Daga: Hamza Ibrahim Baba
Ƙ
|
aramar Hukumar Dawakin-Tofa na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi mafi daɗewa
a Jihar Kano, kai har da ma Najeriya gabaɗaya domin kuwa tana daga cikin farkon
ƙirƙirowa tun sanda aka fito da tsarin ƙananan hukumomi a ƙasarnan a shekarar
1976.
Allah (SWT) Ya albarkanci Dawakin-Tofa da ƙasar noma mai tarin yawa da kuma
ƙwari domin kuwa girman ƙasar Dawakin-Tofa ya kai murabba’in kilomita ninki 479
ko kuma 479km2. Bayan haka tana maƙotaka da manya-manyan matattarar
ruwa da aka fi sani da dam da ake ji
da su a Kano kamar su Watari, Thomas da
Bagwai. Wannan ƙaramar hukuma tana da arzikin ƙasar laka wacce ake iya
yin gini da ita kuma ake iya yin tukwane da sauran dangogin ta da ita banda
kuma tarin ma’adinai a ƙarƙashin ƙasa waɗanda rashin maida hankali irin na
gwamnatocin tarayya bai bari an ganosu ba.
Idan ka bar ɓangaren albarkatun ƙasa, ka koma siyasa da gwamnati,
Dawakin-Tofa uwa ce ga Mataimakan Gwamnonin Jihar Kano guda uku wanda har a
halin yanzu ma ɗan Dawaki ne ya ke riƙe da wannan kujera, kai a taƙaice ma tun
da aka dawo dimokraɗiyya a shekarar 1999, mutum ɗaya ne (Abdullahi T. Gwarzo)
wanda ba ɗan Dawaki ba da ya riƙe wannan kujera. Mutanen da suka riƙe wannan
kujera sun haɗa da Alhaji Abdu Dawakin-Tofa a lokacin Abubakar Rimi, Injiniya
Magaji Abdullahi a lokacin Mallam Shekarau da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje
a lokutan Mulkin Kwankwaso na farko da na yanzu. Bayan haka sau biyu ana ɗaukar
Saleh Shehu Kwuidawa a matsayin ɗan
takarar Mataimakin Gwamna amma Allah bai sa an kai ga nasara ba. Bayan wannan,
Abdu Dawakin-Tofa ya taɓa riƙe muƙamin Gwamna na wucin-gadi lokacin da Abubakar
Rimi ya yi murabus, kun ga a taƙaice, mun taɓa samun Gwamna kenan. Sannan kuma
akwai tsofaffin kwamishinoni da masu ci yanzu da muka taɓa samu tun ma lokacin
mulkin soja. Wasu daga cikinsu sun haɗa da Injiniya Magaji Abdullahi, Dakta
Abdullahi Umar Ganduje, Alhassan Muhammad Dawaki da kuma Soveya Muhammad Yahaya
Nadu. Kai a taƙaice, da wahala wata gwamnati ta zo ta ƙare ba tare da ɗan
Dawaki ya samu kwamishina ba.
Dawakin-tofa ita take da kasuwar abinci mafi girma a Nahiyar Afrika, wato
Kasuwar Dawanau kuma ita ta ke da kasuwar ƙarafuna da manyan motoci mafi girma
a Arewacin Najeriya, wato Kasuwar Kwakwaci.
Duk da wannan ɗunbin tarihi da nasarori da Dawakin-Tofa ta samu, ta na daga
cikin koma bayan ƙananan hukumomi wajen ci gaban rayuwa musamman idan aka
kwatanta ta da takwarorin ta kamar Bichi, Gwarzo, Danbatta da dai sauransu.
Duba da irin wannan tarin arziki wanda ba ya amfanar mu da komai, kowa zai
yarda da ni idan na ce, a wannan lokacin, Dawakin-Tofa ta na buƙatar
jajirtaccen mutum mai ilimi wanda zai jagorance ta. To amma abin baƙin ciki, a ƙaramar
hukuma ta,
ilimi haram ne. Idan har kana so a zaɓe ka a wani matsayi, to ka tabbata kun yi
hannun riga da ilimi domin kuwa masu ido da kwalli ba za su amince da kai ba. Yanzu
a dalilin siyasa, wasu manyan mutane marasa kishi kuma waɗanda suka ci moriyar
wannan tarihi suna neman lalata ƙaramar hukumar ta hanyar rashin adalci da kuma
yaƙar ilimin da su da kansu suka ci moriyarsa.
Lokacin da jam’iyyar APC ta
fitar da kira ga masu sha’awar takara su nuna buƙatarsu, mutane da yawa sun
nuna farin cikinsu domin suna ganin cewa wannan dama ce da Dawakin-Tofa za ta
gyara kura-kuranta musamman a yanzu da ake ƙarƙashin tafiyar Kwankwasiyya wacce
ta ke ɗabbaka adalci, gaskiya da riƙon amana. Wannan ya biyo bayan tsananin buƙatar
da Dawakin-Tofa ta ke da shi ga samun shugaba wanda ya san gudanarwar mulki
kuma ya san yadda a ke sarrafa arziki wajen inganta ilimi, lafiya, kasuwanci,
noma da kuma tallafa wa mata da matasa.
An kirawo ‘yan takara, ciki har
da ni gidan Maigirma Mataimakain Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin yin
sulhu. Bayan ‘yan takara, akwai manyan mutane irinsu tsohon Mataimakin Gwamna
Injiniya Magaji Abdullahi, tsohon zababben Sanatan Kano ta arewa Dakta Maikano
Rabiu, tsohon mashawarci ga kwamitin samar da wutar lantarki na Gwamnatin
Tarayya kuma sabon mai bayar da shawara ga gwamnan Kano akan aiyyukan raya
ƙasa, Injiniya Muazu Magaji, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dawakin tofa
Alhaji Saleh Kuidawa, tsohon kwamishinan sufuri da noma Alhaji Alasan Dawaki, Babban
Sakataren Hukumar Bayar da Agaji ta Jihar Kano Alhaji Ali bashir da dukkan
jiga-jigai da dattawan tsofaffin jam’iyyun ANPP, CPC, ACN da kuma Kwankwasiyya.
Wanda aka naɗa ya shugabanci taron kuma ya kula da sulhun shi ne Kwamishinan Ƙasa
da Safayo, Soveya Muhammad Yahaya Nadu.
Bayan kowanne ɗan takara ya
gabatar da kansa da kuma matakin karatunsa da irin gwagwarmayar da ya yi a
rayuwa sai aka umaremu da mu keɓe domin yin sulhu a tsakaninmu. Bayan
tattaunawa mai yawa sai mu ka yi ƙuri’a
a tsakaninmu inda mutane 11 a cikin 14 suka zaɓi Hamisu Danguguwa kuma
nan take muka nuna gamsuwarmu da amincewarmu da hakan. Mun zaɓi Hamisu ba wai
dan ya na da digiri har guda biyu ba, a’a sai dan kasancewarsa mutum mai
gaskiya, riƙon amana, nutsuwa da kuma kyakkyawan tarihi.
Da muka zo muka bayyana wa
dattijai matsayar da muka cimma, manya irinsu Magaji Abdullahi da Injiniya
Mu’azu sai suka nuna gamsuwarsu tare da yaba mana akan wannan zaɓi namu. Amma maimakon
kwamishina Nadu ya bi sahunsu, nan take sai ya nuna rashin amincewarsa inda ya
umarci da a shiga zaɓe. Nan take muka ƙaurace wa wannan zaɓe amma duk da haka
sai suka shirya wannan haramtaccen zaɓe kuma suka fitar da Saleh Rabi’u
Dandalama a matsayin ɗan takara, ba don komai ba, sai don cewa suna ganin za su
iya juya shi kamar waina. Wannan ba ƙaramin abin takaici ba ne. Maigirma Kwamishina
Nadu Yahaya mutum ne wanda ya zama Soveya Janar na ƙasar Najeriya baki daya
kuma ya fi kowa sanin muhimmancin ilimi a Najeriya. Bayan haka shi ne ya ƙi
yarda ya yi aiki da mai taimaka masa na musamman wato S.A Hashimu Sulaiman
Dungurawa saboda bai yi karatun boko mai zurfi ba, yace lallai sai ya yi
karatun digiri a Geography ko a fannin zane-zane, amma sai ga shi yanzu ya na
gudun waɗanda suka yi ilimi mai zurfi. Bayan haka duk wannan abu da aka yi da
sanin Maigirma Mataimakin Gwamna Dakta Abdullahi Ganduje wanda ya ke digirinsa
uku kuma ƙwararre ne a dukkan fannoni na rayuwa a ciki da wajen Najeriya.
Wani abin ban takaici mai kama
da almara shi ne, bayan sun zaɓi Sale Rabi’u, sai guri ya kaure da ihu ana tafi
ana kiran ‘sai jahili’ ‘sai jahili’, ‘Dawaki sai jahili’. Wannan abin takaici
da me ya yi kama? To fa irin siyasar da ake yi kenan a Dawakin-Tofa, wasu
sassan Jihar Kano kai har da ma Arewacin Najeriya baki daya.
Wannan ƙarfa-ƙarfa ba ta tsaya nan ba, idan ka na takarar kansila, dole sai
an sa ka ka janye ta ƙarfin tsiya ko ba ka so, ta hanyar ba ka tsoro da yi maka
barazana. Idan kuma ka ƙi sai a shirya wani haramtaccen zaɓe a kayar da kai. Shin
kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ba ‘yar tinƙe yace a yi ba ne idan sulhu bai
yiwu ba?
Tun farko da an san wannan tsarin za a yi, da ba sai an wahalar da mutane
ta hanyar yaudararsu cewa su fito takara dimokraɗiyya da adalci za a yi ba.
Ashe duk maganar adalci, haɗin kai, dimokradiyya, ci gaba da kyautatawa da ake
yi ya zama shirme kenan?
Yanzu dai a ƙaramar hukumar
Dawakin-Tofa, yin ilimi musamman na boko ya zama laifi sannan kuma yin adalci
musamman a siyasa ya zama haram. Maimakon iliminka ya zamar maka jari idan ka na
neman wani muƙami, a’a sai dai ya zamar maka naƙasu. Iyayenmu da yayyenmu waɗanda
suka amfanu da ilimi a kyauta a lokacin da suke ɗalibai kuma suka ci moriyarsa,
yanzu ga shi mu sun hanamu cin moriyarsa. Kuma su ne suka kwaɗaita mana ilimin
tun da farko, mun yi ilimin kuma yanzu sun ce mu abin ƙyama ne. Yanzu
an rarraba kawunan jama’a, an nuna musu cewar mai ilimi illa ne kuma abin gudu
ne. Shin da me Gwarzo, Danbatta da Bichi ta tsere mana in ba da ilimin ba?
Yanzu an nuna wa yaranmu cewa ai idan suka yi sakandire kawai ta ishesu su riƙe
kowanne irin muƙami don haka ba sai sun yi ilimi mai zurfi ba kuma masu assasa
wannan su kuma suna tura ‘ya’yansu da ‘yan uwansu manyan makarantu. Yanzu
fisabilillahi, a matsayin Saleh Shehu Kuidawa na mai ilimi, za mu ce bai kawo
canji a mulkinsa ba? Za mu ce iliminsa bai yi amfani wajen taimakon Dawakin-Tofa
ba?
Wannan abu da yake faruwa, ba
wai mu ‘yan yanzu ake yi wa illa ba, a’a ƙannenmu da ‘ya’yanmu masu tasowa su
ake yi wa illa. Don haka dukkan mai ƙaunar ci gaban Dawakin-Tofa, Jihar Kano da
Arewacin Najeriya, dole sai ya tashi tsaye domin yaƙar wannan cuta domin kuwa
in dai muka ƙyale ta, to za ta ruguza mana rayuwarmu ta nan gaba mai zuwa.
Hamza I. Baba ya na cikin ‘yan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa a jam’iyyar APC kuma ya rubuto ne daga Abuja.
No comments:
Post a Comment