwamnati ko dai kai-tsaye ko kuma kai-zaune wajen tilasta wannan aƙida ta sa a kan jama’ar Kano. Babu yadda za a yi Kwankwaso ya shigo da kai cikin gwamnatinsa sai ka sa jar hula, idan kuma ka na cikin ta sai ka saka ta don kada a yi waje da kai. Abin kamar almara.
Kwankwaso ya yi amfani da kuɗin gwamnati da dukiyar al’umma ya yi aiyuka amma duk ya bi ya rubuce su da sunan ɗarikarsa wacce kuma ita ba hukuma ce ta gwamnati ba. Idan ɗan kwangila ya yi wa gwamnati aiki bai rubuta sunan Kwankwaso a jiki ba, to ba lallai ne gaba idan ya nemi kwangila a ba shi ba, don haka tsirarun aiyuka ne kawai za ka ga babu sunan Kwankwasiyya a jiki.
Kafin zuwa Kwankwaso ya zargi gwamnatin baya da sanya siyasa a cikin harkokin gwamnati inda ya yi kira ga kantomomin ƙananan hukumomi na wancan lokaci, a matsayinsu na ma’aikata da su daina yarda ana yin amfani da su a siyasa. Sai ga shi babu kantomomin da suka kai na Kwankwaso shiga da taka rawa a cikin siyasa. Bayan haka sama da kimanin 90% na mata, matasa da sauransu da ya bai wa jari ko tallafi a ƙarƙashin shirinsa na CRC dukkansu ko dai ’yan Kwankwasiyya ne ko kuma ‘yan uwan ‘yan Kwankwasiyya ko waɗanda suka kama ƙafa da su. Akwai matan da suka dinga samun jarin sau da yawa a maimakon sau ɗaya domin su ‘yan ɗariƙar ta sa ne.
Sannan kuma an zargi gwamnati da yin amfani da kuɗaɗen jama’a ta na sayen jajayen huluna buhunna-buhunna ana rabawa a ƙananan hukumomi, wai dole sai an yi aƙidar Kwankwasiyya.

4. TAKURAWA DA TAUYEWA: zai yi wahala a samu gwamnatin da ta takurawa mutane, ma’aikata da ma muƙarrabanta kamar  gwamnatin Kwankwaso ba. Gwamnatin ba ta fiye duba masalahar jama’a ba a mafi yawancin abin da ta ke yi. A wasu lokutan, aiyukan da gwamnatin ta sa kan ta, shi za ta yi ko da kuwa ba shi ne mafi dacewa ga jama’ar wannan guri ba. Sannan kuma kullum tunanin gwamnatin shi ne  sai an yi komai ta ƙarfi sannan zai samu nasara kuma a hakan ma sai an yi shi cikin gadara. Sannan gwamnatin ba ta fiye girmama dokar da ba ita ta kafa ba.
Tsaruka na Ihsani da gwamnati ta ke yi domin kyautatwa ma’aikatan ta , Kwankwaso ko dai ya raunata su ko kuma ya yi musu ƙanshin mutuwa. Sai an ga dama a ke bayar da ɗan kuɗin gero da na rago da ma’aikatan suka saba samu a baya. Tsaruka na kyautatwa jama’a da gwamnatin baya ta ke yi kamar su ciyarwa lokacin azumi duk sun yi rauni a gwamnatin sa.
Gwamnatin Kano a ƙarƙashin Kwankwaso ta hana har da ma muƙarrabanta su yi aikinsu. Sai ka ga abin da bai kai ya kawo ba wanda bai wuce a bai wa wani jami’in gwamnati dama ya aiwatar da shi ba, amma gwamna sai yace zai aiwatar da kansa, da alam bai yarda da kowa ba sai kansa. Sannan kuma majalisar dokokin Jihar Kano ba ta taɓa zama hoto ko ‘yar amshin shatar gwamna ba kamar a wannan lokaci. Duk dokar da gwamna yak e so a ƙirƙira ko a yi wa gyaran fuska, to an gama kawai ba tare da wani ɓata lokaci ba. Hatta shugabancin majalisar ma, gwamna ne ya ke da ta cewa a kan sa.
Bayan haka, gwamnatin ta kawo tawaya a tsarin aiyukan ta da kanta domin aiyuka da yawa ta kan yi su ne kawai a inda za a gani, kamar bakin titi amma ba a inda suka dace ba. Misali, manyan ajujuwa benaye na firamare, da wahala gwamnatin ta gina muku shi idan makarantar ku ba a bakin titi ta ke ba, komai buƙatar ku da shi, kuma ko da makarantar a bakin titi ta ke, ba lallai ne a duba inda ya dace ba a cikin makarantar, a’a sai inda zai kallo titi a ga tambarin Kwankwasiyyar nan ƙarara.

3. ƘANANAN HUKUMOMI : A ƙarƙashin gwamnatin Kwankwaso ne Jihar Kano ta samu kantomomi waɗanda sune mafi daɗewa a kan mulki a tarihi ba tare da an shirya zaɓe ba. Sannan kuma gwamnatin ita ta shirya kuma ta aiwatar da zaɓen ƙananan hukumomi mafi muni da rashin inganci a tarihin Jihar Kano. Bayan haka gwamnatin ta yi amfani da ƙarfin ta wajen ɗaurewa waɗanda bas u cancanta ba gindi domin samun mulkin ƙananan hukumomi. An zargi wasu daga cikin Ciyamomin da rashin ilimi, ƙwarewa da kuma iya aiki.
Duk waɗannan abubuwa ƙari ne a kan maƙurewa da gwamnatin ta ke yi wa ƙananan hukumomi ta hanyar hanasu kuɗaɗensu da kuma haƙƙoƙinsu. Gwamnatin ta hanasu cikakken ‘yanci tare da damar da za su yi wa mutane aiki, sai dai zaɓi irin aikin da za ayi musu a lokacin da ka ga dama ko da kuwa ba shi suke muradi ba. Shugabannin ƙananan hukumomi na wannan lokacin kusan ba su da maraba da hotuna.
Bayan haka gwamnatin ta ƙi yi wa jama’a cikakken bayanin adadin kuɗaɗen da suka shigo aljihun ƙananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya tun daga watan Mayun 2011 zuwa yanzu tare da faɗar abubuwan da ta yi da su, kuma nawa ne ya rage, kuma me ya sa ta ke hanasu kuɗaɗensu, sannan wacce doka ce ta ba ta damar yin hakan?

2. ƘWACE FILAYE DA RUGUJE GIDAJE : gwamnatin Kwankwaso ta yi rushe-rushen gidaje da ƙwace filaye nau’i biyu. Nau’in farko shi ne waɗanda ta ruguje ko ta karɓe da ba sa kan ƙa’ida ko kuma suna kan ƙa’ida amma ta na buƙatar yin wani abu mai muhimmianci da su kuma  ta bayar da isasshiyar sanarwa tare da biyan kuɗin diyya a inda hakan ta dace. Kashi na biyu shi ne wanda ta karɓe ko ta ruguje ko dai, suna kan ƙa’ida ko ba sa kan ƙa’ida, ba tare kuma da cikakkiyar sanarwa ba kuma ba tare da biyan diyya ba, sannan kuma bayan ta karɓe sai ta ɓige da yin wani abu wanda ba shi ne masalahar jama’a ba.
Mutane da yawa sun zargi gwamnatin da zalunci da kuma cutarwa ga jama’a yayin da ta ƙwace wasu filaye da dama kuma ta ruguje gidajen da aka fara ginawa ba tare da ta biya kowa diyya ba, kuma ta sake yanka waɗannan filaye ta rarrabawa ‘yan siyasa. Wannan ya na daga ciin abubuwan da suka zubarwa da gwamnatin daraja musamman a idon masu ƙaramin ƙarfi.
Bayan haka duk rushe-rushen da gwmanatin ta ke yi a tsawon shekaru uku, amma ta kasa kawo ƙarshen kasa kaya a bakin tituna da kuma ƙaro rumfunan shaguna zuwa bakin titi tare da gina kes-kes, duk dai a kan titin.

1. AIKIN TITIN KILOMITA BIYAR-BIYAR: aikin titin kilomita biyar-biyar da gwamnatin Kwankwaso ta ke yi a ƙananan hukumomi 44 zai iya zamowa aiki guda ɗaya da gwamnatin ta fi narka kuɗaɗe fiye da kowanne aiki a cikinsa kuma sannan ya zamo aiki mafi rashin nasara da gwamnatin ta yi a tsawon shekaru ukun da suka gabata. Da farko dai da wahala a samu titi guda ɗaya a cikin 44 ɗin da ake yin sa a ƙasa da naira miliyan 1000 (Biliyan 1).
A cikin kusan shekaru biyu da aka yi ana aiyukan titunan, da wahala a samu guda goma waɗanda aka kammala a cikin guda 44, wasu ƙananan hukumomin ma an daina aikin. Bayan haka wasu aiyukan titin an yi sune akan manyan titunan Gwamnatin Tarayya wanda hakan zai iya jawowa gwamnatin ta tarayya ta ɓarje su yayin da ta buƙaci yin amfani da titin ta, wannan kuwa ba ƙaramar ɓarnar dukiya bace. Irin waɗanda wannan matsala za ta iya shafa sun haɗa da Bichi, Tsanyawa, Rimin-Gado da sauransu.
Duk wannan ma kaɗan ne idan aka yi la’akari da rashin ingancin aiyukan domin wasu ma sun fara lalacewa tun kafin a fara amfani da su. A taƙaice dai gwamnatin ta yi asarar sama da naira biliyan 50 akan wannan aiki, ba tare da an samu sakamakon da ya kamata ba.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.



No comments:

Post a Comment