Fassara

Sunday, August 9, 2015

ZUMA, GA ZAƘI GA HARBI: Saƙon ‘Yan Jari Hujjar Nijeriya Zuwa Ga Janar Buhari

2 ga Maris, 2014



Daga: Musbahu Ahmad Chedi

B
ayan gasiuwa irin ta girmamawa. Muna matuƙar baƙin cikin bayyana maka cewa muna cikin ‘yan Najeriya wanda suke adawa da kai saboda kasancewarka mutum mai gaskiya da riƙon amana, kuma kai mutum ne wanda ba ya yin wuru-wuru a al’umurransa, sa’annan ga ka kaifi ɗaya, wato in ka ce “gabas”, to gabas ka ke nufi. A taƙaice ba ka yaudara a harkokin ka. Mu da ke adawa da kai muna yi ne saboda mun tabbatar in ka sami mulki za ka hana yin shagali da bushasha kamar yadda muka saba. A gaskiya ba za mubi shugaban da ba zai kiramu ba wajen kwasar ganimar dukiyar ‘yan Najeriya ba ta hanyar ƙasaitacciyar rashawa da cin hanci.
Tunda mun bayyana matsayinmu, muna so ka san cewa mun san yunƙurin da ya sanya ka shiga siyasa. Tunanin da ka ke yi na gyara matatun man fetur da muke da su ta yadda za su koma aiki gadan-gadan saboda a dakatar da shigo da man fetur daga waje wanda da mu da ‘yan uwanmu da abokanmu da surukanmu muke samun maƙudan kuɗaɗe, ba za mu amince da shi ba. Yin haka ya yi matuƙar saɓawa buƙatunmu duk da cewa hakan zai inganta rayuwar jama’ar Najeriya.’Yan Najeriya suna da wata daraja ne har ka ke ganin biyan buƙatarsu ya fi biyan buƙatar mu muhimmanci? To ka tabbata, ba za mu yafe maka ba in har ka cigaba da ɗaukar cewa biyan buƙatar waɗannan talakawa ya fi namu muhimmanci.
Janar Buhari! Muna gaya maka gaskiya, in kana so mu mara maka baya, to dole ne ka yi watsi da shirin gyara
matatun man fetur da muke da su in aka samu mulki. Tunda mu ne manyan dillalan shigo da man fetur wanda muke samun ƙazamar riba, sannan kar fa ka manta mu ma mun yi mulkinnan fa, mun ɗebi kuɗin talakawa mun je ƙasashen waje mun gina matatun man fetur, wanda muke kwasar ɗanyen man fetur ɗin Najeriya mu kai shi matatun man fetur ɗin mu na waje, sannan mu tace shi, mu sake dawo da shi Najeriya a sake saya da kuɗin talakawa. To a nan so ka ke ka kashemu, ka raya talakawa? Kai ma ka san duk yanda za mu yi, dole ne mu karya ka.
Mun fuskanci kullum maganganunka a kafafen yaɗa labarai da jaridu bai wuce tunaninka na samar da wadatacciyar wutar lantarki ba. Idan mutane irin ka suna kukan cewa ba wutar kantarki, wai me kake nufi? Kana nufin ba ka ganin turakun wutar lantarki da aka kafa da wayoyi da suke ɗauke da duhu dare da rana? Saboda me ka ke tsammanin an sanya waɗannan abubuwa in ba domin su kai duhu zuwa gidajen jama’a ba?
Yallaɓai, muna son mu ba ka shawara. A matsayinmu na dilolin injinan bayar da hasken wutar lantarki, kuma masu ɗaurin gindi a sama, ba za mu ƙyale wutar lantarki ta daina sanya Najeriya cikin duhu ba. Haƙiƙa waɗannan maganganu da ka ke yi suna barazana ga hanyar samun kuɗaɗenmu, kuma kana sanya ran kar mu yi maka murɗiyar zaɓe? Ai mu ba mahaukata ba ne da za mu kyale mutumin da zai tauye mu daga samun biyan buƙatun ƙashin kanmu ba ya kai ga karagar mulki. Babu inda aka taɓa yin haka, kuma ba za mu kasance na farko da za mu yi haka ba.
Yallaɓai, sai shirinka na yaƙi de cin hanci da rashawa da ya ke matuƙar barazana ga hanyoyin samun kuɗaɗen mu da yin bushasha. Ko kana son ka gama da mu ne? To ta yaya ba za mu murƙushe ka ba ta hanyar yin amfani da cin hanci da rashawa da amfani da kuma kuɗaɗen haram? Yaya za a yi mu rayu in babu cin hanci da rashawa? Cin hanci da rashawa su ne hanyoyi mafi sauƙi da kyau wajen samun shugabanci a Najeriya. Saboda haka duk wanda ya fito ya na  yaƙi da cin hanci da rashawa, shi ne babban maƙiyinmu kuma za mu yi duk abin da zai yiwu domin gamawa da shi. Muddin ka yi ƙoƙarin kashe cin hanci da rashawa, za mu gama da kai domin ta hanyarsu ne kawai mu ke iya rayuwa, kuma mu yi rawar gaban hantsi. Kar ka manta cewa mu ma da Janar ɗinmu, ko Janar Janar masu ɗumbin yawa da ƙarfi.Yaya za ka ce za ka yaƙi cin hanci da rashawa gaba da gaba? Bayan duk wanda ya ɗaura ɗamarar yaƙi da cin hanci da rashawa sun gama da su, kuma kai ma za su gama da kai. In kana son kanka da arziki, ka fita daga wannan harka ta neman yaƙi da cin hanci da rashawa.
A gaskiya kana neman mai bayar da sharawa game da yadda za ka riƙa haɗa kai da azzalumai, maimakon jayayya da su. Idan baka san yanda za ka bunƙasa ayyukan ɓarna ba, to ka koma gonarka da ke Daura ka riƙa kulawa da tumaki da awakinka. Bunƙasa ayyukan ɓarna abin alfahari ne, kuma dole ka amince da su in kana so ka samu karɓuwa a harkokin siyasar Najeriya. Kana maganar halayen kirki da tsare gaskiya, to su za mu ci? Ai mun sha gaya maka cewa kuskure ne ka zama mutumin kirki. Rashin tsare gaskiya ya na taimaka mana wajen samun abubuwa ta hanyar cin hanci da rashawa. Baka ga yadda halayen kirci suka ɓata nasarar da ka samu ba, suke miƙata ga wasu? Mugayen halaye suna da rana kamar nasara wani sa’annan kuma a miƙata ga wanda ba tasa ba ce. To ya kamata ka rungumi miyagun halaye domin zubar da mutuncinka, kuma ka samu ɗaukaka a harkar siyasarka.Wannan gaskiyar da ka ke taƙama da ita ba za ta taimaka maka ba,kamar yadda bata taɓa tamakakon ka ba. Gakiya laifi ce a Najeriya wadda hukucin ta shi ne faɗuwa zaɓe ta hanyar amfani da cuta da zamba da zalunci.Ya kamata ka hardace wannan bayani domin ka samu inganci a harkokin siyasarka a nan gaba.
Yallaɓai, in kana son mu yarda da kai kuma mu goya maka baya a nan gaba, to ka daina maganar ɗauka wutar lantarki, ƙarancin man fetur, rashawa da cin hanci, rashin tsaro, fatara da talauci, gazawar gwamnati, rashin aikin yi ga matasa, tashe-tashen hankula a yankunan Arewa maso gabas da Niger Delta da dai sauransu da wani muhimmanci. Ba mu buƙatar rabuwa da waɗannan abubuwa. In kuma ka nace akai lallai sai ka ci gaba da yaƙi da su, to za mu ci gaba da amfani da akwatunan zaɓe domin murɗe ka. A jimlace, ba za mu amince da wannan kyakkyawan shiri naka ba. Kaji ko?
Musbahu Ahmad Chedi

08034549599

No comments:

Post a Comment