Fassara

Sunday, August 9, 2015

Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa: Ga Ƙoshi Ga Kwanon Yunwa!!


Daga: Yasir Ahmad Chedi

Kowa ya sani, Allah Maɗaukakin Sarki Ya albarkaci wannan Ƙaramar Hukuma da duk abubuwan da ake buƙata na cigaban al’umma. Kamar su hanyoyin kuɗin shiga, waɗanda aka kasa inganta yadda za su shigo da kuma sarrafasu zuwa ayyukan cigaban al’umma. Muna da jama’a masu yawa, mafi yawancinsu matasa masu ilimi da ƙarfi a jika. Kuma muna da manya-manya kasuwanni kamar su kasuwar amfanin gona ta ƙasa da ƙasa dake Dawanau, kasuwar Gwamai, Kasuwar Dawakin-Tofa, sai kuma kasuwar gyare-gyare da sayar da tsofaffin kayan gyaran mota dake Kwakwaci. Sannan muna da gonakin noma da muke noman damuna da rani. Har ila yau, muna da manyan mutane da Allah Ya fifitasu kuma Ya ɗaukakasu kuma suka samu kansu tsundum a cikin harkokin siyasa kuma suke riƙe da manya-manyan muƙamai a gwamnatocin da suka gabata da kuma wannan gwamnatin da muke ciki. Sai dai duk da wannan abubuwa da muka lissafa a sama, an bar wannan Ƙaramar Hukuma a baya sosai idan muka kwatanta ta da sauran takwarorinta kamar su Bichi, Danbatta da sauransu, ta fuskar cigaba da samuwar aikin yi.

Matasanmu da suka yi ilimi, an barsu ba aikin yi, ‘yan kasuwarmu babu jari na kirki da dabarun kasuwanci na zamani, manomanmu babu kayan aikin noma kamarsu takin zamani, maganin ƙwari, rancen kuɗin noma da dabarun noma na zamani da kuma sauran kayayyakin aikin noman zamani kamarsu tantan, ƙwararren Baturen noma domin ilimantar da manoma akan cigaban noma a zamanance, da sauransu domin samun nasarar harkokinsu. Mafiya yawansu an barsu babu ilimantarwa akan kiwo na zamani da sauran abubuwa na bunƙasa rayuwar al’umma, duk an barsu sun taɓarɓare.

Mu mutanen Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, mutane ne masu biyayya ga shugabannimu, Masarauta, Malamai, manyan ‘yan siyasa da sauransu. Saboda haka, duk abin da suka umarcemu da yi, muna yi nan take.  Muna zaɓar duk mutumin da suka ce mu zaɓa ba tare da wani binciken ingancinsa ba. Suna yi mana alƙawarin inganta jin daɗinmu, tattalin arziƙinmu da ciyar da garuruwan Ƙaramar Hukumarmu gaba. Amma kash! Duk lokacin da muka zaɓesu, suka hau mulkin, sai su manta da mu da kuma duk alƙawurorin da suka yi mana, sai su maida hankalinsu wajen tara wa kansu da ‘ya’yansu dukiya, mu kuma su barmu cikin talauci, ‘ya’yanmu babu ingantaccen ilimi, su sakamu cikin munanan hanyoyi da ƙuncin rayuwa. Idan ƙarshen mulkinsu ya zo kuma, suna so mu sake zaɓensu, sai su yago wani abu daga cikin dukiyar da suka sata su zo su rinƙa rarrabawa masu kwaɗayin cikinmu waɗanda ba sa haƙuri da ƙaddara da talaucin da ya yi wa mutane kanta. Wannan mutane sai su zo mana da sabuwar yaudara cewa sun yi kuskure, amma za su gyara. Idan muka yarda muka sake zaɓarsu, abin da suka yi daga farko, shi za sucigaba da yi, amma yaudara da zalunci da sata sun isa haka, saboda shashashane kawai yake yarda a cuceshi koda yaushe. Alƙur’ani Maitsarki da Hadisan Annabinmu, Annabi Muhammad (SAW) sun umarcemu da kada mu zaɓi dukkan mutumin da yazo mana yace mana mu zaɓeshi ya shugabancemu domin gudun ko akwai wata manufa a zuciyarsa da yake son cimma, kuma suka umarcemu da mu zaɓo mutuminn kirki masu riƙon amana da tsoran Allah waɗanda muka tabbatar ba za su ci amanar mu ba, mu ba su shugabancimu.

A bisa doron abubuwan da na zayyana a sama kuma a nawa tunanin, akwai buƙatar canja wannan mummunar alƙiblar siyasa zuwa kyakkyawan tsari mai cike da adaci, gaskiya da riƙon amana kuma za mu iya canja wannan mummunar alƙiblar ne kawai hanyar ta waɗannan hanyoyi;
1.      Bai wa ilimi fifiko fiye da komai a cikin rayuwarmu.
2.      Kawar da ɓangaranci da munanan manufofi a tsakaninmu.
3.      Daina yin siyasa saboda a bamu kuɗi, mu koma neman ‘yancinmu, kare addininmu, cigaban ƙasarmu, jiharmu, garinmu da al’umma baki ɗaya.
4.      Daina sayar da ƙuri’armu a ranar zaɓe.
5.      Daina yin siyasar maula, wato bin gidajen ‘yan siyasa ana ƙarairayi iri-iri domin samun kuɗi.

Bayan wannan, duk wanda za’a tsayar takara, za mu zaɓe shi ne kawai domin cancantarsa da kuma sauran abubuwa kamar;
1.      Za mu zaɓe shi ne kawai domin ya shugabancemu akan manufofin bunƙasa garuruwanmu da wannan Ƙaramar Hukuma.
2.      Zai nemi ra’ayin jama’a akan dukkanin wasu aiyyuka na cigaban wannan Ƙaramar Hukuma kafin aiwatarwa.
3.      Zai rinƙa ziyartar ɗaukacin garuruwa da ke cikin wannan Ƙaramar Hukuma lokaci zuwa lokaci domin ya ga yanayin cigabansu da kuma abubuwan da suke buƙata.
4.      Zai ba mutanen wannan Ƙaramar Hukuma damar ganawa da shi domin su ba shi shawarwarin da za su ciyar da wannan Ƙaramar Hukumar cigaba.


No comments:

Post a Comment