24th
October, 2013
Daga: Amir
Abdulazeez
D
|
alilai biyu
ne suka kawo dalilin yin
rubutu a kan
wannan batu duk da cewa akwai dubunnan
mutane da suka sha yin sharhi da rubuce-rubuce a kan cin hanci
da rashawa a Najeriya.
Dalili na farko, a shekarar 2009 na kai wa wani aminina ziyara, mu na zaune
mu na tattaunawa sai wani matashi wanda nake tsammanin su na da wata alaƙa da
shi ya zo inda mu ke. Daga ganin alamarsa a buge ya ke ko kuma ya na yawan
buguwa da kayan maye. Wannan matashi sai ya tambayi amininnan nawa N500 a kan zai yi kuɗin mota zuwa ƙauyensu
saboda ya karɓo takardar shaidar zama ɗan asalin ƙaramar hukumarsu domin ana
dab da ɗaukarsa aikin ɗan sanda, kuma lallai ne za’a buƙaci wannan takarda.
Wannan aminin nawa sai ya ɗauko N 500
ya ba shi,
sai ya tafi. Bayan ya tafi sai ya juyo ya kalleni, yace: ‘abokina, Najeriya ba
za ta taɓa gyaruwa ba’. Na tambayeshi, me ya sa? Sai yace: ‘ka duba wai wannan
bugaggen, mara tarbiyyar za’a ɗauka aiki mai muhimmanci irin na ɗan sanda wanda
kuma in da rai da rabo, watarana shi ka ke sa ran zai zama shugaban ‘yan sandan
Najeriya. Na girgiza kai, ban sake cewa komai ba amma na kai tsawon shekaru huɗu
ina jinjina wannan magana ta sa.
Amma kafin
in kawo dalilina na biyu, ga wasu tambayoyi. Shin me zai sa Dagatai da Masu Unguwanninmu
su dinga sanya wa mutane hannu a kan takardar shaidar zama ɗan asalin yankinsu
ba tare da sun tantance amfanin da mutum zai yi da takardar ba? Me zai sa ba za
su yi ƙoƙarin hana lalatattun mutane irin waɗannan shiga irin wannan aiki ba ta
hanyar bada mummunar shaida a kansu? Ko kuwa ba su da wani zaɓi, tunda mutanen
kirki duk sun guji aikin sai mutanen banza ne da kuma waɗanda suka rasa aikin
yi su ke shiga aikin? To ko shi ya sa rundunar sojoji, ‘yan sanda da sauran
masu ɗamara ta Najeriya ta cika da masu karɓar cin hanci da rashawa?
Dalilina na
biyu na yin wannan rubutu shi ne; an taɓa gayyata ta wani taro da wata ƙungiya
mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Jihar Kano ta shirya a shekarar
2011 a Babban Ɗakin Karatun Jihar Kano na Murtala Muhammad. Taken wannan taro
shi ne: ‘Gudunmawar da zan Bayar a
Matsayina na ɗan Ƙasa Wajen Kawar da Cin Hanci da Rashin Gaskiya a Najeriya’.
Wannan taro ya samu halartar ƙwararru da dama, ciki har da wakilan hukumar yaƙi
da cin hanci ta ICPC. Duk da cewa taken wannan taro ya bayyana mana ƙarara cewa
ana so ne kowa ya faɗi me ya ke ganin ‘yan Najeriya za su yi a matsayinsu na waɗanda
ake mulka domin kawar da cin hanci da cin amana a ƙasarnan, amma abin haushi, mahalarta
wannan taro, waɗanda kuma aka kira da ƙwararru, duk wanda ya miƙe maimakon ya
yi magana a kan abin da aka tsara sai ya ɓige da zagin Shugaban Ƙasa, ‘yan
majalisu, ministoci, ‘yan siyasa da sauran ma su mulki. Ni kaɗai na fita zakka,
yayin da aka bani damar magana sai na tunatar da mahalarta taron cewa ya kamata
mu daina barin jaki muna dukan taiki, kamata ya yi mu kalli namu matsalolin
kafin mu kalli na shugabanninmu. Kafin kace kwabo, sai aka yi min caa a ka, wai
ai babu laifin mabiya, ai shugabanni ne ɓarayi don haka dole a faɗa, kai a taƙaice
ma ni ban san me na ke yi ba. Ganin cewa babu wanda ya goyi bayana, sai na
sulale cikin kunya na fita daga wannan taro kuma ban ƙara waiwayar wannan magana
ba sai yanzu.
Abin tambaya
a nan shine, wai me ya sa sau dubu sai mu take laifin mu amma muna da idon
hango na shugabanninmu? Wai me ya sa, sai mutum ya tafka ta’asar da ya ga dama,
idan an yi magana wai sai yace ai haka Najeriya ta ke, kowa ba shi da gaskiya
don haka ma in ka yi gaskiya kana ɓatawa kanka lokaci ne kawai? Wai me ya sa
dukkan abin alkhairin da ƙasarmu ta yi, ba ma faɗa amma komai ƙanƙantar sharri
ko da ba mu yi bincike mun tabbatar da shi ba sai mu yi ta yayata shi? Shin wai
lalacewar Najeriya ta kai yadda mu ke kururutawa kuwa? Wai muna kallon wasu ƙasashen
na ƙasa da mu ko kuwa muna la’akari ne kawai da na sama da mu?
Tunda munji waɗannan
dalilai, bari na dawo kan tambayata ta asali, shin wanene zai kawar da cin
hanci da rashawa a Najeriya? Wannan tambaya tana da wahalar amsawa kai tsaye
kuma tana da amsoshi da yawa domin kowa a Najeriya idan ka tambayeshi, ya na da
amsar da zai bayar a kan ta. Amma kafin na bayar da tawa amsar ina so mu sani
cewa, kowa da kowa ya na da gudunmawar da zai bayar wajen gyaruwar Najeriya ko
lalacewar ta komai girmansa kuma komai ƙanƙantarsa.
Babu wani
shugaba a duniya komai nagartarsa da zai iya zuwa ya ci nasarar kawo wani gyara
ko canji a rayuwar mutane ba tare da su mutanen sun ba shi haɗin kai ba. Wannan
shi ya tuna min da wani furuci na tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo inda
ya ke cewa: “Dole ne idan za ka yi maganar
kyakkyawan shugabanci, to ka yi maganar ingantattun mabiya.” Bayan wannan,
za mu iya ɗaukar darasi daga gurin Joseph Stalin na tsohuwar rugujajjiyar Tarayyar
Soviet wacce ita ce ƙasar Russia a yanzu wanda ya mulki tarayyar na tsawon
kusan shekaru 25. Rahotanni daga masana tarihi sun nuna cewar ya yi sanadiyyar
mutuwar tsakanin mutane miliyan 5 zuwa 10 a ƙudurinsa na kawo wasu sauye-sauye
a ƙasar, amma duk da haka bai cimma nasara cikakkiya ba domin ya na mutuwa
sauye-sauyen na sa suka ruguje domin mutane ba sa tare da su.
A nan, ko
kusa ba ni da niyyar in tsame shugabannin Najeriya daga laifukan da ake
zarginsu da shi domin na yarda cewa suna da laifuka masu yawan gaske, amma ya
kamata mu sani cewa waɗannan shugabannin ba aljanu ko mala’iku ba ne, ko kuma
ba sauko mana su aka yi daga sama ba, daga cikinmu suke fitowa. Don haka ashe
mu ɗin ne a lalace kenan? Wani abin lura da shi a nan shi ne, mun sha juya wa
shugabanninnan baya a zaɓe ta hanyar musanyasu da wasu kuma ƙarshe su ma waɗanda
mu ka sauya ɗin su ba mu kunya. To tunda shugabanninan daga cikinmu su ke
fitowa, wajibi ne sai mun gyara kanmu.
Bugu da ƙari,
duk irin satar kuɗin jama’a da shugabanninmu suke yi, mu talakawa mu muka ba su
dama. A yanzu da mutum zai riƙe muƙamin Gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma kuma
ya sauka ba shi da naira miliyan 100 misali ko kuma ya sauka ya cigaba da
rayuwar da ya saba da ita kafin ya hau muƙamin, sai ka ji ana zaginsa ana cewa
ba shi da ƙashin arziki. Ko muna tsammanin masu riƙe da muƙaman ba su san
wannan ba? Mu tuna fa cewa, idan zaɓe ya zo, masu mulki ne da masu neman mulki
suke zagayawa suna raba mana cin hanci don mu zaɓe su. Wasu daga cikinmu ma har
yawo suke yi da ganye a kai, wai su na sayarwa ne.
Wai meye cin
hanci ne? Cin hanci shi ne duk wani abu da za’a ba ka na kuɗi ko na amfani
wanda zai sa ka ka yi abin da ba shi ya kamata a yi ba a wannan muhallin. Mu ɗinnan
ne fa muke taruwa a gidaje da ofisoshin masu mulki muna tilasta mu su su bamu
kuɗi duk da cewa mun san cewa albashinsu bai kai su bamu abinda muke nema a gurinsu
ba. To tsammaninmu a waɗanne kuɗaɗen su ke ɗebowa suna bamu? A cikin
wannan al’aumma tamu ne, ba’a ganin mutunci ko darajar mutum a kan iliminsa,
gaskiyarsa ko iya mu’amalarsa, sai dai a kan kuɗinsa kuma ba tare da an yi duba
da hanyar da ya bi ya samu waɗannan kuɗin ba.
Mu tuna fa
mutum ne zai saci kuɗin mutane, amma sai ka ga ya fito ana kwanciya ana gaishe da
shi. A wannan ƙasar ne kotu ta ke ɗaure mutum a kurkuku saboda ya saci kuɗin
jama’a. Amma ranar da ya fito, sai a yi amfani da talakawa su yi gangamin taron
tarbarsa da kuma girmamashi. To a
nan wanene ya
ke ɗaure
wa cin hanci gindi, mu ne ko kuwa shugabanninmu? Don haka ko
shakka babu, amsa ta ita ce, mu talakawa mu muke da kaso mafi tsoka wajen hana
cin hanci da rashawa a Najeriya duk da cewa su ma shugabannin akwai rawar da za
su taka ba ƙarama ba.
Duk mai
tunanin gyara a Najeriya, ya fara kallon kansa tsaf, ya ga shi a gyare ya ke? Mutum
ya gyara kansa, ya yi gaskiya a kan kansa, sannan sai ya yi ƙoƙarin gyara
gidansa. Idan ya gama da gidansa, sai ya fara tunanin gyaran unguwarsu, sannan
ƙaramar hukumarsu, sannan jiharsa, kafin ya fara tunanin gyaran Najeriya gabaɗaya.
Cin hanci da
rashawa da sata ba za su taɓa rabuwa da mu ba, sai mun yi gaskiya a kasuwancinmu,
aikinmu, iyalinmu, ƙungiyoyinmu, abotarmu, masarautunmu da dukkan al’amuranmu.
Bayan mun yi wannan, sai mu kalli shugabanninmu ido da ido, mu ci kwalar rigarsu,
ƙila ma har da lakace mu su hanci sannan mu ce mu su: me ya sa ba ku da gaskiya?
© Malam Amir Abdulazeez 2013.
No comments:
Post a Comment