Fassara

Sunday, August 9, 2015

Guguwar Sauyin Sheƙar Jam’iyyu A Siyasar Najeriya

10 Ga Fabrairu, 2014

Daga: Amir Abdulazeez

“A siyasa, wawanci ba naƙasa ba ne.” - Napoleon Bonaparte (1769-1821)

T
un daga lokacin da guguwar sauyin sheƙar jam’iyyu ta fara kaɗawa a siyasar Najeriya, musamman a tsakanin manyan mutane ma su faɗa a ji a ƙasar nan, har yanzu ba a yi wani abu da ya ba ni mamaki ko haushi ba. Wataƙila sai dai mutum ya ce ya ga abubuwan da suka ba shi dariya ko kunya iri-iri, to amma in dai wanda ya saba da siyasar Najeriya ne sosai kuma ya san alƙiblar ta a yanzu, to abin kunyar ma sai ya ce shi bai gani ba. Domin kuwa a siyasar Najeriya, dan ka sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa wata sau ɗari, ba wani abin kunya ba ne a wajen ma’abota siyasar ƙasarnan. Babu wata jam’iyyar da na ke tunanin za ta ce ba za ta karɓe ka ba wai kawai don ka cika sauya sheƙa. Ko kuma hakan za ta fara faruwa a nan gaba, ba mu sani ba?

Tun daga kan komawar gwamnonin PDP biyar da kuma sanatoci 11 da ‘yan majalisun PDP 37 da kuma komawar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar cikin jam’iyyar APC  zuwa komawar Shekarau da Bafarawa cikin jam’iyyar PDP, ba na tsammanin mai yin nazari a kan al’amuran siyasar ƙasar nan, zai ce wai an yi wani abu da ya ɗaure ma sa kai. Idan kuma har kanka ya ɗaure, to ko dai ba ka fahimci siyasar Najeriya ba ko kuma ba ka da labarin lalacewar siyasa a wannan jamhuriya da mu ke ciki.

Dalilin hakan kuwa, lissafi ne mai sauƙin ganewa. Duk inda wani mai faɗa a ji ya hanga ya ga ba zai iya sarrafa jam’iyyar da ya ke ciki ko ya sarrafa shugabancinta ba don cimma buƙatunsa, to shike nan babu sauran zaman lafiya. Idan kuma irin wannan dama a hannunsa ta ke kuma ta koma wajen waninsa, to shikenan an yi masa ba dai-dai ba. Ya kamata mu ƙalubalanci dukkan jiga-jigan mutane na kowacce jam’iyya waɗanda su ka sauya sheƙa a kwanannan, lokacin da dama ta ke hannunsu, shin ba su yi abin da ya ninka wanda a ka yi musu muni ba? Sun sauya sheƙa ne saboda damar sakawa da hanawa a cikin jam’iyya ta koma hannun wasu.

Duk lokacin da ka ji wani babba a ƙasar nan ya na tayar da jijiyar wuyan cewa ba zai bar jam’iyya kaza ba har abada ko kuma ba zai taba shiga jam’iyya kaza ba ko da zai rage saura shi kaɗai ko kuma ya ce ba zai taɓa haɗa jam’iyya ɗaya da su wane ba, to ka saurare shi kawai amma da zarar ya ga za a hana shi rawar gaban hantsi ko ya ga wata buƙata ta ratso, to a cikin  lokacin ƙankani zai ƙaryata kansa da kansa.

Kullum manyan ƙasar nan su na ce mana wai ai sauya sheƙa a dimokraɗiyya ci gaba ne ko kuma su kafa hujjar an ɓata mu su. To in dai da zarar an ɓata maka ko an yi maka rashin adalci a jam’iyyarka, babu wata mafita banda ka fice, to da ba za ka yi jam’iyya ko ɗaya ba a Najeriya. Domin kuwa duk Najeriya babu jam’iyya ɗaya tak wacce ta ke bin tsarin shimfiɗaɗɗun dokokin da ta ƙirƙiro wa kan ta da kan ta balle ma ta bi shimfiɗaɗɗun ƙa’idojin dimokraɗiyya da dokokin siyasa da aka yarda da su a duniya baki ɗaya. Haka zalika, in dai ficewa daga jam’iyya shi ne kaɗai masalaha idan ka na ganin an maka rashin adalci, to da sannu mutum sai ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyu daban-daban sau ba iyaka, wataƙila sai mutum ya wayi gari babu jam’iyyar da bai taɓa yi ba a Najeriya. Ko kai da abokinka ko ɗanka kaɗai za ku yi jam’iyya, to watarana sai ya yi maka abin da babu wata mafita banda ka yi haƙuri, ka yafe kuma ka tara gaba tare da ƙudurcewa a zuciyarka cewa kai ma babu mamaki za ka yi masa abin da dole ya yi haƙuri da kai.

Ai idan mutum siyasa zai yi da  gaske, don aƙida, don jarumta, don ceto talakawa, don cimma manufa kuma uwa uba don Allah, to sai ya zauna ya ƙwato wa jama’a ‘yanci komai wahala a inda aka ɓata masa ko aka yi masa rashin adalci, ba gajiyawa kuma ba ja da baya. Amma ficewa daga jam’iyya ai alama ce ta tsorata da rauni da kuma cewa an fi ƙarfinka ko an yi rinjaye a kanka.
A yanzu dai manyan ƙasarnan su na ta cin karensu ba babbaka ta hanyar sauya jam’iyyu kamar yadda suke sauya riguna yadda ransu ya ke so, wani ma idan ka ji dalilinsa na sauya sheƙar sai abin ya ba ka dariya. To abin tambaya a nan shi ne, menene makomar ‘yan a bi yarima a sha kiɗa?

Su dai manyan, mun fahimci dalilansu, ko da kuwa sun faɗa mana wani abin daban, aiyukansu su na ƙaryata abin da suka faɗa. Waɗanda ba mu san dalilinsu ba, su ne ma su bin manyan a gindi a gindi wai da sunan biyayya kuma su na kiran kansu ‘yan siyasa? Mutumin da ka ke yi wa kallon babba ko jagora, sai aka ce ya sauya jam’iyya bisa wani laifi da ya ke ganin jam’iyyarsa ta yi masa, su kuma ma su bin su riii duk inda suka nufa, su kuma mecece hujjarsu? Tun da dai waɗannan manya ba irin jagoranci makaho da ɗan jagora suke mu su ba, a’a jagoranci ne tsakanin mai ido da mai ido, to mai zai sa mutum kawai ya ja ka wata jam’iyyar da ranka da tunaninka ba sa so? Ko da za ka sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya, to ka tabbata ka na da dalili, hujja da manufa amma ba wai kawai don wani mutum ya sauya ba.

Yanzu misali, kwanannan sanatan Kano ta tsakiya Bashir Lado ya yi ta godiya a rediyo bisa aikace-aikace da Gwamnatin Tarayya ta yi a mazaɓarsa da jiharsa gabaɗaya, to ka ga shi a nan PDP ta kyautata masa, ba ta yi masa laifin komai ba. Ko kuma kawai saboda Kwankwaso ya koma APC, shi ma dole ne ya koma?

Misali, Wammako a cikin PDP ya samu mataimakinsa Mukhtari Shagari, yanzu don shi Wammako ya ɓata da PDP ya fice daga cikin ta, Mukhtari Shagari sai ya ce a dole shi ma an ɓata da shi?
Wani misalin kuma shi ne, shekarar su Kawu Sumaila kusan 10, jam’iyyar PDP ta na gana mu su azaba a majalisar wakilai saboda rashin rinjayen da suke da shi har Allah Ya kawomu wannan lokaci da jam’iyyarsu ta adawa ta APC ta kawo ƙarfi inda suka fara samun ‘yancin kansu tare da sararawa. To kawai yanzu sai Kawu ya saki wannan ni’ima ya bi Shekarau PDP? Dan APC ta yi wa Shekarau laifi, shi ma Kawu sai ya ce dole bara ya koma cikin waɗanda suka dinga azabtar da shi kawai saboda tsananin biyayya ga Shekarau?

Idan ka koma can ƙasa, yanzu a unguwarku an fi son jam’iyyar PDM misali, kuma idan ka tsaya takarar kansila a ƙarƙashin PDM, akwai kyakkyawan zaton za ka ci zaɓe saboda farin jinin ta. Kawai dan wanda ka ke wa kallon jagora ya bar PDM, kai sai ka bar ta?
Ma su bin manya duk jam’iyyar da suka shiga su na tare da wahala domin akwai jam’iyyar da wani zai koma, shi alkhairi ce a gare shi amma kai idan ka koma sharri ce a gareka. To, saboda ka cika cikakken wawa, mai yin biyayyar wuce ƙa’ida sai ka kai kanka cikin sharri ka na sane?

Idan ka na tare da wani babban mutum a siyasance kuma ka na girmamashi, idan ya zo zai canza jam’iyya sai ka yi tunani mai zurfi. Idan binsa alkhairine a gareka da kuma kyawawan manufofinka da na jama’arka, to sai ka bi shi, idan ya gayyace ka. Idan kuma akasin haka ne, to ka yi masa bankwana a siyasance amma ka ci gaba da ba shi girmansa a matsayinsa na babba.

© Malam Amir Abdulazeez 2013.

            

No comments:

Post a Comment