20
ga Janairu, 2014
Daga:
Amir Abdulazeez
L
|
okaci ya yi da ya kamata mu tambayi gwamnonin Najeriya a kan dalilin da ya
sa ba sa so mataimakansu su gaje su. Ko kuma su mataimakan gwamnonin, mu
tambaye su laifukan da su ka yi wa iyayen gidan nasu da har tsananinsu ya kai su
ke ƙyamar su gaji kujerunsu.
Tun da aka kafa jamhuriya ta huɗu, bayan da mulkin dimokraɗiyya ya dawo a
shekarar 1999 har zuwa yanzu, mataimakin gwamna ɗaya ne tak ya taɓa gadar
kujerar gwamnansa kai tsaye tare da goyon bayan mai gidan nasa, wannan kuwa shi
ne tsohon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon gwamnan Jihar, Alhaji
Mahmuda Aliyu Shinkafi wanda ya karɓi mulki a hannun Sanata Ahmad Sani Yariman
Bakura.
Akwai
tsirarun mataimakan gwamnonin da su ka gaji gwamnonin nasu amma a cikin yanayi
na rikicin siyasa ko baram-baram ko kuma a dalilin wani tsautsayi da ya ratsa.
Misali, Goodluck Jonathan ya gaji Diepreye Alamasiegha a matsayin gwamna bayan
da Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa ta
tsige gwamnan kan zargin cin hanci da rashawa, Mukhtar Ramalan Yero na Kaduna
ya zama gwamna bayan da Sir Patrick Yakowa ya rasa ransa a hatsarin jirgin
sama, Adebayo Alo Akala na Jihar Oyo ya zama gwamna na ɗan wani lokaci bayan
da Majalisar Dokokin jihar ta tsige Gwamna
Rashidi Ladoja kafin daga baya kotu ta dawo da shi kan kujerarsa, Michael Botmang
na Jihar Plateau wanda ya rasu kwanannan, ya zama gwamna na ɗan wani taƙaitaccen
lokaci bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta tsige Gwamna Joshua Dariye kafin
daga bisani kotu ta dawo da shi kan kujerarsa, Uwargida Virgin Etiaba ita ma ta
zama gwamna bayan Majalisar Dokokin Jihar Anambra ta tsige Mr. Peter Obi kafin
kotu ta rushe wannan tsigewa, Aliyu
Wammako ya zama gwamnan Sokoto sakamakon baram-baram ɗin da su ka yi da
maigidansa Bafarawa inda ta kai shi ga komawa PDP shi kuma Bafarawan ya na
sabuwar jam’iyyar da ya kafa ta DPP, Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe ya zama
gwamna bayan da Gwamna Mamman Ali ya yi mutuwar ba-zato-ba-tsammani. Babu wasu
alamu da su ka nuna cewa waɗannan mutane za su samu sahalewar iyayen gidansu
wajen zama gwamnoni kafin waɗancan dalilai. Yanzu haka a Jihar Taraba, ba a son
ran Gwamna Suntai da mutanensa, Mataimakin Gwamna Garba Umar ya ke riƙe da
ragamar Jihar ba, duk kuwa da cewa shi Suntai ɗin ya na can rai a hannun Allah.
Bayan
wannan, mun ga irin yadda wasu gwamnoni su ka dinga zaman doya da manja da
mataimakansu, a wasu lokutan, kawai saboda mataimakan sun nuna sha’awar su gaje
su. Akwai Jihar da aka ce gwamnan ya hana mataimakinsa ko da takarar sanatan da
ya nema ba ganin cewa ba za a ba shi takarar gwamna ba, bisa dailin cewa wai
bai kamata a ce shi ya na sanata kuma mataimakinsa ma ya na sanata ba. Ƙiri-ƙiri ya ɗauko
wani can ya ba
shi takarar. Wani lokacin ma gwamnonin su kan tilasta wa mataimakan nasu
barin kujerunsu a kan wannan dalili ko kuma a kan wani dalili daban kamar yadda
mu ka gani kwanannan a Jihar Imo tsakanin Rochas Okorocha da mataimakinsa. Irin
haka ta faru a Jihar Jigawa a lokacin Saminu Turaki wanda a shekara takwas, ya
yi mulki da mataimaka kusan uku da kuma a Jihar Bauchi tsakanin Mallam Isa
Yuguda da Garba Gadi. A wasu jihohin irin su Kano, mun ga yadda Mallam Shekarau
ya ƙare zangunan mulkinsa cikin yanayain rashin jituwa da mataimakansa guda
biyu.
Wani lokacin
yanayin ya kan nuna tamkar laifin na mataimakan gwamnonin ne, to amma mun ga
yadda wasu mataimakan su ka dinga biyayya sau da ƙafa har tsawon shekaru takwas
ga ma su gidan nasu, wani lokacin wannan biyayya ba irin baƙin jinin da ba ta
janyo mu su, amma sai biyayyar ta tashi a banza. Maimakon gwamnonin su bai wa
mataimakan nasu damar su gaje su, sai ka ga sun ɗauko kwamishina, sakataren
gwamnati ko shugaban jam’iyya su saka a gaba. A wasu lokutan ma sai su ɗauko
wani can daban su kawo. Misali a nan, Marigayi Yakowa ya na nan zaune, amma Ahmed
Makarfi na Kaduna ya ɗauki tsohon kwamishina Namadi Sambo ya ba shi takarar
gwamna kuma aka sa Yakowan ya bi shi a matsayin mataimaki, Abdullahi Gwarzo na Kano
na nan kuma ya na nema amma Shekarau ya ɗauko kwamishina Salihu Takai ya ba shi
takara, Gwamna Abdulfatah Ahmed na Jihar Kwara tsohon kwamishinan Bukola Saraki
ne, Gwamna Shettima na Jihar Borno tsohon kwamishinan Ali Modu Sheriff ne,
Gabriel Suswam na Jihar Benue tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya ne kuma
ya samu goyon bayan Gwamna George Akume, Gwamna Babangida Aliyu na Jihar Niger
tsohon Babban Sakatare ne a Ma’aikatar Birnin Tarayya Abuja, Gwamna Liyel Imoke
na Jihar Cross-Rivers tsohon sanata ne kuma ya samu goyon bayan Gwamna Donald Duke.
Misalan su na nan birjik, amma ba za ka ji tsohon mataimakin gwamna ba. Da alama
dai kwamishinoni sun ma fi ƙima a idon gwamnonin fiye da mataimakan nasu.
Sashe na 187
na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya bayyana mataimakin gwamna a
matsayin wanda kujerar gwamna ba ta samuwa da kuma tafiyuwa sai da shi. Hakan
na nuna cewar a tsarin aiki, babu wani makusancin gwamnan kuma abin amincewarsa
kamar mataimakinsa. Haka zalika, bayan gwamnan, babu wanda ya san sirrin
gwamnatin kamar mataimakinsa. To, amma, me ya sa gwamnoni ba sa
son ba su dama? Wani ma ya na karɓar kujerar mataimakin ne tun farko bisa
tunanin cewa idan zangonsu ya ƙare, mai gidansa zai ba shi dama, amma ina. A
tunaninmu irin na talakawa, mun ɗauka wanda ku ka yi aiki tare kafaɗa da kafaɗa
na tsawon shekaru huɗu ko takwas, ai ba wanda zai ɗora a inda ka tsaya kamar
sa.
To wai, ko
shin mataimakan ne ba su da farin jinin cin zaɓe, shi ya sa gwamnonin su ke ƙin
tsayar da su? Ko kuwa dama wani dalili ne irin na siyasa ya tilasta wa
gwamnonin ɗaukar mataimakan nasu tun farko amma ba su ne zaɓin su ba? shin
gwamnoni su na tunanin mataimakan nasu za su ci amanar su bayan sun gaje su? Shin biyayya da mu ke gani a fili mataimakan na
yi wa gwamnoninsu, a fili ta ke kawai, amma a ɓoye abin ba haka ya ke ba. Shin
gwamnonin, mugunta da baƙin ciki su ke yi wa mataimakan nasu don kar su taka
irin matasyinsu ko kuwa su na tsoron ba za su iya juya su ba ne bayan sun gaje
su?
Ni dai, ba
zan iya bayar da waɗannan amsoshi ba, wataƙila sai su gwamnonin da mataimakan
nasu, amma na taɓa ji daga majiya mai tushe, lokacin da wani mataimakin gwamna
ya ke miƙa mulki a ofishinsa ga wani sabon mataimakin gwamnan a wata jiha, sai
ya ke ce ma sa: ‘ɗan uwana, babu aiki mai wahalar riƙewa a siyasance irin na
mataimakin gwamna. Domin kuwa, idan gwamna ya yi bajinta sai jama’a su yabe shi
shi kaɗai, amma idan ya yi kuskure, sai a zageku tare’.
Hasashen da
manazarta siyasar ƙasar nan su ke yi shi ne, a wannan karo ma gwamnoni da dama
ba za su bai wa mataimakansu damar su gaje su ba a zaɓen 2015. A wsu jihohin ma
hakan ta fito fili ko kuma gwamnonin sun bayyana wa mataimakan nasu a baki ko a
aikace cewar ba za su gaje su ba. Wannan abu dai ya na da ɗaure kai musamman
idan aka yi la’akari da abin da ya ke faruwa a siyasun wasu ƙasashe. Mislali,
tun a farkon mulkin Marigayi Nelson Mandela, ya fara assasawa a aikace cewa
mataimakinsa Thabo Mbeki shi zai gaje shi, kuma shi ya gaje shi ɗin. A ƙasar Amurka,
duk da cewa su ma mataimakan ba su fiya gadar masu gidan nasu ba, amma George Bush
(babban) ya gaji shugaba Ronald Reagan bayan da ya yi masa mataimaki na tsawon
shekaru takwas kuma tare da goyon bayan mai gidan nasa. Shugba Bill Clinton ya
goya wa mataimakinsa Al-Gore baya inda har ya samu takara a jam’iyyarsu, duk da
cewa bai lashe zaɓen ba a shekarar 2000. To amma mu a nan Najeriya, ba haka abin ya ke ba. Wasu
gwamnonin ma da gangan su ke ɗaukar rarraunan mataimaki, a wasu lokutan ma
tsoho ko rago wanda ba ma zai yi sha’awar ya gaje su ba.
Yanzu dai
mun zuba ido a shekarar 2015 mu ga ko za ta canza zani duk da cewa babu alamun
hakan. Idan har ba ta canza zani ba, to duk mai sha’awar zama gwamna a
rayuwarsa, a yanzu ko a gaba, ya yi tunani mai zurfi kafin ya karɓi kujerar
mataimakin gwamna idan an yi masa tayi tun da dai ƙarfin gwamnonin Najeriya a
siyasance, idan ya na yawa, har ya yi yawa, su kuma ba su yarda mataimakinsu ya
gaje su ba.
© Malam Amir Abdulazeez 2014.
No comments:
Post a Comment