02 Ga Fabrairu, 2015
L
|
okacin da
al’ummar Najeriya suka kaɗa ƙuri’a a zaɓukan shekarar 1999, mafi yawa daga
cikin mutane, buƙatarsu ba ta wuce mulki ya komo gurin farar hula ba. Su kansu
jam’iyyu a wannan lokaci an kafa su ne a gaggauce duk da yake dai wasu daga
cikinsu gyauron jam’iyyu guda biyar na lokacin Marigayi Abacha ne, kuma idan aka
ɗauke ɗaiɗaikun wasu muhimman ‘yan siyasa da ke cikin wasu jam’iyyun, kusan
babu wani ma’auni abin dogara da za a iya amfani da shi wajen bambance
jam’iyyun ta fuskar kyawawan manufofi ko rashinsu. Kodayake jam’iyyun Najeriya
ba a sansu a kan wata tartibiyar alƙibla ko wasu manufofi na musamman ba, sai
dai ba a rasa su da ‘yan ƙudurce-ƙudurce a rubuce, amma ba lallai a aikace ba.
Me yiwuwa a
wancan lokaci, PDP ta fi kowacce jam’iyya ƙarfi ne sakamakon yawan gogaggun
‘yan siyasar Najeriya da suka tattaru a cikin ta, ko kuma saboda gudunmawa ta
bayan fage da gwamnatin sojoji ta wancan lokaci ake zargin ta na bai wa jam’iyyar,
ko kuma saboda dalilai biyun baki ɗaya. Tunanin wannan goyon baya na gwamnatin
sojoji ga PDP, wataƙila ya wanzu ne daga bayyanar buƙatar masu madafan iko na
wancan lokaci a fili na ganin sun samar da ƙwaƙƙawar jam’iyya don cimma burinsu
na dawo da Obasanjo a matsayin Shugaban ƙasa. Kodayake jama’ar Najeriya da dama
sun zaɓi Obasanjo domin kyautata zaton da suke yi a gareshi, amma wa ya sani ko
cewa da ba wancan goyon baya na gwamnati, Olu Falae wanda ya tsaya wa APP/AD
takara, zai iya kayar da shi?
Kasancewar mun ɗauki
lokaci mai tsawo a ƙarƙashin mulkin sojoji kuma mun ratso ta lokuta daban-daban
na saɓa alƙawuran bai wa fararen hula damar mulki daga su sojojin, sai ya
zamana mun shigo tsarin dimokraɗiyya a wannan jamhuriyya ta huɗu a matsayin masu
lalube cikin duhu, a matsayin marasa tabbas ɗin mai gaba za ta haifar, a
matsayin waɗanda basu damu da tsarin sosai ba, sannan kuma a matsayin waɗanda
suke tsoron shiga a dama da su. Wannan ya na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa
muka samu kanmu a wasu daga cikin matsalolin da muke fama da su a yanzu. Alal
misali, a shekarar 1999, mutane da yawa masu kishi, cancanta da nagarta a
matakai daban-daban duk sai suka ƙi tsayawa zaɓuka, don tunanin cewa harkar ba
za ta ɗore ba. Sakamakon haka, wasu ‘yan tamore da a-ci-bulus, marasa kishi da
masu neman kuɗi da yawa suka samu dama suka shiga zaɓuka kuma suka kama madafan
iko, suka tara kuɗaɗe, suka fi ƙarfin kowa kuma har kawo yanzu madafun iko na hannunsu da kuma hannun ‘yan
korensu. Abin takaici, sai a shekarar 2003 da 2007 waɗancan nagartattun mutane
da suka ƙyamaci tsarin a 1999 suka dawo su na son damar ruwa a jallo a lokacin
da kuma ta fi ƙarfinsu. Har kawo yanzu, ƙalilan daga cikin irin waɗannan mutane
ne suka samu damar banƙarawa suka shiga tsarin, a dai-dai lokacin da kuma ɓarnar
da aka tafka ta yi munin da gyaran nasu bai yi wani tasirin a-zo-a-gani ba. Kai
hasali ma, su ma ɓarnar ta mamayesu, sai ‘yan kaɗan waɗanda ko ɗuriyarsu ba a
iya ji.
Haƙiƙa abubuwa
da yawa sun gudana daga 1999 zuwa 2015, waɗanda dukkan ‘yan Najeriya sun koyi
darussa a siyasance, ta yadda kusan kowa yanzu kansa a waye ya ke, kuma idonsa
a buɗe ya ke, sai dai wanda ba ya bibiyar al’amura, ko kuma ya na bibiya amma
bai damu da al’amuran ba, sai kuma ɗan abin da ba a rasa ba.
Wannan zaɓe na
2015 lalube ne, amma kuma a cikin haske domin kuwa a tsawon shekaru 16 da suka
gabata, kusan babu wani ɗan siyasa tun daga sama har ƙasa da jama’a basu ga
kamun ludayinsa ko kuma basu fahimci manufofi da aƙidunsa ba. Sannan ga
sababbin ‘yan takara, waɗanda wannan kusan shi ne karo na farko da suka shigo
harkar siyasa, zai yi wahala a ce mutane basu san wani muhimmin abu na rayuwar
aikinsu, mu’amalarsu ko gwagwarmayarsu ba, wacce za ta basu damar yin alƙalanci
a kansu. Babu wani salon ƙarya, yaudara, makirci, sata, yarfe, cuta, danniya da
rainin hankali da talakawa basu gani ba a tsawon wannan shekaru 16 na dimokraɗiyya
a Najeriya ba. Kawo yanzu ya kamata a ce za mu iya bambance tsakanin ɓarayi da masu
amana, maƙaryata da masu cika magana, masu bautawa talakawa da masu bautar da
su da dai sauransu. Ashe kenan mutane ya kamata su je gindin akwatunan zaɓe da
cikakkiyar masaniya da fahimta a kan kowa da kuma komai kuma ya kasance sun
tanadi irin alƙalancin da ya kamata su yi. Wanda kuma ya yanke shawarar ya zaɓi
rashin cancanta da gangan ko a bisa dalilai na son zuciya, ya ci amanar kansa,
iyalinsa da al’umma kuma ya na daga kan gaba a cikin waɗanda za su girbi abin
da ya shuka.
Duk da cewa mun
riga mun san inda muka dosa a wannan tafiya, amma akwai buƙatar mu yi la’akari
da wasu abubuwa kafin ranar zaɓe mai zuwa nan da ‘yan kwanaki kaɗan ababen
ƙirgawa.
Muhimmin abu na
farko da ya kamata mu kiyaye shi ne bambancin ‘yan siyasa da kuma masu zaɓe. Ɗan
siyasa shi ne wanda ya ke da jam’iyya kuma ya ke mata aiki tuƙuru don ganin ta samu nasara. Ya yarda da
ita ɗari bisa ɗari, walau ya fahimci manufofin ta da aƙidun ta ko bai fahimta
ba, sannan a shirye ya ke ya kare su, shi a gurinsa babu wanda ya kamata a zaɓa
sai ɗan jam’iyyarsa, komai rashin cancantarsa kuma kowa bai cancanta ba in dai
ba a jam’iyyarsa ya ke ba. Wasu ‘yan siyasar sun ɗauke ta a matsayin cikakkiyar
sana’a wasu kuma a matsayin sana’a ta wucin gadi, wasu ma da ita suke samun kuɗi,
wasu kuwa su na yin ta gadan-gadan amma su na da hanyar neman kuɗinsu daban.
Kullum burin ɗan siyasa shi ne jam’iyyarsa ta samu mulki ba lallai wai don ta
taimaki talakawa kawai ba, a’a saboda zai samu wata dama ta kuɗi ko mulki ko kuma
ta ɗaguwar dajararsa ko kuma wani abun da shi ya bar wa kansa sani. Ba duka
‘yan siyasa ba ne, ci gaban ƙasa ya dame su sosai ba. Irin waɗannan mutane ‘yan
siyasa basu wuce 1% na yawan al’ummar ƙasa ko yawan waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a
ba, sai dai kuma a siyasarmu ta Najeriya, su na da gagarumin tasiri a kan
ragowar 99% ɗin da sune masu zaɓe.
Shi kuwa mai kaɗa
ƙuri’a ko mai zaɓe, ɗan ƙasa ne kawai wanda ya cika ƙa’idojin Hukumar Zaɓe da za su ba shi dama a yi masa rajista domin
kaɗa ƙuri’a. Mafi yawan masu zaɓe talakawa ne, marasa gata kuma sune aiyukan shugabanni
masu kyau da marasa kyau ya ke shafa kai tsaye. A kan samu mai zaɓe ya kasance
ya na da ra’ayin wata jam’iyya a ransa amma ba za a kirashi ɗan siyasa ba domin
ba zai iya sakawa ko ya hana ba a kowanne irin mataki a cikin jam’iyyar kuma
daga nesa ya ke kallon ta. Mai yiwuwa bai ma san manufofin ta ko shugabannin ta
ba, kai ba ma ya daga cikin waɗanda za a tuntuɓa idan wata sabgar jam’iyyar ta
taso.
‘Yan siyasa da
bazar masu zaɓe suke rawa, shi ya sa burin mafi yawa daga cikinsu shi ne su ga
mai zaɓe a cikin duhun kai ta yadda komai suka faɗa masa zai yi aiki da shi ba
tare da lissafi ba. ‘Yan siyasa suna shiga kafafen yaɗa labarai suna cewar wai
a zaɓi jam’iyyarsu tun daga sama har ƙasa. Wannan son zuciya ne, domin a
zahirin gaskiya ba shi ne mafi alkhairi ga talakawa ba. Jam’iyyun Najeriya duk ɗaya
suke, a yau mutum zai fita daga wata jam’iyya ya koma wata, gobe ko jibi ka ji
shi a cikin wata. Idan muka kalli dukkan ‘yan APC da PDP sai mu ga cewa mutane
ne da suka sha canja sheƙa kusan sau ba iyaka. Misali, a cikin gaggan ‘yan
siyasar Najeriya na ƙoli a yanzu, Janar Buhari da Bola Tinubu ne kaɗai basu taɓa
yin jam’iyyar PDP ba, sai wasu ‘yan tsirarun gwamnoni da sauransu. To kuwa a kan
wane dalili za a ce mai zaɓe ya zaɓi jam’iyya, tun da jam’iyyun ba su da
manufofi, asali ma a mafi yawan lokuta, ƙarfa-ƙarfa suke yi wajen tsayar
da ‘yan takarkarinsu?
Abin da ya
kamata masu zaɓe su yi shi ne, su kalli kowanne mataki, su auna mutanen da suke
takara a wannan matakin, sai su zaɓi wanda suka fi kyautatawa zato a cikinsu. Shi
kuwa ɗan siyasa ko ɗan jam'iyya mu ƙyale shi can ya je ya zaɓi jam’iyyarsa daga
sama zuwa ƙasan domin shi zai ci moriyar hakan amma ba mu ba. Wani abin
kiyayewa shi ne, kada mai zaɓe ya ce wai sai waɗanda suka tsaya zaɓe a babbar
jam’iyya kamar APC ko PDP ne kaɗai ‘yan takara, a’a komai ƙanƙantar jam’iyya,
in dai mutumin cikin ta, shi ya fi cancanta, to a ba shi ƙuri’a. Raja’a da muka
yi a kan APC da PDP, shi ya sa suke yin cin kashin da suka ga dama, domin su na
ganin kamar mai zaɓe ba shi da wani zaɓi sai su. Kullum muna kokawa da yadda
jam’iyyu suke ƙaƙaba ‘yan takara amma kuma mun kasa yin maganinsu duk kuwa da
cewa mu ne masu zaɓe. Mai zai hana mu zaɓi ɗan PDM ko APGA a inda APC da PDP
suka yi mana ƙarfa-ƙarfa? Wataƙila hakan ya koya mu su hankali, su kiyayi gaba.
Daga 2003 zuwa
yanzu, akwai gagarumar matsalar maguɗin zaɓe da ta ke damun siyasar mu kuma da
alama mun kasa maganin ta duk kuwa da cewa da akwai matakan da za mu iya ɗauka.
Dukkanmu mun sani cewa ba zaɓen gaskiya aka yi a 2003, 2007 da 2011 ba. Idan
masu zaɓe suka ci gaba da zura idanu, to fa haka za a ci gaba. Kasancewar mun
bar komai a hannun ‘yan siyasa, mun kalmashe hannuwanmu mun koma gefe, shi ya
sa muka kasa kawo ƙarshen wannan matsala. Mu a ganinmu idan aka yi wa wanda
muka zaɓa maguɗi, to shi abin ya shafa, haƙƙin sa ne ya tafi kotu, mu ba
ruwanmu, wani lokacin ma waɗanda za su yi masa shaida a kotunma, sai ya biyasu.
Ko kuma idan ‘yan siyasa su na kawo ruɗani a gaban akwatin zaɓe, to a gurinmu su
ta shafa, mun manta cewar ƙuri’inmu ne a cikin akwatin, kuma ƙuri’ar mu ita ce
‘yancinmu wacce a dalilin ta muka bar duk abin da muke yi, muka bi dogayen
layuka na tsawon lokaci a cikin rana don mu tabbatar mun bayyana ra’ayinmu. Ya
zama wajibi a kanmu, a kowanne akwatin zaɓe,
a kafa kwamitin amintattu wanda ba ‘yan siyasa ba, waɗanda za su zagaya
cikin garuruwa da unguwanni ba wai don su tallata wata jam’iyya ba, a’a sai don
su faɗakar da mutane a kan muhimmanci zaɓe da fitowa zaɓen, nemo katin zaɓe a
kawo shi kusa ba sai ranar zaɓe ba, koyar da yadda ake kaɗa ƙuri’a domin kada a
lalata takardar ƙuri’a, bayar da shawarwari da muhimman bayanai a kan muƙamai
daban-daban da alhakin da ke kansu, bayanai a kan kowanne ɗan takara da dai
sauransu.
Amma abin
takaici, mafi yawa ba ma yin wannan, maimakon haka wai sai mu bar ‘yan siyasa da
masu zaɓe, su yi ta yi mu su ƙarya kuma su ne wai a gindin akwati, su za su ƙirga
ƙuri’a kuma su za su ɗauki akawatin tare da malaman zaɓe su tafi ofishin zaɓe,
sai abin da suka ga dama. Kamata ya yi a ce akwai wakilin wannan kwamitin
amintattu mutum ɗaya ko biyu a cikin tsarin wanda za su sa ido, a ɗauki bayanai,
hotuna da bidiyo kuma a shirya duk wasu hujjoji sannan a kafa shaidu ko da za
su ji an faɗi wani sakamako ba dai-dai ba. A yi irin wannan tsari a matakin
akwatuna, mazaɓu da ƙananan hukumomi. To amma mu kowa gani ya ke siyasa wata ƙazamar
aba ce, ko kuma shi mai mutunci ne bay a son shiga rigima ko kuma ba ya so a
zage shi, amma kuma a gefe ɗaya so ya ke yi a samu gyara, ko da yaya za a samu
gyaran?
Akwai buƙatar mu
fahimci cewa rigima, tayar da zaune tsaye, ko tashin hankali da lalata dukiyar
gwamnati kafin, a lokacin da kuma bayan zaɓe, ba zai taimaki ɗan takarar mu ba
balle kuma mu kanmu. Duk da cewa mafi yawancin masu tayar da rigimar ba masu
nutsuwa bane, wasu ma ‘yan iskan gari ne, to amma haƙƙin mu ne mu hanasu, ba wai
mu goya musu baya ko mu ji daɗin abin da suke yi ba. Akwai hanyoyi halatattu da
za mu nuna rashin amincewar mu da sakamakon zaɓe kuma in dai mun haɗa kai mun
jajirce mun daure kuma mun cire kwaɗayi da tsoro, babu wanda ya isa ya mulke mu
a wannan lokaci ta hanyar haramtaccen zaɓe.
‘Yan siyasa suna
yaudarar jama’a da addini a lokacin zaɓe domin su samu ƙuri’a. Abin haushi, su
kansu mafi yawancin ‘yan siyasar ba su damu da addinin ba ko dai a aƙidance ko
a aikace, sai zaɓe ya zo tukunna, kuma idan sun samu damar, babu wani taimako da suke yi wa addinin sai
dai kawai su yi amfani da shi don cimma burinsu. Idan aka tsayar da Musulmi a wata
jam’iyya, sai ɗan siyasa yace maka ai ka zaɓi jam’iyyar domin ita ce ta Addinin
Musulunci, idan kuma aka tsayar da wanda ba Musulmi ba sai ka ji ya na ce maka,
ai mataimakinsa Musulmi ne, ko kuma yace da kai ai siyasa ba ruwan ta da addini.
A can sama kuma Musulmin da waɗanda ba Musulmin ba sun haɗe kai suna ta lalata ƙasa.
Ya kamata mai zaɓe ya san cewa wannan babbar yaudara ce ba ƙarama ba. Ya kamata
mu duba waɗanda suka cancanta, mu zaɓe su kuma mu tilasta mu su su kyautata
rayuwarmu da ta ‘ya’yanmu.
Siyasa ta zama
kasuwanci, kuma masu zaɓe suna da muhimmiyar rawar da za su iya takawa a wannan
karon wajen kawar da wannan al’amari. Sau tari wasu su kan ce wai idan ɗan
takara ya bayar da kuɗi a zaɓe shi, to a karɓa amma a zaɓi cancanta. Sai dai
kuma, ya kamata mu tuna cewar, duk wanda ya ci ladan kuturu, to dole ya yi masa
aski. Maganin kada a yi, to kada a fara! Goyon bayan mutum da ra’ayinsa, ya
wuce a sayesu da kuɗi miliyoyi, ballantana ‘yan dubunnai ko ɗaruruwan nairori
da ‘yan siyasa suke rabawa ranar zaɓe. Ba ya daga cikin ƙimar mutum, ya karɓi
kuɗi a kan zai yi abu, kuma ya ƙi yi, kodayake ma wannan kuɗin marabar su kaɗan
ce da cin hanci ko rashawa. Me zai sa kuwa ka karɓi cin hanci? Mu guji sayar da
‘yancinmu, domin abin da za a baka ka sayar da ‘yancin, ba zai ishe ka cefanen
kwana huɗu ba kuma a cuce ka na tsawon shekaru huɗu.
Duk da ya ke mu ɗan
makara a yanzu, amma lokaci ya yi da jama’a za su dinga ɗaukar nauyin yaƙin
neman zaɓen ‘yan takara da kuɗaɗensu, domin ya kasance su ne da iko da shi ko
da bayan ya ci zaɓe, ba wai ya zuba kuɗi ya ci zaɓe ya zo ya na ganin shi ne da
kansa ba. Tsarin da Janar Buhari ya ke amfani da shi na neman tallafin ɗari da
kwabo daga wajen talakawa masu zaɓe, abu ne mai kyau kuma haka ya kamata
kowanne ɗan takara ya yi. Idan kuma bai yi haka ba, to dole ya bayyana wa jama’a
waɗanne kuɗaɗe ya ke amfani da su kuma a ina ya same su?
Abu na ƙarshe,
lokaci ya wuce, da za mu zaɓi mutane, mu ƙyale su sakaka su na yin abin da suka ga
dama, sai sun zo sun fi ƙarfinmu kuma mu koma gefe muna jiran shekara huɗu ta
cika mu samu damar canja su. Akwai
tanadin doka a cikin Kundin Tsarin Mulki da ya bai wa masu zaɓe dama su yi wa ɗan
majalisa kiranye idan ba su gamsu da wakilcinsa ba. Idan shugaban ƙasa ko
gwamnoni suka nemi su zarce gona da iri, ya zama wajibi mu matsawa ‘yan majalisu
lamba su tsigesu daga kan mulki, idan kuma sun ƙi, to mu yi mu su kiranye, mu
tura waɗansu. Rashin yin amfani da damar da Kundin Tsarin Mulki ya bai wa
talakawa, ita ta sa masu mulki suke cin karensu ba babbaka bisa tunanin babu
abin da za a yi musu.
Su kansu shugabanni
nagarin, ba haka kawai za mu ƙyale su ba, wajibi ne mu saka mu su ido, mu
tabbatar sun ɗore a kan aiyuka masu kyau kuma kada mu bari su ɗauka wai alfarma
ko taimako suke yi mana, a’a dama abin da muka ɗaukesu aiki su yi mana kenan.
Maganar bambaɗanci, fadanci ko ɗaga kai ba ta taso ba. Shugaba shi ne bawan
talakawa, amma talakawa ba bayinsa ba ne.
© Malam Amir Abdulazeez 2015.
No comments:
Post a Comment