Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Ta Yaya Za a Gyara Ilimi A Najeriya?

16 Ga Yuni, 2015.


Daga: Amir Abdulazeez

A
n jima ana tattaunawa tare da yin yunƙuri a kan batun farfaɗo tare da inganta ilimi a Najeriya, amma kusan babu wani abu bayyananne a ƙasa wanda ya ke nuna cewar an samu nasara ko kuma ana kan hanyar samun nasarar. Wataƙila wani ya tambaya, me ya sa za a farfaɗo da ilimi; shin a wane hali ya ke? Duk abin da ake zancen farfaɗo da shi, to ana  nufin a wani lokaci can a baya, ya na da ƙarfinsa da kuma kuzarinsa, amma a yanzu ya yi rauni. Haƙiƙa shekaru  kamar 30 zuwa sama baya, ilimin boko a Najeriya ya na da inganci ƙwarai da gaske; duk fannin da aka ce mutum ya karanta, to ba a wata tantama akan ƙwarewarsa a wannan fannin ko da kuwa shi ya fi kowa rashin mai da hankali a ajinsu. Wanda yak e da cikakkiyar shaidar gama makarantar sakandiri, ya fi mai karatun digiri a yanzu ilimi. Babu wanda ya ke tsoron tura ‘ya’yansa makarantar gwamnati domin ya na da tabbacin cewar zai samu ingantaccen ilimi. Amma a yanzu in dai ilimi mai inganci a ke so, sai dai makarantar kuɗi.

Idan muka duba tarihin shugabanni da manya-manyan masu faɗa-a-ji na ƙasarnan, sai mu ga cewar makarantar gwamnati ya yi kuma dukkan wani ilimi da wata ƙwarewa da ya ke taƙama da ita, to wancan ilimi shi ne tushensa. Abin da ya ke faruwa a wannan zamanin shi ne, ilimin ya na ƙara yawaita, amma ingancinsa ya na ƙara lalacewa. A wancan lokacin, ilimin ya na da ƙarancin yawa sakamakon rashin yawan jama’a da kuma rashin rungumarsa da al’umma ba su yi ba sosai, don haka ilimin boko sai wane da wane, to amma kuma ya na da matukar inganci.

Mafi yawancin makarantun kudi ba su haura shekarau 30 zuwa 35 da kafuwa ba, ma’ana an kafasu daga shekarar 1975 zuwa sama. Ko a wancan lokaci, ba wai an yi su ba ne saboda rashin ingancin ilimi a makrantun gwamnati, a’a ; an yi su ne saboda neman kuɗi da kuma ƙarancin makarantun su kansu. Yanzu kuwa, kusan babu inda  ake samun ilimi mai inganci sai a makarantun kuɗi masu zaman kansu. Makarantar gwamnati ta zama larura, babu wanda yak e son ta sai dole, ba don komai sai don cewar ba a bayar da wani ilimin kirki a cikinsu. A kan samu yara sun gama firamare amma ba za su iya rubuta ko da sunansu ba, haka za su tafi sakandire su gama, ba su san komai ba.

Muhimmancin ilimi ga rayuwar Ɗan Adam abu ne kusan da ba zai iya misaltuwa ko kwatantuwa ba. A dukkan abin da mutum zai yi dole sai ilimi ya shigo ciki; tun daga kan zaman rayuwar shi kansa, addini, sana’a har izuwa mu’amala da zamantakewa. Wannan ta sa dole ne a tsaya a gyara shi kuma a inganta shi domin samun kyakkyawar makoma.

Matsalar da aka sha fama da ita a baya shine gudun ilimi da ake yi musamman a Arewacin Najeriya, to amma yanzu wannan matsalar ta kau domin mafi  yawan mutane a yanzu sun koma makaranta kuma ba sa wasa wajen saka ‘ya’yansu a makaranta. Dawowar mulkin siyasa a shekarar 1999 ta bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen wannan. Mutane kusan kowa ba ya son a bar shi a baya kuma ya na so a dama da shi ko dai a cikin siyasa ko gwamnati ko a wani abu mai alaƙa da ita. Wannan ita ta sa yawan masu neman ilimi ya dinga ƙaruwa tun daga shekarar 2000 har zuwa yanzu a Najeriya. To amma ingancin ilimin kuma fa; baya ya ke ci ko gaba?

Idan muka ɗauki tsarin ilimi  a Najeriya tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, sai mu ga cewa akwai matsaloli masu tarin yawa da suka dabaibaye shi. Matsalolin sun haɗa da rashin ingantattun malamai, rashin kyautatwa ma’aikatan ilimin, rashin kishin ilimin, rashin kyawun guraren ɗaukar ilimin, rashin kayan aiki  tare kuma da rashin aiki da shi kansa ilimin. Kodayake gwamnatoci a matakin tarayya, jihohi da ƙananan  hukumomi sun taka rawar gani a shekraun baya musamman daga 1999 zuwa 2003 wajen ganin ta samar da kyakkyawan yanayin karatu ta hanyar gine-ginen da gyare-gyaren ajujuwa, to amma har yanzu hakan bai wadatar ba domin yawan mutanen da suke buƙatar karatun ya ninninka ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi wajen samar da shi da kuma inganta shi.

Duk ma ba waɗannan matsalolin da suke zayyane a sama ne babbar mishkila ba, babbar matsalar ita ce kullum ingancin ilimin baya ya ke yi kuma gwamnati ta kasa samo bakin zaren yadda za ta gyara al’amarin. Abin kuma ƙara dagulewa ya ke duba da cewa kullum mutanen Najeriya ƙara yawa suke yi, kuma masu buƙatar ilimin ƙara ninninkawa suke yi. Wani batun kuma shi ne abubuwa sun yi wa gwamnati yawa sosai kuma kullum kuɗaɗen shigar ta ko dai ƙara baya suke yi ko kuma darajar su ƙara faɗuwa ta ke yi saboda matsalar hauhawar farashi.

Duba da wannan, akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki hanya mai sauƙi kuma nagartacciya wajen ganin ta ceto ilimi a ƙasaranan. Masu iya magana na cewa: ‘in duka ya yi yawa, na ka ake karewa’. Ko da ba zai yiwu a bi dukkan matakan inganta ilimi a Najeriya ba, to ya kamata a bi wasu daga cikin hanyoyin. Hanyoyin kuwa sun haɗa da inganta harkar malanta da koyarwa, bai wa ilimin martaba da daraja shi, sannan da tabbatar da cewa ana aiki da ilimin.

Babban mataki da gwamnati za ta ɗauka, shi ne ta bai wa kula da malamai fifiko akan komai. Wajibi ne gwamnati ta tabbatar cewa sai malamin da ya ke da cikakken ilimi da ƙwarewa ne kaɗai zai koyar a dukkan matakai. Bayan haka ta tabbatar ta na ɗaukar nauyin malaman lokaci bayan lokaci domin ƙaro karatu da yin kwasa-kwasai waɗanda za su ƙara musu ƙwarewa da sanin makamar aiki. Ban da wannnan, ya zama lallai ta ɗauki isassun malaman ta yadda aiki ba zai dinga yi wa malami yawa ba. Wato ya kasance malami bai fi ya shiga aji sau biyu ko uku a rana ba domin samun sararin yin bincike-bincike da sauran abubuwa masu alaƙa da kula da ɗalibai da kuma inganta iliminsa, sannan kuma ya kasance malami ya na koyar da ɗalibai kamar 30 zuwa 40 a lokaci ɗaya ta yadda zai iya kula da su gabaɗaya kuma ya nazarci yanayin ganewarsu da fahimtarsu amma ba ya saka ɗalibai sama da 100 a gabansa ba. Bayan haka, a samar da kyakkyawan albashi da alawus-alawus ga malaman makaranta, idan da hali ma ya kasance su suka fi kowa kyawaun albashi a cikin ma’aikatan ƙasa. Wannan zai  sa a dinga alfahari da sana’ar koyarwa  a maimakon a ƙyamace ta. Bayan duka wannan kuma sai a samar da wani tsari na sanya ido a kan malamai tare da yin tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama ya na wasa da aikinsa. Idan a ka yi wa malamai haka, to ko ba a gyara ajujuwa ba, ilimi zai farfaɗo domin sai da malami za a samu makaranta amma makaranta ba za ta samu ba in ba malami. Saboda haka gara a gyara malami a ƙyale makaranta a maimakon a ƙyale malami a gyara makaranta. Mutanen da a baya wasu ma a ƙarƙashin bishiya suka dinga karatu, amma saboda akwai ingantattun malamai, sai suka sami ilimi mai inganci.

Wani abu da gwamnati ya kamata kuma ta kiyaye shi ne muhimmancin ilimi daga tushe. Ya kamata gwamnatoci su fi mayar da hankula kan ilimin firamare fiye da na sakandire da na jami’a. Alamu sun nuna kamar cewa gwamnati, musamman ta tarayya ta fi damuwa da jami’o’i, ta fi yin aikace-aikace tare da kula da malaman jami’a fiye da sauran. Kuskuren a nan shine, ana ɗora gini ne  akan fandisho mara kyau da inganci. Ilimin firamare shi ne fandisho. Maimakon kafa jami’o’i barkatai waɗanda su kan lashe maƙudan kuɗaɗe wajen kula da su, kamata ya yi a koma a inganta ilimin firamare, domin mafi yawa tun a can suke baro ilimin.

Wata muhimmiyar matsala da ilimi ya ke fuskanta a Najeriya, ita ce ɗaukar sa da aka yi a matsayin hanyar neman abinci kaɗai. Misali kusan kowa ya na yin ilimin boko ne saboda ya gama ya karɓi takardar shaida domin ya samu aiki. Wannan ita ta kawo koma baya da cikas akan ainihin ginshiƙi da manufar yin ilimin shi kansa. Asali dai ilimi ana yin sa ne domin a koyi yadda za a sarrafa rayuwar Ɗan Adam, to amma yayin da aka ƙasƙantar da shi ya koma hanyar neman sana’a kaɗai, to dole a bi dukkan hanyoyi marasa kyau da nagarta domin ganin an same shi tunda buƙatar kawai ita ce a kawo shaidar karatu domin a ɗauki mutum aiki. Wannan ta sa manufar ilimi ta asali ta samu mummunar tawaya.

Wani ƙarin naƙasu kuma shi ne, shi kansa ɗaukar aikin, ba a yin sa dai-dai da irin ilimin da mutum ya karanta. Alfarma ta yi yawa a cikinsa, misali mutum zai karanta ilimin tarihi, amma sai ya ɓige da aikin banki, ko ya karanci ilimin fasahar injiniyanci amma sai ya ƙarke da aiki a matasyin sakatare mai sarrafa takardu.  Idan da akwai wani tasri da zai dinga tabbatar da cewa kowa abin da ya karanta, shi zai aikata, to wataƙila kowa zai mayar da hankali sosai a makaranta wajen ganin ya ƙware akan fannin ilimin da ya ke karanta gudun ka da ya ji kunya a wajen sharar fagen ɗaukar aiki ko a wajen gudanar da aikin kansa.

Abu na ƙarshe da ya kamata mu kula da shi shi ne, mu guji ɗaukaka takardar shaidar samun ilimi fiye ma da ilimin shi kansa. Wannan kuskure ne ba ƙarami ba. A zamanin yanzu sai ka ga mutum ya na da ilimin, amma saboda ba shi da shaidar ilimin sai a ƙasƙantar da shi akan wanda ya ke da takardar shaidar ilimin amma ba shi da ilimin a kansa. Wannan ita ta sa ake ta rububin samun takardar shaidar ilimi a maimakon ilimin. Zai yi kyau a dinga gwada ilimin mutum a aikace fiye da akan takarda domin wannan za ta sa kowa ya shiga taitayinsa a makaranta wajen ganin ya tsaya ya samu ingantaccen ilimi.
Ya zama wajibi a kan mu, da mu da gwamnati, mu taru mu ceto ilimi daga durƙushewa a Najeriya.


© Malam Amir Abdulazeez 2015.

KANO 2015: Amfani da Rashin Amfanin Ganduje ko Takai a Mulkin Jihar

6 Ga Afrilu, 2015

Daga: Amir Abdulazeez

Idan dai ba wani ƙadaru na Ubangiji ba, Ranar Asabar mai zuwa, ɗaya daga cikin mutum biyu ne za a zaɓa a matsayin magajin Gwamnankwankwaso; wato Dakta Abdullahi Umar Ganduje ko Malam Salihu Sagir Takai.
To, amma kafin Ranar Asabar ɗin ta yi ‘yan Jihar Kano su yanke hukunci, ga wani hasashe a kan amfani da rashin amfanin zaɓar kowannensu;

Amfanin Zaɓar Ganduje
1. Idan aka zaɓi Ganduje a matsayin gwamnan Kano, to an zaɓi jam’iyyar APC sak tun daga tarayya har jiha. Mai yiwuwa wannan za ta bai wa Jihar Kano wata gagarumar damar amfanar aiyuka da alfarmomi masu yawa daga Gwamnatin Tarayya.
2. Gwamnati kamar wata mota ce kullum akan titi, take tafiya izuwa wani waje, idan an samu canjin direba, ana so ace ta ci gaba da tafiya akan wata kyakkyawar turba guda ɗaya har a cimma manufar ci gaban al’ummar da aka sa a gaba. Babu shakka Ganduje zai ci gaba da aiyukan Kwankwaso, wataƙila tamakar ma ba a samu wani canjin direba ba ma.
3. Ganduje dattijo ne wanda dukkan alamu na haƙuri da juriya suka bayyana a tattare da shi. A ko’ina an san dattijo da haɗa kan jama’a cikin hikima, dabara da nagarta, ina kuma ga idan an ba shi shugabancin su?
4. Ganduje ƙwararre ne kuma gogaggen ma’aikaci mai tarin ƙwarewa ta kusan shekaru 40 a kan ilimi, aikin gwamnati, siyasa, shugabanci da zamantakewa. In dai ƙwarewa dai-dai ta ke da aiki, to babu shakka, Ganduje zai kasance wanda ya fi kowa aiki a matasyin gwamna a Najeriya.

Matsalolin Zaɓar Ganduje
1. Idan aka zaɓi Ganduje, zai kasance jam’iyyar APC ta cinye komai aKano, babu sauran wata jam’iyyar adawa. Yanzu haka APC ita ta ke da Shugaban ƙasa, Sanatoci 3, ‘Yan majalisun tarayya 24 duka, Ciyamomi 44 da kansiloli 484 duka. Illa ce babba a ce babu adawa ko kaɗan; za a wayi gari jam’iyya mai mulki ta na yin abin da ta ga dama ba ta shayin komai kuma ba ta tsoron kowa.
2. Duk da nasarorin gwamnatin Kwankwaso, akwai wasu manyan kura-kurai da ta yi waɗanda bisa ga alama Ganduje zai iya ɗorawa a kansu. Babba daga cikinsu shi ne tauye ƙananan hukumomi, hanasu kuɗaɗensu da kuma mayar da su hoto.
3. Ganduje ya shafe kusan shekaru 20 (tun DPN 1996) ya na neman gwamna bai samu ba. A tsawon wannan lokaci, ya sadaukar da lokacinsa, ƙarfinsa, dukiyarsa, tunaninsa da sauran abubuwansa da yawa akan wannan buƙata. Babu tabbacin cewar idan ya samu nasara ba zai fi myar da hankali wajen ƙoƙarin mayar da gurbin abubuwan da ya rasa ba a tsawon wannan lokaci.
4. Bisa ga alamu, tsananin haƙuri da kawaicin Ganduje sun haifar masa da rauni, wanda zai iya yin illa ga irin salon shugabancinsa. Bayan haka, shekaru kusan 16 da ya shafe a ƙarƙashin Kwankwaso sun bayyana shi a matsayin tamkar wani mutum wanda ba shi da cikakken ra’ayin kansa ko ba zai iya tsayawa da ƙafafunsa ba.



Amfanin Zaɓar Takai
1. Idan aka zaɓi Takai, to an samar da canji a sama, canji a ƙasa. Hakan zai bayar da damar cewa kowanne ɓangare za su amfani mulki ba tare da ya tattare a waje ɗaya ba, balle har a samu shantakewa ko kama-karya.
2. Kano, yanzu a tamke ta ke tamau kuma ta na buƙatar a ɗan sassauta kaɗan. Gwamnatin Kwankwaso ta fi mayar da hankali akan gine-gine da manyan aiyuka. Takai, kamar yadda ya ke faɗa, ya na da burin ya karkatar da akalar manufar gwamnati domin ta fi mayar da hankali akan gina jama’a, sauƙaƙa musu da kuma taimaka musu, taimakawa ma’aikata, taimakawa marasa ƙarfi, kula da noma da kiwon lafiya da sauransu.
3. Ga dukkan alamu, Takai a matsayin gwamna zai sakarwa ƙananan  hukumomi mara su yi fitsari. Yanzu ƙananan hukumomi a mace suke murus, akwai buƙatar a farfaɗo da su in dai ana so ci gaba ya kai can ƙasa wajen jama’a da sauran marasa galihu.
4. Alamun nutusuwa, yakana da kirki sun bayyana a tattare da Takai. Bayan haka an shaideshi kan gaskiya da riƙon amana- duk waɗannan abubuwa jari ne a harkar shugabanci. Bayan haka, kasancewarsa mai matsakaicin shekaru  wanda ya ke da sauran siyasa a gaba, zai so ya yi abubuwan da zai kafa tarihi mai kyau.

Matsalolin Zaɓar Takai
1. Akwai alamun cewar iyayen gidan jam’iyyar PDP na Kano ba za su bar Takai ya sarara a mulkin Kano ba. Kasancewar sun rasa Gwamnatin Tarayya, duk za su iya dawowa Kano su tare akan ta da buƙatu iri-iri.
2. Akwai masu tsoron cewar Takai ba zai iya aikin gwamna yadda ya kamata ba, kasancewar gogewarsada ƙwarewarsa basu kai yadda ake so ba, musamman idan aka yi la’akari da cewar Kano ba ƙaramar jiha ba ce kamar Yobe, Zamfara, Ekiti ko Ebonyi ba.
3. Kwankwaso ya ɗora Kano akan wata miƙaƙƙiyar hanya, akwai tsoron cewar Takai zai iya karkacewa izuwa wata hanyar daban ko ya mayar da hannun agogo baya.
4. A siyasar wannan zamani, mun ga tasirin ɗaukar nagartaccen mataimaki. Saɓanin irin Mataimakin Ganduje, Mataimakin Takai ba shi da wata nagarta sosai. Abin Allah Ya kiyaye, idan wani tsautsayi ya samu gwamna, da yawa ba za su gamsu da Abba Risqua a mulkin Kano ba.


© Malam Amir Abdulazeez 2014. 

Zaɓen 2015: Lalube A Cikin Haske

02 Ga Fabrairu, 2015


Daga: Amir Abdulazeez

L
okacin da al’ummar Najeriya suka kaɗa ƙuri’a a zaɓukan shekarar 1999, mafi yawa daga cikin mutane, buƙatarsu ba ta wuce mulki ya komo gurin farar hula ba. Su kansu jam’iyyu a wannan lokaci an kafa su ne a gaggauce duk da yake dai wasu daga cikinsu gyauron jam’iyyu guda biyar na lokacin Marigayi Abacha ne, kuma idan aka ɗauke ɗaiɗaikun wasu muhimman ‘yan siyasa da ke cikin wasu jam’iyyun, kusan babu wani ma’auni abin dogara da za a iya amfani da shi wajen bambance jam’iyyun ta fuskar kyawawan manufofi ko rashinsu. Kodayake jam’iyyun Najeriya ba a sansu a kan wata tartibiyar alƙibla ko wasu manufofi na musamman ba, sai dai ba a rasa su da ‘yan ƙudurce-ƙudurce a rubuce, amma ba lallai a aikace ba.

Me yiwuwa a wancan lokaci, PDP ta fi kowacce jam’iyya ƙarfi ne sakamakon yawan gogaggun ‘yan siyasar Najeriya da suka tattaru a cikin ta, ko kuma saboda gudunmawa ta bayan fage da gwamnatin sojoji ta wancan lokaci ake zargin ta na bai wa jam’iyyar, ko kuma saboda dalilai biyun baki ɗaya. Tunanin wannan goyon baya na gwamnatin sojoji ga PDP, wataƙila ya wanzu ne daga bayyanar buƙatar masu madafan iko na wancan lokaci a fili na ganin sun samar da ƙwaƙƙawar jam’iyya don cimma burinsu na dawo da Obasanjo a matsayin Shugaban ƙasa. Kodayake jama’ar Najeriya da dama sun zaɓi Obasanjo domin kyautata zaton da suke yi a gareshi, amma wa ya sani ko cewa da ba wancan goyon baya na gwamnati, Olu Falae wanda ya tsaya wa APP/AD takara, zai iya kayar da shi?

Kasancewar mun ɗauki lokaci mai tsawo a ƙarƙashin mulkin sojoji kuma mun ratso ta lokuta daban-daban na saɓa alƙawuran bai wa fararen hula damar mulki daga su sojojin, sai ya zamana mun shigo tsarin dimokraɗiyya a wannan jamhuriyya ta huɗu a matsayin masu lalube cikin duhu, a matsayin marasa tabbas ɗin mai gaba za ta haifar, a matsayin waɗanda basu damu da tsarin sosai ba, sannan kuma a matsayin waɗanda suke tsoron shiga a dama da su. Wannan ya na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa muka samu kanmu a wasu daga cikin matsalolin da muke fama da su a yanzu. Alal misali, a shekarar 1999, mutane da yawa masu kishi, cancanta da nagarta a matakai daban-daban duk sai suka ƙi tsayawa zaɓuka, don tunanin cewa harkar ba za ta ɗore ba. Sakamakon haka, wasu ‘yan tamore da a-ci-bulus, marasa kishi da masu neman kuɗi da yawa suka samu dama suka shiga zaɓuka kuma suka kama madafan iko, suka tara kuɗaɗe, suka fi ƙarfin kowa kuma har kawo yanzu  madafun iko na hannunsu da kuma hannun ‘yan korensu. Abin takaici, sai a shekarar 2003 da 2007 waɗancan nagartattun mutane da suka ƙyamaci tsarin a 1999 suka dawo su na son damar ruwa a jallo a lokacin da kuma ta fi ƙarfinsu. Har kawo yanzu, ƙalilan daga cikin irin waɗannan mutane ne suka samu damar banƙarawa suka shiga tsarin, a dai-dai lokacin da kuma ɓarnar da aka tafka ta yi munin da gyaran nasu bai yi wani tasirin a-zo-a-gani ba. Kai hasali ma, su ma ɓarnar ta mamayesu, sai ‘yan kaɗan waɗanda ko ɗuriyarsu ba a iya ji.

Haƙiƙa abubuwa da yawa sun gudana daga 1999 zuwa 2015, waɗanda dukkan ‘yan Najeriya sun koyi darussa a siyasance, ta yadda kusan kowa yanzu kansa a waye ya ke, kuma idonsa a buɗe ya ke, sai dai wanda ba ya bibiyar al’amura, ko kuma ya na bibiya amma bai damu da al’amuran ba, sai kuma ɗan abin da ba a rasa ba.

Wannan zaɓe na 2015 lalube ne, amma kuma a cikin haske domin kuwa a tsawon shekaru 16 da suka gabata, kusan babu wani ɗan siyasa tun daga sama har ƙasa da jama’a basu ga kamun ludayinsa ko kuma basu fahimci manufofi da aƙidunsa ba. Sannan ga sababbin ‘yan takara, waɗanda wannan kusan shi ne karo na farko da suka shigo harkar siyasa, zai yi wahala a ce mutane basu san wani muhimmin abu na rayuwar aikinsu, mu’amalarsu ko gwagwarmayarsu ba, wacce za ta basu damar yin alƙalanci a kansu. Babu wani salon ƙarya, yaudara, makirci, sata, yarfe, cuta, danniya da rainin hankali da talakawa basu gani ba a tsawon wannan shekaru 16 na dimokraɗiyya a Najeriya ba. Kawo yanzu ya kamata a ce za mu iya bambance tsakanin ɓarayi da masu amana, maƙaryata da masu cika magana, masu bautawa talakawa da masu bautar da su da dai sauransu. Ashe kenan mutane ya kamata su je gindin akwatunan zaɓe da cikakkiyar masaniya da fahimta a kan kowa da kuma komai kuma ya kasance sun tanadi irin alƙalancin da ya kamata su yi. Wanda kuma ya yanke shawarar ya zaɓi rashin cancanta da gangan ko a bisa dalilai na son zuciya, ya ci amanar kansa, iyalinsa da al’umma kuma ya na daga kan gaba a cikin waɗanda za su girbi abin da ya shuka.

Duk da cewa mun riga mun san inda muka dosa a wannan tafiya, amma akwai buƙatar mu yi la’akari da wasu abubuwa kafin ranar zaɓe mai zuwa nan da ‘yan kwanaki kaɗan ababen ƙirgawa.

Muhimmin abu na farko da ya kamata mu kiyaye shi ne bambancin ‘yan siyasa da kuma masu zaɓe. Ɗan siyasa shi ne wanda ya ke da jam’iyya kuma ya ke mata aiki  tuƙuru don ganin ta samu nasara. Ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, walau ya fahimci manufofin ta da aƙidun ta ko bai fahimta ba, sannan a shirye ya ke ya kare su, shi a gurinsa babu wanda ya kamata a zaɓa sai ɗan jam’iyyarsa, komai rashin cancantarsa kuma kowa bai cancanta ba in dai ba a jam’iyyarsa ya ke ba. Wasu ‘yan siyasar sun ɗauke ta a matsayin cikakkiyar sana’a wasu kuma a matsayin sana’a ta wucin gadi, wasu ma da ita suke samun kuɗi, wasu kuwa su na yin ta gadan-gadan amma su na da hanyar neman kuɗinsu daban. Kullum burin ɗan siyasa shi ne jam’iyyarsa ta samu mulki ba lallai wai don ta taimaki talakawa kawai ba, a’a saboda zai samu wata dama ta kuɗi ko mulki ko kuma ta ɗaguwar dajararsa ko kuma wani abun da shi ya bar wa kansa sani. Ba duka ‘yan siyasa ba ne, ci gaban ƙasa ya dame su sosai ba. Irin waɗannan mutane ‘yan siyasa basu wuce 1% na yawan al’ummar ƙasa ko yawan waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a ba, sai dai kuma a siyasarmu ta Najeriya, su na da gagarumin tasiri a kan ragowar 99% ɗin da sune masu zaɓe.

Shi kuwa mai kaɗa ƙuri’a ko mai zaɓe, ɗan ƙasa ne kawai wanda ya cika ƙa’idojin Hukumar Zaɓe  da za su ba shi dama a yi masa rajista domin kaɗa ƙuri’a. Mafi yawan masu zaɓe talakawa ne, marasa gata kuma sune aiyukan shugabanni masu kyau da marasa kyau ya ke shafa kai tsaye. A kan samu mai zaɓe ya kasance ya na da ra’ayin wata jam’iyya a ransa amma ba za a kirashi ɗan siyasa ba domin ba zai iya sakawa ko ya hana ba a kowanne irin mataki a cikin jam’iyyar kuma daga nesa ya ke kallon ta. Mai yiwuwa bai ma san manufofin ta ko shugabannin ta ba, kai ba ma ya daga cikin waɗanda za a tuntuɓa idan wata sabgar jam’iyyar ta taso.

‘Yan siyasa da bazar masu zaɓe suke rawa, shi ya sa burin mafi yawa daga cikinsu shi ne su ga mai zaɓe a cikin duhun kai ta yadda komai suka faɗa masa zai yi aiki da shi ba tare da lissafi ba. ‘Yan siyasa suna shiga kafafen yaɗa labarai suna cewar wai a zaɓi jam’iyyarsu tun daga sama har ƙasa. Wannan son zuciya ne, domin a zahirin gaskiya ba shi ne mafi alkhairi ga talakawa ba. Jam’iyyun Najeriya duk ɗaya suke, a yau mutum zai fita daga wata jam’iyya ya koma wata, gobe ko jibi ka ji shi a cikin wata. Idan muka kalli dukkan ‘yan APC da PDP sai mu ga cewa mutane ne da suka sha canja sheƙa kusan sau ba iyaka. Misali, a cikin gaggan ‘yan siyasar Najeriya na ƙoli a yanzu, Janar Buhari da Bola Tinubu ne kaɗai basu taɓa yin jam’iyyar PDP ba, sai wasu ‘yan tsirarun gwamnoni da sauransu. To kuwa a kan wane dalili za a ce mai zaɓe ya zaɓi jam’iyya, tun da jam’iyyun ba su da manufofi, asali ma a mafi yawan lokuta, ƙarfa-ƙarfa suke yi wajen tsayar da ‘yan takarkarinsu?

Abin da ya kamata masu zaɓe su yi shi ne, su kalli kowanne mataki, su auna mutanen da suke takara a wannan matakin, sai su zaɓi wanda suka fi kyautatawa zato a cikinsu. Shi kuwa ɗan siyasa ko ɗan jam'iyya mu ƙyale shi can ya je ya zaɓi jam’iyyarsa daga sama zuwa ƙasan domin shi zai ci moriyar hakan amma ba mu ba. Wani abin kiyayewa shi ne, kada mai zaɓe ya ce wai sai waɗanda suka tsaya zaɓe a babbar jam’iyya kamar APC ko PDP ne kaɗai ‘yan takara, a’a komai ƙanƙantar jam’iyya, in dai mutumin cikin ta, shi ya fi cancanta, to a ba shi ƙuri’a. Raja’a da muka yi a kan APC da PDP, shi ya sa suke yin cin kashin da suka ga dama, domin su na ganin kamar mai zaɓe ba shi da wani zaɓi sai su. Kullum muna kokawa da yadda jam’iyyu suke ƙaƙaba ‘yan takara amma kuma mun kasa yin maganinsu duk kuwa da cewa mu ne masu zaɓe. Mai zai hana mu zaɓi ɗan PDM ko APGA a inda APC da PDP suka yi mana ƙarfa-ƙarfa? Wataƙila hakan ya koya mu su hankali, su kiyayi gaba.

Daga 2003 zuwa yanzu, akwai gagarumar matsalar maguɗin zaɓe da ta ke damun siyasar mu kuma da alama mun kasa maganin ta duk kuwa da cewa da akwai matakan da za mu iya ɗauka. Dukkanmu mun sani cewa ba zaɓen gaskiya aka yi a 2003, 2007 da 2011 ba. Idan masu zaɓe suka ci gaba da zura idanu, to fa haka za a ci gaba. Kasancewar mun bar komai a hannun ‘yan siyasa, mun kalmashe hannuwanmu mun koma gefe, shi ya sa muka kasa kawo ƙarshen wannan matsala. Mu a ganinmu idan aka yi wa wanda muka zaɓa maguɗi, to shi abin ya shafa, haƙƙin sa ne ya tafi kotu, mu ba ruwanmu, wani lokacin ma waɗanda za su yi masa shaida a kotunma, sai ya biyasu. Ko kuma idan ‘yan siyasa su na kawo ruɗani a gaban akwatin zaɓe, to a gurinmu su ta shafa, mun manta cewar ƙuri’inmu ne a cikin akwatin, kuma ƙuri’ar mu ita ce ‘yancinmu wacce a dalilin ta muka bar duk abin da muke yi, muka bi dogayen layuka na tsawon lokaci a cikin rana don mu tabbatar mun bayyana ra’ayinmu. Ya zama wajibi a kanmu, a kowanne akwatin zaɓe,  a kafa kwamitin amintattu wanda ba ‘yan siyasa ba, waɗanda za su zagaya cikin garuruwa da unguwanni ba wai don su tallata wata jam’iyya ba, a’a sai don su faɗakar da mutane a kan muhimmanci zaɓe da fitowa zaɓen, nemo katin zaɓe a kawo shi kusa ba sai ranar zaɓe ba, koyar da yadda ake kaɗa ƙuri’a domin kada a lalata takardar ƙuri’a, bayar da shawarwari da muhimman bayanai a kan muƙamai daban-daban da alhakin da ke kansu, bayanai a kan kowanne ɗan takara da dai sauransu.

Amma abin takaici, mafi yawa ba ma yin wannan, maimakon haka wai sai mu bar ‘yan siyasa da masu zaɓe, su yi ta yi mu su ƙarya kuma su ne wai a gindin akwati, su za su ƙirga ƙuri’a kuma su za su ɗauki akawatin tare da malaman zaɓe su tafi ofishin zaɓe, sai abin da suka ga dama. Kamata ya yi a ce akwai wakilin wannan kwamitin amintattu mutum ɗaya ko biyu a cikin tsarin wanda za su sa ido, a ɗauki bayanai, hotuna da bidiyo kuma a shirya duk wasu hujjoji sannan a kafa shaidu ko da za su ji an faɗi wani sakamako ba dai-dai ba. A yi irin wannan tsari a matakin akwatuna, mazaɓu da ƙananan hukumomi. To amma mu kowa gani ya ke siyasa wata ƙazamar aba ce, ko kuma shi mai mutunci ne bay a son shiga rigima ko kuma ba ya so a zage shi, amma kuma a gefe ɗaya so ya ke yi a samu gyara, ko da yaya za a samu gyaran?

Akwai buƙatar mu fahimci cewa rigima, tayar da zaune tsaye, ko tashin hankali da lalata dukiyar gwamnati kafin, a lokacin da kuma bayan zaɓe, ba zai taimaki ɗan takarar mu ba balle kuma mu kanmu. Duk da cewa mafi yawancin masu tayar da rigimar ba masu nutsuwa bane, wasu ma ‘yan iskan gari ne, to amma haƙƙin mu ne mu hanasu, ba wai mu goya musu baya ko mu ji daɗin abin da suke yi ba. Akwai hanyoyi halatattu da za mu nuna rashin amincewar mu da sakamakon zaɓe kuma in dai mun haɗa kai mun jajirce mun daure kuma mun cire kwaɗayi da tsoro, babu wanda ya isa ya mulke mu a wannan lokaci ta hanyar haramtaccen zaɓe. 

‘Yan siyasa suna yaudarar jama’a da addini a lokacin zaɓe domin su samu ƙuri’a. Abin haushi, su kansu mafi yawancin ‘yan siyasar ba su damu da addinin ba ko dai a aƙidance ko a aikace, sai zaɓe ya zo tukunna, kuma idan sun samu damar, babu wani taimako da suke yi wa addinin sai dai kawai su yi amfani da shi don cimma burinsu. Idan aka tsayar da Musulmi a wata jam’iyya, sai ɗan siyasa yace maka ai ka zaɓi jam’iyyar domin ita ce ta Addinin Musulunci, idan kuma aka tsayar da wanda ba Musulmi ba sai ka ji ya na ce maka, ai mataimakinsa Musulmi ne, ko kuma yace da kai ai siyasa ba ruwan ta da addini. A can sama kuma Musulmin da waɗanda ba Musulmin ba sun haɗe kai suna ta lalata ƙasa. Ya kamata mai zaɓe ya san cewa wannan babbar yaudara ce ba ƙarama ba. Ya kamata mu duba waɗanda suka cancanta, mu zaɓe su kuma mu tilasta mu su su kyautata rayuwarmu da ta ‘ya’yanmu.

Siyasa ta zama kasuwanci, kuma masu zaɓe suna da muhimmiyar rawar da za su iya takawa a wannan karon wajen kawar da wannan al’amari. Sau tari wasu su kan ce wai idan ɗan takara ya bayar da kuɗi a zaɓe shi, to a karɓa amma a zaɓi cancanta. Sai dai kuma, ya kamata mu tuna cewar, duk wanda ya ci ladan kuturu, to dole ya yi masa aski. Maganin kada a yi, to kada a fara! Goyon bayan mutum da ra’ayinsa, ya wuce a sayesu da kuɗi miliyoyi, ballantana ‘yan dubunnai ko ɗaruruwan nairori da ‘yan siyasa suke rabawa ranar zaɓe. Ba ya daga cikin ƙimar mutum, ya karɓi kuɗi a kan zai yi abu, kuma ya ƙi yi, kodayake ma wannan kuɗin marabar su kaɗan ce da cin hanci ko rashawa. Me zai sa kuwa ka karɓi cin hanci? Mu guji sayar da ‘yancinmu, domin abin da za a baka ka sayar da ‘yancin, ba zai ishe ka cefanen kwana huɗu ba kuma a cuce ka na tsawon shekaru huɗu.

Duk da ya ke mu ɗan makara a yanzu, amma lokaci ya yi da jama’a za su dinga ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓen ‘yan takara da kuɗaɗensu, domin ya kasance su ne da iko da shi ko da bayan ya ci zaɓe, ba wai ya zuba kuɗi ya ci zaɓe ya zo ya na ganin shi ne da kansa ba. Tsarin da Janar Buhari ya ke amfani da shi na neman tallafin ɗari da kwabo daga wajen talakawa masu zaɓe, abu ne mai kyau kuma haka ya kamata kowanne ɗan takara ya yi. Idan kuma bai yi haka ba, to dole ya bayyana wa jama’a waɗanne kuɗaɗe ya ke amfani da su kuma a ina ya same su?

Abu na ƙarshe, lokaci ya wuce, da za mu zaɓi mutane, mu ƙyale su sakaka su na yin abin da suka ga dama, sai sun zo sun fi ƙarfinmu kuma mu koma gefe muna jiran shekara huɗu ta cika mu samu damar canja su.  Akwai tanadin doka a cikin Kundin Tsarin Mulki da ya bai wa masu zaɓe dama su yi wa ɗan majalisa kiranye idan ba su gamsu da wakilcinsa ba. Idan shugaban ƙasa ko gwamnoni suka nemi su zarce gona da iri, ya zama wajibi mu matsawa ‘yan majalisu lamba su tsigesu daga kan mulki, idan kuma sun ƙi, to mu yi mu su kiranye, mu tura waɗansu. Rashin yin amfani da damar da Kundin Tsarin Mulki ya bai wa talakawa, ita ta sa masu mulki suke cin karensu ba babbaka bisa tunanin babu abin da za a yi musu.

Su kansu shugabanni nagarin, ba haka kawai za mu ƙyale su ba, wajibi ne mu saka mu su ido, mu tabbatar sun ɗore a kan aiyuka masu kyau kuma kada mu bari su ɗauka wai alfarma ko taimako suke yi mana, a’a dama abin da muka ɗaukesu aiki su yi mana kenan. Maganar bambaɗanci, fadanci ko ɗaga kai ba ta taso ba. Shugaba shi ne bawan talakawa, amma talakawa ba bayinsa ba ne.


© Malam Amir Abdulazeez 2015.
   


DAWAKIN-TOFA: Siyasa ko Masifa?

10 Ga Satumba, 2014.

Daga: Amir Abdulazeez

K
u yi m in  afuwa idan kalmar ‘masifa’ da na yi amfani da ita a wannan sharhi ta yi tsauri da yawa. Amma magana ta gaskiya,  da wahala a iya amfani da wata kalmar ba ita ba wajen kwatanta ko bayyana irin yanayin da masu juya akalar siyasar Dawakin-Tofa suka sanya ta a ciki.
Kimanin sati uku da suka gabata, wani bawan Allah da muka fara mu’amala da shi a shekarar bara ya tare ni a gidan wani ɗaurin aure. Bayan mun gaisa, sai ya bani haƙuri bisa ƙauracemin da ya yi na kwana biyu. Yace ya ƙauracemin  ne saboda dalili na siyasa, domin wai ya na tsoron kada waɗanda ya kira iyayen gidansa na siyasa a Jam’iyyar APC ta Dawakin-Tofa su gane ya na mu’amala da ni ko kuma mutane iri na, su saka ƙafar wando ɗaya da shi, wai tunda a cewarsa da ni da jaridar da na ke wallafawa, ana yi musu kallon masu adawa da Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma wasu masu juya akalar APC a Dawakin-Tofa.

Da farko dai na so na tsare shi sai ya bayyana min abin da ni na yi ko jaridar wanda ya ke nuna ana adawa da Gandujen ko kuma da su iyayen gidan nasa, to amma sai na ga hakan ɓata lokaci ne, ba lallai ne in samu wata gamsuwa ba. Kawai sai na yi masa godiya , muka yi sallama, muka rabu ina jin tausayinsa bisa wannan hali da aka saka shi  ko kuma ya saka kansa a ciki.
Bayan ‘yan kwanaki da faruwar wannan sai na haɗu da wani mai riƙe da muƙami a gwamnatin ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa ya na bayyana wa wani abokinsa (shi ma wani shahararraen ɗan siyasa) cewar iyayen gidansa sun shaida masa cewar kada ya ƙara alaƙa da wannan abokin nasa, idan ba haka ba zai ji a jikinsa. Waɗannan mutane biyu abokai ne shekara da shekaru kuma tare suka yi makaranta amma duk da wannan, wai ba a tunanin cewar wata hulɗar daban za ta iya haɗasu wadda ba ta siyasa ba. Kai in ma hulɗar siyasa za su yi tare, to sai me? Wai yaushe siyasa ta koma gaba ne. Wanna masifa da me ta yi kama?

Kwanakin baya aka dinga yaɗa labari cewar Honarabul Kawu Sumaila, ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano, ya kira dukkan shugabannin mazaɓu na Jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, amma wai sai aka hana na Dawakin-Tofa zuwa. Abin haushi da kunya, na ƙananan hukumomi 43 sun je amma ban da na Dawakin-Tofa.  Wannan ko mun ƙi ko mun so, saƙon da muke isar wa da duniya shi ne har yanzu Dawakin-Tofa siyasar gaba, duhun kai da jahilci muke yi ko da kuwa hakan ba gaskiya ba ne. Shin suna tsammanin da haka za a taimaki takarar Gandujen? Yanzu idan Maigirma, Dakta Ganduje ya kira shugabannin Sumaila suka ƙi zuwa, mu ‘yan Dawakin-Tofa ya za mu ji a ranmu? Idan kuma Kawu Sumailan Allah Ya ba wa Gwamnan Kano, ya ake tunanin zai ɗauki ‘yan Dawakin-Tofa misali? A siyasance don kana son wani, ba za ka yi mu’amala da kowa ba kenan?
Ya kamata Maigirma Mataimakin Gwamna ya tsawatarwa waɗannan mutane masu kiran kansu muƙarrabansa ko kuma masu sawa da hanawa a jam’iyyar APC ta Dawakin-Tofa, waɗanda su ake zargi da aikata irin waɗannan abubuwa. Idan kuma da yawunsa da yardarsa suke yin hakan , to sai a yi mana bayani domin mu san yadda abin ya ke. Ita dai gaskiya matuƙar ɗaci ne da ita, kusan kowa ba ya so a faɗa masa ita, amma idan ya daure ya karɓe ta ya yi amfani da ita, sakamakon ta zai zamo masa mai zaƙi.

Akwai buƙatar mu tuna cewar, shi goyon baya da haɗin kan jama’a, ba a samunsa ta ƙarfi, ana samunsa  ne a siyasance ta hanyar kyautatawa da laluma. Ko’ina sai ɓatawa Ganduje suna a ke yi da sunan tallata shi, kuma wannan ba ƙaramar mummunar illa ba ce ga wanda ya ke neman Gwamnan Kano ba wai Gwamnan Dawakin-Tofa, kuma a shekarar 2015 ba wai 2019 ba. Idan har muka ga shiru ba a samu gyara ba ko kuma ba a tsawatar ba, to za mu ƙaddara cewar Maigirma Ganduje shi ya ba su izinin duk wannan abu da suke yi.

Shi jagoranci da ɗaukaka, Allah Ne Ya ke ba da su, don haka mun yarda waɗannan mutane tauraruwarsu ita ta ke haskawa kuma lokacinsu ne, kuma su ne jagorori. To amma ya kamata su yi amfani da wannan dama don su bar kyakkyawan tarihi ta hanyar kawo gyara da cigaba, amma ba su dinga kama-karya, son zuciya tare da haddasa gaba a tsakanin jama’a ba.

Haka kawai yanzu an ɗauko wani salo, idan ka na neman wani muƙami na siyasa, sai a ce wai ai ba ka son Ganduje don haka a yaƙe ka, ko kuma a ce Ganduje ba kai ya ke so ba, don haka wai aikin banza ka ke, da kai da banza duk ɗaya,  ba za ka ci ba. To ko an manta cewar Allah Shi ya ke bayar da mulki? Duk wanda ya ke kan wata dama a yanzu, akwai wanda ya kai shi idan ba Allah ba? To ya kamata a sani, Ganduje uba ne, kuma mu a tunanin mu matsayinsa ya wuce a ce wai ya na son wane ko bay a son wane. Ya kamata a ce kowa na sa ne, kai har wanda ma ba ɗan jam’iyyarsa ba.
Dawakin-Tofa ƙaramar hukuma ce mai ɗumbin tarihi da daraja ba ma a Jihar Kano ba, a’a har a Najeriya baki ɗaya. Ta na daga cikin ƙananan hukumomi ƙirƙirar farko a Najeriya baki ɗaya kuma ita uwa ce da ta haifo kuma ta raini wasu ƙananan hukumomi irin su Bagawai, Tofa da Rimin-Gado. Amma abin takaici, yanzu dariya su ke mana suna cewar muna ƙarƙashin siyasar mulkin-mallaka, siyasar rashin ‘yanci da tsoro da danniya.

Wannan ƙaramar hukuma ba mallakin wani ba ce, ta mu ce baki ɗaya kuma haƙƙin mu ne  mu haɗu tare mu ga cewar mun ciyar da ita gaba. Amma idan wani ko wasu suna ganin cewa Dawakin-Tofa mallakar su ce kuma za su tilastawa mutane ta ƙarfin tsiya su yi abin da suke so, to ba kansu farau ba, kuma sai mu ce mu su: ‘Allah Ya bada sa’a’, gas u ga ‘yan Dawakin-Tofar nan, ai kowa ya san inda ya ke masa ciwo.

© Malam Amir Abdulazeez 2014.


Dalilai 7 da Suka Sa Bai Kamata a Zaɓi Kwankwaso a Matsayin Sanata ba

14 Ga Maris, 2015



Daga: Amir Abdulazeez

M
ai yiwuwa idan da za a kaɗa ƙuri’a a tsakanin ‘yan Jihar Kano akan cewar ko sun yarda a yi wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa gyara domin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya zarce a matsayin Gwamnan Kano, to ana kyautata zaton za su iya amincewa da wannan sauyi; wataƙila ma da gagarumin rinjaye. Ba don komai ba sai don cewar Kwankwaso ya yi rawar gani ƙwarai da gaske daga dawowar mulkinsa a 2011 zuwa 2015. Wannan ko kusa ba ta nufin cewar Kwankwason bai yi kura-kurai a mulkinsa ba; a’a ta na nufin cewar alkhairan da ya shuka sun rinjayi matsalolinsa a sha’anin mulkin Kano sosai da sosai, sannan kuma ya bar abubuwa na tarihi waɗanda za a daɗe ana mora kuma su sa a dinga tunawa da shi.

Kwankwaso ya samar wa da kansa gurbi na din-din-din a cikin tarihin Jihar Kano, kuma ko iya haka ya tsaya, babu wani abu da zai zo ya share wannan gurbi nasa. Me yiwuwa Marigayi Audu Baƙo da Marigayi Muhammad Abubakar Rimi ne kaɗai za su sha gabansa ta fuskar ciyar da Kano gaba a gwamnatance; sannan kuma a siyasance ya taka rawar ganin da bayan irin su Malam Aminu Kano da ire-irensa, to sai irinsu Kwankwason za a yi magana.

Masu hikima su kan ce, wani lokaci ba wai samun nasara ita ta fi wahala ba, a’a sarrafa nasarar, alkinta ta, ƙasƙan da kai a cikin ta da kuma sanin lokacin da ya kamata kada a zarce rawa da makaɗi bayan an samu nasarar. Daga dukkan alamu Gwamna Kwankwaso ya samu gaagrumar nasarar siyasa, amma ya na nema ya zarce rawa da makaɗi, ko dai da gangan ko kuma cikin rashin sani. Ya kamata jama’ar Kano su fargar da shi, su taimake shi ya dawo hayyacinsa.

Lokacin da wasu daga cikin masoya na haƙiƙa na Maigirma Kwankwaso suka dinga ba shi shawara ya tsaya takarar Sanata bisa ganin cewar wannan kujera ita ta fi dacewa da shi a wannan yanayin da ake ciki, shi kuma a lokacin sai ya ke ganin kujerar shugabancin ƙasa ce kawai dai-dai da shi. Duk da cewar ita ma takarar shugaban ƙasar da ya yi ta yi amfani kuma da ya samu nasara ana kyautata masa zaton zai yi abin kirki ƙwarai saboda ƙwarewarsa a ɓangaren zartarwa, amma bai kamata a ce bayan ya sha kaye, kuma a ce ya dawo ya na neman kujerar da ya ƙi nema tun da farko ba. Ga wasu daga cikin dalilan da suka sa bai kamata a zaɓe shi ya zama Sanatan Kano ta Tsakiya ba;

Nuna Haɗama Da Tsananin Son Mulki;
Kwankwaso ya nuna tsananin kwaɗayi da haɗamar mulki, irin wanda kusan ba a taɓa ganin irinsa a Jihar Kano ba a wannan siyasar jamhuriya ta huɗu da muke ciki. Saboda tsabar haɗama, Kwankwaso ya yi takarar kujeru biyu lokaci ɗaya; kujerar shugaban ƙasa da ta Sanata; yayin da ya tafi ya na yin takarar shugaban ƙasar da kansa, ita kuma ta Sanatan sai ya bayar da ita ajiya ana yi masa a ƙarƙashin kwamishinansa kuma surukinsa. Banda cewar wannan ya saɓa da tsarin dimokraɗiyya, adalci da sanin ya kamata, ya ma saɓa da tsarin gaskiya da kuma jagoranci. Ai ko Kano da APC ɗin mallakin mutum ne na kansa, ai bai kamata ya yi haka ba. Da wani ne ya yi wannan, da ba a san irin maganganun da Kwankwaso zai faɗa a kansa ba.
Wannan ta nuna burin Kwankwaso shi ne ya dauwama a kan mulki ba tare da ya sauka ba, ko kuma babu wanda ya cancanta sai shi. Tunda Kwankwaso ya nuna shi ya ƙasaita har ya tafi takarar shugaban ƙasa, kuma yace da gaske ya ke yi, to ai bai kamata kuma ya raba ƙafa ko ya dawo da baya, bayan an kayar da shi, yace zai nemi Sanata ba. Inda ya san ba da gaske ya ke ba, da tun farko sai ya haƙura ya nemi Sanatan.
A shekarar 1993, Injiniya Magaji Abdullahi ya tsaya Sanata a jam’iyyar SDP kuma ya yi nasara bayan ya faɗi zaɓen gwamna, haka a shekarar 1999 ya kuma yin irin haka a jam’iyyar APP amma sai Sanatan Kano ta Arewa mai ci yanzu Bello Hayatu Gwarzo ya yi nasara a kansa. To amma bambancin Injiniya Magaji da Kwankwaso, shi ba raba ƙafa ko takara biyu ya dinga yi a lokaci ɗaya ba, kuma ba ajiyar kujerar Sanatan ya bayar ba, a’a zuwa ya yi ya sake shiga zaɓe kamar kowa, kuma aka zaɓe shi.

Aikin Gwamna Daban da na Ɗan Majalisa;
Me yiwuwa idan aka ce a kaf Najeriya a yanzu babu wani Gwamna da ya ke da ƙwarewa da sanin makamar aiki kamar Kwankwaso, to ba lallai a yi kuskure ba. Wannan ma a bayyane ta ke domin shi kaɗai ne ya dawo mulki shekaru takawas bayan rabuwa da mulkin. Wannan shekaru takwas ta ba shi ilimi mai yawa a matasyinsa na ɗan kallo, kuma a dawowarsa ya yi aiki da wannan ilimi wajen samun nasarorin da ya samu. Saboda haka Kwankwaso ya na da ƙwarewa a ɓangaren zartarwa sosai. Hakan ce ta sa wasu mutanen suke ganin in da ya zama shugaban ƙasa, zai iya kawo gyare-gyare masu amfani ko kuma idan aka ba shi Ministan wata muhimmiyar ma’aikata a Gwamnatin Tarayya, zai taka rawar gani.
Duk wannan ba wai ta na nufin Kwankwaso zai samu nasara idan ya zama Sanata ba. Farko dai shi ba mutum ne ma mai girmama majalisa ba. Idan muka kalli yadda ya sa ƙafa ya shure Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya mayar da ita ‘yar amshin Shata, ya shaƙe ta, ya maƙure ta, to ya ishe mu hujjar cewa majalisa ba wajen zuwansa ba ne. Majalisa waje ne na tattaunawa, shawartawa, bibiya, lallama da tuntuɓa kafin a gabatar da duk wani ƙuduri; duk kuwa wanda ya san Kwankwaso sosai, ya san bai dace da waɗannan abubuwa ba domin mutum ne da ake yi wa zargin ya shahara wajen yanke hukunci shi kaɗai.
Kodayake a kullum ya kan fake da cewa ya yi Ɗan Majalisar Tarayya a 1993 a ƙarƙashin Jam’iyyar SDP kuma har ma ya zama Mataimakin Kakakin Majalisa a wancan lokaci. Sai dai a gaskiya wannan kaɗai ba za ta ba shi cancantar da ake buƙata ba domin a wancan lokaci sun yi aiki ne da Shugaban ƙasa na soja, don haka su ‘yan amshin shata ne lamba ɗaya kuma ba su ma daɗe ba, Janaral Abacha ya yi waje da su.   

Zarce Gona Da Iri, Rashin Manufa;
Kwankwaso ya samu gagarumar nasara a rayuwarsa ta mulki da siyasa; wannan ce ta sa ya ke neman ya zarce gona da iri. A tunaninsa wataƙila babu wanda zai iya abu sai shi ko kuma abu in dai babu shi, to bai cika ba. Ya zama wajibi a taka masa burki a dai-dai wannan lokacin. Idan aka yi haka ma an taimakeshi domin kada duniya ta ruɗeshi ya ɗauka babu wani mai baiwa sai shi.
Bayan haka da alama shi da Shekarau gasa suke yi; wannan ya yi Gwamna, wancan ma ya yi, wannan ya yi Minista wancan ma ya yi, wannna ya yi takarar shugaban ƙasa wancan ma ya yi, don haka to bari wannan ya tafi Sanata domin ya sha gaban wannan. Kuskure ne a dinga amfani da kujerar wakilci wacce ake so a yi amfani da ita don bauta wa jama’a ta wannan hanyar.
Babu wasu alamu na zahiri da suka nuna cewar Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya na da wata tartibiyar manufa wacce zai aiwatar idan ya je Majalisar Dattawa ta Sanatoci; kawai burinsa ya samu kujerar. Babu mamaki bayan an zaɓe shi, idan aka ba shi wata babbar kujerar ya rabu da ita kamar yadda tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Adamu Aliero ya yi, ya ajiye kujerar Sanata wacce jama’a suka zaɓe shi, ya tafi ya karɓi ministan Abuja kuma ƙarshe aka sallame shi daga ministan.

Majalisar Dattawa Ba Wajen Ritayar Gwamnoni Ba Ce;
Gwamnonin Najeriya, ciki har da Kwankwaso sun ɗauko wata hanya ta mayar da Majalisar Dattawa wani zaure wanda za su dinga yin ritaya ko hutawa a cikinsa. Wannan ya taimaka matuƙa wajen zubar da darajar majalisar tare da kawo mata gagarumin naƙasu wajen ci gaban ta.

Na farko dai, mafi yawan Gwamnonin Najeriya ba wata dokar kirki ko tsarin doka suka sani ba, sannan kuma idan sun sani, ba damuwa suka yi da aiki da ita ba. Hasalima, wasu daga cikinsu gani suke yi sun ma fi ƙarfin dokar. Banda kama-karya babu abinda suka saba da shi. To akan me za a zaɓe su wai su zo su yi doka? Mafi yawancinsu suna zuwa majalisar ne don wai ala dole sai sun ci gaba da mulki tunda wa’adin mulkinsu na gwamna ya ƙare, kuma mafi yawancinsu ta hanyar ƙarfa-ƙarfa suke karɓar takarar daga hannun waɗanda suke kan kujerar.
Daga 1999 zuwa yanzu, tsofaffin gwamnoni  11 ne suka zama sanatoci, yayin da 14 suka yi takara basu ci ba a tsawon wannan shekaru 16 na dawowar dimokradiyya. Amma wannan bai sa majalisar dattawan ta canza zani daga zargin da ake yi mata na kasa yin aikin da ya dace ba. Maimakon haka ma, sai ƙara taɓarɓarewa da ta ke yi dalilin shigowarsu. A yanzu haka akwai tsofaffin gwamnoni guda 9 a zauren Majalisar Dattawa yayin kuma da adadin tsofaffin gwamnoni da kuma masu barin gado waɗanda suke takarar Sanata a jam’iyyu daban-daban ya kai 26.

Kwankwaso Ba Ya Kamfen;
Duk bayan waɗannan  dalilan, shi Kwankwaso da alama gani yake kamar dole ne ma a zaɓe shi Sanata. Me yiwuwa gani ya ke yi kamar cancantarsa, isarsa da ƙasaitarsa sun wadatar, ba sai ya fita kamfen ya nemi alfarma a gurin masu zaɓe ba. Wataƙila a tunaninsa nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamna su za su sa shi ya samu kujerar Sanata ba hamayya.
Abin da kwankwaso ya kasa ganewa shi ne dukkan aiyukan da ya yi, ba wai alfarma ko taimako ya yi wa mutane ba. Shi ya kawo kansa da ƙoƙon bararsa a hannu tare da manufofinsa akan ya na neman sahalewar mutane da su ɗauke shi aiki domin ya zamar musu gwamna, su kuma suka ba shi dama, ya yi ƙoƙarin da zai yi kuma mutane suka ce sun yaba masa. Saboda haka idan yanzu ya na neman su sahale masa ya zama Sanata, ai ba kwanciya zai yi ya dinga taƙama da aikin da ya yi musu a gwamna ba, fitowa zai sake yi da ƙoƙon bara a hannu da buɗaɗɗiyar murya kuma ba tare da wata taƙama ba, ya bayyana manufofinsa, yace ya na neman a ɗauke shi aikin wakilci na Sanata. Idan an ga ya dace, ya cancanta, sai a zaɓe shi.
Tunda da alama Kwankwaso gani ya ke yi kamar shi zai taimakawa mutane ko kuma aiyukansa na gwamna sun isheshi, ba sai ya yi kamfen ba, to ya kamata jama’ar Kano ta tsakiya su nuna masa kuskurensa ta hanyar ƙin zaɓar sa. Nan gaba idan ya shirya wa neman Sanatan, sai ya fito ya yi kamfen ya nuna musu cewar Sanata yake nema domin maganar gwamna ta riga ta wuce.

Lado Bai Gaza Ba;
Idan mutum ya na kan kujera, kuma wa’adinsa bai zo ƙarshe ba ko kuma ya na da sauran damar ci gaba, to ba hikima ba ne canza shi, matuƙar bai gaza ba. A dukkanin sanatocin da Kano ta tsakiya ta yi daga 1999 zuwa yanzu, da wahala a samu wanda ya taka rawar ganin da Lado ya taka tun daga kan Sanata Kura Muhammed, Sanata Rufa’i Sani Hanga da kuma Sanata Muhammad Bello.
Lado ya kawo ƙudururruka masu muhimmanci a majalisa kuma ya na bayar da gudunmawa dai-dai gwargwado. Bayan haka ya kawo manya da ƙananan aikace-aikace a ciki da wajen mazaɓarsa ta Kano ta tsakiya. Idan aka yi la’akari da cewar wannan shi ne zuwansa na farko, to ya kamata a yaba masa.
Matsalolin Sanata Lado guda biyu ne kacal; na farko manyan aiyukan da yake taƙama da su (titin gadar sama na Gyaɗi-Gyaɗi da kuma raba titin Kano zuwa Katsina) duk ba a kammalasu ba. Shi titin Kano zuwa Katsina ma kusan a ce ba a yi kashi ɗaya bisa hamsin na aikin ba duk da cewa shekara kusan ɗaya da rabi kenan da bayar da kwangilar aikin titin. Wasu daga cikin manyan aiyukan da yake faɗa ma kamar gadar sama a Shataletalen Miltara da kuma a Kurna Babban Layi, har yanzu babu wanda ya ga alamar farasu.
Matsalar Lado ta biyu ita ce tsarin kamfen ko yanayin yaƙin neman zaɓensa. Mutane da yawa suna yi masa kallon wanda ya birkice ya sukurkuce ya ke neman duk hanyar da zai bi kada kujerarsa ta suɓuce. Wannan ta saka shi yin wasu abubuwa da suka saɓa da al’adar yaƙin neman zaɓe, kamar rabon kayan miya da nama, rabon ruwan zafi a asibitoci, sallamar Lado da dai sauransu. Abin da ma aka fi ƙalubalantarsa da shi shi ne, bai tashi yin waɗannan abubuwa ba, sai da zaɓe ya matso.
To amma duk da haka, Lado sai ya fi Kwankwaso amfani nesa ba kusa ba a majalisa domin shi zai kwantar da kai ya yi biyayya ya nemo aiyuka. Zai yi shawara ya tattauna da ‘yan uwansa domin samun mafita ga mazaɓarsa, saɓanin Kwankwaso da ya saba shi a gurinsa ake neman alfarma da aiyukan. Bayan haka kuma, ana kyautata masa zaton zai yi ƙoƙarin matsa lamba don ganin an ƙarasa waɗannan aiyukan da ya nemo domin so yake ya bar tarihi tunda kusan a ce yanzu ya fara siyasa, shi kuwa Kwankwaso ya riga ya gama kafa tarihi, babu wani abu da ya ke buƙata ya yi a nan gaba.

Kwankwaso! Lokacin Zama Cikakken Dattijo Ya Yi;
Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yanzu haka shekaraunsa na haihuwa 60 ba kaɗan, kuma kullum burinsa a ce shi ne jagora, kowa  a ƙarƙashinsa ya ke. Dattijantaka ta kan ƙarawa jagoranci armashi; ita kuwa dattijantaka ba ta samuwa idan mutum kullum burinsa  a ce shi zai riƙe muƙami ko zai tsaya takara. A 1999 Marigayi Dakta Muhammad Abubukar Rimi da Malam Musa Gwadabe ba su fi shekaru sittin sittin ba, amma suka zama dattijai a siyasa. A lokacin suna da damar su tsaya kowwanne irin muƙami a Jihar Kano kuma su ci ba hammaya, amma maimakon haka sai suka ɗaurewa irinsu Kwankwaso gindi, a lokacin shi Kwankwason bai fi shekaru 42 zuwa 43 ba. Akwai lokacin da aka yi ta bai wa Rimi shawarar ya tsaya Sanata, amma yace shi ba zai tsaya ba tunda ga yaransa nan na siyasa birjik waɗanda za su iya aikin Sanata, bai kamata ya zama cinye-duk yace sai ya yi da kansa ba.
Kwankwaso ya ɗauko tafiya mai nisa, kuma an kawo gaɓar da zai zama dattijo a siyasar Jihar Kano. Duk wata kujera da ta ke da alaƙa da Kano, in dai ba ya zama dolen-dole ba, to a daina rububinsa da ita. Idan ya na so, ya iya ci gaba da takarar shugaban ƙasa domin ita wannan dama kujera ce ta dattijai kuma ƙwararru. Idan kuma ba haka ba, watarana sai ya wayi gari tsamo-tsamo ya na takarar kujera ɗaya da ya-ku-bayi irina.


© Malam Amir Abdulazeez 2015.