26 GaMaris, 2014.
Daga: Amir Abdulazeez
S
|
au tari mutum shi ya kan yi wa kansa
mummunar illa ko dai yana sane da gangan ko kuma ba ya sane cikin
jahilci. Domin kuwa duk abin da ka ke yi a kowanne lokaci ya na da gagarumin
tasiri a kan duk abin da zai sameka a yanzu ko kuma a wasu shekaru masu zuwa.
Lokacin da masu ruwa da tsakin tsohuwar jam’iyyar PDP Kwankwasiyya suka
dinga zagayawa mazaɓun ƙaramar hukumar Dawakin-tofa suna tara mutane tare da
neman goyon bayansu ta hanyar bayyana musu irin zalunci da kama karyar da uwar
jam’iyyarsu ta PDP ta ƙasa a wancan lokaci ta ke yi musu tare da jagororinsu,
da yawa daga cikin jama’a sun ɗauka da gaske suke yi, gyara suke nema.
A lokacin wannan zagaye, al’ummar Dawakin-tofa sun kasu kashi uku. Kashin farko
sun amince da maganganun waɗannan mutane saboda tsananin ƙiyayayrsu ga PDP a ƙarƙashin
jagorancin Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan. Wasu kuma sun amince tare da amanna
da su saboda ganin girma da darajar Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da
Mataimakinsa Dakta Abdullahi Ganduje.
Kashi na biyu sune wadanda kwata-kwata basu amince da maganganun waɗannan mutane ba domin sun san dama ce kawai ta suɓuce
daga hannunsu da kuma jagororinsu saboda lokacin da damar jagorancin PDP ɗin ya
ke hannunsu ai ba a ji kansu ba. Domin haka a yanzu suna so su yi amfani da
wannan dama don su yaudari mutane.
Kashi na uku sune wadanda suka tsaya a tsakiya, su basu gaskata ba, su basu
ƙaryata ba, illa dai kawai sun zuba musu ido da zummar cewa lokaci shi zai nuna
gaskiyar komai. Ga shi kuma lokacin ya fara nunawa.
Tun ba yau ba, ni ina ganin cewa mafi yawan ‘yan siyasa kusan duk halinsu ɗaya
wato son zuciya da kuma kokarin kama karya ta hanyar ƙarfa-ƙarfa da handame
dukkan wata dama. Don haka ina daga cikin wadanda suke da matuƙar shakku akan APC tun daga sama har ƙasa. Kowa ya riga ya san
ita PDP azzaluma ce gar da gar wani lokacin ma ko ɓoyewa ba ta yi, amma ita
kuwa APC munafuka ce wacce ta ke nuna adalci a fili amma zalunci a ɓoye. Ko
kuma ta yi adalci akan abu mara tasiri kamar jin ra’ayoyin mutane misali amma kuma ta yi zalunci akan abu mai
matuƙar tasiri kamar fidda ‘yan takara.
Duk da wannan tunani nawa, kullum addu’a na ke yi, Allah SWT Ya sa kada ya zama gaskiya. Allah
Ya sa APC ta bai wa wannan tunani nawa kunya ta hanyar yin gaskiya da adalci,
amma kash! Hakan ba ta samu ba.
A karamar hukuma ta ta Dawakin-tofa, Kwankwasiyya ta karɓe ragamar
jagorancin APC ta danne sauran jam’iyyu, kai ka ce ACN, CPC, ANPP su suka shigo
suka samu Kwankwasiyyar a cikin APC ba
wai Kwankasiyyar ce ta shiga ta same su ba.
Jagorancin APC a hannun Kwankwasiyya
a Dawakin-tofa ba shi ne abin damuwa ba, domin dama a siyasa mai ƙarfi, mulki,
kuɗi da jama’a ai shi ne da jagoranci. To amma kama karya mai kama da rainin
hankali da ake yi a wajen fidda ‘yan takarkarin shugabancin karamar hukuma da kansiloli
ita ce abar damuwa.
Abin sai ka ce wasan yara, wai an kafa an tsare, dole sai ‘yan Kwankwasiyya
ne za su yi takarar kansiloli ko ana sonsu ko ba a sonsu. Kuma a cikin ‘yan Kwankwasiyyar
ma sai shafaffu da mai. Wannan katoɓara ce ba ƙarama ba.
Tun farko da an san wannan tsarin za a yi, da ba sai an wahalar da mutane
ta hanyar yaudararsu cewa su fito takara dimokraɗiyya da adalci za a yi ba. Ashe
duk maganar adalci, haɗin kai, dimokradiyya, ci gaba da kyautatawa da suke yi
ashe duk yaudara suke wa mutane?
Ita kuma jam’iyyar ANPP ta Dawakin-tofa wacce za ta ɗan iya taɓuka wani abu
na gyara akan wannan lamari, ta samu kanta a ƙarƙashin jagorancin mutane marasa
kishi wadanda buƙatar kansu ce kawai a gabansu.
Idan kana takarar kansila, dole sai an sa ka ka janye ta ƙarfin tsiya ko baka
so ta hanyar baka tsoro da yi maka barazana. Idan kuma ka ƙi sai a shirya wani
haramtaccen zaɓe a kada kai. Shin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ba ‘yar
tinƙe yace a yi ba ne idan sulhu bai yiwu ba?
Masu yin wannan kama karya su tuna cewa fa kafin su, dubannan mutane sun
samu wannan dama kuma yau ba ta hannun su sannan bayansu kuma damar za ta koma
hannun wasu. Su tuna kama karyar da ANPP ta yi a zaɓen kananan hukumomi na
2007, yau ina ANPP? Ta tarwatse kuma ta wulaƙanta. Itama PDP duk wannan
zaluncin da ta ke yi a Najeriya, za ta tarwatse a kan idonmu inshaAllah, domin
Allah ba Ya barin masu kama karya, sai dai ya jinkirta musu kawai. Suma ANPP ɗin
yana sonsu da shiriya shi ya sa ya koya musu hankali tun da wuri.
Na san ‘yan Kwankwasiyya suna ganin za su ci zaɓe ko ana so ko ba a so.
Wannan gaskiya ne, to amma su tuna mai zai je ya zo, ba wai yanzu ba, a’a
watarana.
Ya kamata wannan katoɓarar da APC take yi a Dawakin-tofa da sauran kananan
hukumomin Jihar Kano su daina. Idan kuma ba za su iya dainawa ba to su rage
domin aƙalla abin ya ɗan dace da hankali domin yanzu abin ya yi muni da yawa.
Allah ya kyauta.
© Malam Amir Abdulazeez 2014.
No comments:
Post a Comment