6 Ga Afrilu, 2015
Daga: Amir Abdulazeez
Idan dai ba wani ƙadaru na Ubangiji
ba, Ranar Asabar mai zuwa, ɗaya daga cikin mutum biyu ne za a zaɓa a matsayin
magajin Gwamnankwankwaso; wato Dakta Abdullahi Umar Ganduje ko Malam Salihu
Sagir Takai.
To, amma kafin Ranar Asabar ɗin
ta yi ‘yan Jihar Kano su yanke hukunci, ga wani hasashe a kan amfani da rashin
amfanin zaɓar kowannensu;
Amfanin Zaɓar Ganduje
1. Idan aka zaɓi
Ganduje a matsayin gwamnan Kano, to an zaɓi jam’iyyar APC sak tun daga tarayya
har jiha. Mai yiwuwa wannan za ta bai wa Jihar Kano wata gagarumar damar
amfanar aiyuka da alfarmomi masu yawa daga Gwamnatin Tarayya.
2. Gwamnati
kamar wata mota
ce kullum akan titi,
take tafiya izuwa wani waje, idan an samu canjin direba, ana so ace ta ci gaba
da tafiya akan wata kyakkyawar turba guda ɗaya har a cimma manufar ci gaban
al’ummar da aka sa a gaba. Babu shakka Ganduje zai ci gaba da aiyukan
Kwankwaso, wataƙila tamakar ma ba a samu wani canjin direba ba ma.
3. Ganduje dattijo ne wanda
dukkan alamu na haƙuri da juriya suka bayyana a tattare da shi. A ko’ina an san
dattijo da haɗa kan jama’a cikin hikima, dabara da nagarta, ina kuma ga idan an
ba shi
shugabancin su?
4. Ganduje ƙwararre ne kuma gogaggen ma’aikaci
mai tarin ƙwarewa ta kusan shekaru 40 a kan ilimi, aikin gwamnati, siyasa,
shugabanci da zamantakewa. In dai ƙwarewa dai-dai ta ke da aiki, to babu
shakka, Ganduje zai kasance wanda ya fi kowa aiki a matasyin gwamna a Najeriya.
Matsalolin Zaɓar Ganduje
1. Idan aka zaɓi
Ganduje, zai kasance jam’iyyar APC ta cinye komai aKano, babu sauran wata
jam’iyyar adawa. Yanzu haka APC ita ta ke da Shugaban ƙasa, Sanatoci 3, ‘Yan
majalisun tarayya 24 duka, Ciyamomi 44 da kansiloli 484 duka. Illa ce babba a
ce babu adawa ko kaɗan; za a wayi gari jam’iyya mai mulki ta na yin abin da ta
ga dama ba ta shayin komai kuma ba ta tsoron kowa.
2. Duk da nasarorin gwamnatin
Kwankwaso, akwai wasu manyan kura-kurai da ta yi waɗanda bisa ga alama Ganduje
zai iya ɗorawa a kansu. Babba daga cikinsu shi ne tauye ƙananan hukumomi, hanasu
kuɗaɗensu da kuma mayar da su hoto.
3. Ganduje ya shafe kusan
shekaru 20 (tun DPN 1996) ya na neman gwamna bai samu ba. A tsawon wannan
lokaci, ya sadaukar da lokacinsa, ƙarfinsa, dukiyarsa, tunaninsa da sauran
abubuwansa da yawa akan wannan buƙata. Babu tabbacin cewar idan ya samu nasara
ba zai fi myar da hankali wajen ƙoƙarin mayar da gurbin abubuwan da ya rasa ba
a tsawon wannan lokaci.
4. Bisa ga alamu,
tsananin haƙuri da kawaicin Ganduje sun haifar masa da rauni, wanda zai iya yin illa ga irin salon shugabancinsa. Bayan haka, shekaru
kusan 16 da ya shafe a ƙarƙashin Kwankwaso sun bayyana shi a matsayin tamkar
wani mutum wanda ba shi da cikakken ra’ayin kansa ko ba zai iya tsayawa da ƙafafunsa
ba.
Amfanin Zaɓar Takai
1. Idan aka zaɓi
Takai, to an samar da canji a sama, canji a ƙasa. Hakan zai bayar da damar cewa
kowanne ɓangare za su amfani mulki ba tare da ya tattare a waje ɗaya ba, balle
har a samu shantakewa ko kama-karya.
2. Kano, yanzu a tamke ta ke tamau
kuma ta na buƙatar a ɗan sassauta kaɗan. Gwamnatin
Kwankwaso ta fi mayar da hankali akan gine-gine da manyan aiyuka. Takai, kamar
yadda ya ke faɗa, ya na da burin ya karkatar da akalar manufar gwamnati domin ta
fi mayar da hankali akan gina jama’a, sauƙaƙa musu da kuma taimaka musu,
taimakawa ma’aikata, taimakawa marasa ƙarfi, kula da noma da kiwon lafiya da
sauransu.
3. Ga dukkan
alamu, Takai a matsayin gwamna zai sakarwa ƙananan hukumomi mara su yi fitsari. Yanzu ƙananan
hukumomi a mace suke murus, akwai buƙatar a farfaɗo da su in dai ana so ci gaba
ya kai can ƙasa wajen jama’a da sauran marasa galihu.
4. Alamun
nutusuwa, yakana da kirki sun bayyana a tattare da Takai. Bayan haka an shaideshi
kan gaskiya da riƙon amana- duk waɗannan abubuwa jari ne a harkar
shugabanci. Bayan haka, kasancewarsa mai matsakaicin shekaru wanda ya ke da sauran siyasa a gaba, zai so
ya yi abubuwan da zai kafa tarihi mai kyau.
Matsalolin Zaɓar Takai
1. Akwai alamun cewar
iyayen gidan jam’iyyar PDP na Kano ba za su bar Takai ya sarara a mulkin Kano
ba. Kasancewar sun rasa Gwamnatin Tarayya, duk za su iya dawowa Kano su tare
akan ta da buƙatu iri-iri.
2. Akwai masu
tsoron cewar Takai ba zai iya aikin gwamna yadda ya kamata ba, kasancewar
gogewarsada ƙwarewarsa basu kai yadda ake so ba, musamman idan aka yi la’akari
da cewar Kano ba ƙaramar jiha ba
ce kamar Yobe,
Zamfara, Ekiti
ko Ebonyi
ba.
3. Kwankwaso ya ɗora Kano akan
wata miƙaƙƙiyar hanya, akwai tsoron cewar Takai zai iya karkacewa izuwa wata
hanyar daban ko ya mayar da hannun agogo baya.
4. A siyasar
wannan zamani, mun ga tasirin ɗaukar nagartaccen mataimaki. Saɓanin irin Mataimakin
Ganduje, Mataimakin Takai ba shi da wata nagarta sosai. Abin Allah Ya kiyaye,
idan wani tsautsayi ya samu gwamna, da yawa ba za su gamsu da Abba Risqua a
mulkin Kano ba.
© Malam Amir Abdulazeez 2014.
No comments:
Post a Comment