Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Tsakanin Fitar da Zakka da Rashin Fitar da Ita

17 Ga Nuwamba, 2013.

Daga: Amir Abdulazeez

S
au tari sai ka ga mun samu kan mu a wani mawuyacin hali wanda babu abin da ya jefa mu a cikinsa face aiyyukanmu. Abin takaicin shine, muna yin wasu abubuwan da mun san sakamakonsu sarai amma kuma idan sakamakon ya same mu sai mu koma gefe muna takaici da mamaki kamar dama can bamu san cewa wannan abin da ya same mu shine sakamakon aiyyukanmu ba. Kamar mutum ne ya bulbule gidansa da fetur kuma ya ƙyasta ashana da hannunsa, sai bayan gidan ya ƙone kuma sai ya koma gefe yana mamaki kamar dama bai san hakan za ta faru ba. Wannan shi ne kwatankwacin wanda ya ƙi bayar da zakka kuma ya dinga mamakin me yasa jama’a suke masa hassada ko baƙin ciki akan dukiyarsa. Haka zalika, wanda ya ƙi bayar da zakka, kada ya yi mamaki don talauci ya yi yawa a gari  wanda har tsananin talaucin ya kai ga wasu sun shiga sana’ar sata kuma a wayi gari ɓarayi sun hauro gidansa sun masa sata.

A matsayin zakka na ɗaya daga cikin manyan turakun Musulunci guda biyar, ya kamata a ce wani hamshaƙin malami ne zai yi rubutu a kan ta amma idan aka duba yadda aka yi watsi da ita da kuma yadda a ke wulaƙanta ta duk da irin tasirinta a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, to sai mu ga cewa haƙƙi ne akan kowa ma ya yi tsokaci dai-dai gwargwado a kan ta har da ma ɗalibai iri na.
Idan muka kalli turakun Musulunci guda biyar, za mu ga cewa zakka ta sha bamban da ragowar turakun guda huɗu waɗanda suka haɗa da Kalmar Shahada, Tsaida SAllah, Azumi da Aikin Hajji. Ba don komai ba sai don cewa, ita zakka bayan kasancewarta ibada, akwai kuma wani gagarumin tasirin da take  da shi a fannin tattalin arziki, zamantakewa, tsaro, kai har ma da siyasa. Wataƙila wasu su yi mamakin menene alaƙar zakka da siyasa?

Idan muka kalli siyasar duniya, za mu ga cewa ɗaya daga cikin abin da yake ƙarawa ƙasashe ƙarfin faɗa a ji a duniya shi ne kyauta da taimako. Za mu ga cewa ƙasashen Kiristoci da Maguzanci masu ƙarfin tattalin arziƙi irinsu Amurka da China sun daɗa faɗaɗa ƙarfinsu ta hanyar ɗibar dukiyar da Allah Ya basu suna taimakawa ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi. Duk da cewa ba za mu kira abin da suke yi a matsayin zakka ba kuma ba suna yi ne don Allah ba, amma mu duba irin yadda wannan alheri nasu yake ƙara musu ƙarfi a siyasance. Inda a ce wadatattun ƙasashen Musulmi  masu arziƙi suna fitar da zakka  su kaita ƙasashen Musulmi da ake buƙatarta, ya za’a ga ƙarfin faɗa a jinsu a siyasance?

Ko da a ce babu malami a kusa wanda zai jawo mana ayoyi ko hadisai akan muhimmancin zakka, ya kamata mu yi tunani mai zurfi don gano hikimar da ta sa Allah SWT Ya wajabta ta. Domin sanin kowa ne cewar Allah ba Ya yin abu face sai da hikima a cikinsa, sai dai rashin ilimi, bincike, zurfin tunani ko kuma gazawa irin ta Ɗan Adam ta sa ya kasa gano hikimar. Misali, dukkan duniya an taru akan cewa dukiya ni’ima ce babba, wasu ma suna ganin ita ce mafi girman ni’ima domin tana iya kawo maka sauran ni’imomin. Ita kuma ba kowa Allah Ya ke ba wa  ita ba sai ‘yan tsiraru. Za ku yarda da ni idan nace masu kuɗin duniya ba su kai kashi uku cikin ɗari ba. Kuma me yiwuwa ku yarda da cewa yawan waɗanda suka mallaki naira miliyan ɗaya tasu ta kansu a Najeriya, ba su wuce kashi ɗaya cikin ɗari ba.
Kasancewar Allah Ya san cewa ba kowa ya ba wa dukiya ba, sai ya ɓullo da zakka domin dukiyar duniya ta dinga zagayawa a tsakanin kowa tunda ba zai yi ma’ana a ce an halicci kowa mai kuɗi ba domin rayuwar ma ba za ta yiwu a haka ba.

Ita dai zakka ba cewa aka yi kowa sai ya fitar da ita ba, a’a sai wanda dukiyarsa ta kai nisabi, idan kuma dukiyar ta kai nisabi to sai ƙarshen shekara kuma kashi ɗaya bisa 40 kacal za’a fitar. Da kai da dukiyarka fa duk mallakar Allah ne, ajiya kawai Ya baka, idan kuma ya ga dama gobe sai ya karɓe ajiyar ya baiwa wani. Haba jama’a!! Ina laifi a cikin abin da aka baka ajiya ba don ka fi kowa dabara ba kuma aka ce a sau ɗaya a kowacce shekara ka fitar da kashi ɗaya bisa 40. Kuma Wanda Ya baka ajiyarnan, ba shi za ka bai wa ba, a’a ɗan uwanka Ɗan Adam mai ƙaramin ƙarfi za ka ba wa.
Amma abin takaici yanzu, a al’ummarmu ta Hausawa ba’a mayar da zakka a bakin komai ba. Wasu ko fitar da ita ma ba sa yi, waɗanda kuma suke daurewa su fitar da ita sai ka ga  suna fitar da ita a wulaƙance, sai su tara mutane suna raba musu N100 ko N500 wai sun fitar da zakka.

Marigayi Sheikh Ja’afar Adam ya taɓa cewa zai yi wahala ka ga maikuɗi ya zo wajen malami neman fatawa akan zakka, sai dai ya zo neman fatawa akan neman aure, kasuwanci, siyasa ko wani abin daban. Yace sai ‘yan ƙalilan ne suke zuwa neman bayani akan yadda za su fitar da zakka.
Wani abin da ya kamata mu kiyaye shi ne, akwai manoma, da makiyaya waɗanda su ma suke watsi da al’amarin zakka musamman a ƙauyukanmu. To lallai ya kamata mu shiga taitayinmu. Wataƙila wannan ce ta sa noman namu na wannan zamanin ma ba ya yin wata albarkar kirki saboda ba ma fitar masa da zakka.

Zakkar nan idan mun fitar, amfanin kanmu yake dawowa, idan kuma mun ƙi fitarwa, masifar a kanmu take ƙarewa. Ita dai zakka idan ka fitar da ita, bayan cewa ka bi umarnin Allah, zai baka lada kuma zai ruɓanya maka dukiyarka, Ya yi mata albarka kuma ya ajiye maka sakamakonka a lahira, akwai amfaninta a nan duniya waɗanda ba za su ƙirgu ba. Ga kaɗan daga cikinsu.

1.      Kakkaɓe talauci: Bankin Duniya wato World Bank da ke ƙasar Switzerland yace sama da kashi 60 bisa 100 na ‘yan Najeriya suna rayuwa a ƙasa da Dalar Amurka ɗaya, kwatankwacin N160 a kullum saboda talauci kuma mafi yawancinsu a Arewacin Najeriya suke (inda Musulunci shi ne addini mafi ƙarfi a yankin). Duk wanda ya mallaki naira miliyan 40 kuma ya fitar da miliyan 1 zakka ya bai wa mutum biyu masu hankali misali. InshaAllahu baɗi su ma sai sun fitar da zakka. Idan aka cigaba a haka, to za’a wayi gari, gari guda sun zama mawadata ko masu rufin asiri, sai dai wata shekarar a ɗebi zakkar wannan garin a kai wani garin da suke da buƙata. Da muna haka a Arewacin Najeriya, da talauci zai dame mu?

2.      Maganin Hassada: Dukiya tana daga cikin abin da ake yi wa mutum hassada a kan ta. Idan kana ɗiban dukiyarka, kana bayar da zakka, za ka samu ƙarancin masu yi maka hassada da ƙiyayya domin dama wani rashin ba ka ba shi ba ne ya sa yake maka hassada.

3.      Maganin Masifa: na taɓa jin Mallam Aminu Ibrahim Daurawa yana cewa, lokacin da suka kai wa waɗanda gobarar ta rutsa da su a Kasuwar Kantin Kwari ziyara a shekarun baya, yace bayan sun jajanta musu kuma sun ba su shawarar su dinga fitar da zakka domin wannan ibtila’in ya yi kama da jarrabawa dalilin rashin fitar da zakka. Dama kuma ita zakka idan ka ƙi fitar da ita, to za ta fitar da kanta ta hanyar da ba ka so kuma ga shi babu lada, gara ma ka fitar da kanka ka samu lada. A wannan gobara ni kaina na san mutum ɗaya da naira miliyan 20 ɗinsa ta ƙone ƙurmus a cikin shago banda ɗumbin kayayyaki.

4.      Tsaro: Ɗaya daga abin da yake kawo rashin tsaro shi ne talauci. Ita kuwa zakka tana rage talauci. Don haka ɓarayi da ‘yan fashi waɗanda suke taka muhimmiyar rawa wajen haddasa rashin tsaro za su yi sauƙi.

A ƙarshe, idan da ace yadda mu ke tururuwar yin salloli biyar a masallatai, yadda muke tururuwar yin azumi lokacin Ramadan, yadda muke takarar zuwa aikin hajji, a ce haka muke takarar bada zakka, da munga canji a cikin al’amuranmu. Kuma ko da ma zakka ba ta da wani amfani a nan duniya, shin ba za mu bi umarnin Allah, mu fitar da ita ba?
Da fatan za mu nemi malamai su yi mana cikakken bayani akan yadda za mu fitar da zakka, lokacin da za mu fitar da ita da kuma waɗanda za mu baiwa ita.

© Malam Amir Abdulazeez 2013.

No comments:

Post a Comment