Fassara

Tuesday, August 11, 2015

Dalilai 7 da Suka Sa Bai Kamata a Zaɓi Kwankwaso a Matsayin Sanata ba

14 Ga Maris, 2015



Daga: Amir Abdulazeez

M
ai yiwuwa idan da za a kaɗa ƙuri’a a tsakanin ‘yan Jihar Kano akan cewar ko sun yarda a yi wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa gyara domin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya zarce a matsayin Gwamnan Kano, to ana kyautata zaton za su iya amincewa da wannan sauyi; wataƙila ma da gagarumin rinjaye. Ba don komai ba sai don cewar Kwankwaso ya yi rawar gani ƙwarai da gaske daga dawowar mulkinsa a 2011 zuwa 2015. Wannan ko kusa ba ta nufin cewar Kwankwason bai yi kura-kurai a mulkinsa ba; a’a ta na nufin cewar alkhairan da ya shuka sun rinjayi matsalolinsa a sha’anin mulkin Kano sosai da sosai, sannan kuma ya bar abubuwa na tarihi waɗanda za a daɗe ana mora kuma su sa a dinga tunawa da shi.

Kwankwaso ya samar wa da kansa gurbi na din-din-din a cikin tarihin Jihar Kano, kuma ko iya haka ya tsaya, babu wani abu da zai zo ya share wannan gurbi nasa. Me yiwuwa Marigayi Audu Baƙo da Marigayi Muhammad Abubakar Rimi ne kaɗai za su sha gabansa ta fuskar ciyar da Kano gaba a gwamnatance; sannan kuma a siyasance ya taka rawar ganin da bayan irin su Malam Aminu Kano da ire-irensa, to sai irinsu Kwankwason za a yi magana.

Masu hikima su kan ce, wani lokaci ba wai samun nasara ita ta fi wahala ba, a’a sarrafa nasarar, alkinta ta, ƙasƙan da kai a cikin ta da kuma sanin lokacin da ya kamata kada a zarce rawa da makaɗi bayan an samu nasarar. Daga dukkan alamu Gwamna Kwankwaso ya samu gaagrumar nasarar siyasa, amma ya na nema ya zarce rawa da makaɗi, ko dai da gangan ko kuma cikin rashin sani. Ya kamata jama’ar Kano su fargar da shi, su taimake shi ya dawo hayyacinsa.

Lokacin da wasu daga cikin masoya na haƙiƙa na Maigirma Kwankwaso suka dinga ba shi shawara ya tsaya takarar Sanata bisa ganin cewar wannan kujera ita ta fi dacewa da shi a wannan yanayin da ake ciki, shi kuma a lokacin sai ya ke ganin kujerar shugabancin ƙasa ce kawai dai-dai da shi. Duk da cewar ita ma takarar shugaban ƙasar da ya yi ta yi amfani kuma da ya samu nasara ana kyautata masa zaton zai yi abin kirki ƙwarai saboda ƙwarewarsa a ɓangaren zartarwa, amma bai kamata a ce bayan ya sha kaye, kuma a ce ya dawo ya na neman kujerar da ya ƙi nema tun da farko ba. Ga wasu daga cikin dalilan da suka sa bai kamata a zaɓe shi ya zama Sanatan Kano ta Tsakiya ba;

Nuna Haɗama Da Tsananin Son Mulki;
Kwankwaso ya nuna tsananin kwaɗayi da haɗamar mulki, irin wanda kusan ba a taɓa ganin irinsa a Jihar Kano ba a wannan siyasar jamhuriya ta huɗu da muke ciki. Saboda tsabar haɗama, Kwankwaso ya yi takarar kujeru biyu lokaci ɗaya; kujerar shugaban ƙasa da ta Sanata; yayin da ya tafi ya na yin takarar shugaban ƙasar da kansa, ita kuma ta Sanatan sai ya bayar da ita ajiya ana yi masa a ƙarƙashin kwamishinansa kuma surukinsa. Banda cewar wannan ya saɓa da tsarin dimokraɗiyya, adalci da sanin ya kamata, ya ma saɓa da tsarin gaskiya da kuma jagoranci. Ai ko Kano da APC ɗin mallakin mutum ne na kansa, ai bai kamata ya yi haka ba. Da wani ne ya yi wannan, da ba a san irin maganganun da Kwankwaso zai faɗa a kansa ba.
Wannan ta nuna burin Kwankwaso shi ne ya dauwama a kan mulki ba tare da ya sauka ba, ko kuma babu wanda ya cancanta sai shi. Tunda Kwankwaso ya nuna shi ya ƙasaita har ya tafi takarar shugaban ƙasa, kuma yace da gaske ya ke yi, to ai bai kamata kuma ya raba ƙafa ko ya dawo da baya, bayan an kayar da shi, yace zai nemi Sanata ba. Inda ya san ba da gaske ya ke ba, da tun farko sai ya haƙura ya nemi Sanatan.
A shekarar 1993, Injiniya Magaji Abdullahi ya tsaya Sanata a jam’iyyar SDP kuma ya yi nasara bayan ya faɗi zaɓen gwamna, haka a shekarar 1999 ya kuma yin irin haka a jam’iyyar APP amma sai Sanatan Kano ta Arewa mai ci yanzu Bello Hayatu Gwarzo ya yi nasara a kansa. To amma bambancin Injiniya Magaji da Kwankwaso, shi ba raba ƙafa ko takara biyu ya dinga yi a lokaci ɗaya ba, kuma ba ajiyar kujerar Sanatan ya bayar ba, a’a zuwa ya yi ya sake shiga zaɓe kamar kowa, kuma aka zaɓe shi.

Aikin Gwamna Daban da na Ɗan Majalisa;
Me yiwuwa idan aka ce a kaf Najeriya a yanzu babu wani Gwamna da ya ke da ƙwarewa da sanin makamar aiki kamar Kwankwaso, to ba lallai a yi kuskure ba. Wannan ma a bayyane ta ke domin shi kaɗai ne ya dawo mulki shekaru takawas bayan rabuwa da mulkin. Wannan shekaru takwas ta ba shi ilimi mai yawa a matasyinsa na ɗan kallo, kuma a dawowarsa ya yi aiki da wannan ilimi wajen samun nasarorin da ya samu. Saboda haka Kwankwaso ya na da ƙwarewa a ɓangaren zartarwa sosai. Hakan ce ta sa wasu mutanen suke ganin in da ya zama shugaban ƙasa, zai iya kawo gyare-gyare masu amfani ko kuma idan aka ba shi Ministan wata muhimmiyar ma’aikata a Gwamnatin Tarayya, zai taka rawar gani.
Duk wannan ba wai ta na nufin Kwankwaso zai samu nasara idan ya zama Sanata ba. Farko dai shi ba mutum ne ma mai girmama majalisa ba. Idan muka kalli yadda ya sa ƙafa ya shure Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya mayar da ita ‘yar amshin Shata, ya shaƙe ta, ya maƙure ta, to ya ishe mu hujjar cewa majalisa ba wajen zuwansa ba ne. Majalisa waje ne na tattaunawa, shawartawa, bibiya, lallama da tuntuɓa kafin a gabatar da duk wani ƙuduri; duk kuwa wanda ya san Kwankwaso sosai, ya san bai dace da waɗannan abubuwa ba domin mutum ne da ake yi wa zargin ya shahara wajen yanke hukunci shi kaɗai.
Kodayake a kullum ya kan fake da cewa ya yi Ɗan Majalisar Tarayya a 1993 a ƙarƙashin Jam’iyyar SDP kuma har ma ya zama Mataimakin Kakakin Majalisa a wancan lokaci. Sai dai a gaskiya wannan kaɗai ba za ta ba shi cancantar da ake buƙata ba domin a wancan lokaci sun yi aiki ne da Shugaban ƙasa na soja, don haka su ‘yan amshin shata ne lamba ɗaya kuma ba su ma daɗe ba, Janaral Abacha ya yi waje da su.   

Zarce Gona Da Iri, Rashin Manufa;
Kwankwaso ya samu gagarumar nasara a rayuwarsa ta mulki da siyasa; wannan ce ta sa ya ke neman ya zarce gona da iri. A tunaninsa wataƙila babu wanda zai iya abu sai shi ko kuma abu in dai babu shi, to bai cika ba. Ya zama wajibi a taka masa burki a dai-dai wannan lokacin. Idan aka yi haka ma an taimakeshi domin kada duniya ta ruɗeshi ya ɗauka babu wani mai baiwa sai shi.
Bayan haka da alama shi da Shekarau gasa suke yi; wannan ya yi Gwamna, wancan ma ya yi, wannan ya yi Minista wancan ma ya yi, wannna ya yi takarar shugaban ƙasa wancan ma ya yi, don haka to bari wannan ya tafi Sanata domin ya sha gaban wannan. Kuskure ne a dinga amfani da kujerar wakilci wacce ake so a yi amfani da ita don bauta wa jama’a ta wannan hanyar.
Babu wasu alamu na zahiri da suka nuna cewar Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya na da wata tartibiyar manufa wacce zai aiwatar idan ya je Majalisar Dattawa ta Sanatoci; kawai burinsa ya samu kujerar. Babu mamaki bayan an zaɓe shi, idan aka ba shi wata babbar kujerar ya rabu da ita kamar yadda tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Adamu Aliero ya yi, ya ajiye kujerar Sanata wacce jama’a suka zaɓe shi, ya tafi ya karɓi ministan Abuja kuma ƙarshe aka sallame shi daga ministan.

Majalisar Dattawa Ba Wajen Ritayar Gwamnoni Ba Ce;
Gwamnonin Najeriya, ciki har da Kwankwaso sun ɗauko wata hanya ta mayar da Majalisar Dattawa wani zaure wanda za su dinga yin ritaya ko hutawa a cikinsa. Wannan ya taimaka matuƙa wajen zubar da darajar majalisar tare da kawo mata gagarumin naƙasu wajen ci gaban ta.

Na farko dai, mafi yawan Gwamnonin Najeriya ba wata dokar kirki ko tsarin doka suka sani ba, sannan kuma idan sun sani, ba damuwa suka yi da aiki da ita ba. Hasalima, wasu daga cikinsu gani suke yi sun ma fi ƙarfin dokar. Banda kama-karya babu abinda suka saba da shi. To akan me za a zaɓe su wai su zo su yi doka? Mafi yawancinsu suna zuwa majalisar ne don wai ala dole sai sun ci gaba da mulki tunda wa’adin mulkinsu na gwamna ya ƙare, kuma mafi yawancinsu ta hanyar ƙarfa-ƙarfa suke karɓar takarar daga hannun waɗanda suke kan kujerar.
Daga 1999 zuwa yanzu, tsofaffin gwamnoni  11 ne suka zama sanatoci, yayin da 14 suka yi takara basu ci ba a tsawon wannan shekaru 16 na dawowar dimokradiyya. Amma wannan bai sa majalisar dattawan ta canza zani daga zargin da ake yi mata na kasa yin aikin da ya dace ba. Maimakon haka ma, sai ƙara taɓarɓarewa da ta ke yi dalilin shigowarsu. A yanzu haka akwai tsofaffin gwamnoni guda 9 a zauren Majalisar Dattawa yayin kuma da adadin tsofaffin gwamnoni da kuma masu barin gado waɗanda suke takarar Sanata a jam’iyyu daban-daban ya kai 26.

Kwankwaso Ba Ya Kamfen;
Duk bayan waɗannan  dalilan, shi Kwankwaso da alama gani yake kamar dole ne ma a zaɓe shi Sanata. Me yiwuwa gani ya ke yi kamar cancantarsa, isarsa da ƙasaitarsa sun wadatar, ba sai ya fita kamfen ya nemi alfarma a gurin masu zaɓe ba. Wataƙila a tunaninsa nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamna su za su sa shi ya samu kujerar Sanata ba hamayya.
Abin da kwankwaso ya kasa ganewa shi ne dukkan aiyukan da ya yi, ba wai alfarma ko taimako ya yi wa mutane ba. Shi ya kawo kansa da ƙoƙon bararsa a hannu tare da manufofinsa akan ya na neman sahalewar mutane da su ɗauke shi aiki domin ya zamar musu gwamna, su kuma suka ba shi dama, ya yi ƙoƙarin da zai yi kuma mutane suka ce sun yaba masa. Saboda haka idan yanzu ya na neman su sahale masa ya zama Sanata, ai ba kwanciya zai yi ya dinga taƙama da aikin da ya yi musu a gwamna ba, fitowa zai sake yi da ƙoƙon bara a hannu da buɗaɗɗiyar murya kuma ba tare da wata taƙama ba, ya bayyana manufofinsa, yace ya na neman a ɗauke shi aikin wakilci na Sanata. Idan an ga ya dace, ya cancanta, sai a zaɓe shi.
Tunda da alama Kwankwaso gani ya ke yi kamar shi zai taimakawa mutane ko kuma aiyukansa na gwamna sun isheshi, ba sai ya yi kamfen ba, to ya kamata jama’ar Kano ta tsakiya su nuna masa kuskurensa ta hanyar ƙin zaɓar sa. Nan gaba idan ya shirya wa neman Sanatan, sai ya fito ya yi kamfen ya nuna musu cewar Sanata yake nema domin maganar gwamna ta riga ta wuce.

Lado Bai Gaza Ba;
Idan mutum ya na kan kujera, kuma wa’adinsa bai zo ƙarshe ba ko kuma ya na da sauran damar ci gaba, to ba hikima ba ne canza shi, matuƙar bai gaza ba. A dukkanin sanatocin da Kano ta tsakiya ta yi daga 1999 zuwa yanzu, da wahala a samu wanda ya taka rawar ganin da Lado ya taka tun daga kan Sanata Kura Muhammed, Sanata Rufa’i Sani Hanga da kuma Sanata Muhammad Bello.
Lado ya kawo ƙudururruka masu muhimmanci a majalisa kuma ya na bayar da gudunmawa dai-dai gwargwado. Bayan haka ya kawo manya da ƙananan aikace-aikace a ciki da wajen mazaɓarsa ta Kano ta tsakiya. Idan aka yi la’akari da cewar wannan shi ne zuwansa na farko, to ya kamata a yaba masa.
Matsalolin Sanata Lado guda biyu ne kacal; na farko manyan aiyukan da yake taƙama da su (titin gadar sama na Gyaɗi-Gyaɗi da kuma raba titin Kano zuwa Katsina) duk ba a kammalasu ba. Shi titin Kano zuwa Katsina ma kusan a ce ba a yi kashi ɗaya bisa hamsin na aikin ba duk da cewa shekara kusan ɗaya da rabi kenan da bayar da kwangilar aikin titin. Wasu daga cikin manyan aiyukan da yake faɗa ma kamar gadar sama a Shataletalen Miltara da kuma a Kurna Babban Layi, har yanzu babu wanda ya ga alamar farasu.
Matsalar Lado ta biyu ita ce tsarin kamfen ko yanayin yaƙin neman zaɓensa. Mutane da yawa suna yi masa kallon wanda ya birkice ya sukurkuce ya ke neman duk hanyar da zai bi kada kujerarsa ta suɓuce. Wannan ta saka shi yin wasu abubuwa da suka saɓa da al’adar yaƙin neman zaɓe, kamar rabon kayan miya da nama, rabon ruwan zafi a asibitoci, sallamar Lado da dai sauransu. Abin da ma aka fi ƙalubalantarsa da shi shi ne, bai tashi yin waɗannan abubuwa ba, sai da zaɓe ya matso.
To amma duk da haka, Lado sai ya fi Kwankwaso amfani nesa ba kusa ba a majalisa domin shi zai kwantar da kai ya yi biyayya ya nemo aiyuka. Zai yi shawara ya tattauna da ‘yan uwansa domin samun mafita ga mazaɓarsa, saɓanin Kwankwaso da ya saba shi a gurinsa ake neman alfarma da aiyukan. Bayan haka kuma, ana kyautata masa zaton zai yi ƙoƙarin matsa lamba don ganin an ƙarasa waɗannan aiyukan da ya nemo domin so yake ya bar tarihi tunda kusan a ce yanzu ya fara siyasa, shi kuwa Kwankwaso ya riga ya gama kafa tarihi, babu wani abu da ya ke buƙata ya yi a nan gaba.

Kwankwaso! Lokacin Zama Cikakken Dattijo Ya Yi;
Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yanzu haka shekaraunsa na haihuwa 60 ba kaɗan, kuma kullum burinsa a ce shi ne jagora, kowa  a ƙarƙashinsa ya ke. Dattijantaka ta kan ƙarawa jagoranci armashi; ita kuwa dattijantaka ba ta samuwa idan mutum kullum burinsa  a ce shi zai riƙe muƙami ko zai tsaya takara. A 1999 Marigayi Dakta Muhammad Abubukar Rimi da Malam Musa Gwadabe ba su fi shekaru sittin sittin ba, amma suka zama dattijai a siyasa. A lokacin suna da damar su tsaya kowwanne irin muƙami a Jihar Kano kuma su ci ba hammaya, amma maimakon haka sai suka ɗaurewa irinsu Kwankwaso gindi, a lokacin shi Kwankwason bai fi shekaru 42 zuwa 43 ba. Akwai lokacin da aka yi ta bai wa Rimi shawarar ya tsaya Sanata, amma yace shi ba zai tsaya ba tunda ga yaransa nan na siyasa birjik waɗanda za su iya aikin Sanata, bai kamata ya zama cinye-duk yace sai ya yi da kansa ba.
Kwankwaso ya ɗauko tafiya mai nisa, kuma an kawo gaɓar da zai zama dattijo a siyasar Jihar Kano. Duk wata kujera da ta ke da alaƙa da Kano, in dai ba ya zama dolen-dole ba, to a daina rububinsa da ita. Idan ya na so, ya iya ci gaba da takarar shugaban ƙasa domin ita wannan dama kujera ce ta dattijai kuma ƙwararru. Idan kuma ba haka ba, watarana sai ya wayi gari tsamo-tsamo ya na takarar kujera ɗaya da ya-ku-bayi irina.


© Malam Amir Abdulazeez 2015.
   


No comments:

Post a Comment