28 ga Mayu, 2014
Daga: Amir Abdulazeez
T
|
un a zamanin NEPU da PRP,
duniya ta ke yi wa Jihar Kano kallon madubin siyasar Arewacin Najeriya. Wannan
ya biyo bayan aiki tuƙuru da gwarazan ‘yan kishin ƙasa irinsu Mallam Aminu Kano
suka yi wajen nema wa Jihar Kano irin wannan matsayi. Domin kuwa irin
nagartaccen samfurin siyasar da su Marigayi Aminu Kano, Muhammad Abubakar Rimi,
Dan Masanin Kano da sauran irinsu suka gudanar a wancan lokaci, ya taka muhimmiyar
rawa wajen ɗaga darajar siyasar Kanon musamman a Arewacin Najeriya.
A wancan lokaci, Jihar Kano ta
yi fice wajen zaɓen mutum ko jam’iyyar da ta ke so a kowanne irin mataki ba
tare da tsoro, kwaɗayi ko maguɗi ba.
A shekarar 1979, Jihar Kano ta zaɓi
jam’iyyar PRP duk kuwa da cewa NPN ita a ke yayi a Najeriya kuma ita ce jam’iyyar
da ta fi kowacce ƙarfi. A shekarar 1983, an juya wa Muhammad Abubakar Rimi baya
duk da cewa shi ne ya ke da mulki kuma a ka zaɓi Sabo Bakin-Zuwo duk da cewar
bai fi Rimin farin jini a karan kansa ko
kuma sanin siyasa ba. A waɗannan lokuta,
duk ƙarfin mulkin ka, ba ka isa ka tilastawa mutane su yi irin siyasar da ka ke
so ba, ko kuma ka murɗe mu su zaɓe ba. Ire-iren waɗannan abubuwa su suka sanya
a ke sha’awar siyasar Kano a ko’ina a Arewa kuma ya sanya ta shahara a fadin Najeriya.
A shekarar 2003, siyasar Jihar Kano ta cigaba da kafa tarihi inda ta samu ƙarin matsayi daga madubin Arewacin Najeriya zuwa madubin siyasar Najeriya baki ɗaya. Wannan ya biyo bayan zaɓen Mallam Ibrahim Shekarau da kuma faɗuwar Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. A lokacin, an yi ikirarin cewar Shekarau ya ci zaɓe alhalin ba shi da ajiyayyar
Tun daga wannan lokaci, duk
inda ka je sai ka ji ana cewa ai ba ka isa ka yi maguɗi ko ƙarfa-ƙarfa a Jihar
Kano ba, saboda yanayin siyasar jihar ya fi ƙarfin a yi mata irin cin kashin da
a ke yi a sauran jihohi.
Duk waɗannan abubuwa da na ke
zayyanowa a yanzu sun zama tarihi, domin kuwa yanzu siyasar Kano ta lalace kuma
ta dawo gama-gari irin ta ko’ina a Najeriya. Kai a taƙaice ma idan aka ci gaba a
haka, to jihohi irin su Oyo, Edo, Imo, Nassarawa da Zamfara za su iya shan
gaban Kano ta fuskar inganticciyar siyasa ta ra’ayi da ‘yanci.
Wannan lalacewar da siyasar Kano
ta yi ba komai ba ne face laifin tsohon Gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau da
kuma Gwamna mai ci yanzu, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ko da yak e mu kanmu
mabiya mun bayar da tamu gudunmawar. Mutane da dama su na da ra’ayin cewar, a
tarihin Kano, ba a taɓa samun mutanen da suka ci moriyar siyasar jihar irin waɗannan
mutane guda biyu ba, amma yau ga shi su ne suka fi kowa lalata ta da yi mata
mummunar illa.
Kwankwaso da shekrau su ne suka
share wa maguɗin zaɓe wajen zama a Kano kuma su ne suka assasa al’adar sanya
jam’iyya da shugabanninta a cikin aljihu.
Ba wai ina nufin waɗannan
mutane babu wata gudunmawa da suka kawo ga ci gaban Kano ba. A’a, kowannensu ya
yi mulki kuma ya bar tarihi mai kyau dai-dai iyawarsa ta hanyar yin abubuwa
nagartattu da suka shafi
rayuwar jama’a. To
amma sun yi amfani da mulkinsu wajen gina rundunar siyasarsu da tara magoya
baya. Sannan kuma sun yi amfani da damar su wajen yin abin da zai ciyar da
siyasar su da ta jam’iyyar su gaba
kawai, amma sun lalata tsari da ginshiƙin siyasar Kano kuma da
alama hakan bai dame su
ba. Aiyyukansu sun nuna cewar bas u damu ba dan tarihin siyasar Kano ya
lalace in dai ta su siyasar za ta ci gaba da haɓɓaka. A taƙaice
dai, sun lalata tsarin da su suka fi kowa cin moriyarsa a Kano.
Lokacin da Kwankwaso ya zama gwamna a shekarar 1999, babu wani abu na nagarta da alfarma a zahiri wanda Dakta Abdullahi Umar Ganduje bai fi shi ba. Amma saboda tsaftar siyasar Kano a wancan lokaci, ba a murɗe masa zaɓen fidda gwani na PDP an baiwa Gandujen ba. Amma lokacin da jagorancin PDP ya dawo hannun Kwankwaso, a shekarar 2007, shi kaɗai ya yi fatali da nagartattun ‘yan takara kusan guda bakwai waɗanda suka shiga zaɓe tare da shi, ya ɗauki takara ya bai wa Ahmad Garba Bichi.
Idan muka waiwayi Shekarau, a
shekarar 2003, tsaftar siyasar Kano na wancan lokaci ta sa aka yarda cewar
Ibrahim Little ya karya doka ta hanyar tsayawa takara ba tare da ya ajiye muƙaminsa
na shugaban jam’iyya ba, kuma ba a kalli kuɗinsa, yawan jama’arsa ko ɗaurin
gindin sa ba, aka karɓe takara aka ba shi duk da cewar ba shi da kuɗi ko wani
ubangida a siyasance kuma ana ganin ma ba zai iya takarar ba. Amma a shekarar
2011, lokacin da jagorancin jam’iyyar ANPP ya ke hannun Shekarau, sai ya
jingine matsayinsa na jagora, ya tsaya kai da fata sai an zaɓi abokinsa Mallam Salihu
Sagir Takai, kuma ya dage a kan haka inda ya yi amfani da dukkan damar da ta ke
hannunsa wajen cimma burinsa duk kuwa da cewar mafi yawan ‘yan jam’iyyarsa ta
ANPP ba su yarda da zaɓin nasa ba.
Sakamakon waɗannan abubuwa da Kwankwaso
da Shekarau suka yi a baya, yau an wayi gari saboda lalacewar siyasa a Kano,
kowa tsoron tsayawa takarar gwamna a ƙashin kansa ya ke yi domin in dai ba gwamna
ko jagoran jam’iyya mai ci ne ya tsayar da shi ba to wai ɓata lokacinsa ya ke
yi. Kuma komai nagartarka, ba za a taɓa samar da yanayin da zaka iya wata
takarar kirki da ɗan lelen gwamna ba.
Idan muka dawo ɓangaren zaɓe, Jihar
Kano ba ta san mummunan maguɗin zaɓe da danniya ba sai a kan Shekarau da Kwankwaso. Duk da cewa a
lokacin SDP da NRC, mutane da yawa na da ra’ayin cewar an yi murɗiya a zaɓen
gwamna tsakanin Injiniya Magaji Abdullahi da Gwamna Kabiru Gaya; to amma wannan
ma wasan yara ne a kan abin da muke gani a yanzu.
Na farko dai, mafi yawan zaɓen
cike gurbi da aka yi a ƙarƙashin mulkinsu ba su da inganci. Tun daga zaɓen cike
gurbin ɗan majalisar Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa a
shekarar 2006, har zuwa zaɓen cike gurbi na ‘yan majalisun Kano ma su wakiltar
Gaya da Garko da aka yi a shekarar 2013; akwai rashin inganci a cikinsu.
A shekarar 2007 ne, gwamnatin
Mallam Shekarau ta shirya zaɓen ƙananan hukumomi mafi muni a tarihin siyasar Kano
inda ƙiri-ƙiri a ka dinga musanya sunayen waɗanda aka sanar sun ci zaɓe a filin
zaɓe da sunan abokan takararsu a can wani wajen daban ko a wani lokacin daban,
wannan zaɓe ya yi muni ƙwarai da gaske kuma mu a wannan lokacin mun ɗauke shi a
matsayin tsautsayi da ƙaddara wacce muke fatan ba za ta ƙara faruwa a Kano ba.
Sai ga shi ƙasa da sati biyu da suka gabata, gwamnatin Kwankwaso ta shirya wani
zaɓen mummuna irinsa wai da sunan ta rama abin da Shekarau ya yi mata. A wannan
almara mai kama da zaɓe, an ayyana cewar jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun
kansiloli 484 da ciyamomi 44 a Kano. To yanzu, menene abin birgewa a nan a ce
babu adawa ko ɗaya kuma bayan kowa ya san hakan ba
zai yiwu ba a Kano?
Da alama dai an saka talakawan Kano
a tsakiya
ana wasan ƙwallon ƙafa da su. Wannan ya sa su su shiga rana su hau layi don zaɓar
ra’ayinsu, sai kuma a faɗi sakamakon da aka ga dama, sannan wancan ma ya aikata
irin hakan wai sannan ya ce ai ramawa ya yi. Talakawan Kano su ne abin ya ke ƙarewa
a kansu kuma abin takaici wai shugabanninsu su ke mu su haka.
A lokutan mulkin Shekarau da Kwankwaso,
babu wanda ya ke da ikon ya zama shugaban jam’iyyar da suke ciki sai wanda suke
so kuma shugabannin jam’iyya ba su da wani ‘yancin kansu sai dai ra’ayin
gwamnati domin ta mayar da su jami’anta. Idan mutum ya na takara da gwamna ko ɗan
lelen gwamna, shugabanni ba za su zama alƙalai ma su adalci ba, ƙarara za su
nuna maka kai ba ma ɗan jam’iyyar ba ne
ko kuma ka ma yi laifi da ka tsaya takara da gwamna. Mu a da sai dai
mu ji labarin irin wannan abin
takaicin a wasu
jihohin amma ba dai a
Kano ba.
A dalilin haka, yau mun wayi
gari, gwamnoni su suke nada shugabannin
jam’iyya kuma ba su da wani amfani. Da ka nemi shawararsu ma, gara ka tunkari
gwamnan mai mulki kai tsaye domin aikinsa kawai su ke yi ba na jam’iyya ba. Ya
kamata waɗannan jagorori su koyi darasin da tarihin siyasarsu ya koya mu su. Su
tuna cewar sun samu dama kuma sun rasa ta.
A gaskiya duk da cewa Injiniya
Kwankwaso da Mallam Shekarau sun bai wa Kano gudunmawa a gwamnatance amma kuma
sun kawo tarnaƙi ga tsarin da ta hanyar sa ne kawai za a iya samun wasu irinsu su ɓullo su ma su bayar
da tasu irin gudunmawar. Yadda tsarin siyasa ya fito da su aka sansu, jama’ar Kano
suka karɓe su kuma har suka samu dama, to su ma su ƙyale adalci
ya tabbata a tsarin domin kowa ya samu dama ba tare da
tsangwama ba. Har yanzu akwai dama a hannunsu domin su ne suke haska fitilar
siyasar Kano har gobe. Idan suka bari wannan dama ta suɓuce daga hannunsu cikin
wannan yanayi ba tare da sun gyara ba, to tarihi ba zai taɓa yafe mu su ba
domin kuwa ba za a dinga tunawa da su irin tunawar da ake yi wa Mallam Aminu Kano
ba. Mallam Aminu Kano ya samu babbar damar sa ne wajen yin jagoranci, Shekarau
da Kwankwaso sun samu damar yin mulki a gwamnatance da kuma jagoranci a
siyasance baki ɗaya.
© Malam Amir Abdulazeez 2014.
No comments:
Post a Comment