Fassara

Sunday, August 9, 2015

Nazari Akan Alƙiblar Siyasar Dawakin-Tofa Idan Kwankwaso Ya Koma APC

19th November, 2013



Daga: Amir Abdulazeez

S
iyasa mai abin mamaki da kuma abin dariya. A siyasa ne, sai ka gama kushe mutum ciki da bayansa saboda bambancin ra’ayi sai kuma ku wayi gari a jam’iyya ɗaya kuma akan manufa ɗaya tare kuma da neman makoma iri ɗaya. Wani lokacin kuma sai ka gama yin Allah wadai da wata jam’iyya, sai ka samu kanka tsamo-tsamo a cikinta.
Idan banda haka, da Janaral Muhammadu Buhari ba za su zauna jam’iyya ɗaya da Cif Bisi Akande, shugaban riƙo na APC na ƙasa ba domin kuwa lokacin da Buhari ya yi juyin mulki, Bisi Akande shine Mataimakin Gwamna Bola Ige na Jihar Oyo kuma Buhari ya yanke musu ɗaurin shekaru barkatai a kurkuku dukkansu su biyun, amma yanzu gasu nan ba mai jin kansu. Yau ga Mallam Nuhu Ribadu a teburi ɗaya da mafi yawan mutanen da ya kira ɓarayi kuma maciya amana lakoacin da yake shugaban hukumar EFCC. Gashi yau babu amintattu masu gaskiya a gunsa kamarsu saboda jam’iyyarsu ɗaya..

A nan Kano ga Mallam Ibrahim Shekarau ya sake haɗewa da tsofaffin mataimakansa, Injiniya Magaji Abdullahi da kuma Injiniya Abdullahi Tijjani Gwarzo waɗanda suka rabu baran-baran, kuma mai yiwuwa nan da wasu ‘yan kwananki zai haɗe da babban kishiyarsa wato Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a cikin tafiya guda.

Dukkan alamu tun daga sama har ƙasa sun nuna cewa, Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso yana kan hanyarsa ta shigowa jam’iyyar APC. Koda yake ba za mu iya tantacewar ko za su shigo ne gabaɗaya tare da sauran ‘yan uwansa gwamnoni waɗanka aka fi sani da ‘yan 7 ko G-7, ko kuma shi kaɗai zai shigo ba. Amma babu shakka shigowarsa APC a yanzu zai canja al’amuran siyasa a Jihar Kano, wataƙila ma har da Najeriya baki ɗaya.

A nan Dawakin-Tofa, wani babban jigo a jam’iyyar PDP wanda bai bamu izinin bayyana sunansa ba ya tabbatar mana da cewa jam’iyyar tana kiran taro a kowacce mazaɓa don jin ra’ayin ‘ya’yanta, kuma kawo yanzu dukkan mazaɓun da suka ziyarta sun jaddada goyon bayansu ga Maigirma Gwamna kuma umarninsa kawai suke jira. Duk da cewa bai bayyana mana mazaɓun da aka gudanar da wannan taro ba, amma Muryar Dawakin-Tofa ta halarci taron da aka gudanar a mazaɓun Dawanau da Ƙwa, kuma tana sane da lokacin da aka gudanar da taron a mazaɓar Tumfafi, bugu da ƙari kuma ta san lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da wannan taro a mazaɓun Dawakin-Tofa ta Gabas da Dawakin-Tofa ta Yamma.

To, ko ma dai da irin wannan taruka ko babu, dukkan mai bibiya ko nazari akan al’amuran siyasar PDP Kwankwasiyya, ya san cewa tafiya ce da aka gina ta akan umarni da kuma biyayya, wannan ce ma ta sa mutane da yawa za su yi mamakin yin taron jin ra’ayin jama’a saɓanin yadda aka saba a baya na a yanke hukunci sannan a turo umarni daga sama zuwa ƙasa. Wannan ya nuna jan ƙafa da kuma ɗar-ɗar ɗin da shi kansa Gwamna Kwankwaso yake yi kafin shigarsa APC ɗin.
Duk da cewa akwai tsirarun ‘yan Kwankwasiyya anan Jihar Kano da ake sa ran ba lallai su bi Kwankwaso zuwa APC ba, to amma da wahala a samu irinsu a nan Dawakin-Tofa. Koda yake a ‘yan kwanakinnan raɗe-raɗe sun cika gari cewa Mataimakin Gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba zai bi Kwankwaso izuwa wata sabuwar jam’iyya ba, amma kuma makusantansa sun fito sun ƙaryata wannan jita-jitar ta hanyar sanarwa a kafafen yaɗa labarai cewa Ganduje yana tare da Kwankwaso ɗari bisa ɗari komai ruwa komai iska.

Shi kansa Sakataren Yaɗa Labaran Ofishin Mataimakin Gwamnan, Bala Salihu Dawakin-Kudu da muka tuntuɓe shi, ya yi watsi da jita-jitar a matsayin aikin ‘yan adawa.To tunda ‘yan PDP Kwankwasiyya na Dawakin-Tofa, babu wanda suka sani banda Ganduje, to da wahala wani ya bijire.
Wani bincike da muka gudanar, ya nuna cewa, wasu daga cikin ‘yan Kwankwasiyya a Dawakin-Tofa za su bi Kwankwaso izuwa APC ne saboda basu da wani zaɓi amma ba don suna so ba saboda sun riga sun ɓata da kowa, kuma sun yi watsi da duk wani ɗan siyasa sun riƙe Kwankwaso da Ganduje. Don haka basu da kowa sai su, to kuma yanzu an kawo gaɓar da ba za su iya sauya iyayen gida ba. Wasu kuma za su bi ne saboda suna morar gwamnatin kuma ba za su so su rabu da mulkin ba.

Wani babban jigo a PDP wanda sha’anin komawarsa APC yake da ‘yar sarƙaƙiya da kuma rikitarwa shine Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Honarabul Saleh Ahmed Marke domin shi akwai tanadin doka a cikin tsarin mulkin Najeriya wacce ta tanadi cewa duk wani ɗan majalisa ba zai iya sauya jam’iyya ba sai ya yi asarar kujerarsa, koda yake zai iya fakewa da cewa ai jam’iyyar tasa ta rabe gida biyu. Amma idan aka yi la’akari da ƙarfin nufi da kuma zafin kishi irin na ɓangaren tsohuwar PDP ƙarkashin Alhaji Bamanga Tukur wacce ta yi barazanar tabbatar da cewa dukkan wani ɗan majalisa ɗan sabuwar PDP da ya bar PDP, to ya rasa kujerarsa. Kuma dolene a ɗauki wannan barazana da matuƙar muhimmanci, duba da cewa shugaban ƙasa a ɓangarensu yake banda kuma kotuna da lauyoyi da suke dasu.

Idan muka kalli jiga-jigan da suke cikin PDP da waɗanda suke cikin APC a Dawakin-Tofa, sai mu tambayi kanmu: wai shin idan suka cakuɗe waje guda, siyasar ma zata yiwu kuwa? Gashi dama dukkan manyan Dawakin-Tofa basa wuce wannan jam’iyyun guda biyu tun daga 1999. Ko shakka babu girma da muhimmancin wasu dole ya ragu saboda tsananin gasa da takara da za’a samu. Wata tambayar ita ce: shin za’a samu sauran wata jam’iyyar adawa kuwa? Babu mamaki ƙanana da sababbin jam’iyyu irinsu PDM da LABOUR PARTY su yi amfani da wannan dama su kawo kansu Dawakin-Tofa kuma mai yiwuwa su samu tarin magoya baya. Bayan haka, kada a manta da cewa akwai ‘yan tsohuwar PDP a Dawakin-Tofa waɗanda ba ‘yan Kwankwasiyya ba kuma suna nan za su yi zamansu daram a PDP tare da samun isasshiyar iskar shaƙa da sararin watayawa. Banda haka, za su samu dukkan goyon baya da gudunmawar da suke buƙata tun daga Abuja har zuwa kan Hassan Kafayos banda kuma Biloniya Muhammad Abacha wanda a shirye yake ya taimakesu. Duk da cewa ba’a san wanda zai jagoranci waɗannan mutane ba, to amma akwai Dakta Mahmood Baffa Yola, Babban Kwamishina a Jihar Kano na Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a ta Tarayya. To amma wani hanzari ba gudu ba shine, kowa ya san kusancin Dakta Mahmood da Sanata Bello Hayatu Gwarzo wanda ana ganin duk inda za su a siyasance, tare za su je. Shi Maigirma Sanata, a farkon wannan rigima, an rawaito shi a cikin sanatoci 22 na sabuwar PDP amma kuma yanzu alamu sun nuna ya yi baya-baya duk da cewa yana da kyakkyawar alaƙa da Kwankwaso tun ba yau ba. Don haka ba za’a iya sanin inda Dakta Mahmood ya nufa ba sai an tantance makomar Sanata. To amma wani abin dubawa anan shine, idan har ‘yan tsohuwar PDP suka samu Dakta Mahmood Baffa Yola a matsayin jagora, to akwai yiwuwar su yi babban tasiri kasancewar mutane da yawa na yi masa kallon dattijon arziki wanda yake iya riƙe mutane.

Yanzu haka kuma guna-guni ya yawaita a cikin ‘yan APC ɗin da basa maraba da shigowar Gwamna Kwankwaso da Ganduje cewar, a ranar da suka shigo APC, su kuma kashegari za su sauya sheƙa zuwa PDP. Ko wannan barazana tasu gaske ce ko kuma kuri ce? Lokaci shi zai yi alƙalanci. Rahotanni sun nuna cewa su ‘yan tsohuwar PDP waɗanda aka yiwa laƙabi da ‘yan Garkuwa har sun fara shirye-shiryen kafa shugabancin riƙo na jam’iyyar a nan Dawakin-Tofa, wasu ma sun tabbatar da cewa an kafa wannan shugabanci ta ƙarƙashin kasa.

Ita kanta sabuwar amaryar wato APC, masana suna ganinta da tarin matsaloli iri-iri anan Dawakin-Tofa. A bayyane yake a fili cewa ‘yan tsohuwar ANPP sun riga sun kankane jam’iyyar tun kafin a je ko’ina kuma a shirye suke da su kafa shugabancinta ko da kuwa babu haɗin kan CPC da ACN. Abinda kawai zai hanasu cimma burinsu shine Injiniya Magaji Abdullahi wanda shine turken CPC. To amma idan aka yi la’akari da cewa kusan dukkan mutanen CPC da ANPP ɗin duk mabiyansa ne na da da na yanzu, ba lallai ne ya damu da waɗanda za su zama shugabanni ba. Ita kanta tsohuwar CPC ɗin ta Dawakin-Tofa, wani tsagi nata ana kyautata zaton ya bi Sanata Rufa’i Sani Hanga zuwa Jam’iyyar PDM. Rigimar da ta fatattaka ANPP zuwa CPC da ACN babu tabbacin ta warware, me yiwuwa ta ciki na ciki. To amma idan aka yi la’akari da aiki ba dare ba rana da wata ƙungiya mai rajin tabbatar da adalci da dimokraɗiyya a APC take yi, sai mu iya cewa za’a samu gyara. Wannan ƙungiya ta haɗa jiga-jigan tsofaffin ANPP, CPC da ACN ɗin. To amma matsalar shine, har yanzu da alamun cewa jiga-jigan tsohuwar ANPP basu yi amanna da wannan ƙungiya ba.

Wannan shine halin da APC take a yanzu, to yaya kuma a ce PDP Kwankwasiyya ta antayo cikinta?
Wani mutum da zai iya yin gagurumin tasiri a wannan rintsi shine, Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Dawakin-Tofa, Tofa da Rimin-Gado, Honarabul Tijjani Abdulkadir Joɓe domin kuwa ko ba komai a shekaru shida da ya shafe akan mulki, ya kafa sansani mai ƙarfi nasa na kansa anan Dawakin-Tofa wanda tunɓuke shi ko hanashi tasiri zai yi wahala. Kuma a matsayinsa na wanda yake riƙe da mulki, ko da ‘yan Kwankwasiyya sun shigo ba dolene su yi masa wani mummunan rauni ba musamman idan bai nuna zai yaƙesu ba. 

A yanzu bata fito fili akan wanene yake jagorantar jam’iyyar APC a Dawakin-Tofa ba tsakanin Injiniya Magaji Abdullahi da Dakta Maikano Rabi’u ba, balle kuma a ce ga Dakta Ganduje ya shigo. Gefe ɗaya kuma akwai jiga-jigai irinsu Mallam Alhassan Dawaki, Honarabul Saleh Shehu Kwuidawa da sauransu waɗanda har yanzu ba’a ji ƙwaƙƙwaran motsinsu ba. Ko kuma dan ba’a buga gangar siyasar ba ne?

A ƙarshe dole mu bar wa lokaci damarsa domin shi ne zai warware mana dukkan wannan ƙulle-ƙulle amma babu shakka za mu sha kallo nan ba da daɗewa ba domin kuwa koda Kwankwaso bai shigo APC ba to akwai yiwuwar ya bar PDP.


© Malam Amir Abdulazeez 2013.

No comments:

Post a Comment