Fassara

Sunday, August 9, 2015

Bayan da Aka Ƙarar da Musulman Afrika ta Tsakiya

12 Ga Maris, 2014



Daga: Amir Abdulazeez

“Idan har ba mu kawar da yaƙi daga wannan duniyar ba, to ba shakka watarana shi yaƙin zai kawar damu daga duniyar.”
- Harry S. Truman (1884-1972)

T
a faru ta ƙare wai an yi wa mai dami ɗaya sata. Rahotanni daban-daban daga manya-manyan masu sanya idanu a kan harkokin ƙasa da ƙasa sun tabbatar da cewa yanzu dai kusan an ƙarar da baki ɗayan Musulman ƙasar Afrika ta Tsakiya. Wasu kuma rahotannin na cewa basu ƙare ba tukunna saura ‘yan ƙalilan. To ko menene ribar kawar da ɗan uwanka ɗan Adam wanda ba kai ka halicce shi ba kuma Mahaliccinku ya riga ya ƙaddara muku zama tare a matsayin ‘yan ƙasa ɗaya daga doron duniya?

To! Ko an ƙarar da Musulman Afrika ta Tsakiya ko ba a ƙarar da su ba dai, babban abin da za mu iya tabbatarwa shi ne an tafka babbar asara da kuma taɓargaza ga jinsin Bil Adama gadaɗaya wacce ta ke abar nadama duk da cewa wannan ba wani baƙon abu ba ne a nahiyar mu ta Afrika. A wani ƙiyasi da gidan talabijin na Al-jazeera ya yi a kwanakin baya, sun gano cewa yawan musulman da ke zaune a Bangui, babban birnin ƙasar Afrika ta Tsakiya ya ragu daga yawan mutane 100,000 zuwa mutane 900 kacal. Su ma waɗannan mutane 900 babu tabbacin za su kai nan da wani lokaci ba a kashe su ba ko kuma ba su gudu ba domin kullum cikin farautarsu a ke yi.

Kafin wannan rikici dai, ita ƙasar Afrika ta Tsakiya wacce ta ke rainon ƙasar Faransa ce, ta na da Musulmai kusan  kashi goma sha biyar cikin ɗari wanda yawansu ya kai kusan mutane 750,000 kuma mafi yawancinsu suna zaune  a arewacin ƙasar. Daga cikin wannan adadi, akwai wani kaso mai tsoka na Musulmai baƙin haure daga wasu ƙasashen Afrika, ciki har da Najeriya. Wannan rikici mai kama da na ƙare dangi ya sanya ƙasashe da dama irinsu Chadi, Niger, Najeriya da sauransu kwashe  dukkan ‘yan ƙasashensu yayin kuma da wani kaso mai tsoka na waɗannan Musulmai baƙin haure suka gudu suka bar ƙasar. Har yanzu babu sahihin yawan alƙaluman mutanen da aka kashe a wannan rikici amma jaridun Najeriya sun rawaito cewa akwai ƙiyasin kusan ‘yan Najeriya guda 100 da suka rasa rayukansu, banda ɗaruruwa da suka gudu bayan an lalata musu dukiyoyinsu kuma suka sha da ƙyar.
Ita dai wannan rigima ta samo asali daga lokacin da ‘yan tawayen Seleka a ƙarƙashin shugabansu Michel Djotodia suka karɓe mulki a hannun tserarren shugaban ƙasar Froncois Bozize. Michel Djotodia ya zama shugaban ƙasar Musulmi na farko kuma mafi yawancin mayaƙansa na Seleka duk musulmai ne. Bayan faruwar hakan, ko giyar nasara ce da mulki ta ɗebi ‘yan Seleka? Ko kuma huce daɗaɗɗen takaicin daɗewa a ƙarƙashin mulkin Kiristoci ne? Ko kuma dai kawai kama karya ce da shashanci irin ta wasu ‘yan Afrika? Oho! Sai suka shiga yin fyaɗe da ƙwace dukiyoyi tare da kashe kiristocin wannan ƙasa. Shugaba Michel Djotodia ya yi ƙoƙarin hanasu wannan ta’asa amma suka ƙi hanuwa. Daga baya kiristoci suka fara mayar da martani a ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Anti-Balaka inda suka fara yaƙa tare da kashe ‘yan tawayen Suleka. Daga baya kuma a garin yin hakan har sai suka zarce gona da iri inda suka dinga yin kan mai uwa da wabi a tsakanin Musulmai ko da kuwa basu da wata alaƙa da ‘yan tawayen Suleka. Abin sai da ya kai har yanka naman mutum suke yi, su ci shi ɗanye. Bayan haka Anti-Balaka basu tsaya ga kashe musulmai ba, a’a har da waɗanda suka kira kiristoci munafukai masu bai wa musulmai kariya. A wasu lokutan ma sun sha kashe  kiristoci bisa zaton cewa wai muslmai ne.

Abin takaici kuma abin tambaya a nan, wai shin yaushe mu ‘yan Afrika za mu yi wa kanmu faɗa? Allah SWT Ya yi mana gata, ya yi mu mutane masu ƙwaƙwalwa da zuciya amma aiyyukan wasu daga cikinmu irin na dabbobi. Dabbobin ma na daji, daƙiƙai marasa kan gado.
Mu tuna fa har yanzu ba a cika shekaru 20 ba da yin kisan ƙare dangi a ƙasar Rwanda inda mutane sama da 800,000 suka rasa rayukansu a cikin ‘yan satattaki.  A wannan rikici, ‘yan ƙabilar Hutu sun kashe ‘yan ƙabilar Tutsi da kuma ‘yan uwansu ‘yan Hutu masu sassaucin ra’ayi waɗanda ba sa goyon bayan kashe-kashen.

Mu tuna cewa fa sama da mutane miliyan guda aka kashe a yaƙin basasa a Najeriya a cikin watanni 34 kacal. Mu tuna rikicin Sudan wanda aka kwashe sama da shekaru 25 ana yi tsakanin Musulman arewaci da Kiristocin kudancin ƙasar wanda ya yi sanadiyyar raba ƙasar gida biyu bayan an yi asarar rayuka da dama. Masana tarihi sun bayyana wannan rikici na ƙasar Sudan a matasayin yaƙin basasa mafi daɗewa a duniya. Yanzu haka tsugunne ba ta ƙare ba, domin kuwa rikicin ƙabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar dubunnan mutane tare da raunata mutane da yawa bayan wasu da dama da suka ƙaurace wa gidajensu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira a sabuwar ƙasar Sudan ta Kudu. Rikicin addini da ta’addanci a ƙasar Somalia wanda ya haura shekaru 20 ana yinsa har yanzu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Mu tuna rikicin bayan zaɓen shugaban ƙasa a Cot’devoire a shekarar 2010 wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da raunata mutane da dama. Ko mun manta da yawan mutanen da aka kashe a rikicin ‘yan tawaye a ƙasashen Liberia, Zaire, Sierra Leone da Chad? Mutane da dama sun halaka a Najeriya, Congo, Ethiopia, Eritrea da Mali saboda rikice-rikicen adddini, ƙabilanci da tawaye. Ana ci gaba da kashe mutane a kullum a ƙasar Masar da Libya saboda rikice-rikice na siyasa.

Kullum Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta da wani aiki banda turo da sojojin wanzar da zaman lafiya a ƙasashen Afrika. Kullum babu abin tattaunawa a taron Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta AU banda batun rikice-rikice da kashe-kashe marasa manufa. Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da gwamnatoci a nahiyoyin Turai da Amurka koda yaushe suna kan hanyar aiko da sojoji ko kayan agaji zuwa ga ma’abota rikici a ƙasashen Afrika. Yanzu haka ƙasashe ɗai-ɗai ne a Nahiyar Afrika inda babu sansanonin ‘yan gudun hijira.

Daga lokacin da aka kafa Kotun Manyan Laifukan Yaƙi ta Duniya mai suna ICC a shekarar 2002, kaso mafi tsoka na waɗanda ta chafke duk ‘yan Afrika ne kuma duk waɗanda ta yanke wa hukunci kawo yanzu duk ‘yan Afrika ne. To wai ko mu ne cibiyar rikicin addini da ƙabilanci ta duniya ne?
Yayin da duniya ta ke maganar kasuwanci, kimiyya da fasaha, ƙere-ƙere da masana’antu, mu a nan Afrika kullum rikice-rikice ne da zubar da jinin juna a gabanmu. Yaushe rayuwa za ta ci gaba a haka? Idan har Nahiyar Afrika ba ta yi wa kanta faɗa kuma ‘ya’yanta basu daina yi wa juna asarar dukiyoyi da rayuka ba, to mu da ci gaba sai dai mu ji ana yi.


© Malam Amir Abdulazeez 2014.

No comments:

Post a Comment