Fassara

Sunday, August 9, 2015

Jam'iyyar PDP: Ashe Wanzami Ba Ya Son Jarfa?

20 ga Disamba, 2013


Daga: Amir Abdulazeez

A
 ‘yan shekarun baya kaɗan, a fagen siyasar Najeriya, duk inda ka samu labarin cewa wani babban ɗan siyasa ko mai mulki ya canja jam’iyya, to ya sauya sheƙa ne daga jam’iyyarsa ta adawa zuwa jam’iyya mai mulki ta PDP. Yanzu kuma ga shi Allah cikin ikonSa, an samu wani juyin juya halin da duk lokacin da ka samu labarin wani babban ɗan siyasa ko mai mulki ya canja jam’iyya, to ya sauya sheƙa ne daga jam’iyyar PDP mai mulki zuwa wata jam’iyyar daban ta adawa.

A halin yanzu, babu wata jam’iyyar da take ƙirga riba ta hanyar samun ƙarin masu madafun iko a gwamnati suna shigowa cikinta, kamar babbar jam’iyyar adawa ta APC. A gefe ɗaya kuma, babu jam’iyyar da ta ke ƙirga asara ta hanyar samun masu madafun iko a gwamnati suna ficewa daga cikinta kamar babbar jam’iyya mai mulki ta PDP. Babu shakka, wannan wani al’amari ne da zai dagulawa jam’iyyar PDP lissafi, jam’iyyar da kafin yanzu ta ke kiran kan ta a matsayin jam’iyya mafi girma da ƙarfi a Nahiyar Africa baki ɗaya. Duk da cewa wannan al’amari babban naƙasu ne a gurin PDP, sai dai kuma hakan zai zamo babban cigaba ga dimokraɗiyyar Najeriya. Domin kuwa shekaru 14 da PDP ta shafe a matsayin mai gagrumin rinjaye a kowanne fanni na siyasar Najeriya, ba abu ne da zai haifarwa da siyasar Najeriyar ɗa mai ido ba.

A Ranar Laraba ne, 18 ga watan Disamba, 2013, ‘yan Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya guda 37 suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC. Wannan ita ta bai wa jam’iyyar APC wani ƙaramin rinjaye a majalisar da yawan wakilai 174, yayin da PDP ta ke da wakilai 171. Ragowar wakilan guda 15 kuma sun fito ne daga jam’yyun APGA, LP (Labour Party), DPP da AP (Accord Party). Kafin hakan kuma, wasu ‘yan satattaki da suka gabata, gwamnonin PDP guda biyar suka koma APC wanda hakan ya kawo yawan gwamnonin APC zuwa 16 yayin da PDP ta ke da 18, inda kuma LP da APGA suke da guda ɗai ɗai. Bayan haka, akwai rahotanni masu ƙarfi da ke nuna cewa sanatoci guda 20 ko 22 na PDP ɗin na kan hanyar ficewa zuwa APC.

Wannan lissafi ya tayarwa da PDP hankali har ta garzaya kotu da buƙata ga kuliya manta sabo akan ta kori gwamnonin biyar da kuma ‘yan majalisu 37 daga kujerunsu. Bayan haka kuma jita-jita ta yawaita cewa ita PDP ɗin tana kitsa yadda za ta tunzura ‘yan majalisun dokokin jihohin Kano, Rivers, Kwara, Sokoto da Adamawa domin su tsige gwamnonin nasu da suka sauya sheƙa. Duk wannan alamu ne na damuwa da ruɗewa a ɓangaren na PDP. Ashe dama wanzami ba ya son jarfa?
Lokacin da wasu gwamnoni, ‘yan majalisun tarayya da na jihohi da sanatoci suka dinga ‘cin amanar’ jam’iyyunsu suna komawa PDP, ai rungumarsu PDP ɗin ta yi hannu bibiyu kuma ta basu kariya. Idan da abin da suka yi ba dai-dai ba ne, ai da sai ta ƙi karɓarsu, tace: ‘ku koma jam’iyyunku domin hakan cin amana ne kuma karya dokar ƙasa ne’.

Talakawan Najeriya ba za su taɓa mantawa da cin amanar da gwamnan Bauchi, Mallam Isa Yuguda ya yi wa tsohuwar jam’iyyar ANPP ba, inda bayan jama’a sun sadaukar da rayukansu sun tabbatar da shi akan mulki a zaɓen 2007 amma ya sa ƙafa ya fice zuwa PDP. Haka zalika, tsohon gwamnan Zamfara, Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi, a matsayinsa na Mataimakin Gwamna na farko a Najeriya tun daga 1999 zuwa yau da gwamnansa ya taɓa ba shi damar ya gaje shi a ƙarƙashin tsohuwar ANPP, amma bayan mulkin ya tabbata a hannunsa, ya sa takalmansa ya fice zuwa PDP. Ragowar sun haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Adamu Aliero wanda ya koma PDP daga ANPP a 2007, tsohon Gwamnan Jigawa Saminu Turaki, ya koma PDP daga ANPP a 2007. Akwai kuma tsohon Gwamnan Jihar Imo, Ikedi Ohakim wanda ya koma PDP daga jam’iyyar PPA a shekarar 2008 da kuma Gwamnan Jihar Abia na yanzu Theodore Orji wanda shi ma ya bar jam’iyyar PPA zuwa PDP jim kaɗan bayan ya ci zaɓe. Duk waɗannan ba su yi laifin komai ba a gurin PDP, domin kuwa har shiryawa kowannensu gagrumin taron bikin maraba ta yi lokacin shigowarsa. Bayan wannan, ba ɓoyayyen abu ba ne cewar PDP tana zawarcin muhimman mutane daga jam’iyyun adawa, a wani lokaci ma barazana ta ke musu ta hanyar haɗasu da Hukumar EFCC akan dole sai sun dawo PDP musamman idan ta ga maguɗinta ya kasa yin awon gaba da su. Mutane nawa Obasanjo ya kira lokacin mulkinsa ya faɗa musu su dawo PDP ko ransu ya ɓaci? Kuma wasu da suka ƙi komawa, ransu bai ɓacin ba?

Daga shekarar 1999 zuwa 2013, ƙiyasin yawan ‘yan majalisun dokoki na jihohi, ‘yan majalisun tarayya da sanatocin da suka bar jam’yyunsu zuwa PDP sun haura 200. Duk wannan ba laifi ba ne? A taƙaice dai, na fahimci cewa, idan ka bar jam’iyyar ka zuwa PDP, to ba ka karya kowacce irin doka ba kuma kujerarka na nan daram. Idan kuma ka bar PDP zuwa wata jam’iyya, to ka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasa laifi kuma za ka yi asarar kujerarka. Abin takaici, a ƙasar nan , ba’a waiwayar Kundin Tsarin Mulkin Najeriya sai za’a zalunci wani ko kuma ana son kassara wasu.
A shirme da ruɗewa irin na PDP, ta manta cewa kundin tsarin mulki bai hana gwamnan jiha sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya ba. Sannan kundin ya bai wa ‘yan majalisa damar sauya sheƙa matuƙar akwai rikici ko tsagi ko rarrabuwa a cikin jam’iyyunsu. Sun manta lokacin da ‘yan majalisu suka dinga shiga PDP ba tare da ɗaya daga cikin waɗancan dalilai ba kuma babu wanda yace mu su uffan.
Akan al’amuran siyasar da suke faruwa a yanzu, ni ina da shawarwari guda uku ga PDP, APC da kuma ‘yan Najeriya.

Na farko, PDP ta rungumi ƙaddara, ta tuna cewa komai lokaci ne kuma kafin kowa ya fara karya dokar kundin tsarin mulki, ita ta fara, don haka kada ta zargi kowa akan haka. Bayan haka ta sani cewar tana da damar da za ta ɗinke ɓarakarta tun da wuri amma ta ƙi har ta tunzura waɗannan mutane suka fice daga cikinta. PDP ta sani cewa duk da mutanen da suka fice daga cikinta, har yanzu ita ce kan gaba a Najeriya ko dan albarkacin Gwamnatin Tarayya da take riƙe a hannunta, don haka maimakon wannan hargowa da borin kunya da ta ke faman yi, ta tsaya ta ɗinke ɓarakarta gudun kada wasu su cigaba da ficewa daga cikinta. Bayan haka, ta koma gudanar da al’amuranta tsakanin ta da Allah kuma cikin adalci, ta tuba ta yi nadama akan laifukanta kuma su ƙaddara cewa abin da yake samunsu tamkar azaba ce Allah Yake musu akan laifukan da suka aikata a baya. Idan suka yi haka, ba mamaki jama’a su yafe musu kafin 2015.

Shawara ta biyu ita ce ga jam’iyyar APC,  lallai ta ɗauki darussa daga abin da yake samun PDP a yanzu domin kaucewa samun kanta a cikinsu. Bayan haka APC ta daina rawar jiki da masu shigowa cikinta, ta bi a hankali domin mafi yawancinsu buƙatar kansu ce a gabansu ba wai cigaban jam’iyyar ko Najeriya ba. Idan suka yi sakaci da wannan, to kada su zargi kowa sai kansu akan sakamakon da zai iya biyo baya. Bayan haka, su guji fifita masu mulki da kuɗi waɗanda suka shigo cikinta yanzu yanzu akan ‘ya’yanta waɗanda aka kafa jam’iyyar da su tun asali, domin hakan shi ma wani cin amanar ne a karan kansa. Idan har ba za ta iya daidaita su su zama ɗaya ba, to kada ta fifita wani da gangan, gara kowa iya siyasarsa da yawan magoya bayansa ta ba shi fifikon idan tafiya ta yi tafiya. Idan kuwa ba za ta iya haka ba, to ba ta da maraba da PDP ɗin da ta ke yaƙa. Sannan APC ta yi a hankali da mutanen da suka ci amanar ta a baya, irinsu Adamu Aliero (ANPP da CPC), Saminu Turaki (ANPP), Atiku Abubakar (ACN) da dai sauransu. In son samu ne ma, kada su ƙara danƙa musu wata amana.

Shawara ta ƙarshe kuma mafi muhimmanci ita ce ga ‘yan uwana talakawa ‘yan Najeriya. Kada mu kuskura mu ce za mu zaɓi jam’iyya, mu zaɓi kowanne ɗan takara bisa dacewarsa da cancantarsa. Domin mutane da yawa za su fake da jam’iyyu su cucemu. Bayan haka, mu sani fa kowanne gauta ja ne, kusan dukkan ‘yan siyasa halin su ɗaya. Akan haka, ina bada shawarar, kada mu guji mutum don yana PDP, mai yiwuwa shi nagari ne, jam’iyyar ce ba tagari ba. Kada mu so mutum don yana APC, mai yiwuwa jam’iyyar ce tagari amma shi mugu ne. idan kunne ya ji, to jiki ya tsira!!!

© Malam Amir Abdulazeez 2013.

No comments:

Post a Comment